Skip to content
Part 27 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Shima sai yanzu yaga cewar ba ita kaɗai bace a falon, su uku ne, abinda yasa wayar tasa bata jima ba shine, me martaba ne ya kirashi, yake sanar masa da cewa Galadima bashi da lafiya, wai wani abu ya sameshi kamar junnu, yanzu haka ma sun Tafi india shida Fulani Sadiya da kuma Galadiman.

Addu’ar samun sauƙi yabyi masa sannan wayar tasu ta ƙare, ya ɗauko wani ƙaramin littafi da pen sbd yanaga kamar sunan nan da suka zab’a be dace ba, ya kamata ace sun ƙirƙiri wani sunan da ban, shine ya sauƙo yanzu. Cikin falon yaci gaba da takaowa yana faɗin.

“Baƙi muka yi ne ?”

Zara da Aisha waɗan da suka daskare a wajen suka kalli juna a tare, Tafida ne fa wannan a gabansu, Tafidan da a koda yaushe suke kwana da tunanin sa, yau shine tsaye a gabansu, kuma sune a cikin gidansa, bama wannan ba, ƙawarsu Maryam da a koda yaushe suke yawan mata hirar Tafida dan suna ganin cewa block ɗinsu ɗaya itace matarsa?, matarsa ta aure, Maryam fa ?.

Gaba ɗaya kuma sai kunyar Maryam ɗin ta kamasu, dan sun tuna yanda suke yawan maganganu akan mijinta, amma me yasa btaa taba faɗa musu ba?.

“Eh ƙawayena ne, wanda muke department ɗa ya”

Kusa da ita ya zauna.

“Sannun ku da zuwa”

Abu ɗaya yake yawo a tunanin su biyun, dama ance musu yana jin hausa, amma basu ɗauka har haka ba, duk da suna ganinsa cikin kayan hausawan, amma basu tabbatar ba sai yau.

“Ki kawo musu abin sha mana Miriam”

Kai ta gyaɗa masa sannan ta miƙe ta nufi kitchen, shima kuma sai ya miƙe yabi bayanta.

Zara da Aisha suka haɗa ido, kuma ba tare da suncewa juna komai ba, suka miƙe da sauri suka bar gidan.

Maryam ta gama jere drinks ɗin data ɗebo a fridge akan tray, sannan ta juyo ta kalli Tafida dake tsaye a bayanta.

“Kin gama ?”

Ta gyaɗa masa kai tana shirin wucewa, saida tazo wucewa ta gabansa taji sauƙar hannunsa akan kafaɗarta ya dafata, zuciyar Maryam tayi rawa kirjinta, ta ɗan ɗaga kai ta kalli fuskarsa, taga yanda yafita tsayi sosai, kamar tana tsaye a gaban wani dogon gini ne.

Tafiya suka fara shida ita a tare kamar wata ƙawarsa.

Mamakine ya kamasu sanda suka tarar da babu kowa a falon, abun yaso ya bata dariya, dan tasan guduwa suka yi.

“Ah-ah ina kuma baƙin suka shiga?”

Maryam tana riƙe dariya tace.

“Sun tafi”

“Sun tafi ?!”

Ya dawo mata da tambaya, ta gyaɗa masa kai tana cije lebenta na ƙasa dan ta hana dariyar dake neman kufce mata fitowa.

Lagos

Da misalin 11:20am

MARYAM POV.

Tsaye take a cikin kitchen, hannunta cikin wani silver bowl tana mulmula laddu, sai yanzu tunanin abinda ya faɗa mata ɗazu ya dawo mata, dan ɗazu sam bata samu damar yin tunani me kyau ba, sai yanzu kalaman ke dawo mata daki-daki.

“Miriam you make home inside of my heart, i wish that one day you will know what it feels like to make a home inside of someone’s heart, eventually i find that one person that understand the melody of my soul, and now you are sing it back with ease, and see, it’s beautiful….i find a women that can vulnerable with, while feeling completely safe, you mean everything to me Maryam, you complete me, tum mera aakhoka tara…”

Tunaninta ya datse sanda aka murɗa ƙofar kitchen ɗin, ta yi sauri ta kalli jikinta, babu hijabi a jikinta, daga ita sai ƙaramin mayafin abayar dake jikinta, kuma kafin ta yi wani yun ƙuri har ƙofar ta iyo ciki, wanda yake bayan ƙofar ya sako kai.

Kamar yanda itama take kallonsa shima ita yake kallo, kayan dake jikinsa ɗazu da zai fita sune har yanzu, wata baƙar hoodie ce, sai 3qtr ash color, har yanzu gashin kansa yan kan fuskarsa, bai meda shi baya ba, na bayan ma ya sauko masa kan wuya, kansa sanue da p-cap, amma bai cusata duka a kan nasa ba, ya ɗan dorata ne kaɗan, hakan yasa gashin nasa sauƙowa ta kasanta.

