ANTY daɗi kamar ya sumar da ita, tsam ta rungume ni itama hawaye farin ciki na zubo mata, a hankali tace” nida ke *haɗin Allah ne* kawai ba na mutun ba, har yanzu mahaifi na nake nema! duk shima an sheda min ya mutu ba tun yanzu ba…”
Mommy kam tazo shigowa Daddah ta tare ta, cikin nuna mata zallar fushin ta tace” Amina muddin kika saka kafa a shashin yarinyar nan da zumar neman rigima, wallahi ban yafe miki ba!…”
Mommy ta zaro ido cikin razani tace” Hajiyar mu! abun har ya kai haka?…”
Ko kallan ta Daddah ba tayi ba ta wuce abin ta, Mommy tayi ƙwafa kana ta fice zuciyar ta babu daɗi….
Dady ne ya shigo ɗ’akin, kallon mu yayi a tsanake sannan yace” gaba ɗayan ku ina san ganin ku a falon Hajiya…”
Cikin biyayya ANTY tace ” insha Allah ranka yadaɗe..”
” Ki shiga kiyi wanka, kar ki saka damuwa a ranki kinji, ki shirya irin na ranar nan bayan mu gama dashi zan kai ki wajen Kawunki!…” Cikin murmushi tayi maganar…
Daɗi ne ya rufeni har ban san lokacin da na daka tsalle ba, kafin tayi wata maganar na shige bayi…
Murmushi tayi itama ta fice zuwa ɗ’akin ta, wanka tayi ta sake duƙar ado kana ta wuce falon Hajiya Daddah, zuciyar ta wasi da ita domin ita yau rana ce ta musamma a wajen ta….
Nima ƙwalliya na caɓa har faraa nake na ma manta da abinda ya wakana ɗazu, a haka nazo falon a yanzu abin ya ɗaure min kai, domin Daddah na gani a zaune sai Mamana, ga MAN ANNUWAR, sai auta Mommy kam banga ta ba, a wajen kafar Daddah naje na zauna cikin ladabi, gyaran murya dady yayi cikin isa da izza yace” *to Alhamdulillahi, a cikin nan bana neman amincewar ko wannan ku, na yanke hukuncin insha Allah nan da wata biyu masu zuwa zaa ɗaura auren Haidar da MUNIBBAT! bana son tayar da wani zance wannan hukuncin dagani ne, daga yau kuma duk wanda ya sake nunawa yarinyar wani abu marar dadi zai gamu dani, ku tashi ku bani waje…*”
Wata irin faɗuwar gaba ce ta kamani, cikin firgici nake duban MAN da ya kafeni da ido, ANNU ya gigice cikin mutuƙar baƙin ciki ya miƙ’e babu um babu umum ya fice a wajen, AUTA ta saki murmushi tana duba na a hankali tace” amayar mu!..” simi simi tafice a falon.
MAN ya mikƙe zuciyar sa kar farin ciki, ba wanda ya kula a cikin mu shima ya fita a abin sa, Daddah tace” Allah yayi maka albarka yaro na, Allah ya sanya alhairi ya kai mana lokaci…”
” Ameen ANTY tace game dacewa Alhamdulillahi Allah ya sanya alhairi…”
Duk suka tashi, aka barni daga ni sai Dady, domin ni ma gagara miƙewa sabida nauyin da jikina da zuciyata sukayi min, a yanzu har ga Allah na haƙura da auran MAN ko dan mahaifiyar sa, ban san ina hawaye ba sai jin murya dady nayi yace” MUNIBBAT kina da wanda kike so ne? ko bakya san shi?…”
A hankali na taɓ’a fuska ta, cikin ƙ’arfin hali nace” a’a dady!..”
