Skip to content
Part 34 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

MARYAM POV.

Sallayar da ta gama sallar asuba ta ninke, bayan ta idar da sallah tare da azkar ɗinta na safiya, ta saka sallayar a cikin bed side drawer, yau sauri ta ke, dan haka bata da time ɗin yin tilawa.

Ta shiga bathroom ta yi brush sannan ta fita zuwa ƙasa, store ta shiga ta ɗauko kayan da take amfani dasu wajen tsaftace gidan.

Sannan ta koma ɗakinta, banɗaiki ta fara wankewa, sannan ta share ɗakin tas, ta goge ko ina,, balcony ɗin ɗakin ta koma ta share shi shima, sannan ‘yan flowers ɗin nan nata ta yi musu bayi.

Daga nan kuma ta dawo corridor, ta shiga balcony ɗin corridorn, ta share shi, ta yiwa flowers ɗin wajen bayi, ta bawa akun nan abincinta sannan ta kashe neon light strip ɗin nan, tun da gari ya fara haske.

Baya nan corridorn ta soma sharewa, har zuwa kan stairs sannan ta share falo, ta gareshi tsaf, ta fesa air freshener, Daga nan sai ta koma kitchen, ta aje kayan sharar da zummar sai ta gama girkinta za ta share.

Store ta shiga inda ta zubo dankali a cikin wani ƙaramin basket, sai noodles guda huɗu data ɗauko.

Ta fito ta zubesu a kan island, ta shiga haɗa breakfast, jallof ɗin noodles ɗin ta yi, wadda ta saka mata smoked fish, ta kuma ƙawata ta da daffafen ƙwai.

Dankalin kuma ta dafa shi, sannan ta yayyanka shi ƙananu ta saka masa ɗanyan ƙwai da species, taruhu, albasa da kuma kayan ƙamshi, sannan ta soya shi a masa pan, ya tashi kamar masa.

Coconut and pineapple juice haɗa, duka ta ɗauko kayan da ta yi amfani dasu ta jeresu a cikin dishwasher kana ta kunnata. Kitchen ɗin ta share, ta kuma goge ko ina, ta ɗauki kayan sharar, Sannan ta fita zuwa ɗakinta, bayan ta aje kayan sharar a store.

Zuwa yanzu rana ta gama fitowa, kuma tana da tabbacin Fidar Yara ma ya dawo daga masallaci.

TAFIDA POV.

Yana zaune a ɗakinsa, ya ji sautin takunta tana tako stairs, dan haka ya miƙe ya buɗe ƙofar ɗakin nasa, a dai-dai lokacin da ta shigo corridorn ta tsaya tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta.

Wani ash ɗin hijabi ne a jikinta wanda ya sauƙa har ƙasa, be san me yasa ba amma har yanzu fuskarta akwai kumburi.

Maryam ta ɗan ƙarasa takowa tana ci gaba da kallonsa, Sanye yake da da wasu baƙaƙen jogger set, hannunsa na dama sanye cikin aljihun rigar hoodie ɗin, hular hoodie ɗin ta kwanta a bayansa, sumar kansa ta sauƙo ƙasa kamar kullum.

Hannunsa da baya cikin aljihun ya kai ya tura sumar baya, amma saida ta dawo kan goshin nasa.

“Ina kwana!”

Bai amsata ba, shima ya tako har zuwa gabanta, sannan ya kai hannu ya zare hijabin dake jikinta, yana kallon raunin dake kanta.

Maryam ta rintse idonta tana kawar da kanta gefe, Allah ya temaketa wata maxi dress ce a jikinta, yau da ta sha kunya, wai dan Allah me yake damunsa ne ? Itafa ya sauya mata gaba ɗaya, sai kace ba Tafida ba, yanzu waye zai yarda idan tace wannan kyakyawan jiya ya yi kissing ɗinta, ai sai dai ma a mata dariya.

Tafida ya kalli gashin kanta, Ta masa parking cikin ponytail, jelar da da take me ɗan tsayi tana reto a bayanta, ga wannan hair pin ɗin saƙale a gefen kan nata, idonsa ya zamo kan raunin dake gefen kan nata, ya kai hannu ya riƙe goshin ta ya jujjuya kan nata, sannan ya dawo ya duba na fuskarta.

A sannan ne kuma Maryam ta tambayi abinda ta kwana da shi jiya a ranta.

“Sundar!, wacece Heleen ?”

Ta lura kamar ya haɗiye wani abu, amma still be ce mata komai ba, sai da ya gama duba raunikan nata sannan da kansa ya mayar mata da hijabin.

Sai a sannan ya amsa gaisuwar da ta masa ɗazu.

