Skip to content
Part 16 of 32 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Tana gama faɗa Kawu na ya yanke jiki ya faɗi a waje ko shurawa baiyi ba..

Cikin mutuƙar razani da mahaukaci firgici Anty tayi kan shi tana kururuwa da ihu, haɗi da sumbatu marar ma’ana…

” Na shiga uku na lalace, shikenan zai tafi ya fari da wahala, wayoo Allah Abban Hanna kayi wa Allah da mazan tsira ka tashi!!  in ka tafi ka barni wazai taffeni,  ya zanyi da ɗawainiyar yara biyar, dan Allah ka tashi innalillahi!!..”  ta faɗa cikin hargowa da matsananin firgici…

Sai da na share ƙwallar tausayi

To maƙociyar ta dake shirin shigo ɗiban ruwa, itace ta kƙaraso da sauri jin irin furicin da ANTY take yi, da taimako Suwaiba suka zubawa Kawu na ruwa ya farfaɗo amma har yanzu bai sake kallon inda Anty na take ba, kuma bai motsa ba, tun daga ranar Kawu ya sake sauya mata har ya ci uban na dah, ko abinci tayi baya ci baya mata magana, ɗakin da nake nan ya koma ƙwana ya turo mata yaran ta, gashi kullum sai ya fita nema na, yayi baki ya rame ya dawo abun tausayi ko abinci kirki yanzu bai cika ci ba, kullum cikin tunani na yake, wani lokaci yana zaune shi kaɗai sai ya fashe da kuka, baya samun ishe-shan barci domin ƙwana yake sallah…

To da sauki ma tunda baban su Aysha ya kan zaunar dashi yayi ta bashi baki da nuna mai illar abunda yake, wani lokaci yayi magana wani lokaci kuma ya saka mai kuka, shi kaɗai ya san halin da yake ciki a yanzu…

A zaune ta same shi yau ma, idanun nan nata sunyi jawar da su cikin mutuƙar biyayya da tsumamiyar ladama cikin rauni murya da karayar zuci  tace” kayi haƙuri! dan Allah? ka yafe min dan girman ma’aiki? kaji tausayi na da girman zatti?, ka tallafi rayuwa ta da take cikin ƙunci a yanzu ka dube ni da idanun ka masu sanyi, na san kai me haƙuri ne da tausayi, na amsa laifi na na kuma yarda da hukuncin ka a gareni, na horo iya horo wa na jigatu inun, kai wa Allah kayi haƙuri miji na!??..”  ta ida maganar da wata irin kuka me shiga jika, tana sha-shaƙer kuka…

BISHIRA da tun farkon abun ta shigo ta saki kuka cikin yanayi bacin ciki, domin ta jima tana ganin mahaifiyar ta tana koka wa, haka ma mahaifin ta, gashi ta rasa inda Munni dinta tafi.

Jikin ta na kaɗuwa tazo ta sunkuya gwiwoyin ta a kasa haɗi da haɗe hannun ta waje guda, hawaye na tsire a kuncin ta tace” Abban mu ka yafewa Umman mu dan girman Allah, sannan ka nemo min Munni na dan Allah, naji a waje ana cewa ka kore ta me tayi maka Abba! Muni fa bata laifi! kullum sai tayi mana wanka kullum sai ta mana abinci, Muni tana son mu Abba dan Allah ka dawo mana da ita! sannan kai ma ka daina fushi da kowa ka dawo kana dariya irin na dah bana son wanna fushi!!..” ta faɗa cikin matsanancin kuka…

A hankali Kawu ya musk’uta cikin jarimta ya kamo hannun ta yana mata murmushi ƙarfin hali yace” ki dai na kuka yar gidan Abba, Muni zata dawo ƙwana nan duk wanda yace ni na kore ta karya yake, ina san ta ya za’ayi na kore ta? maman ki ce ta kore ta bani ba, kiyi addu’a Allah ya baiyyana mana ita kinji..” yayi maganar cikin rarashi…

BISHIRA ta dube Anty cike da jin haushi tace” dama kullum sai kince mata me kama da aljanu, shine yanzu kika kore ta to Abban mu zai dawo mata da ita ko Abba?…” ta faɗa tana dawo da duban ta gare sa…

*****

Tunda Mommy ta nuna ɓacin rain ta akan Big man, bai sake zuwa shashin Anty ba sai dai sunyi waya…

To kamar yanda muka faro tun farko yau sweet din Mommy zai dawo kasar sa ta gado, shiya sa ake ta shirye-shirye abinda ya kawo ta kenan shashin Dadda zata gaya mata…

Ɗakin sa ta aika nan ma aka sake gyara shi tsaf dashi, babu abinda yake sai tashin ƙamshi, cikin jin dadi ta dawo falo ta hakimce tana jiran shigowar sa…

Duk irin yanda suka lalaɓa ni naki haƙura ni lallai sai an kaini wajen Kawu ne, duk wani abu da suka san ina so sai da aka ɗauko min amma fafur naki amsa ni kawu kawai..

