Skip to content
Part 10 of 30 in the Series Yar Karuwa by Harira Salihu Isah

Sai can tsakiyan dare sannan Bunayd ya shafa addu’ansa ya kwanta, ba jimawa bacci ya yi awun gaba da shi.

*****

Ni kuwa Banafsha ina son zuwa wajan Umaima, amma na haƙura na kama kai na, dan tunda naga motan ya Danish gabana ya faɗi, yanzu ko hanya banason haɗawa da shi, saboda ni ba zan iya haƙura da faɗa masa magana ba, shi kuma nasan ba zai fasa ci mini mutunci ba.

Wankan juma’a muka yi ni da Mamina dukanmu, idan ka kallemu ka ɗauka ba uwa da ƴa bace, kaman yaya da ƙanwa haka muke, muna zaune Mamina na mini photo da wayanta sai ga Alhaji ya dawo, duk sannu da dawowa muka masa, ya amsa tare da miƙo mini ledan staraban juma’a, sai bayan Alhaji ya huta sannan ya ƙira ni, zuwa nayi na zauna cikin ladabi, duk da banson alaƙan Alhaji Mukhtar da Mamina, amma ya zama dole a gareni yin biyayya, dole ne a ce da mijin iya baba, yana kula da ni yana ɗawainiya da ni kaman ƴar cikinsa, kalmansa na ɗazu da ya ce shi angon Mamina ne da yardan Allah sai ya sa stanansa da nake ya ɗan ragu, yanzu ba abinda ya rage mini sai dagewa wajan ganin Mamina ta yarda da maganan auren, tunda na ga alaman ita ce bata so.

Alhaji hankalinsa ya mayar kai na ya ce, “Banafsha a bani labarin yanda musabaƙan ta gudana.”

Kai na a ƙasa na fara zayyanowa Alhaji komai yanda aka yi, da matuƙar farinciki ya ce, “ke ɗin ce dai kika zo ta ɗaya?”

Jinjina kai nayi alaman eh, nima fiskana ba yabo ba fallasa, Alhaji kabbara yayi ya ce, “Masha Allah! Lallai kinyi ƙoƙari, kuma abu ya mini daɗi sosai ba kaɗan ba, yanzu dai yaushe kuma za ku yi na cikin Adamawan?”

“In Allah ya yarda ba jimawa, duk da dai ba su faɗa mana ba, an dai ce mu dage da karatu, kamun su yayemu ne za’a yi har na State da State duka Insha Allahu” na faɗa kai na a ƙasa.

Alhaji murmushi yayi ya ce, “Allah nuna mana da rai da lafiya, amma yaye ku ɗin zai kai shekara ne?”

“A’a, watanni ne kawai in Allah ya yarda.”

“To Masha Allah! Yanzu dai nima akwai nawa kyautan da zan miki bayan na makaranta, amma dai bari mu jira fitowan result naki tukunna, idan shi ma yayi kyau, to sai ki faɗa duk abinda kike so Insha Allah, idan bai fi ƙarfina ba zan miki shi.”

Murmushi nayi kawai kai na a ƙasa na ce, “Nagode, Allah ƙara girma ya ƙara buɗi.”

Mamina da murmushi ta shigo palourn ta zauna ta ce, “Banafsha je wajan Ummunku za ta baki saƙo ki kawo mini.”

Miƙewa nayi na je ɗaki na sako hijabi na, sai na dawo na yiwa su Mami na fice, tunda na fito a gidanmu gabana ke faɗuwa dan bana son ganin ya Danish, sai dai Allah ya taimake ni ban hango motansa a waje ba, har na shiga cikin gidan duka ban ga motansa ba, hamadala nayi na shige da sauri, da Umma na fara yin tozali, tuni na kawar da kai na ban ƙara kallonta ba, dan gani nake idan na ganta ma ya Danish nake kallo, daga nesa na ce, “Umma barka da yamma.”