” Yarinyar ta bazan takura miki ba, kije kiyi tunani a yanzu bana jin akwai abinda hanani aiwatar da abinda nai niyya muddin bake kika ce bakya so ba, tashi kije ina jiran amsar ki nan da ƙwana biyu…”
Jikina yayi sanyi a haka na mike ina kuka na wuce ɗ’akin Daddah inda naga mama na ta shiga…
Zaune ta tashi fuskar babu walwala tace” ke bana son shashanci menene na kukan kuma, ke da akayi wa gata abinda kuke nema ne fa yazo muku cikin sauki! ko kukan farin ciki ke?..” ta faɗ’a tana saki murmushi me sauti…
Daddah tace” rabu da ƴar farka, mu zatayi wa bariki!..” gaba ɗ’aya suka saka dariya zuciyoyin su cike da farin ciki…”
Shiru nayi bance dasu komai ba, ni hange irin rayuwar da zanyi nake a takure, domin nayi imani da Allah Mommy bazata bari na zauna lafiya ba tunda bata ƙauna ta, tsakanin ɗa da uwa kuma sai Allah, dole nee yayi mata biyayye… na sake rushewa da kuka…
Saboda tsananin jin zafin maganar har bata san lokacin da ta ƙwashe shi da wani wawan mari ba, cikin mutuƙar masifa tace” ka kiyayye ni da irin wannan mugun labarin ko nayi maka kama da saakar ne ANNU?..” a zafafe tayi maganar…
ANNU YA DAFI KUNCI ZUCIYAR SA NA ZAFI YACE” MOMMY WALLAHI!…
DA KARFI TACE” KA SHIGA HANKALIN KA BANA SON MAGANAR BANZA!!…””
A ZUCIYE YA FICE A FALON…
Tsaki tayi haɗi dacewa” haba yaro sai dauko zance marar taushe, bangama da jin wancen bakin ciki ba, zaka sake jifani a wani ai a bari na huta!…” ta sake sakin tsaki..
Bayan ƙwana biyu, a yanzu kam mun shirya da MAN dinna soyayya muke ta kece raini, a gaba kowa nuna min so yake amma banda mutun ɗaya, lokacin da muka samu hutu a makaranta na tafi gidan Kawu ‘na, nayi mamaki sosai da nayi araba da irin gidan da suke ciki a yanzu, ga ma’aikata sai shige da fice suke, ban san yanda akayi ba amma mata biyu na tarar a gida kuma gaba dayan su matan Kawu ne, sun amsheni hannu bibiyu ko wace sai nan dani take, ga su Bishira an zama yam mata yanzu, itama sai murnar gani na suke, duk da bana gidan amma dakina daban yake an zuba mun komai na jin dadin rayuwa..
Murmushi nake nima kamar yanda yake, cikin sanyin murya nace” Kawu na ina ANTY na!!?..”
Yace” taje gidan su, ina tunanin ta kusa dawowa…”
” Yaushe kayi aure Kawu!..”
Murmushi yayi yanzu kana yace” na jima sanyin idaniya ta, bana jin kinyi wata biyu da barin gidan, nima na dawo nan anguwar da saban aure amayar ce ma bata jima ba…”
Kallon shi nake zuciya ta ba dadi nace” ina so naje wajen ANTY Na!!..”
” Ok ki shirya zuwa anjima zanyiwa musa magana ya kai ku har da su Bishira!!..”
” To kawai nace, ina shirin mikewa yace” me yake damun ki yarinyar Kawu?…”
” Ba komai!..” nace cikin sanyin jiki dana zuciya…
Shima rabuwa yayi dani, har na fice a falon…
Ko da bai fad’a min ba d’aga ganin yanayin da ya amsa min na san akwai matsala, zuciya tana bani ba dadine yasa ANTY tafiya ba, duk yanda akayi akwai matsala me yasa ya kara aure bama mata d’aya ba har biyu!? kai na ya kulle na rasa gane mafita…
Bishira ce ta shigo d’akin, kallo na tayi cikin sanyi tace” ANTY MUNI! kizo ANTY RABI tana kiran ki!…”
Cikin rashin fahimta nace” wacece haka!?..”
” Matar Abba ce!..” ta bani amsa a dan tsorace..
Hannun ta na kama had’i dacewa” muje to.”
