Skip to content
Part 21 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Lokacin da aka yi sallar magariba Maryam na zaune a parlo ta aje kayan shan ruwanta a gabanta, tuwan ɗazu ne sai sob’on da ta yi, tana addu’a Tafida ya sauƙo daga sama da alama masallaci zaije, ya tsaya yana kallonta da mamaki. “Wifey wai azumi kika yi ?”

Maryama ta shafa addu’ar wadda rabinta gaba ɗaya akan samun sauƙin Tafida ne, ta kalleshi, sannan ta gyaɗa masa kai. “Ban sani ba ai”.

Sai kawai ta yi murmushi tana shan sob’on da ta yi “Zanje masallaci”. “A dawo lafiya”. Ya janyo ƙofar parlon yana faɗin “Allah ya sa”.

Sanda ya dawo daga masallacin tana zaune a parlon still, dan bayan ta ɗan ci tuwon kaɗan ta tashi taje ta yi sallah, shine ta dawo ta zauna tana duba vedios ɗin data fara ɗorawa a tiktok, dan tafi bashi ƙarfi fiye da inster.

Sannu da zuwa ta masa sannan ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗauko masa nasa sob’on, yau tana so taga abinda zai faru, addu’o’i kala-kala da surorin kur’ani ta tofa a cikin ruwan sobon. Yau tana so taga ko hakan zai zama mafitar matsalar da Tafidan ke ciki.
Miƙo masa sob’on ta yi ya karb’a yana sauya Chanel daga MBC Bollywood zuwa channel ɗin da suke haske wasan cricket.

Maryam ta zauna a ranta tana faɗin, sauran maza iskansu na ball ne, amma shi cricket yake so, sai kuma ta tsaya ta meda hankalinta kansa tana so taga yanda abun zai kasance, a ranta kuma fal fatane na Allah yasa shawarar da zuciyarta ta bata ta yi aiki.

A kan idonta ya kai bakinsa ya yi sipping na farko, tanaga sanda ƙwayar idonsa ta kawo wani hasken ja, kamar an haska cocila, sai kuma ta ɗauke lokaci guda, Maryam ta fara murna ganin kamar abun yana aiki, shi sam baima ji a jikinsa ba.

A dai-dai lokacin da ruwan sob’on ya sauka a cikin Tafida, a dai-dai lokacin ne cikin Maryam ya wani irin murɗa, wanda hakan yasa ta saki wata ƙarar azaba.

“Ahhhhhhhh!”

Ta kai ƙasa hannunta akan cikinta, ji take kamar ana tsitsinka mata hanji ne, kamar zata amayo da kayan cikinta, azabar da take ji ta wuce misali. Da sauri Tafida ya aje glass cup ɗin hannunsa ya yi inda take durƙushe, ya riƙota. “Me ya faru ?”
Bata iya amsa shi ba, sbd yadda cikin nata ya ƙara murɗawa fiye da da, tuni idanunta ya kawo ruwa, azabar da take ji yanzu tafi gaban kwatance, bazata iya cewa ga yanda take ji ba sbd yanda cikin nata ke mata, Tafida ya rikota da kyau ya dawo da ita jikinsa yana faɗin.

“Miriam!, Miriam!, look at me!”

Da ƙyar ta iya ɗaga jajayen idanuwanta ta kalleshi, nan take ya gano abinda ke faruwa, ba a kanta hakan ya fara faruwa ba, ya faru akan Daadi, Neha, Fulani, Mairama harda Me Martaba ma.

“Kin saka wani abu a cikin sob’on ?”
Maryama ta riƙe gaban rigarsa gam, sai gumi take duk da sanyin gari dana acn dake parlon, jikinta sai rawa yake, ji take kamar za’a zare mata ruhinta ne, har wani fis-fisga take.

Da ƙyar ta iya gyaɗa masa kai, ya girgiza kansa cike da tausayawa, ba sai ta faɗa masa ba, yasan inda ke mata ciwo tun da abun shansa ya yi ba shafawa ko shaƙa ba, dan haka ya ɗora hannunsa akan cikinta, ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe Maryam tana ganin yanda ƙwayar idonsa ta yi ja kamar last time.

Sai kuma ta kalli hannunsa dake kan cikinta, wani haske wajen da ya ɗora hannun nasa yake, kuma a hankali a hankali ciwon ke raguwa, ya sani yau shine zai azabtu tunda har ya janye ciwon, kuma ya yarda da gwara ya azabtu da ace yana ganinta ita tana azabtuwa garin ƙoƙarin cetonsa.

