Skip to content
Part 16 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

FASAHA HAIMANIYYA , VOLUME 2

‘Yan Yara

Assalam Alaikum

Ku ‘yan yara

Assalam Alaikum

Ku ‘yan yara.

*****

Ku gaida babanku

Ku ‘yan yara

Ku gaida maman ku

Idan kuka farka.

*****

Za ku samu kifi

A cikin faranti

Za ku samu kifi

In kun kai haka.

*****

Karku raina kowa

Karku zagi kowa

In kuka raina wani

Za ku shiga wuta.

*****

Ku ɗauki halin girma

Ku zama masu hikima

Kar ku yi lalaci

In kuka girma.

*****

Ku so junanku

Har da ‘yan uwanku

Kar ku raba kanku

In kuka girma.

*****

Ku zamo masu tarbiyya

Ku dinga yin biyayya

Kar ku yi ƙiyayya

Idan kuka girma.

*****

Allahu ya shirya ku

Ya gyara rayuwarku

Yasa ku zama Zakaru

In kuka girma.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 15Fasaha Haimaniyya 17 >>

1 thought on “Fasaha Haimaniyya 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×