Skip to content
Part 37 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Dan haka ta ɗauki basket ɗin, tana kashe fitilun kitchen din, ta fito ta kashe ta falon ma, sannan ta fita.

Shiɗin ne kuwa, yana zaune cikin mota yana jiranta, ganinta riƙe da kaya yasa ya fito zai karb’a amma sai tace.

“No Devid, ka barshi kawai”

Ta zagaya gidan baya ta buɗe, ta saka basket ɗin, sannan itama ta shiga. Devid ya tayar da mota yana fita daga gidan.

“Ina zamuje Madam”

“St Nicholas Hospital”

Mamaki ya ɗan kama shi kaɗan, amma de bai ce komai ba har suka isa.

Shi ta tambaya ya faɗa mata a inda office ɗin Eshaan yake.

Tana fitowa daga elevator suka haɗu da wannan Dr. Abubakar ɗin, suka gaisa a mutunci kafin yace.

“Wajen Dr. ki ka zo ko ?”

Maryam ta gyaɗa masa kai, yo idan ba wurinsa ta zo ba, wurin zata zo ?

“Ai suna meeting ne, nima can zanje yanzu haka, amma ga office ɗinsa can, ki je ki jira shi a ciki… Joke zo ki karb’a mata kayan nata, ki kai mata office ɗin Dr. Eshaan”

Ya ƙarashe yana magana da wata nurse, Kamar Maryam zata cewa nurse ɗin ta bari kawai zata iya ɗaukan kayanta, amma kuma karamcin da Dr. Abubakar ya mata yasa bata ce komai ba, ta miƙa mata kayan sannan ta bita a baya har zuwa office ɗin, a kan wani coffee table Joke ta aje basket ɗin, sannan ta fita.

Tana fita ta haɗu da wata ƙawarta suka tafa tana faɗin.

“Yau kuma mutumin naki, wata macace ta zo nemansa”

Ƙawar tata ta kama baki.

“Ke matarsa ce fa, ai sanda kika ta fi gida ya kawota nan bata da lafiya”

“Ke dan Allah?, yanzu kaf matan ƙasartasu, ya rasa wacca zai aura sai wannan ?”

Ƙawar ta tab’e baki.

“Su suka jiyo dai”.

TAFIDA POV.

A hankali ya turo ƙofar office ɗin nasa, sannan ya shigo, mutum ya gani tsaye a balcony, kuma ko daga bayanta da ya gani, ya ganeta, sai ya yi murmushi, wato da tace masa zata fita nan zata zo kenan?.

Lap cort ɗinsa ya saƙala a jikin hook, sannan ya cire hular kansa. Ya shiga takawa a hankali ta yanda baza ta ji takunsa ba.

Bayan da nurse joke ta fice ta bar Maryam, sai ta shiga bin office ɗin da kallo, kafin ta zauna a kan wata sofa, data gaji ma da zaman sai ta fita balcony ɗin office ɗin, ta tsaya a wurin tana kallon dogayen gine-ginen dake wajen, babu wata iska sosai a wajen, amma kuma view ɗin yana da kyan gani.

Bata ankara ba ta ji hannaye sun kewayeta daga baya, cak!, iska ta ɗauke a maƙoshinta, kansa ya sako ta kafaɗarta, sannan kamshinsa ya ziyarci hancinta.

Kuma dama tasan babu me mata haka sai shi, hancinsa ya shiga goga mata a gefen kuncinta.

“Barka da zuwa matar mijinta”.

Cikin raɗa ya mata maganar, Maryam ta ƙanƙame hijabinta da hannunta ke kai, wannan abun data saba ji yana yawatawa a kan fatar ta.

A hankali Tafida ya saketa, yana motsa kunnensa dan ya saurari abinda yake kewa a kullum idan basa tare, juyowa da ita ya yi ta fuskance shi.

“Ziyara ki ka kawo min?”

Maryam ta gyaɗa kanta, a lokaci guda kuma ta girgiza shi, Tafida ya yi murmushi me sauti.

“To kenan me ya kawo ki nan, ko allura ki ke so a miki, ai raunin naki ma ya warke”.

Hannunta ta ɗora a kan nasa da ke shafa fuskarta da shi sannan ta zame hannun nasa tana matsawa baya.

“Abinci na kawo maka”.

Tafida ya ƙara matsa kusa da ita yana kama fuskarta.