Kamar an zare mata ƙaya haka Maryam taji ciwon ya ɗauke, kamar kuma ɗaukewar wutar nepa, sai sauƙe ajiyar zuciya take tunda Maanmu ta kawota duniya batajin ta tab’a cin karo da azaba makamanciyar wannan.
Har yanzu a cikin jikin Tafida take, a hankali ta ɗaga kanta ta kalli fuskarsa, shima ita yake kallo, jikinsa ya ƙara janta sosai ya rungumeta, Maryam taji wani abu na yawo akanta, kamar tana shawagi a sararin samaniya, taji kamar tana a cikin garden ɗin gidan, iskar wajen me daɗi tana shiga hancinta, tajita a wata duniya da ban.
“Miriam why ?, me yasa kika yi hakan?
Muryarsa ta fito cike da damuwa.


“Ni haka nake wifey, you better leave me, na faɗa miki koda guba aka saka min a abu to ba ya cina, saide ya koma jikin wanda ya min abun, haka asiri da addu’a , Fulani ta gwada, Daadi ta gwada, Neha ma ta yi, haka Me Martaba, duk wanda yayi ƙoƙarin bani addu’a to shi zai gamu da ciwo, idan sha na yi, to mutum zeyi ciwon ciki, idan kuma shaƙa na yi wanda ya bani zeyi ciwon kai, idan kuma na shafawa ne a duk inda na shafa a jikina nan ne ze yi ciwo a jikin mutum, wifey ciwo na gaske bana wasa ba, bana so ko wa ya azabtu, bana so wani abu ya sameki a sanadiyya ta Miriam”.

Sai kuma ya saketa yana kallonta, har yanzu a galab’aice take, dan ga idanuwanta nan kamar zasu lumshe
“Stay away from me Miriam, i am monster Miriam!”.

Da misalin karfe 11:00pm

Maryam ce kwance akan gadonta, gaba ɗaya tunanin abinda ya faru ɗazu ya hanata bacci, akai-akai take kai hannu tana share hawayen dake zubo mata, yanzu ita bata san me ya kamata tai masa ba, yana buƙatar temako, to amma yaya zatayi ?

Wani irin gurnani taji yana fitowa daga ɗakin dake maƙotanta, a firgice ta miƙe zaune.

Can kuma sai taji ihu, taji abubuwa na fashewa, sai kuma ƙarar Eshaan, daga inda take taji yanda ya bugu da kasa.
Ta rintse idanunta wasu sabbin hawaye na zubo mata, haka bige-bige da Shure shuren yaci gaba, ga gurnani da take ji kamar na zaki.
Gani tayi zaman nata ba zai iyu ba, dan haka ta miƙe taje ta ɗauto alwala ta shiga miƙawa Allah kukan ta, dan tasan shi kaɗai ne zai masa magani.

UCHENNA POV.

“Allah ya tsine maka Uche”.

”Yesu baze tab’a saka maka albarka ba”.

“Na tsine maka uchenna”.

A hankali ya kai hannu ya shafa sumar kansa, yayinda kalaman mahaifinsa wanda yake furta masa su a mabanbanta lokuta ke dawo masa cikin tunaninsa.

Zaune yake a cikin motarsa ya jingina da kujera, motar na parker ne a compound ɗin gidansa, ƙofar motar ta inda yake a buɗe take, yayinda iskar da ke kaɗawa take shigowa cikin motar, a lokacin ƙarfe tara saura, kansa ya ɗaga sama yana kallon saman motar tasa.

“Ka ce ba zan tab’ayin albarka ba Baba, gashi nanyi, kace bazan tab’a samun abinda nake so ba, gashi na samu, kace min ni tsinanne ne, Abba kuma kullum cikin sakamin albarka yake, kana gani ko ?, kana ganin yanda nake ci gaba a rayuwata, abba gaba ɗaya abubuwan daka faɗa basu faru ba, wanda Allah yasa ƘADDARA TA SO a kaina sune ke faruwa”

Sai kuma ya ƙarashe da murmushi, miƙewa zaune ya yi yana kallon ƙofar entrance ɗin gidan nasa, wai yanzu Hanam ce ciki, Hanam ce a cikin gidan, kuma a matsayinta na matarsa, me yafi wannan daɗi ?, saide kuma duk da haka yana cikin shakkun yanda zata karb’eshi, bai sani ba, wata ƙila tace bata sansa, ya saketa ta koma gidansu, sai kuma yaji gabansa ya faɗi.
Ya fito daga motar da sauri, ƙofar motar ya rufe sannan ya shiga cikin gidan, babu kowa a parlo dan haka yayi sama, ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan gidan yaga a buɗe kuma yaga ƙwan ɗakin a kunne, hakan ke nuna masa cewar tana ciki.