Ba yau ta fara ganinsa cikin kayan ba, dan ta tab’a ganin ya saka kayan, amma yau na daban ne, yanda gashin kan nasa ya sauƙo masa sai ya zama kamar wani yaro ɗan shekaru ashirin, idonta ya kai gefen fuskarsa, har yanzu wannan raunin da ya ji da ball jiya yana nan, amma kumburin ya sace kaɗan.

Duk da idonsa manne yake da baƙin glasses amma tasan cewa ita yake kallo, hannun ƙofar ya saki bayan ya rufeta, ya ƙarasa shigowa ciki, a kan Island ɗin ya aje ledojin hannunsa sannan muryarsa ta fito a hankali, kamar me tsoron kada wani yaji.

“An samu cow tail ɗin”

Maryam ta dakata daga mulmula laddu ɗin da take gaba ɗayi ta kalleshi, a sanda yake zama akan kujerar island ɗin.

“Kai ka siyo dama?”

Ta tambaya ne dan tasan ɗazu da ta faɗa masa cewa tana san cow tail David ya kira a waya ya faɗa masa suna buƙatar cow tail ɗin, kuma yanzu fitar da ya yi cabege yace ze je ya siyo.

Ya kai hannu yana ɗaukar laddu ɗaya daga cikin wanda ta gama mulmulawa ya na kaiwa bakinsa sannan ya girgiza kai.

“Nop, ba ni bane, David ne, na dawo daga siyan cabege ɗin na ganshi shima ya dawo, shine na karb’a”

Taci gaba da abinda take tana gyaɗa masa kai, yaci gaba da kallonta ta cikin glasses ɗin, ba kasafai yake ganinta ba hijabi ba, amma ko yaya ya ganta tana burgeshi, ya kasa kunne yana sabbaben nasa, kafin ransa ya raya masa da ya kamata ya bata abinda ya samo a cikin kayansa yau.

Miƙewa ya yi, kuma a lokacin idonsa ya kai kan takardun dake wajen, wanda da be lura da su ba, yana zagayawa inda take yake faɗin.

“Karatu kike ne ?”

Gabanta na dukan tara-tara ta gyaɗa masa kai, dan Allah ya sani bata iya jurewa abinda yake mata, karatun take sanyi amma ta kasa, abinda ya faru ɗazu ya hanata sukunin yin karatun.

“Mun ku…sa fara… exam ne…”

A ransa yace good, dan lokacin bikin holi ya kusa, baya so lokacin yazo basu yi hutun makaranta ba. Ƙafafunsa suka dakata a setinta, Maryam ta kalleshi ta gefen ido, tana haɗiye wani abu.

So take tace masa dan Allah ya matsa ko zata samu ta shaƙi iska me daɗi, dan wadda take shaka yanzu ta garwaye da ƙamshin turarensa, idan ya matsa ɗin ma wata kila zafin zazzab’in dake jikinta ya sauƙa, zazzabi ?, wata ƙilama a cikin kasusuwanta take jin zafin zazzab’in, babu akan fatarta, dan da ace akwai akan fatarta da yaji zafin, wata ƙilama ya lona masa hannu, dan Allah ne yasan irin zafin da take ji a jikinta.

Hannu yasa ya juyo da ita gaba ɗaya, kafin ya kalli hannayeta da suke da danƙwan sugar dana condensed milk, sai kuma ya kalli fuskarta, yana jin yanda zuciyarta ke tsere a kirjinta, be san meke damunta ba, amma duk sanda zai riƙeta yana jin yanda bugun zuciyar tata yake sauyawa.

Hannunsa na dama ya kai ya kewaye waist ɗinta tare da janyota gaba ɗaya cikin jikinsa, Maryam ta dunƙule yatsun hannunta tana rintse ido, wai meke damun bawan Allahn nan yau ?, shi fa da kansa yake cewa su nisanci juna, amma kuma shine yake mata haka?, wani ya temaka ya faɗa masa cewar ba zata iya ba, wallahi bazata iya ɗauka ba.

Ba ta yi aune ba taji ya zame mayafin data ɗaura a kanta, hakan yasa ta yi saurin buɗe idonta tana dubansa, gashin kan nata da babu ribbon ya sauƙo a gadon bayanta, har wani na sauƙowa a kafaɗarta, ya kai hannunsa yana kawarwa da gashin, kafin muryarsa ta fito can ƙasan maƙoshi.

“Yana damun ki ne ?”

Yadda kalaman suka fito akan fatar Maryam yasa ta kuma rintse idonta tana kawar da kai, wata ƙila za ta ji sauƙin abinda yake mata idan ta yi hakan.

