“Meema Even Center za ka kai mu.”
Muryar Anti Fati ta faɗi bayan sun fito daga gidan sun tsaya a bakin titi, sannan suka tsaida me napep.
“Ku shiga muje to”
Anti Fati ta juyo tana kallon Maryam wadda ke tsaye a bayanta sai gyara zaman gyalen dake jikinta take, ita jinta take kamar tsirara, gaba dayanta a takure take dan bata saba ba.
“Muje”
Tana ta jajjan mayafin daga baya ta shiga adaidaitar, ta kar6i Imran daga hannun Anti Fati, sai waige-waige take kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.
Da haka suka isa katafaren sabon event center din. . .