Tsaki kawai Umma ta ja, wanda ina da tabbacin har da harara ta haɗo mini da shi, ban staya ƙara yin wani maganan ba na nufi ɗakin Ummu, kuma dai-dai lokacin ta fito, sai da naga Ummu sannan na saki raina na yi murmushi, ita ma Ummu murmushin ta mini ta ce, “ƴar gidan Maminta an shigo ne.”

Ɗaga kai nayi ina buɗe haƙora na, gaishe da Ummu nayi ta amsa, sannan na ce, “Ummu inji Mamina wai na zo za ki bani saƙo na kai mata.”

Murmushi Ummu tayi tana miƙo mini saƙon ta ce, “Daga zuwa sai tafiya, yau ko ta kan Umaima ba za’a bi bane?”

Ni gaba-ɗaya da yake cikin sauri nake nabar gidan, sai yanzu na tuno da wata Umaima ma, sosa kai nayi na ce, “Ummu bari na dubota, idan na fito sai a bani saƙon”, ina gama faɗa na juya na shiga ɗakin su Umaima da sallama.

Umaima baccinta take sha hankali kwance, ganin haka kawai na ƙyaleta na fito, ba dan ina sauri banson haɗuwa da ya Danish ba ai da na sola mata dundu na tashe ta, kawai ta ci sa’a ne, faɗawa Ummu nayi tana bacci a bani saƙon kawai na tafi, Ummu ta bani na amsa na musu sai anjima na fice.

Bayan fitan Banafsha a palourn sai Mami ta tashi a inda take zaune ta dawo kujeran da Alhaji ke zaune, kallonta Alhaji yayi yana murmushinsa ya ce, “Amaryata ya aka yi?”

Tura baki Mami tayi da shagwaɓa ta ce, “kaga banaso Alhaji, haka kawai za ka ɓata mini rai, ni bansan ma me yasa nake sonka har haka na kasa rabuwa da kai ba, kuma kullun cikin ɓata mini rai kake yi, yanzu ko so na ka daina kullum faɗa kake nema da ni”, ta faɗa tana juyawa wai tayi fushi.

Murmushi Alhaji yayi ya ce, “Allah ne ya ɗaura miki soyayyata kaman yanda nima ya ɗaura mini ƙaunarki da sonki, kuma in Allah ya yarda zan mallakeki, nidai yanzu roƙo na ɗaya ki faɗa mini abu game da danginki, kinƙi bani labarinki kuma kinƙi aminta da aurena, meyasa kike mini haka Ramla? Ina sonki da yawa fa ki taimakeni ki amince da auren nan dan Allah, kar Banafsha ta samu miji a ce za’a yi bikinta kina zaman kanki, sam-sam abin bai yi tsari ba, dan Allah ki amince da maganan auren nan Ramla, wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki na rashin mallakanki, ni ba zan iya ci-gaba da saɓa wa Allah ba balle na kai ga aikata babban zunubi, ita zina bashi ce kayi da mahaifiyar wani sai anyi da taka, ka yi da ƴqar wani sai anyi da taka, kayi da matar wani sai anyi da taka, kayi da ƙanwar wani sai an yi da taka, ni kuma ko ɗaya bana addu’an haka, dan Allah Ramla ki amince mini muyi komai akan Sunna.”

Mami ɓata fiska tayi ko kallon Alhaji taƙi yi, Alhaji kaman zai yi kuka ya kamo hannun Mami amma ta ƙwace, riƙo hannunta ya kuma yi ya ce, “Please Ramla say something, dan Allah ki ce kin amince, ko mutum daya a danginki sai mu nema a mana aurenmu, idan bakya so ma sai a ɗaura mana haka al’umman Annabi su zama shaidu da waliyai, dan Allah Ramla, wallahi na miki alƙawarin zamowa uba nagari abin alfahari ga yarinyarki da ma sauran da za ki haifa mini, na miki alƙawarin zamowa miji na gari jajirtacce gare ki, wanda zai tsaya miki a komai ya kuma kula da duk abinda ya shafe ki, sam-sam kada kiji da matata kiyi tunanin ina da mata, banda zafi kam, amma na isa da gidana, dan Allah ki ce kin amince.”

