Ameen yace yana murmushi ya biyo baya na da sauri, Allah Allah nake ‘na shige shashin Anty caraf naji ya danƙo mun hannu nayi saurin juyowa a tsorace, tamkar leɓen bakina jira yake nace” MAN!!..”
Haɗi fuska yayi yana nazari ‘na kana yace” jeki!…” yana matsa mun a hanƴa…
Cikin sanyin murya nace” kayi haƙuri kai ma dan Allah?…”
A tsanake yace” me ya faru kuma?..”
Shiru nayi ina tunanin to ko bai sani ba? tambayar da nayiwa kai na kenan, daga bisani kuma na sauya akalar zancan nawa da cewa” in ba damuwa ina so na koma gidan mu!..”
” Wani abu akayi miki a nan d’in?…”
” Ina son komawa ne wajen Kawu na..” cikin rauni nayi maganar…
” Ok ki faɗawa Daddah to…” ya faɗa fuskar a haɗe..
Shiru nayi ban sake magana ba, amma a zuciya ta daɗi nake ji yau gani ga MAN dinna har muyi magana me tsayi…
*” Har yanzu kina nan akan bakarki na san ki aure ANU?..”*
D’um kirjina yayi wata irin faɗuwa, nayi maza nace” a’a…”
” a’a me?..” ya tambaya yana kare mun kallo, “Ya kuka yi da aminiyar taki?..”
Shiru nayi domin bani da amsar tambayar sa, gajiya yayi kana yace” a karo na ƙarshe Daddy zai tambayeki saura kuma naji wannan bakin naki yace wani!…” yana rufe bakin sa Nafisat na fitowa idanun ta fal hawaye…
Ban jira naji me zata ce ba nayi saurin shigewa ciki, a jikin sa ta ƙwanta cikin shasheƙar kuka tace” Ya MAN! bana son wannan halin na Ya ANU! ya dage sai zuga Mommy yake har sai da ta mareni kawai ‘dan na kare ƙawata…”
” Shittt bana son jin komai Auta, kiyi haƙuri kinji wataƙila kema kinyi kuskure ne haka kawai Mommy bazata hukuntaki ba…”
” Banyi komai ba ‘fa, haka yace…” “Nace miki bana son jin kinji?..”
Shiru tayi zuciyar ta nayi masa zafi…
Bayan ƙwana biyu, lafiya kalau muke zaune da kowa a gidan, su Mommy sun huta sosai, tazo har ɗakin Daddah ta bata haƙuri, Daddah sam bata da roƙo a take tace ta yafe mata, haka kuma bata gayawa kowa abinda ya faru ba, Anty ta zamo daga kan kujera cikin biyayya tace” Maman Auta! kiyi haƙuri kema akan abinda kika tarar…”
Wani irin daɗi ne ya kama Mommy, cike da nuna ita wata ce tace” No Antyn su! ai ke zan bawa haƙuri, domin nayi saurin yanke hukunci cikin rashin sani, kiyi haƙuri kema!…”
Daddah ta karewa Mommy kallo, ganin yanda take ta wani murza zoban zinaren dake hannun ta tace” lafiyar ki kalau Amina?..”
Cikin sauri Mommy tace” Eh me kika gani Hajiyar mu?..”
” To saki hannun haka kar kiji rauni!..” da murmushi akan face din ta ida zancen…
Murmushi Mommy tayi kana tace” HAJIYAR MU bari na leƙa ɗakin yaran nan…”
Ok kawai tace, ita kuma ta fice a ɗakin…
Shiru nayi ina tunani halin da Kawu na yake ciki yanzu, maganar MAN ce ta faɗo mun na lumshe idanuna zuciya ta fari ƙwal…
Idanun ta sun kaɗa sunyi jawur dasu, cikin tsananin ɓacin rai tace” me? kana nufin mahaukaciyar yarinyar nan itace har yanzu tana cikin gidan nan basu mayar da ita inda ta fito ba, ga wani wawan zance da kake wai soyayya da MAN abun ma babu daɗin ji! yanzu dama akan haka ne suka rufar maka da mari?…”
” Mommy na sha wahala sosai da bakya nan, ba yanda banyi da mutanan ba akan kar su sake dauko yarinyar nan amma suka ƙi, a karshe ma sai mari ‘na sha a hannu Dadda…”
Mommy ta miƙi zuciyar ta na azazala mata, ANU yayi saurin dawo da ita zaune, cikin hikima irin tashi ya ɗurata aka burin sa ‘na aure na daga baya yayi min sakin da babu dawo ba, bare ‘na sake kasancewa a cikin a halin su…
Ƙare mai kallo tayi sosai bayan ya gama maganar, kana ta sauke ajiyar zuciya haɗ’i da cewa” MY SON! ba wai naƙi ta taka bane, a’a ina hangen abunda zaije ya dawo nan gaba, bazanyi fatan Auta tayi aure a sako min ita ba, dan haka kai ma bazan yarda ka aure ta ba, bare har saki ya shiga tsakanin ku, bazan so a fara irga maka aure ba kana ji, daga yanzu bana so ka sake magana akan ta inda na isa da kai! shi kuma Yayan naku zaizo ya same ni…” ta faɗa zuciyar ta ajagule…
Langwaɓewa yayi a cinyar ta kamar wani ƙaramin yaro, yace” Mommy ya maganar Hafsat din?..”