“Allah ya miki albarka, Dasso”

Ya ƙarashe yana sumbatar kanta, Maryam ta ƙara ture hannunsa.

“Abincin zai huce, muje kaci”

Ta faɗi tana dawo wa cikin office ɗin.

Bayanta ya biyo ya zauna a kan sofa yana kallonta, plate ta ɗauko a cikin basket ɗin, ta zuba masa dambun tana faɗin.

“Dambu na maka, amma ba zogale na saka ba, alayahu ne”

“Me yasa baki saka zogalen ba?”

Ta saka masa spoon a ciki tana miƙa masa.

“Babu mana, shi yasa ban saka ba, kuma ban san inda zan samu ba”

Ya karb’a yana ‘yar dariya.

“Akwai bishiyar zogale a garden fa”

Ta ɗan tsaya, sannan ta ci gaba da zuba masa kunun aya a cikin glasa cup.

“Ban sani ba, kuma banma tab’a gani ba”

“Ni da kaina na shuka shi”

Ta gyaɗa kanta tana zama.

“Akwai chicken kibab, kana so?”

Ya miƙo mata plate ɗin yana faɗin.

“Me zai fito daga hannun ki nace bana so?”

Ta ɗan yi murmushi tana buɗe warmer ɗin chicken kibab, ta saka masa guda uku.

“Ke ba zaki ci ba?”

“Zan ci mana”

“Ok zo muci”

Sai ta miƙe ta dawo kusa da shi ta zauna, a kan cinyarta ya ɗora mata plate ɗin, sannan ya dunkule hannunsa na dama, ya buɗe, wata rose ce ta bayyana a hannun nasa, Maryam ta saki baki tana kallonsa, yanzu lamarin Eshaan ya dena bata mamaki.

“Abar ƙauna, ga tukwicinki”

Maryam ta kai hannu ta ɗauki rose ɗin.

“To mu ci”.

A tare suka ci abincin, bayan sun gama Maryam ta shiga haɗa kayan a cikin basket.

“Zan koma”

Tafida ya ɗan kalleta kaɗan, sannan ya mike.

“Ina zuwa”

Wata ‘yar ƙaramar chest drawer ya buɗe, ya ɗauki wasu kaya, sannan ya shiga bathroom, Maryam na zaune tana jiran fitowarsa.

Jim kaɗan sai gashi ya fito, ya sauya kayan jikinsa zuwa ƙananu, wata ash T-shirt ce a jikin nasa, wadda ya ɗora mata baƙar hoodie a kai, sai track trouser fari.

Sumar kansa kwance a baya, duk da ta yi tsayi sosai.

“Taso muje ?”

Ya miƙa mata hannu, Maryam ta miƙe tana kallon hannun nasa kamar me shawarar kar ta riƙe.

“Ina ?”

“Chilling za muje”

Maryam ta yi dariya, wai chilling, ganin bazata kama hannun nasa ba yasa shi ya kamo nata da kansa, sannan ya fara janta zuwa ƙofa.

“Basket ɗin fa ?”

“Devid zai kawo miki”

Haka ta bi bayansa hannunta cikin nasa, duk inda suka ratsa a asibitin kallonsu ake, gaba ɗaya Maryam tabi ta takura, so take ya saki hannunta, amma yaƙi saki.

Da haka har suka sauƙa floor ɗin farko, a nan suka haɗu da Devid.

“Akwai basket a office, ka ɗauka ks kai mana gida”

Devid ya amsa masa, kuma daga haka suka fita farfajiyar asibitin, Maryam taga sun nufi gate gadan-gadan, da ƙyar ta samu ta zame hannunta daga nasa.

“Dr. Ina zuwa ne ?”

Suka ɗan dakata daga tafiyar, daga ita har shi suka kalli Dr. Damilola.

“Chilling zamu je”

Dr. Damilola ya yi dariya.

“Kuma a ƙafa zaku tafi ?”

Cikin pegin English ya yi maganar.

“A’a blue rail line zamu hau”

“To a dawo lafiya”

Tafida ya amsa suna ci gaba da tafiya.

Bakin titi suka fita, sannan suka hau Taxi, wadda ta sauƙe su a Marine station, wato tashar da ake hawa blue rail line, sabon jirgin ƙasa me yawo unguwa unguwa.

Tafida ya siya musu cowry card guda biyu, wato katin da ake amfani da shi wajen hawa jirgin, kamar tiket.