Nokewa tayi hadi da yin kasa da kanta tace” a’a kawai kije ni zanyi wani aikin ne!..”
” Dole ne ki rakani tunda ba sani kan gidan nayi ba…”
Hawaye idanun ta ne ya digo a hannu na, cikin mamaki nace” ke lafiyarki kalau kuwa? kukan na menene kuma?..”
Rungume ni tai kukan ta na tsananta tace” ANTY dan ALLAH ki tafi ke kadai in naje zata dakeni!..”
Ido na waje nace” duka kuka!??..” cike da mamaki..
“Eh duka ANTY tun daga ranar da Abba ya kawo ANTY Rabi a matsayin mata…
Bai faɗawa kowa zaiyi aure ba sai ganin shi mu kayi da matar sa, hankali Mama yaƙi ƙwanciya tun yana jure abinda take har yazo yana mata faɗa a sirince, amma duk a banza Mama taƙiji taƙi ƙwantar da hankalin ta su zauna lafiya, ANTY Rabi itama bata da sauki ko kaƙ’ai akan kishi, duk wasu hanyoyi na rashin mutunci da kisan mimiƙe ta sani, a wajen Abba ita macece me mutuƙar haƙ’uri da biyayya, amma da zarar ya fita macece me tsiwa da masifa wace bata jiran kaɗ’ai, wallahi ANTY Mama RABI tafi maman mu jidali nesa ba kusa ba, ko Mama tayi shiru a wani abu wani abu ANTY bata shiru, domin sam bata da hakuri ko kaɗ’ai…
Abba mu ya samu ƙarin girma a wajen aikin sa albashin sa ya riɓanya, kuɗi suna shigo mai ta ko ina a hankali ya sauya mana komai na gida, muma aka sauya mana makaranta, inda ka tsaye shi yake biya miki kuɗi makarantar ki kema, Mama taƙi haƙuri akan wannan nan ma sai da tayi magana, duk dan sabida a zauna lafiya suma duk wata yana basu wani abu a matsayin ihsani…
Lokacin da ya sauya saban gida, haka muka tataro muka dawo nan da zama, wannan ɗakin da kike ciki anyi masifa akan shi, domin Mama cewa tayi bata san zance ba, duk wata lalaɓawa da kika san Abba nayi mata yayi amma a banza, ANTY Rabi kuwa tunda tace Allah ya sanya alhairi, bata sake maganar ɗakin ba, domin kayan dake dakunan su yafi wannan kyau da tsada har da inganci…
Kullum ciki yada magana Mama take, Abba baya kulata a cewar sa tana da matsala, ba tare da Abba ya sani ba Mama ta siyar da komai na ɗakin nan, ya zama na babu komai a cikin sa, duk da haka bata haƙura ba kullum rigimar da zatayi daban…
A ɓangaren guda kuma ga faɗan kishi da kullum sai anyi shi, a gaban mu suke komai…
Saban salon da ANTY Rabi ta fito dashi, shine na kamamu tayi mana duka haka nan ba tare da muyi lefin komai ba, in Mama tayi magana sai tace ƴayan mijinta ne ta da ikon da zata hukunta mu duk lokacin da buƙutar hakan ta taso, muna shan wuya a hannun ta sosai, ita bata abu a boye wani lokaci ma a gaban Abba take dukan mu a cewar ta muyi lefi, shi ko sai dai yayi tai mana faɗa akan muna jin magana, to anyi haka ya kai sau uku Mama mu tana zuba ma Abba ido ko zaiyi wani abu aka, shiru babu alamar ya san me take…