Cikin gajiyawa Daddah tace” kina ji na! bari naje na dubo ko me ya riƙe shi da har yanzu bai shigo ba…”

Cikin biyayya Nusaiba tace” Hajiya ai da kin hutu ni bari naje..”

Murmushi tayi na jin dadi kana tace” a’a ke zaki zauna dan banzan iya da wannan rigimamiyar ba..” tana rufe bakin ta ta mike…

Bayan fitar Daddah Anty ta cigaba da rarashi na cikin dabara, da kulawa luff nai a jikin ta ba tare dana motsa ba, gani kamar nayi barci ne yasa ta mike da zuwa bayi…

Mommy jin jirin mota ya tabbatar mata Big man ya ɗauko mata farin cikin ta, cike da murna ta sake gyara zaman ta, a hankali na tashi cikin turo baki gani babu kowa a inda nake yasa na mike duk hanyar da na gani binta nake, a haka har na kawo falon sai kalle-kalle nake sam Mommy bata kula dani ba, domin hankalin ta da nutsuwar ta yana wajen yaran ta, na jima sosai a wajen ina kalle-kalle abu na, tamkar ance min na ɗago shigowar sa kenan, ya sha ƙanana kaya hasken nan ya sake fitowa, cike da kaisaita yake taka kasa yana wani basar wa..

Mommy ta mike tsaye cikin jin dadi da kulawa ta bude mai hannu alamar yazo gare ta, shima ya sakar mata wani murmushi me cike da ƙauna, cikin jin dadi ya ware hannuwan sa yana  kara ƙami wajen tafiya sa, wani irin murmushi na sake na jin dadi, na ƙwasa da wani mugun gudu nayi wajen sa a sulo na wani rungume shi, cikin mutuƙar farin ciki….

A fili nace” oyoyo Kawu na!!!…

AN’NUWAR yayi mutuwar tsaye cike tsananin bakin ciki da alajab’i, take an’nuri fuskar sa ya ɗauke, Mommy ta zare ido zuciyar ta na bugawa da ƙarfi, Dadda da Anty sun biyo baya na kenan suka ga abinda na aikata ko wace ta dafi gashi cike da damuwa, Haidar ya doso kai kenan ya hango ni ƙwance a kirjin AN’NUWAR, fuskata yalwace da murmushi, zuciyar sa ta buga da ƙarfi..

Na ɗago kai na ina dariya cike da shirme nace” nace baka ɗaga ni ba yau?..” yanda nayi maganar ne ya birge shi, kawai sai ya nemi fushi ya rasa, na sake turo baki a karo na farko ina wasa da gashin idanuna da sukayi gazar-gazar, nace” an daina kula ka in!!..” nayi maganar cike da shagwaɓa…

Babu wanda ya lura da xuwan ta sai gani akayi ta wancakalar dani gefe guda, cikin mutuƙar ɓacin rai ta ɗaga hannu ta sama kana ta zaffga min wani ingantacen mari wanda ya kaɗawa kowa ciki, ban gama watsikewa ba ta sake daura min wani a ɗaya kuncin, haidar ya taho da wani mugun gudu gani ba ta daniyar danewa, Daddah ta gigice gani mommy na shirin kurman tar dani, Hajiya Nusaiba ta fashe da kuka cike da tausayi na, Mommy ta sake ɗaga hannun ta da shirin ƙara min na uku sai ji tayi an damƙe mata hannu kam- Kam…

Da wani irin fushi Mommy ta waigo. fuskar sa yalwace da murmushi yace” sorry Mommy yarinya ce, wannan hukuncin yayi mata tsauri…”

A hankali tayi kasa da hannun ta, ranta nayi mata ƙuna..