Ajiyar zuciya ta sauke tace” ta nan har yanzu, zuwa anjima zaka kaini gidan su…”
Muna zaune gaba ɗaya, hira suke cikin jin daɗi yayin da nake gefe ina tunanin Kawu na, ni ban saba da Dady ba shi yasa in naga Auta tana wani abu sai Kawu na ya ringa faɗo min a rai, ƙamshin turaren tane ya dake hancin kowa, babu wanda bai kalle inda sautin takun ta yake fitowa ba, a zuciyar sa yayi hamdala da samu mace irin Mommy ga ANTY a gefe, ya saki murmushi cikin jin daɗi yace” Hajiya! ga mutuninyar ki nan fa zuwa…”
Shiru Daddah tai kamar bata ji me yace ba, da salama a bakin ta shigo falon, bin ko ina take da kallo kamar me neman wani abu, ta yamutse fuska cikin yanga tace” Sannu ku da hutawa!…”
” Yauwa.” suka faɗa a tare!…
Shiru ne ya ratsa wajen, a hankali na miƙe zan gudu ɗaki na domin har ga Allah ni Mommy tsoro take bani, naji murya Daddah na cewa” MUNI! wai me yake damunki ne yau? gaba ɗaya naga baki da sukuni..”
Murmushi nai kaina a ƙasa nace” ba komai Daddah! kawai bana jin daɗin yanayi ne!..”
” Yo ina zakiji daɗi, tunda ba sabawa akayi ba! wallahi ina mutuƙar takaicin ganin gilmawar yarinyar nan a gidan nan, fisabilillahi a rasa wace za’a ƙwaso mana sai mahaukaciya, yanzu dama akan wannan abune ranar dana dawo na tare kuma dakar min yaro, shi da yake ɗan asali wanda ya gaji arziki gaba da baya, yaro ɗan madara me aji da babban matsayi…” Cikin tsananin masifa take maganar…
Auta ta mike jiki a sanyaye ta fice a falon, ya rage dagani sai su dama mazan basu shigo ba, ANTY, Daddah, Dady, Mommy sai ni…
Dady bai ce komai ba ila zaman shi da ya gyara, ta ƙare musu kallo a masifance tace” magana nake fa! naji duk kunyi min shiru kuna kallo na!..”
” MUNIBBAT! zo ki wuce ciki!..” cewar ANTY..
” Ciki ina???.” Mommy ta faɗa a ƙausashe..
Jikina yayi bala’in sanyi, daƙar nake ɗ’aga ƙafa ta haka nazo wucewa ta kusa da ita, kai na a ƙasa aiko tai saurin danƙo hannu na cikin mutuƙar ɓacin rai tace” KE!! nan yayi miki kama da gidan gadonki?…”
Da sauri na girgiza kai alamar AA domin na firgita sosai da roƙon da tayi min, ta ɗaura da cewa” yarona yayi sanadiyar zuwanki, nayi haƙuri an riƙeki har kin warke to zaman uban me kike kuma? baki da iyaye ne? ko baza su iya riƙ’eki ba ne? ko baki da dangi ne?…”
Kuka kam tunda ta riƙeni nake faman iyasa, cikin shasheƙar kuka nace” kiyi haƙuri Hajiya!..”