Zuwa yanzu Mami ji take kaman ta kwaɗawa Alhaji mari, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, ƙarshe Alhaji kawai sai ya rungumeta ƙam a ƙirjinsa, a take suka sauƙe wani nauyayyen ajiyan zuciya kaman waɗanda suka yi kokawa ko kuma suka yi gudu, Mami lafewa tayi a jikin Alhaji, ba zato ba tsammani yaji hawayenta na ɗiga a kan hannunsa, Alhaji hankalinsa a tashe ya dubeta cikin damuwa ya ce, “Ramla akan aure kike kuka? Dan na ce ki amince ki aure ni? Shikkenan kiyi haƙuri Allah huci zuciyanki, dama kullum idan nayi magana a faɗa muke ƙare wa hakan baya damuna، to faɗa da sauƙi akan hawayenki, hawayenki masu stada ne a gare ni ba zan jure zubansu ba, idan wani yayi sila ma sai inda ƙarfina ya ƙare balle a ce ni da kai na, Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda daga yau na daina miki maganan aure, in Allah ya ƙaddara hakan, to Allah fahimtar da ke da kansa ya tabbatar mana da alkairi, inkuma babu hakan a ƙaddaranmu shi ma Allah zaɓa mana abinda ya fi alkairi, Allah bamu ikon tuba kamun mutuwa, Allah sa mu gama da duniya lafiya muna amintattun bayi salihai”, Alhaji na gama magana ya miƙe ya ɗau key na motansa ya fice.

Mami zama tayi a wajan tana risgan kukanta kaman wacce aka aiko wa saƙon mutuwa, a haka har Banafsha ta shigo ta sameta tana kukan, bata ma ji shigowanta ba sai ji tayi muryanta na rawa tana faɗin, “Mamina me ya sameki? Me ya faru?” Haka na ƙarishe maganan nima cikin tashin hankali ganin Mamina na kuka.”

Mami ƙoƙari tayi ta stayar da kukan ta ce, “Bakomai Banafsha, ki ɗaura mana abincin dare”, tana gama faɗa ta miƙe ta amshi saƙonta ta shige ɗakinta, ni kuma guntun ƙwallan da ya zubo mini na share ina addu’an Allah ya yayewa Mamina damuwan da ke damunta, haka na miƙe na yi sallahn la’asar, sannan na shige kitchen na ɗaura mana tuwon dare, duk da ina cikin damuwan abinda ke damun Mamina, amma na tsaya nayi aiki mai kyau, na yi girki na gama, na share palourn har stakar gidanmu tass, na gyara har ɗakin Alhaji ko ina na gidan ya ɗau kyalli, na kunna turaren wuta ko ta ina, ɗakin Mamina na shiga da sallama, sai lokacin na samu tana nata sallahn, banɗakinta na fara wankewa sannan na share ɗakin na kunna turaren wuta, har na fice tana jan carbi, ɗakina na koma na gyara abuna, sai da na gama na shiga wanka na ɗaura alwala tunda Magrib ya kusa, dogon rigana ƴar kanti na saka ta shan iska, zama nayi ina jan carbi har sai da aka yi sallah nayi nima sannan na shafa addu’a na fice.

Palourn namu shiru har lokacin Mamina bata dawo ba, Alhaji kuma da naji shiru ni na ɗauka ya tafi ma, sai na je ɗakin Mamina da sallama na shiga, samunta nayi yanzu ma akan sallaya, jikina a sanyaye na ƙarisa gabanta na durƙusa na ce, “Mami abincin na gama.”

Ba tare da Mamina ta kalleni ba ta ce, “ki ɗiba naki ki ci, sai zuwa anjima zan ci, ki sakawa Alhaji a kula.”

Amsawa nayi na fice a ɗakin, yanda Mami ta ce haka nayi, amma ni ban ɗiba ba, ina dai jiran Mamina muci tare.