ANTY kin dai san yanda Mamanmu take mutuƙar ƙaunar mu, haka ta tayar da hankalin kowa gidan nan, kullum da irin abunda take fitowa dashi, duk sabida mu! gani taƙi tayi hankali yasa shi ƙaro musu wata abokiyar zaman suka zama su uku, ANTY halimatu bata da matsala ko kaɗai domin ita gaba ɗ’aya mutanan gidan basa gaban ta, sai ta wuni a ɗ’aki ma bata fito ba, in kinga ta a waje to lokacin zafi ne ko wani dalili ne ya fito da ita da zarar ta gama kuma zata koma ciki ta rifu ɗakin ta, wannan abu yana ƙonawa Mama rai amma ta ɗaure, kishi tsakanin ta da ANTY Rabi ne kawai babu sausauci, duk wani abu da suke Abba yana sane dasu gaba ɗaya ya tatara su ya watsar gefe guda, ya cigaba da harkokin gaban sa babu wace bata san da zamanki a gidan nan ba domin kullum da sunaki a bakin sa…
Fitin-tinu iri-iri Mama take kunowa, zuciyar ta taƙi dangana da wannan aure da yayi a cewar sa shine hukunci da ya dace da ita, ranar gidan ba kowa duk sun tafi anguwa dagani sai Mama ko su Hanna basa nan, a gaba ido na Maman mu ta sakawa ɗakin ANTY Rabi wuta, sai da ya cinye tass sannan tayi waje neman ɗauki a cewar ta wutar lantarki ce, abinda bata sani ba Abba ya saka CC camera, kaf anguwar nan babu wanda baiyi mamakin yanda gobar nan ta tashi ba, Abba baice mata komai ba illa gyara dakin nan naki da yayi yace ANTY ta zauna kafin a gyara mata nata, to tace hankalin ta a ƙwance domin ta san waye mijinta…
Bayan ƙwana biyu yau ma Mama da masifa ta tashi, cikin sanyin jiki Abba yazo ya ja hannun ta har sashin sa, cikin salama ya karanta mata lefin ta, data dage batayi ba kuma ya nuna mata zahiri har kayan ɗ’akin ki da ta siyar duk ya sani hakuri yake, maganar dukan yara ma yace mata yana sane da gaskiya komai abinda yasa bazaiyi magana ba yana so taji yanda yakeji duk lokacin da ya dawo yaga MUNIBBAT din sa a wahale, yanzu yana buƙ’atar hutu taje gidan su ya haɗa ta da saki ɗaya! taso ta daga mai hankali cikin sanyi Abban mu yace muddin ta bari yaran sa suka san abinda ke faru to ta tabbatar in ta tafi ta tafi kenan, ko abokan zaman ta baice ta shedawa ba, kuka kam Mama tayi shi, ko da ta fice a ɗ’akin shima hawaye ya share maganar da nake gaya miki yanzu kullum Abbamu da soyayyar Mama yake ƙwana da ita yake tashi, a yanzu mu bamu da wani yanci a gidan ubanmu sai abinda ANTY tace shi akayi, nima a history din Abba na karanta duk abinda kikaji na faɗ’a miki, sai wanda akayi a gaba na, duk iri san da Maman mu take mana haka Abbanmu ya hanata daukar ko mutun ɗ’aya a cikin mu…
Tafiyar Mama yasa ANTY ta raga mana sosai, yanzu taba cika dukan mu ba amma akwai tsawa da faɗa marar tushe, kuma taba sakeyi a gaban Abban mu ba tunda Mama ta tafi, a wajen ANTY halimatu kawai muke samun sausauci, wani lokaci ma ita ke ƙwatar mu…
Cikin kuka ta ida zancen…
Tausayin ta ne ya ratsani, jikina yayi sanyi cikin dakewa nace” kiyi shiru ƙanwa ta kinji! Mama zata dawo insha Allah, ki shirya zamuje wajen ta yau! nima bazan tafi ba har sai ta dawo, nayi miki alƙawari babu wanda zai sake dukan ki a gidan nan…”
” Da gaske ANTY!?..”
Murmushi nai mata haɗin da ƙwaiƙwayon ta nima Ina turo baki nace” da gaske mana!..”