” Ba haƙ’uri nake nema ba, ki tatara kayanki ki bar mun gida kar nake ganin ki, a cikin gida na! tunda babu gadonki a ciki ‘in ba haka ba kuma zan gigita miki rayuwa…”
*” Gidanki ko nawa? yaushe ya zama naki?..”*
Cak ta tsaya cikin mutuƙar mamakin mijin nata, bakin ta a buɗe zuciyar ta na bugawa tace” please bana so ka shiga cikin wannan cas din! ka barni na gyara a hali na!..”
” ANTY! zo ki kai yarinyar ki ɗaki!…” ya faɗa yana me ƙurawa Mommy idanu alamar tayi babban lefi!…”
Mommy taƙi saki na, domin tayi min mugun riƙo, sai da ANTY tai da gaske sannan ta ƙwaceni a hannun ta, shima Daddah ce ta miƙe shine dalilin saki na da tayi, ina kuka ANTY ta turani muka bar falon zuciyoyin mu a jagule…
Daddah tazo har gaba ta tace” Amina! a wannan karan bazance miki komai ba, tunda a gaban mijinki kikayi…” ta wuce a abun ta…
Mommy taja da baya cike da fargaba, Daddy ya shafi hancin sa da bayan hannun sa, alamar ranshi a ɓace yake yace” baki bani amsa ba yaushe ya zama gidan ki!??…” A yanzu a ƙausashe yake maganar…
” Honey baka gane bane!..” ta faɗ’a tana miƙe hannu zata shafi kirjin sa, yayi saurin matsawa baya Mommy ta zare ido cikin razani, tace” Abdul!!!..”
” Amina!! kin sha aikata abubuwa da dama a gaba na ba tare da nayi miki wani hukunci ba, ki sani a yanzu bazan lamunta ba! Ameena! ki kiyayye ni wallahi akan marainiyar nan zan saɓa miki!…”
Mommy ta ware ido cikin mutuƙar tsoro tace” akan wannan yar mitsiyatan kake ikirarin saɓa mun?..”
” Ameena!!!…” ya faɗa yana ware hannun shi zai kifa mata mari, Mommy tayi saurin kare fuskar ta hawaye na bin k’uncin ta, tsakanin miji da mata sai Allah, jikin sa yayi sanyi gani yanda take zubar da ƙwalla hankali ya sauƙe hannu shi, gajeran tsaki ya saki kana ya bar mata wajen da sauri…
Mommy ta share ƙwallar ta cikin ɓakin ciki tayo shashin ANTY a zuciye…
Tsaf na haɗa kaya na, cikin ƙwarin gwiwa nace” kiyi haƙuri ANTY nima bazan so ‘na tafi na barki ba, amma tafiyar tawa itace mafi alkhairi tunda na shigo cikin ku kullum nice sanadin ɓacin ranku, zanje ‘na zauna ni kaɗai koda su Kawun basu dawo ba, nayi imani da Allah Mommy bata taɓa marinki ba amma ta sanadiya ta, a gaban idona aka marar min *mahaifiya!!* amma ban iya aikata komai!…” kuka yaci ƙarfina, na share ƙwalla ta, na kalle Anty da take kallon gefe ko bata faɗa ba na san kuka take, cikin jan numfashi nace” *eh na san komai zuwa yanzu, ke ƙanwar baba na ce ko?*..”