Ta maza ya yi ya dake, ya shiga taku har zuwa ƙofar ɗakin, a bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta, duk da ba fuskarta yake kallo ba, dan ta bashi baya.

Wata baƙar tank top ce a jikinta, sai farin cuffed trouser, gashin kanta paker a bayanta, ƙafarta sanye da crocs farare.

Kayan Arya data taho dashi take shiryawa a cikin wata chest drawer, Gaba ɗaya ta fawwala Allah lamuranta, dan abinda ya faru ɗazu ya bata mamaki, taya Abba zai aura mata Cristian, kuma bama haka ba wai har su Baba goyon bayansa suke, wannan wata iriyar rayuwace?, dan anaso ta yi aure ai ba sai an aura mata Cristian ba, ko jabeer yaƙi aurenta sai ta nemo wani da ban.

A ɗazun bata iya cewa komai ba sai tashi da tayi ta fice daga parlon, kanta na juyawa, ga wani duhu daya mamaye kafofin ganinta.

Kamar yanda Abba ya faɗi, ita ba zata tab’a bijire masa ba, tundade aurenta da Cristian yake so to za ta yi haƙuri ta zauna da shi, amma babu wani abu da zai shiga tsakaninsu, ita matarsa ce shi mijinta ne, kuma suna rayuwa a gida ɗaya, shikenan, bayan hakan kuma bata jin akwai ƙarin wani abu.

Motsin takun dataji a bayanta yasa ta waiga, Uche ta gani yana nufar inda Arya yake zaune yana wasa, taci gaba da binsa da kallo har ya ɗauki Arya ɗin, da ace wani zai faɗa mata cewar za ta iya auren Uche, da ta ƙaryata shi, koda a mafarki bata tab’a kawo hakan ba.

Itafa sam bata tab’a san Uche koda da second ɗaya ba, tana ganinsa a matsayin wani mutum da ban ne, bashi ma da matsayi a wajenta ko kaɗan, kawai ta ɗauki aurensa ne a matsayin YADDA KADDARA TA SO.

“Sannu da zuwa”.

“Yauwwa”.

Ta amsa masa tana juyawa taci gaba da jera kayan dake hannunta, bayan haka bata ƙara cewa komai da shi ba, har ya gama yi wa Arya wasa bata ko kalleshi ba, shi dan kansa ya aje Aryaan ɗin sannan ya kama hanya zai fita.

“Zanci gaba da aikina, fatan Abba ya faɗa maka”.

Ya tsaya cak, sannan ya jiyo ya kalleta, wasu kayan take jerawa a wani basket, ko kaɗan ba shi take kallo ba, amma yasan maganar tasa ce.

“Babu matsala, zaki iya ci gaba”.

Yana kaiwa nan ya ƙarasa ficewa. Ƙasa ya sauƙa ya dudduba gidan kamar wani baƙonsa, yana dubawa yaga irin kayan da ya kamata ace ya ƙaro a gidan.

MARYAM POV.

Zaune take a parlo tana jiran fitowar Tafida dan yazo su fita, yau da safe ta ganshi sanda ya fito cin abinci, tana ganinsa tausayinsa ya ƙara kamata dan har ya rame a iyaka jiya kawai, Allah ne kaɗai yasan abinda yake ji a jikinsa.

Takunsa da taji yasa ta ɗaga kanta sama ta kalleshi, sanye yake da wani yadin voil milk color, sai wata baƙar hula a kansa, da baƙaƙen takalma, hannunsa riƙe da wayarsa daya, ɗayan hannun kuma riƙe da key.

Ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta da jakarta.

“Kin shirya ?”

Ta gyaɗa masa kai idonta a kansa, da hannu ya mata alama da suje, shi yayi gaba ita tabi bayansa, wani yanka taga a bayansa setin wuyansa, hakan yasa ta zaro ido tare da tsayawa da tafiyar da take, a kiɗime ta ƙira sunansa.

“E…Esh…Eshaan”.

Shima ɗin ya tsaya da tafiyar da yake, karo na biyu kenan da ta tab’a kiran sunansa, na farko ranar da wuta ta ɗauke a gidan, sai kuma yau, ta iya kiran sunansa kamar ita ta raɗa masa shi, ya juyo yana kallonta with his blue eyes.