Daga haka kuma suka shiga jirgin, inda suka yi sa’a suka samu wajen zama.

Maryam ta shiga bin wajen da kallo.

“Wai ina zamuje ne ?”

“Chilling!”

Yanzun ma Dariya ta yi, ita idan ya faɗi kalmar ma har dariya ta ke bata.

“Ina nufin inda zamuje chilling ɗin”

Sai ya gyara zamansa, ya fito da hannunsa daga cikin aljihun hoodie ɗin jikinsa, ya tura sumar kansa baya sannan ya shiga lissafo mata inda zasu je.

“Farko Zamu fara zuwa siyyaya, daga nan sai muje jara beach, sai nike art gallery, sai Nok by Alara, za muje National museum of Lagos, sai lufasi nature park, sai mu koma gida”

Maryam ta rage girman idonta tana kallonsa, to duk yaushe ya tsara wannan ita bata sani ba?, ko a iyaka wannan zuwan nata ya shirya zuwa wajen.

A national theatre suka sauƙa. Bayan sun fito suƙa, suka hauTaxi zuwa wani mall da ake seda kayan indians na sakawa.

“Kaya zaka siya ?”

Maryam ta tambaya yayin da Tafida ya buɗe mata ƙofar shiga mall ɗin. Sai da ta shiga sannan shima ya shigo.

“Ke de, ai ni inada kayan sakawa, baki gansu a wardrobe ɗina ba ?”

“Ni kuma? Me zan yi da kaya ?”

Ta yi tambayar ba tare da ta san sanda ta furtata ba, sai kawa ya tsaya da tafiyar da yake, Maryam ta ci gaba da kallonsa tana jiran amsa, sai taga ya gyaɗa mata kai.

“Idan ina nigeria bana saka kayan india, duk da ko a indian ma ba saka su nake ba sai idan ana biki ko wani shagalin, amma ina martaba al’aduna duka biyu, idan ina nigeria ko hindi bana yi, zan saka kayan hausawa, naci abincinsu na yi komai kalar nasu, idan kuma naje india bana komai na hausawa, bana saka kayan hausawa, bana magana da hausa, bare naci abincin su, zan yi komai kamar ba’indiye, Na karb’i al’aduna duka biyu, dan haka kema hakan za ki yi, za ki je ƙasarmu sai ki saka kaya irin na matan ƙasar mu”

Maryam ta haɗiye wani abu, ita fa ba zata iya naɗa wannan saree ɗin ba, ba sanin yanda ake ɗaurashi ta yi ba, kuma ma ai ita be kamata ta saka saree ba, sbd rigarsa ta yi gajarta.

“Nifa bana san saree”

“Eh akwai wasu kayan ai, ba saree bane kawai kayan matan india, akwai chickankari da kuke cewa Pakistan, akwai lehenga wato riga da skirt da mayafi, akwai kurti na mata, sai ki zab’i wanda kike so…”

“ Excuse me please”

Muryar wata mata ta faɗi tana kallon Tafida da ya tare mata hanya, Tafida ya matsa matar ta wuce, ya dawo ya kamo hannun Maryam.

“Muje ko ?”

Ta zame hannun nata daga nasa, sannan suka ƙarasa shiga ciki, Maryam ta ga yana gaisawa da ma’aikatan wurin, da harshen hindi, bisa ga dukkan alamu dai sun saba.

“Ye mere biwi hai bhai”

(Wannan matata ce ɗan uwa)

Mutumin da ke tsalleken wani teburi da ya raba tsakaninsu da shi ya kalli Maryam.

“Ai naga ‘yar nigeria ce”

Mutumin ya faɗi cikin wani irin turanci, da Maryam a film kawai take iya jinsa, turanci indiyawa, wanda suke fitar da ‘R’ da kuma ‘T’, Maryam ta kusa tintsirewa da dariya, amma sai dariyar tata tab’ata, a sanda Tafida yake amsa shima, kuma cikin irin turancin nasa.

“Eh ‘yar garinmi ce ai”

Wato shima ya iya kenan ?, to amma me yasa idan zai mata magana baya mata da irin wannan?. Maryam bata ce komai ba ta bishi da kallo kawai.

“Sunansa Vellamkonda, ɗan telugu ne, yana jin hindi amma baya iya mayarwa”

Yanzu ma bata ce komai ba, sai shima ya jiya ya kalli Vellamkonda.