Daddah ta shafa min fuska ta cike da tausayi na, kana ta kalle mommy dake nishi tayi wani guntin murmushi me ciwo tace” kin kyau ta! kinyi abinda ranki ke so! amma karki manta akwai ranar nadama! wannan da kike rainawa insha Allah wata rana sai kin nemi taimakon ta! yaron ki ya hauka ta musu yarinya daga ƙarshe kin ɗaure mai gindi har da tura shi wata kasa, sabida yau ya dawo tana mai kallo Jan zaki! Shine kika zage ƙarfin ki akan ta kika wanka mata mari? ina jiye miki wallahi! sakare kawai marar wayo da tunani! Allah ya dawo dashi lafiya dole ne ma naji shi ya ɗaure miki gindi wannan rashin hankali Koko? zai dawo ya same ni ne, tunda ni kin nuna min ba a bakin komai nake ba, ko banci ɗaya darajar matsayi na ba ai naci na ƙarshe, tunda ni na haifa mijin da kike tunƙaho dashi, wallahi zaki sha mamaki ne Ameenatu!…”  da ƙarfi Daddah take magana, kana duban fuskar ta ka san tana cikin bacin rai me tsanani, a fusace tace” muje ciki Nusaiba!!..”

Luf nayi a jikin Anty ina kuka kasa-kasa a hankali tsoron matar yake ratsa ni, wallahi har cikin raina bana ƙaunar na sake haɗa hanƴa da ita ko na ga fuskar ta…

AN’NUWAR ya dubi Mommy cikin yanayi ba dadi yace” why!! Mommy? ai da kin barni da ita, gashi yanzu kin ɓatawa Daddah rai!..” yanayi maganar sa cikin gajiya wa…

Mommy da jikin ta ya sanyi, jin irin kalaman Hajiya domin basu taɓa haka da ita ba sai yau, take tsanar yarinyar ya sake ratsa ta, tayi sauri basar wa haɗi da cewa” manta da su Son! yanzu ka shiga ciki ka watsa ruwa ka kwanta ka huta zuwa anjima ka fito mu gaisa.. “

Ba haka ranshi yaso ba, amma ya iya dole ya amsa da to…

Tunda muka koma ciki nake kuka, su Daddah sai aikin rarashi na suke, gani naƙi yin shiru yasa Daddah sake komawa shashin Mommy fuskar nan ta ta a murtike, zaune ta same shi ya dafe kai kamar marar lafiya, tace” Aliyu! zo ka rarashi yarinyar nan!!..”

Cikin sauri Mommy ta ɗago tana duban ta, kirjin ta na halbawa, hango tsagwaron rashin mutunci a idanun Hajiya yasa tayi saurin kasa da idanun ta,  shiko kamar jira yake ya mike da sauri ya shige ciki, duk da irin harara da Mommy take aika mai…

Daddah ta fara tafiya Mommy tace” kinyi haƙuri Hajiya! nakasa jurewa ne! dan Allah karki gaya mai…”

Ko kallon ta Daddah ba tayi ba ta wuce ciki abun ta…

Cikin sigar rarashi yace” yan matan Kawu waye ya taɓa mini ke!..?”  ina jin murya sa nayi saurin faɗawa jikin sa ina sake sakin kuka, cikin dabara ya tureni daga jikin sa, tausayi na na kara mamaye mai zuciya yace” kiyi shiru kin ji! ba ruwan mu da Mommy!..” ya ƙarke maganar da share min hawaye…

Na turo baki na gaba murya a shake nace” kuma sai na faɗawa Anty na!..”

“Eh ki faɗa mata, yanzu kiyi shiru muje na kai ki yawo, ai zaki je ko..” duk da ban san me yake nufi da yawo ba amma haka nan naji ina son bisa…

 ” ina zaka je zagi?..” cewar Mommy dake zaune tana cin tufah..

Ya sunƙuyar da kai kasa zuciyar sa na halbawa, tsoran sa ɗaya kar ta hana shi fita…

” Inda kika aike shi? Cewar Dadda dake riƙe da aƙwati…”  Cikin Mommy ya ƙulle cike da tsoro take duban Dadda bakin ta na rawa tace” Hajiya!…”

” Wuce kuje Allah ya tsare hanya sai kun dawo, ka kula da ita sosai kaji yaro na..” ta faɗa cikin soyayya..

A dan tsorace ya amsa..

Mommy tace” Daddah ina zaki da jaka wai!??..” cikin damuwa take maganar..

” Menene damuwar ki da inda zani? tunda kin nuna ina takura miki a gidan mijinki, zan koma inda na fito, wanda nake zama domin sa in ya dawo ya biyo ni can, domin shine nake dolen sa…” ta faɗa tana tafiya zata fita,

Da wani mugun sauri Mommy ta damƙe aƙwatin, jikin ta har rawa yake cikin firgici tace” tunda nake na taɓa cewa bana san zama dake Hajiya? kiyiwa Allah kiyi haƙuri wallahi bana komai dan na muzguna miki…”  cikin mutuƙar biyayya da sadaukar wa take maganar…

Daddah tace” ki sakar min jaka na malama tunda bake kika siya min ba! Ameena bazan iya zama waje ɗaya da mutumin da bai san darajar dan Adam ba, tunda wannan rayuwar kika zaɓa bazan miki baki ba, amma karki manta abunda kayi shi zaka tarar, ni bani hanya na wuce…” ta faɗa tana ture ta..