Da sauri ta juyo fuskar ta fal mamaki tace” baby! ya akayi kika sani?…”
” Mama! karki musa mun, naji da ƙunne na, sannan ‘na gani a zahiri kema kina da irin pic ɗin da baba ya bani a matsayin kaka ta, haka ne?…”
Tsareni da ido tayi ‘na wani lokaci kana tace” Eh haka ne! ‘na so nayi ido biyu da ɗan uwana amma Allah bai nufa ba, a yanda jama’a suka sheda, kuma aka gani mahaifiyar mu ta rasu, amma a zahiri mahaifiyar mu bata shiga cikin motar ba, mahaifun mu ne kawai a ciki sai wata baiwar Allah dake zaune a kusa dashi, a tunanin shi innah ce sai da tafiya tayi nisa, sannan ya ankara itama anata bangaren tana idar da sallah taga babu mota babu dalilin ta, Inna tayi kuka sosai sannan ta hawo wata motar domin bin sahun su, a haka har Allah yasa ta hange su bata da ko fice a hannun ta wanda zata biya me motar da take ciki, dan haka ta nemin alfarma akan ya tsayar dashi zata koma can, haka kayi kuwa Baban mu yana kallon ta, itama tama kallon shi fuskar sa cike da murmushi, basan abinda ke faruwa ba ƙwatsam sai ga motar da babanmu yake ciki ta dake titin baban gida, motar su Innah kuma tayi wani irin hantsilawa, a haka ta ringa gangarawa har ta faɗa wani ƙaramin kauye dake rangara, ita kaɗai ce ta rayu a cikin motar ta shiga mayuwacin hali sosai, hankalin ta ya gushe da taimakon wani bawan Allah Innah ta samu kulawa, sai da inda matsalar take sam tunanin ta ya gushe bata iya tuna komai, haka kuma bata ganewa amma ba hauka take ba, a haka Innah ta ci gaba da rayuwa yau da lafiya gobe akasin haka har lokacin haihuwar ta yayi, gidan da take zaune sun mutuƙar tausaya mata ganin irin wahalar da take sha, Allah cikin ikon sa ta samu lafiya, haihuwa yazo mata da warakar ciwan ta, Innah ta riƙe ni tamkar wata yar sarauniya, gidan da muke zaune sun fifitani akan yaran cikin su, na samu gata iya gata uwa uba ga tarbiyar sun bani ilimi isalamiya da boko, kullum Innah cikin bani labarin Yaya na take, bata da wani buri a rayuwar ta sai na fatan ta sake ganin shi ko da sau ɗaya ne, girma ya kama ta ta tsofa sosai kullum maganar ta Yaya na, duk da a lokacin bani da wani ƙarfi haka na ringa fafuta domin na samu mata shi, nayi iyaka bincike na ban haɗu dashi ba, har na cire rain samun shi, ƙwatsam Allah yayi ma Innah cikawa…” Cikin shasheƙa ANTY ta share kwallar ta haɗi da cewa” unguwar mu ɗaya da su Daddah, ba laifi gidan da nake suma masu arziki ne sosai gashi Innah ta tara min dukiya sosai, kullum neman Yaya na nake ko Allah zai sa mu gana, a haka har nayi aure ban dai na nema ba, har muka koma garin Abuja, a haka Allah ya haɗani da maƙonta ku a wajen wani biki nan take bani labarin ɗan uwa na da irin k’addara da ta same shi, a ƙarshe ta sheda min rasuwar sa, nayi bakin ciki marar musaltuwa na shiga damuwa sosai, abu ɗaya ne yake faran ta min rai shine yana da ƴa guda ɗ’aya tal mace amma Kawun ta na wajen uwa ya ɗauke ta, duk da ban taɓa gani yarinyar ba amma soyayyar ta shine yaza me min abun ado, a ko wannan lokaci, fatana shine na ganta cikin hikima na ringa bin didigi har na gano inda kuke, sai da ban taɓa ganin ki ba kulle yaumin nazo sai na tarar da gidan babu kowa, haka zan gaji da jira na tafi, a haka har Allah ya kawo mana AYSHA, wata irin soyayya nake wa yarinyar tun daga ganin farko, nafi kowa shiga damuwar halin da take ciki, wani abun farin ciki ashe ƴata ce ban sani ba, Allah ya kawo min ita har cikin gida, lokacin da kika samu lafiya a sannan ne na samu damar ganawa da Shafi’u na faɗa me koni wacece amma banyi yunƙurin shiga tsakanin ku ba, har sai kin buƙaci haka da kanki, shi da kan shi ya sheda ni din jininki ce yayi murna sosai a ƙarshe ya nemin na bar mai ke duk da ban amsa ba a lokacin sabida zuciya ta na tuzirani dole na haƙura na koma gida zuciya ta cike da begen ki, MUNIBBAT me sunan manya ke ƴata ce! shin zaki iya tafiya kibar mahaifiyar ki?…”
Wani irin tausayin tane ya kamani, gani yanda take zubar da hawaye, tabbas ƙ’aunar da nake mata bazata tashi a banza ba, ashe uwa tace! sai yanzu na hango kamanin ta ɗaya sak da baba na, sai da shi yafita haske sosai na fashe da kukan farin ciki da gudu naje na rungume ta, cikin kuka nace” ina ƙaunar ki Mama na! Ina jin ki sosai har cikin raina! ina son ki!…” nama rasa me zance mata na saka mata, ga wani irin nauyin ta da nake ji…