Tana gama faɗa Kawu na ya yanke jiki ya faɗi a waje ko shurawa baiyi ba..
Cikin mutuƙar razani da mahaukaci firgici Anty tayi kan shi tana kururuwa da ihu, haɗi da sumbatu marar ma'ana...
" Na shiga uku na lalace, shikenan zai tafi ya fari da wahala, wayoo Allah Abban Hanna kayi wa Allah da mazan tsira ka tashi!! in ka tafi ka barni wazai taffeni, ya zanyi da ɗawainiyar yara biyar, dan Allah ka tashi innalillahi!!.." ta faɗa cikin hargowa da matsananin firgici...
Sai da na share