“Rauni a wuyanka…”

Gabaɗaya ta gama tsorata, itafa bata san damuwa, dan raunin yana da girma ga faɗi, kamar da aka saka wuka aka yanka, idonsa ya lumshe, bayan ɗan wani lokaci ya buɗe, sai kuma ya juyo mata bayan nasa.

“Ya haɗe ?”

Ya tambaya ba wai dan bai san ya haɗe ɗin ba, dan de kawai ta gani hankalin ta ya kwanta, dan baya son damuwarta ko kaɗan, baima san da raunin ba shi yasa ya barshi har ta gani, Allah yasa lokacin da yaji shi baƙin ruhin daya shiga jikinsa jiya na nan, dan haka zai iya hadewa.

*****

A kai a kai take sharan hawaye, dan gaba ɗaya ta rasa abinyi, bazata iya zama ta zuba ido irin haka na faruwa da shi tana gani ba, she needs to do something.

Tafida dake driving ta juyo ya kalleta, a dai-dai lokacin da yayi parking a inda ya saba sauƙeta idan ya kawota makaranta.

Ya juyo da kyau yana fuskantar ta, hannunsa ya kai ya kamo nata, Maryam ta zabura sbd yanda yatsunsa suka nade nata cikin bazata, bai tab’a riƙe hannunta ba, shi yasa bata tab’a jin abu makamancin wanda take ji a yanzu ba. Tafida ya shiga murza yastunsa akan nata yana kallon ta.

“Miriam look at me”.

Da ƙyar Maryam ta iya ɗauke idonta akan hannunta ta fora akansa, sai kuma ta kawar da nata idon, dan nasa sun mata tsauri da yawa, kwarjininsa ba zai bari ta ci gaba da kallonsa haka ba.

“Miriam na faɗa miki tun farko, i am monster, so me yasa kike damun kanki, tun tasowata ni a haka nake, haka na taso naga rayuwata, ban tab’a jin daɗin rayuwata na second ɗaya ba, komai baya min daɗi, sbd inayinsa ne yanda aljanin dake jikina ya sa ni, ba dan raɗin kaina ba, Wifey akwai wahala a rayuwata, i don’t wanna hurt you Miriam, i want keep you safe….”
Itade bata ce masa komai ba, har yanzu kallon hanunsa take wanda ke kan nata, kuma kalamansa ɗaya bayan ɗaya iska ke ɗurasu a kunnenta, ta ji kuma ta gane.

“Miriam i am sorry, ban so kika shigo cikin wannan rayuwar da nake ba, da ace an bar ni ni ɗaya da komai sai tafi sauƙi, amma an sakoki ciki kum…”

Kanta da yaga tana girgizawa yasa shi yin shiru, kafin ta ƙarfafi zuciyarta ta ɗago da kanta ta kalleshi.

“Kada ka tab’a tunanin cewa kana cutar da ni, dai-dai dana second ɗaya baka tab’ cutar dani ba Sultan (king), you now become my other half, Eshaan, Maryam Tijjani Muhammad can never ever live without you, you become part of my story, you are my savior, my hero, i can even call you my lifeline…”

Kuma tana kaiwa karshe ta janye hannunta daga nasa ta ɗauki jakarta ta buɗe ƙofar zata fita, ya yi sauri ya riƙo hannunta.

Kalamanta ne ke yayo a kwanyarsa, har yanzu bai kai ga fahimtarsu ba, yana buƙatar sharhi, wata ƙilama sai ya zauna yavyi nazarin word by word kafin ya fahimta.

Maryam ta saka masa kansa a tukunya, hannunta daya riƙo ya saka mata kuɗin daya saba bata kullum idan ya sauketa a matsayin kuɗin kashewa a makaranta, sannan a hankali ya janye hannunsa itama kuma bata jira komai ba ta fita daga motar.

Kuma ba ta yi nisa da tafiya ba ta hangi su Zara na shigowa, Allah ya temaka basu ganta ta fito daga motar Tafida ba.

Yana tsaye a wajen har ta ƙulewa ganinsa, hular kansa ya cire ya shafa sumarsa data fara taruwa sosai, sannan ya meda hular, ya kasa kama tunanin ɗaya ƙwaƙƙwar wanda ya kamata ace ya yi nazari akai, hular ya mayar kansa sannan ya tada motar yayi reverse ya bar wajen.

<< Yadda Kaddara Ta So 20Yadda Kaddara Ta So 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×