“Chickankari muke so…… Ko kina san Lehenga ?”

Ya ƙarashe yana tambayarta, ita bata wani san lehenga ba, chickankari ɗinma ba dan ya faɗa mata ba da bata sani ba, kawai sai tace.

“A’a chickankari ɗin kawai”

Sai ya gyaɗa kansa yana juyawa wajen vellamkonda.

“Chikankari kawai”

“Size ɗinta fa?”

“Sai de ta gwada…”

Kusan guda ashirin ya siya mata, kuma kowanne saida ta gwada a jikinta, daga masu plane yadi sai masu ado.

Bayan sun fito daga mall ɗin suka shiga yawo a gari, duk inda ya lissafa babu inda suka tsallake, sai da suka je ɗin.

Ba su su ka dawo Alaro city ba sai bayan isha, sallalon magriba dana ishar ma a masallaci su ka yi, A ƙofar block ɗin su taxi ta sauƙe su.

Tafida ya fito daga cikin motar hannunsa riƙe da ledojin kayan da suka siyo, dan ko ɗaya bai bari Maryam ta ɗauka ba.

Unguwar tsit, babu kowa sai yan jifa-jifan mutane, duk da dare ne amma ko ina haske dau.

“Gobe zanje saloon”

Tafida ya ɗan juyo ya kalleta

“Duka ki bari sai munje can sai a miki”

Bata ƙara cewa komai ba, dan bata ga amfanin maganar ba, tunda ya riga yace haka ai shike nan.

Ji ta yi yana rera waƙa a hakali yana ɗan kaɗa kansa.

Ta juya ta kalle shi, kode bashi da lafi ?, yo in ba mara lafiya ba waye zai dinga rawa babu kiɗa ?.

Sai de kuma tunaninta ya wargaje, sanda suka shawo kwanar gidansu, ta ji sak waƙar da yake rerawa tana tashi daga wani gida a hankali, ta san gidan dama samari ne a ciki, wata ƙila sune suka kunna.

What if i say?

i know, you know

What if i told you i liked you?

We stay, we go what if i like you?

Iko sai Allah, wato tun daga can yake iya jiyo waƙar dake tashi a nan, waƙar da ba dan ma dare ne ba, da baza ta yi volume haka ba, dan a hankali take tashi.

“Ba  abinci naci”

Muryar Tafida ta faɗa, a sanda suka koma gida, har ta shiga ɗakinta ta yi wanka, kuma bayan ta gama ne ta fito ta same shi zaune a wurin, shima ya sauya kaya, ga gashin kansa dake a jike.

Mamaki take wai yaushe ma suka ci aninci ?, a Nok by Alara ma saida suka ci abinci, amma yace yunwa yake ji yanzu ?, ita kam wata ƙila ko gobe da safe ballale ta ci wani abu ba, dan ta ƙoshi sosai.

Ta gyaɗa masa kai tana zama a kusa da shi, ta ja ladojin da suka yi siyyaya, ta ɗauki wadda aka saka musu abincin da suka yi take a way a Nok by Alara.

Ta ɗauko take a way ɗaya ta bashi, ya karb’a sannan ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗauko masa ruwa da kunun aya.

“Ke ba za ki ci ba ?”

Maryam ta girgiza kai.

“Na ƙoshi”

Sai ya gyaɗa mata kai yana ci gaba da cin abincinsa.

Maryam ta shiga fitar da da kayan da suka siyo, tana ta yaba kyan kayan, ai gwara chickankari ɗin, me za ta wani yi da saree.

Hello!, tafiya india fa ta kankama

Da misalin 02:40am

Maryam na kwance a ɗakinta, ta shiga jin gurnanin da fisge-fisge, ga ƙarar abubuwa na fashewa, ba shiri ta miƙe zaune a kan gadon, dan baccin da take ji ta neme shi ta rasa.

Gurnanin Tafida take ji, da ƙarar da ya ke, kamar yanda ya saba a duk sanda abun nasa ya tashi, ita kam har ga Allah ta gaji, ta gaji da ganinsa cikin wannan halin.

Bata da wata dabara, sai kawai ta miƙe ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, ta zo ta tayar da sallah, tana yi ta na ta zuba masa Addu’a, dan bata jin zata iya wani abu bayanta.

<< Yadda Kaddara Ta So 36Yadda Kaddara Ta So 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.