Alhaji kuwa yana ficewa a gidan ya je hotel ya kama ɗaki, a can har yayi sallahn Magrib da isha’i, har wajan ƙarfe tara yana can, gaba-ɗaya damuwa ta cika shi, lamarin Mami ya fara basa storo, niya yayi ya koma cikin Yola a daren zuwa gobe ya wuce Kano, amma ya kasa baya jin zai iya tafiya bai sanya Ramlatunsa a ido ba, kwana a hotel ɗin ma ba zai iya ba, haka ya tattara wajan ƙarfe goma ya dawo, lokacin kuma dagani har Mamina babu wanda ya saka wani abu a cikinsa, Mami ko fitowa bata yi ba, ni kuma na kasa cin abincin ni kaɗai, sai da Alhaji ya shigo sannan lokacin naji mostin Mamina, har ɗakina ta shigo ta ƙirani muka je muka ci abincin, Alhaji dai taɓawa kawai yayi dan kar masoyiyarsa taji babu daɗi.

Har muka gama cin abinci na musu sai da safe ba wanda ya yiwa wani magana a cikinsu, nidai ina shigewa ɗakina na gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan nabi lafiyan gadona na kwanta.

Alhaji ma stame hannunsa yayi ya tashi ya shige ɗakinsa, Mami cikin damuwa ta tattare komai, sannan ta nufi ɗakin Alhaji, lokacin shi kuma ya fito wanka kenan, murmushi Alhaji ya sakar mata ya ce, “Masoyiya je ki wásta ruwa kema ina zuwa.”

Mami jiki a sanyaye ta buɗe baki ta ce, “Alhaji ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai..”

Dakatar da ita Alhaji yayi yana murmushi ya ce, “kije ki wásta ruwa ina zuwa, kar ki damu kanki ba komai.”

Ba musu Mami ta juya, ɗakinta ta koma ta shige wanka kaman yanda Alhaji ya ce, Alhaji Mukhtar kuwa murmushinsa yake yi har ta fice, sannan ya shirya, ƙira ne ya shigo wayansa, yana murmushi ya ɗauka tare da amsa sallaman da aka masa a wayan, cewa yayi, “Allah taimaki General.”

General a nasa ɓangaren murmushi yayi ya ce، “Yaya anwuni lafiya ya fama da jama’a?”

“Alhamdulillahi General, ya yaran ya kuma ɗan ka mara jin magana?.”

General ɗan dariya yayi ya ce, “yaya wani rashin ji my Man yayi kuma?”

“Au kana tambaya ne? Tun wuri dai ka faɗa masa yabar ƙirana da Sir idan ba haka ba zan saɓa masa, tunda ya renaka yana faɗa maka General kana amsawa to nidai zan saɓa masa ne, yara ne duk sun mayar da mutane kaman sa’o’insu.”

“Ayi haƙuri yaya.”

“Haƙurin dama za ka bayar ai na sani, wannan yaron da macece na tabbata kana aurar da shi za’a dawo maka da ɗan ka, duk la bi ka sakalta shi ka shagwaɓa shi, Allah ya so ma Sojan sama ya ke, da na ƙasa ne kam ai nasan ba iyawa zai yi ba, yanzu ma tausayin matar da za ta zauna da Bunayd nake yi.”

Dariya General yayi ya ce, “Amma dai yaya ba abinda za mu ce sai godiya, ai in akwai abinda ya fi aikin soja staff my Man zai iya, kuma ai sojojin sama sun fi na ƙasa baiwa, saboda ikon Allah kawai ke sa mutum yana sama kuma ya iya yin yaƙi, sannan duk macen da ta samu Bunayd to ina mai tayata murna ta samu miji nagari.”

Girgiza kai Alhaji yayi ya ce, “shi yaron naka ne miji na gari a haka? Allah dai ya haɗa sa da wacce za ta iya da shi.”

General dariya ya kuma yi ya ce, “Nikam ka tuna mini magananmu da shi ranan ma, ya ce na faɗa maka ka nema masa mata wacce za ta dace da shi, ya yarda zai yi auren, kasan yaron nawa da biyayya yake, ga jin magana.”