“Lafiya, fatan kin tashi lafiya”

Itama sai bata ce komai ba, ta gyaɗa masa kai kawai, ta rab’a shi zata wuce, ya riƙo hannunta sannan ya dawo da ita gabansa yana kallonta.

“Heleen ?”

Bata ce masa komai ba, kanta sunkuye a ƙasa.

“Wata yarinya ce da bata da kamun kai bare sanin darajar kai, karuwa ce, mazinaciya, yar shaye-shaye, me kisa haka kuma yar daba. Shekaru biyu da suka wuce, aka kawota asibitinmu, sun yi faɗa da ‘yan wata ƙungiyar daba, sun harbeta, kuma ni ne na karb’eta a time ɗin, har aka sallameta ni ne nake kula da ita, Bata bar asibitin ba saida ta faɗa min cewa tana sona, a lokacin sai kawai na bita da kallon bata da hankali, wata ƙila ƙwayar da take afawa ta tab’a mata ƙwaƙwalwarta”

Sai ya yi shiru yana ɗaga kansa sama, sannan ya tura sumar kansa baya, sai kuma ya sauƙe kan nasa, duka Maryam na tsaye a gabansa tana kallonsa, sai yaci gaba.

“Tun daga lokacin ta shiga bibiyata, kuma a duk sanda zata zo wajen da nake bana ko kallanta bare na mata magana, a haka har muka shafe shekaru biyu, ita bata gajiya da bibiyata, ni kuma bana fasa manna mata(Shariya). Sanda akayi auren mu bata gari, ta aiko a faɗa min wai ta tafi abuja, bata dawo ba sai a satin nan, khabir shine ya faɗa mata cewar na yi aure, shashancin dake cikin kanta ya faɗa mata cewar tazo ta kasheki, tunda kin ƙwace mata Tafida”

Yanzun ma shirun ya yi, ya ƙifta idon yana kamo hannun Maryam na dama.

“Bata sanni ba gaskiya, shekaru biyun da ta yi ta bibiyata a banza suke, tunda har bata san waye ni ba, Miriam idan har ina san abu, to rayuwatama zan iya sadaukarwa a kansa, in har ina numfashi koda inuwarsa bazan bari a rab’a ba, zan tsaya na bashi kariya duk wuya duk daɗi, idan har kuma wani ya samu damar cutar dashi…”

Ya tsaya kallon Maryam na ‘yan sakkanni, sannan ya murza hannunta, ya ɗora hannun na dama kan kuncinta, Maryam ta lumshe ido sannan ta buɗe, tana zuba fararen idanuwanta a kansa.

“Bazan bar mutum ba, hakace ta kasance da Heleen, da ace ni ta cutar, ba lalle ne ma na kalleta ba, amma kuma sai ta cutar min dake, ke ɗin da bana jin zan iya yafewa koda kaina ne ya cutar dake, koda nine na cutar dake Miriam bazan tab’a barin hakan ba”.

“Me ka mata ?”

“Jiya kinsha maganinki ?”

A maimakon ya amsa mata tambayarta ta sai ya mata wata tambayar, yana motsa babban ɗan yatsansa a kan kuncinta, ta gyaɗa masa kai, wata ƙila ya manta ne, amma shi da kansa ya bata maganin, ko kuma de kawai yana san a bar zancen ne.

“Ka je ka yi wanka, na gama abin kari”

Sai ya gyaɗa mata kai, sannan ya sumbaci goshinta, ya barta tsaye a wajen ya shiga ɗakinsa, Maryam ta yi murmushi idonta a lumshe.

Da misalin 04:00

Maryam ce tsaye a cikin ironing room ɗin gidan, kayan da ta wanke jiya take gogewa, earpiece ne saƙale a kunnenta tana waya da Anti Fati.

Kafin daga bisani su ka yi sallama, ta meda himma wajen yin gugarta ta. Sanda ta gama ta ɗebe kayan ta yi sama da su, ɗakin Tafida ta fara shiga, ta buɗe wardrobe ɗinsa, ta samu wurin da babu kaya ta saka masa a wajen.

Sannan ta ɗebi nata ta shiga ɗakinta ta saka nata ma a cikin wardrobe kafin ta fito waje, ta shiga balcony ɗin corridor, ta yi zamanta a kan lilon nan, tana yiwa akun nan magana.

Kafin ta buɗe wayarta ta shiga Tiktok, tun jiya take ta dubawa, dan tana jiran shigowar saƙon Badar, Aikuwa tana shiga wurin message ta ga saƙon nata, hannunta har rawa yake ta shiga ta buɗe, lambar Badar ɗin ce.

Ta kwafe lambar, sannan ta si yi credit daga account ɗinta na banki, dan bata da kati sosai, kafin ta aika mata kira.