A lokaci guda sai kuma ya saketa, ya saka hannunsa ɗaya a aljihun 3qtrn jikinsa na baya, ya fito da wani abu a hannun nasa.

Ya kai hannunsa duka biyu ya kamo gashin da suka sauƙo mata a kafaɗa daga ko wani b’an gare, ya kaisu baya, tareda saƙala hair pin ɗin da ya ɗauko a aljihun nasa.

“Haka zaki na masa, na Maa ne, ki kulamin da shi”

Ta gane miye na Maan, yana nufin hair pin ɗin,ta gyaɗa masa kai, tana ƙoƙarin juyawa, hannunta ya riƙo ya fisgota ta dawo jikinsa, yana jin yanda jikinta ke karkarwa, shi bai sani ba, wata ƙila tsoransa take ji, to in ba tsoronsa take ji ba me zaisa zuciyarta take irin wannan gudun ?, kuma har jikinta yana rawa haka?.

Fuskarta ya riƙo da duka hannayensa biyu, tare da kara tasa akan tata, yana kallon fuskarta ta cikin baƙin glashin idonsa, hancinsa a gefen nata, lebensa ma daf da nata.

Maryam taji kamar ya saki fitsari a wajen, kamar ta ƙwalla ƙara wata ƙila ta samu sauƙin abinda ke yawo a kanta, ina wannan mutumin yake so ya kaita ne?, wata ƙila zautata yake shirin yi.

Yana shirin haɗe tazarar dake tsakaninsu wayarsa ta yi ƙara, hakan yasa yaja kansa baya kaɗan yana kallon yanda ta ƙanƙame idonta, sai ya saketa ya ja da baya kafin ya juya ya zagayo inda wayar take ya ɗauka, domin kirane ɗaga india, abokinsa ne wanda suka yi karata ARJIT.

Maryam ta yi sauri ta juya masa baya, tana maida numfashi, kai kace gasar tsere ta shiga, ita a yanda take ji ma bata da maraba da wanda ya yi tseren, dan wani abu take ji yana mata yawo a jiki, wanda ba zata iya tantancewa sunan sa ba.

Ta godewa wannan wanda ya kira wayar yafi a ƙirga, dan ko ba komai ya dakatar da abibda yake shirin tafiya da iskar da take shaƙa.

Tana jinsa yana magana da harshen hindi, idan kaji yanda yake maganar ba zakace yasan wani yare ba wai shi hausa, cike da ƙearewa yake magana da na wayar, kuma a yanda take jin maganar tasa kamar yana cikin nishaɗi, duk da ita ba wani indiyanci take ji ba, sai ƴan kalmomin da ba’a rasa ba.

Hannunta ta daure ta wanke a sink, sannan ta daurewa zuciyarta ta juyo, tare da mata alkawarin bazama ta kalleshi ba, ta juyo ta dawo inda take a tsaye a da, ta mulmula curin laddu na karshe, sannan ta juyo zata dauƙo plate, sai ta tuna cewa tsayinta baya kaiwa wajen, dan haka ta kuma juyowa ta kalli inda yake, zuciyarta ɗaya, taga shima itan yake kallo, amma yanzu da idonsa yake kallonta, dan ya sauko da glasa ɗin kan hancinsa, yana kallonta ta saman glass ɗin, da ƙyar ta samu ta haɗiye wani abu, kafin tace.

“Side plate zaka ɗan ɗauko min”

Sai yata ya jingina da jikin kujerar da yake kai, ya ɗauki wayarsa da hannun dama, sannan ya yi amfani da hannunsa na hagu ya buɗe cabinet ɗin, ya fito da plates ɗin ya aje mata akan island, duk yana zaune daga inda yake, kuma yana danna wayarsa.

Ta kuma haɗiyewa wani abu, sannan ta ɗauki plates ɗin ta ƙara ɗauraye su, duk da tana da tabbacin a wanke suke, laddu ɗin ta saka masa akan plate ɗaya, ɗayan kuma ta aje shi a gefe, dan dama ɗaya take buƙata, ta gyara wajen tsaf, sannan ta ɗauki ledojin kayan da ya aje mata ɗazu, ta haɗa kan handout ɗinta.

Duka Tafida na zaune a wajen, yana danna wayarsa kamar ba ita yake kallo ba, bayan kuma ita yake kallon, kawai ya waske ne.

Maryam ta buɗe fridge ta ɗauko soymilk ɗin da ta haɗa, ya yi sanyi, ta ɗauko wata jar me starw ta zuba masa sannan tazo ta aje masa a gabansa tare da laddu ɗin.

Zata tafi ya dawo da ita ta hanyar jayo hannunta ya zaunar da ita a kujerar gefensa, zamansa ya gyara yana aje wayar akan island ɗin, a lokaci guda kuma yana kallon abinda ta aje masan.

“Miye wannan ? Ko kunun aya ne ?”