Dariya mu kayi mu duka, muna rungume juna, a zuciya ta nake jinjina irin kiyayyar da ANTY tayi mun haka, wace har ya zamana ko bana tare da ita zata iya nunawa, lallai ANTY na sai addu’a kawai, ni kuma zan miki gata, zan zamo sanadiyar dawowar ki wajen yaranki…””
Cikin izza da isa ta shigo ɗakin nawa, hankalin ta a kwance a haka ta same mu ko ɗar banji ba, domin duk bala’in ta bai kai na Mommy, tunda ko na iya jure nata wannan baza ta dame ni ba wallahi…
Idanun ta a tsatsaye take duba na, gajeran murmushi ta saki iya bakin ta tace” MUNIBBAT! zo mana?…”
Nima murmushi na mayar mata haɗi da cewa” yanzu nake shirin zuwa, rabin raina ke buƙ’atar kulawa ta, dana kamala zan zo ANTY Rabi!..”
Tsareni da ido tayi, cike da mamakin magana ta ko me ta tuno oho sai ta juya kawai ba tace komai ba…
Bishira ta mike zaune idanun ta a waje tace” ANTY! me kika yi haka?..” cike da tsoro take tambaya ta…
Bance mata komai ba illa tashi da nai na shiga haɗa kaya na, sai da na gama komai sannan na tafi kiran ta…
Zaune take akan maƙemiyar kujerar ta, cikin isa da alfhari naje kan ɗ’aya daga ciki na zauna, a tsanake take dubana fuskar ta a sake, tace” yarinya ta matso nan!..”
Mamaki nayi domin ni nayi da gayyane ko zata tanka yanzu na saka mata bori amma sai gashi tana shirin tura min aniyata…
” No nan ma ya isa!..”
Murmushi tai kana tace” yaro yaro ne, a mutunce muka sake gaisawa da ita, daga karshe take bani labarin ta san ko ni wacece da irin rayuwar da nayi a baya, d’aga ƙ’arshe ta sake bani haƙuri, a cewar ta duk wani abu da take tanayi ne domin na…”
Murmushi nai ina duban ta nace” ANTY Rabi! bana so ki saka kanki a matsala a ta dalilina, ni a matsayin uwa na ɗauki ANTY na ba wai uwar riko ba, bana buƙatar kowa ya rama mun abinda ya faru tsakanin da ita, domin ni taimako na tayi da batayi abinda tayi ba da har yanzu Ina nan a zaune ba tare da na haɗu da mahaifiya ta ba, ni bana ganin lefin ANTY na ko kaɗai domin ita ma macece ko kece zaki iya aikata abinda ta aikata gidan mijinta ne, riƙon ɗan wani ba naka ba akwai wahala, ANTY Na tayi mutuƙar ƙoƙari tunda bata ɓata min tarbiya ta ba, har na bar gaban ta ina da mutunci na, sosai nake alfahari da wannan ANTY Rabi bana buƙ’atar taimakon kowa muddin tsakanin na da Anty ne in da raban zata so ni nan gaba ina sa ran haka, na sa a raina duk abinda ya faru dani a duniya kaddaratace a yanzu Ina neman alfarma a wajenki muddin abinda kika faɗa gaskia ne, ki bar su Bishira su sake a gidan uban su, Dan girman Allah, karki manta kema nan gaba kaɗan zaki zama uwa kiyi tunanin in babu ke ya yaranki zasu k’asance!? a wannan irin hannu zasu faɗa a yanzu su tamkar maraiyune domin basu da babban jigo kece ya kama ta ki zamo musu abin alfahari, wallahi Azeem Kawu na yana kallon ki kawaici yake amma ya san me kike aika tawa, tun wuri ki gyara maamularki dasu kafin kema ya fito miki fili, Kawu na yana da haƙ’uri da jureya, yana da kawaici sosai akan yaran sa, amma in kika kaishi bango tabbas zai rufe idanun sa yayi miki hukuci mafi tsuri wallahi! a Yan shekaru biyu zuwa uku kawai kika san shi amma nafiki sanin shi tun Ina yar mutsitsiya ta, *ki bar su su sake ko nima na hanaki sakatt!!!…”