“Allah sarki ƙauna, wallahi na yi kewarki”

Shine abinda ta fafi bayan ta amsa sallamar Badar ɗin. Tana iya jiyo dariyar Badar ɗin kafin ta ji tace.

“Madam Tafida, nima ina kewarki”

“Anti Fatice ke faɗa min wai an miki satar waya”

“Wallahi, kede rabu da mutane ‘yan neman jafa’i, Samsung ɗina saida aka raba ni da ita”

Maryam ta yi dariya, dan tsaf ta tuna yanda Badar ɗin ke matuƙar san Samsung ɗin tata.

“To yanzu wacce kika koma ?”

“Iphone!”

“Ke dan Allah?!”

“Wallahi nake faɗa miki, Aliyu ne ya dalleni da ita”

“To ya su Mama ?”

“Wallahi su Mama lafiyarsu ƙalau”

“Ke yanzu wacce gareki ?, kinsan ku matan manya, ai naga hannunki ma yanda ya yi fari, nasan fuskar kima ta yi farin”

Maryam ta yi dariya.

“A’a ni babu wani fari da na yi, Samsung na koma wallahi”

Tana iya jiyo shewar Badar ɗin, kuma itama ta faɗi ne kawai, ba dan bata san cewa ba ta yi farin ba, itama da kanta ta san cewa ta yi farin, ta kuma sauya.

“A hayye!, kinga fa matan manyan da nake magana!, ke wai tsayama, injide an ɗauko mana ƙaramin Tafida”

Maryam ta yi tsaki.

“Badar bana san iskanci Allah!”

Badar ta saki dariya.

“Ai dama na sani, kin koma makaranta ne?”

Maryam ta gyaɗa kai kamar Badar ɗin na ganinta.

“Na koma wallahi, kinsan a estate muke, to ta estate ɗin ya sakani, ke fa?!”

Badar ta kuma yin dariya, tana tuna sanda take yawan damun Maryam ɗin da zancen Tafida, tana ce mata bata so, yanzu de sai gata a matsayin matarsa. Ikon Allah kenan.

“Na koma, amma ni university ma na fara……”

Haka suka yi ta hira, kafin Maryam ta katse hirar domin ganin kamar magariba na shirin yi, gashi bata dafa komai ba.

Kitchen ta koma sannan ta shiga kiciniyar shirya abincin dare.

TAFIDA POV.

“Khab ?”

(Yaushe ?)

Muryarsa ta tambaya, yayin da kunnensa na dama ke kare da wayarsa, tsaye yake a ƙofar balcony ɗin shiga falo, yayin da yake waya da Arjit abokinsa.

“Teen saptah!!”

(sati uku!!)

Muaryar Arijit ɗin ta bashi amsa da ga cikin wayar, abubuwa da yawa sun zo masa lokaci ɗaya, Bikin holi, Gasar world cup da za’ayi na cricket, sannan bikin abokinsu Mahesh, sannan duka wuraren a india suka, amma a mabanbanta wurare, Bikin holi da ya yiwa Daadi alƙawari mumbai ne, gasar world cup Ahmadabad (Amdavad), yayinda bikin Mahesh ɗin zai kasance a garin Delhi.

Sauƙinsa ɗaya su Maryam sun fara exam, dan bazai iya tafiya babu ita ba, kuma gashin kansa ya dameshi, yana so ya rabu da shi.

Kansa ya ɗaga sama sannan ya furzar da iskar dake bakinsa.

“Kana ji ko Arjit, kawai kuyi magana da su Ranvir (sauran abokansu), ku shirya abinda ya dace, sai na fara zuwa mumbai, sannan zanje Ahmadabad, bayan nan sai na ƙaraso delhin, kuma zan yi magana da Mahesh ɗin”

Cikin harshen hindi ya yi maganar, yayin da a ɗayan b’angaren Arjit yace.

“Theek hai, tum hara biwi kaha par hai ? (ok!, ina matar ka?)”

Tafida ya yi murmushi.

“Tana lafiya, tare zamu taho da ita ai, zaka ganta!”

“Mema kace sunan ta ?”

“Maryam”

“Haan Maryam”

(Ƙwarai Maryam)

“Kana ji ko, sai mun yi waya, zuwa anjima ko gobe zan kira Mahesh ɗin, kuma zan kira Amit ma”

“Ok bye”

“Bye!”

Ya sauƙe wayar tare da ɗaukowa ƙaramar keypad ɗin da ya siya jiya, ya tura saƙo sannan ya meda ta cikin aljihun nasa, ya sa hannu ya tura ƙofar sannan ya shiga da sallama.

Babu kowa a falon, kuma dama yasan ba lalle ya sameta a falon ba, dan kullum i yanzu tana kitchen, sai kawai ya haye sama, yaje ya yi wanka ya sauya kaya.