Kan Maryam a kasa ta girgiza shi.

“Ba kunun aya ba ne, soyamilk ne”

“Soymilk ?, ba kin yi awara da waken soyar ba”

A hankali ta dago ta kalleshi, sannan ta amsa masa da.

“Ba duka nayi awarar da shi ba, biyu na raba shi shine na haɗa wannan ɗin”

Ya riƙe jar ɗin a hannunsa, shi bai tab’a shan abun ba, amma yau zai gwada, bakinsa ya kai ya zuƙa sau ɗaya, amma saida ya yiwa abun babban gib’i, dan sosai na cikin jar ɗin ya ragu.

Mabambantan taste ne suka ziyarci harshensa, akwai garɗin madarar dake ciki, ga zaƙin sugar dana condensed milk, ga kwakwa a ciki, ga kuma ɗansanon shi kansa waken soyar ga sanyin abun, abun yana da daɗi, kuma ya burgeshi sosai, bai san cewa haka yake da daɗi ba ai, ƙara kaiwa bakinsa ya yi kan starw ɗin bai sauƙe ba saida yasha fiye da rabi.

Sannan ya aje jar ɗin, yanata santi a ransa shi ɗaya, kafin ya ja plate ɗin laddun, ya fara ci, daga inda yake yanzuma ya buɗe fridge ya dauki ruwa, saida Maryam taga haka sannan ta tuna da bata kawo masa ruwa ba.

“I am sorry Sultan, mantawa na yi ban baka ruwa ba”

“No Wifey, is not a big deal ai, amma pls ki dena cemin Sultan ɗin nan”

Girarta ta haɗe waje guda alamun mamaki ta furta “Me yasa ?”

Kansa tsaye ya amsata da.

“Saboda Sultan sarki ne, ni kuma ba sarki bane, ki nemo wani sunan da ban de”

“Amma kuma Sultan ɗin ya dace da kai”

Ya kai hannu ya cire p -cap ɗin kansa sannan ya kawar da sumarsa zuwa sama,

“Nop, ba na so, ni duk wata harka ta sarauta bana so, dokine kawai abinda nake so a tsarin sarauta, shi yasa nake hawa duk shekara ko kuma duk biki idan ya taso, amma ni ba na san rayuwa mara ƴanci, idana kana da sarauta baka da ƴanci, misali, idan kai mutumin gari ne zaka iya zuwa ka ci awara a kan hanya, sarki fa ?, babu shi babu wannan damar, ni kuma ina san irin wannan rayuwar, shi yasa nafi san rayuwar india fiye da ta nigeria, dan india muna yawan zuwa muci street food. So you better find another name”.

Maryam ta ci gaba da kallonsa, duk da shi ba ita yake kallo ba, wasu lokutan yana bata mamaki yadda yake hira sosai, bata tab’a auka cewar yanada magana haka ba, sai idan suna hira,wai awara?, wataƙila ma shine a ransa, dan ita ta yi jiya.

“Kinga, idan ke baki da idea ne sai na baki, kamar mi vida, mon prince, my boo, babe, pannah, yaar, jaan, piya, mehboob, my life line da dai sauransu”

Ya ƙarashe yana juyowa haɗi da tura sumar sa baya, Maryam ta girgiza kai

“Ai wanna basu dace da kai ba, wadan da suka dace da kai sai de kamar my little inflatable tube man, jack skeleton, hekter floor lamp…”

Sai kuma ta yi shiru tana shirin bushewa da dariya, ganin yadda Tafida ke kallonta ido waje.

“Nasan ni dogo ne, amma ai ban kai waɗanan abubuwan ba, tab! wa ya ga tube man!”

Maryam ta kwashe da dariya tana kawar da kai, shima murmushi ya mata, sannan yace.

“Gaakiya waɗanan basu yi ba, ki nemo wani dai”

Ta shanye dariyar tana gyara zama.

“Kaga kuwa a tictok na gani, sun ce idan ka faɗawa dogon saurayinka ze so sunayen, amma ga wani…”

“Banda na shirme fa!”

Ya katseta tun kan ta faɗi abinda ke bakinta.

“Ba na shirme bane, hermoso ? (handsome) ”

ya gyaɗa mata kai.

“Wato Spanish aka koma kenan ?”

Tana murmushi ta gyaɗa masa kai.

“Ya yi, amma da dai kin sauya min”

“Ok, ok, ok, ammm!, sundar ?(handsome)”

“Gwara-gwara dai, dan kinsan ni ina kishin yare na, na hindin yafi daɗi”

Ta gyaɗa masa kai kawai tana jan takardunta, tunda yanzu ta ɗan sake ya kamata ace ta yi ɗanyi karatun.

<< Yadda Kaddara Ta So 26Yadda Kaddara Ta So 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.