” Innalillahi, na shegi su ni Ameenatu, haba Hajiya kiyiwa girman Allah ki tsaya ki saurareni, in kika tafi ya zanyi! Hajiya sanin kan ki ne fushin ki a gare ni bala’i ne, kiyi haƙuri inda akan wace abar ne Allah zan sauya…”  ta faɗa hawaye na bin kuncin ta…

Daddah ta saki murmushi a boye, a zuciyar tace” yarinya kenan, ni za kiyi wa hauka.. a fili tace” a’a babu amafani zama na daku gaskiya Ameena gida na zan koma, hankali na sai yafi kwanciya, nan gidan kullum ciki ƙananun zance, sam bakya san zama lafiya baga ABOKIYAR zaman taki ba baga ƴayan naki ba, gaskiya sai na tafi..” tayi maganar tana wani juya jiki ita a lalle sai ta wuce..

Mommy ta rungume ƙam ta baya tana hawaye murya k’asa-k’asa tace” kiyi haƙuri wallahi zan sauya nayi miki alƙawari, zan sauya…”

Tausayi ta bata, a hankali ta sauke aƙwatin, har yanzu fuskar ta nan yanda take tun farko, tace” in kika saɓa alƙawari fa?..”

” Bama zan saɓa ba Hajiya..”

Kan ta na cinyar Hajiya, cikin kuka kasan maƙoshi tace” so kike a zage ni ko Daddah? yanzu dama akan wannan abar zaki iya tafiya ki barni? sare kin san halin  Ya Abdulazizi tsaf zai koreni in yaga bakya nan, ni dai dan Allah karki sake min irin wannan, ba dai kan yarinyar nan ba ne? shikenan na janye zata iya shiga ko ina, haka yara nawa suma ta kula su, shikenan dai ko Hajiya?..”

Murmushin jin dadi Hajiya tayi kana tace” a’a ba shikenan ba, dole ne ki gyara wanna halaiyar taki domin bazan iya da ita ba, tsaya ma wai menene aibun TALAKAWAN nan ne wai? me suka tsare miki? me suka taɓa miki wanda bazaki manta dashi ba? suma da yan adam ne kamar ki, gaba ɗaya mu abu daya ne wallahi karki ga kin gaji arziki a wajen iyayen ki da mijiki, kina ɗaukar kan ki ke wata abace ta daban, a’a babu wanda kika fi, duk wanda kika gani yana da daraja ta wani tafi ta wani, tun wuri ma ki saki gaibu ki kama Allah, duniyar ma nawa take yau kai ne gobe ba kai bane, kafin ke nawa akayi? tun kina da sauran lokaci ki ajiye wannan gidadancin a gefe ki rungume kaddarar ki,  banda rashin wayo ma irin naki Allah ya baki ABOKIYAR zama irin yarinyar nan, ai ba ƙaramin daɗi za kiji ba, amma sabida ta ɗauki yarinyar da ɗanki ya make shine ta dawo abokiyar gabar ki, ke bama gata tayi miki ba! ga wata sabuwar rashin kunya yanzu da kika ɗauko wai ni ni dinnan kika duba sabida nace zata zauna a gida nan kike gaya min magana har da cewa dan bani na haifeki ba, me yasa da uwar taki ta tafi baki bita ba? wannan maganar ta dakar min zuciya kuma har yanzu ina jinta, a gaban ɗanki da kishiyar ki kika wulaƙanta ni! banda yarinyar yar mutunci ce ai da tunni ta jima da raina ni ita ma, in kika tashi haukar ki a gaban kowa yi kike, to wanna ba tarbiyar kika bawa yaranki ba horo kike musu cikin sauki ta yanda ke ma nan gaba za suyi miki, a lokacin ne zaki gane illar abinda kika aikata, bazan miki fatan tsiya ba kullum addu’a ta a gare ki shi ne Allah ya shirye ki ya ganar dake gaskiya, ke uwace yanzu kin san ya kamata kin san ba dai-dai ba, duk abunda ki kayi kina sane Allah ya shiryeki…”

<< Waye Zabin Munibat? 15Waye Zabin Munibat? 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×