Sannan ya dawo ƙasa, kansa tsaye ya wuce kitchen, jingina ya yi da jikin ƙofar bayan da ya buɗe, da alama bama tasan ya shigo ba, ƙarar hand mixern data kunna shine ya cika kitchen ɗin.

Sanye take da wata doguwar riga ta atamfa, me sauƙin ɗinki, bisa ga dukkan alamu baza ta yi nauyi ba, yau bata saka hijabi ba, amma akwai ɗankwali a kanta, shi ma kuma ba wani ɗauri me wahala ta masa ba, ka wai ta ɗan turoshi gaba ne, kamar ture kaga tsiya, yaginda jelar gashin kanta ke reto a bayanta.

Koda Maryam taga kamar lokaci zai ƙure, sai kawai ta dafa farar doya, ta mata egg sauce, dan kamar ta na ga itace zata fi mata saurin dafawa, ko da ta gama sai ta ga tana da sauran lokaci, dan haka kawai sai ta juye komai a cikin warmer.

Ta shiga haɗa cake parfait, tana cikin mixing whipping cream da condensed milk da handa mixer ta ji hannayensa sun kewaye waist ɗinta, kafin ƙamshinsa ya shiga hancinta, kansa ya sauƙa a kan kafaɗarta ta dama.

Hand mixer ɗince ta faɗa cikin bowl ɗin, sbd sakinta da ta yi a bazata, ta ji kamar iska bata isa huhunta da kyau, komai dake aiki a cikin kanta ya tsaya cak, sakamakon wuyanta da ya sumbata.

Ɗip! Wuta ta ɗauke a kan Maryam, ya Allahu ya rahamanu!, ina wannan bawa na ka yake san kai ta?, ta ayyana hakan a zuciyarta.

“Barka da aiki, Daaso”

Da ƙyar Maryam ta haɗiye yawu, sannan ta lalubo muryarta a maƙoshinta ta amsa masa da.

“Humm….humm..hummm!”

Tana jin sautin murmushin sa a kan wuyanta, a hankali ya juyo da ita ta fuskance shi, sannan ya saka hannunsa ya cire dankwalin kanta, ya janye ribbon ɗin ma, gashin ya baje a bayanta, sannan wannan hair pin ɗin ma ya sauƙo, cirowa hair pin ɗin ya yi, ya saƙala mata shi a gefen gashin.

“Ya kike ?”

Sai yanzu ta iya ɗagowa da kanta ta kalleshi, gashin kansa a jiƙe yake, ya saumo masa kan goshi, amma duk da haka tana ganin idonsa da suka fara sauya kala, dan a hankali ƙwayar take rikiɗewa zuwa ja.

“B…Baka d..da lafiya ne”

Girarsa ta tattare waje guda alamun kokwanto.

“Me ki ka ga ?”

“Idonka na sauya kala”

Sai ta ga ya yi murmushi.

“Mantawa ki ke da mijinki monster ne ?, that’s common Wifey”

Maryam ta haɗiye yawu, sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa, shaf ta mance da waye shi, waɗanan abubuwan da yake mata sune suke mantar da ita komai, ciki kuwa har da nisantar juna da ya ce su yi.

Hannunta ya ja ya zaunar da ita a kan kujerar island, shima ya zauna a ta gefenta.

Juyawa ya yi ya kalli inda ta aje mixer da kayan da take haɗa cake parfait, ya motsa hannunsa a setin kayan, mixer ɗin ta tashi daga cikin bowl ɗin, ya ajeta a cikin sink, sannan ya ɗebo kayan ya aje su a kan island.

Maryam tana kallon abinda yake, shi da kansa ya haɗa parfait ɗin, kuma ba tare da ya tab’a koda abu ɗaya da hannunsa ba.

A sanda ya kammala haɗawa a lokacin aka kira Sallar magariba, shi da kansa ya miƙe ya buɗe dishwasher ya fito da kayan dake ciki, sannan ya saka wanda suka b’aci, ya kunna ta.

Waɗan ya fitar ɗin ɗaya bayan ɗaya yabi cabinet ya jere su.

Har yanzu da wannan power natural ɗin yake amfani, juyowa ya yi inda Maryam ke zaune, ya rike fuskarta da hannayensa.

“Ba ki da lafiya, kina buƙatar hutu, hmmm ?”

Sai kawai ta gyaɗa masa kai, dan bakinta ba zai iya cewa komai ba, goshinta ya sumabata, sannan ya saki fuskar tata yana ja da baya da baya har ya fice.

Maryam ta sauƙe wani nauyayyen numfashi, ta kai hannu ta janyo ɗankwalinta ta ɗaura, sannan ta miƙe ta fice daga kitchen.

<< Yadda Kaddara Ta So 33Yadda Kaddara Ta So 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.