Taɓe baki Alhaji yayi ya ce, “Ni ba zan nemawa Bunayd mata ba ya zo ya sa naji kunya, kai dai da kake ubansa sai ka nema masa, koma mene stakaninku ni nawa kallo, yadai tabbatar ya samu matar dan na gaji da kallonsa haka, mutum na neman kai shekaru arba’in amma ya kasa ajiye mata.”

Cikin raha da ɗan faɗa-faɗa Alhaji yayi waya da General har suka yi sallama kaman kada su kashe, General ma ya sanar da Alhaji za su shigo duka da yaran Insha Allah ba jimawa, Alhaji ya ce Allah ya kawo su lafiya, bayan sun yi sallama sai Alhaji ya miƙe dan tafiya ga masoyiyarsa, yana buɗe ƙofa zai fita ita kuma ta sako kai za ta shigo har kusan karo suka yi, kallonta yayi yana murmushi ya ce, “Na ɓata lokaci ko Hajiyata?”

Mami jinjina kai kawai tayi ta juya, ɗakin Mami suka shiga, Alhaji ya samu waje ya zauna, ta zauna gefensa, dukkansu shiru suka yi, sai Alhaji ne ya gaji da shirun ya ce, “Allah ya baki haƙuri, Allah ya huci zuciyanki Ramlatu.”

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, “Kai ma Allah ya huci zuciyanka Alhaji, in Allah ya yarda ba jimawa zan sanar da kai komai a kai na, ka yi haƙuri.”

Murmushi ya yi ya ce, “Bakomai Ramla, yauwa inason faɗa miki daman, bayan kyautan da zan wa Banafsha idan Allah ya sa result nata yayi kyau, to yanzu ina son kiyi haƙuri ki barta ta riƙe waya.”

Mami ba tare da ta ɗaura idonta akan Alhaji ba ta ce, “a’a Alhaji ba yanzu ba tukunna.”

“Meyasa ba yanzu ba Ramla?” Faɗin Alhaji yana kallon Mami.

Mami ta ce, “Alhaji har yanzu Banafsha yarinya ce, bana son waya ya zama sanadiyyar lalacewan tarbiyan ta, nafi son idan ta samu miji to Masha Allah! Idan ya aureta sai ya saya mata, nan ba mastala matarsa ce, amma ni yanzu storon yarinya ta riƙe waya nake yi.”

Murmushi Alhaji yayi ya ce, “Eh to wani gefen da gaskiyanki, wani ɓangaren kuma ba gaskiya a magananki, domin komai da kike gani a rayuwa yana da ɓangare mai kyau da kuma ɓangare mara kyau, tabbas a wannan zamani da muke ciki, ƙaramin abu ne yarinyarka a ɓata mata tarbiya ta waya, musamman ƙawayen banza da fasiƙancin neman jinsi yayi yawa, ko kuwa ɓata garin samari, amma fa ina son ki sani, wani a wayan nan zai iya shuka abin alkairin da zai kai sa aljanna, sannan wani a babu wayan ma yana iya lalacewa, addu’a ita ce ke stare komai ta kare kowa, Banafsha yanzu ba yarinya ba ce, ko saboda abinda ya shafi makaranta yana da kyau ki barta ta riƙe waya, yanzu suna final year nasu ne, to wani abun tana buƙatan waya.”

Mami shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka kuma Alhaji yasan me take nufi na bata yarda ba, sai kawai ya ƙyale maganan, nan suka kama hiransu kaman ba abinda ya haɗa su ɗazu har Mami ta fara gyangyaɗi, Alhaji ya ce su kwanta, ba jimawa Mami tayi bacci shi kuma Alhaji a sulale ya tashi ya fice a ɗakin.

Washe-gari da wuri Banafsha ta tashi sakamakon ranan asabar ne akwai zuwa tahfiz dan ba su da lecture ba za su shiga makaranta da wuri ba.

Banafsha na fitowa gida sai ga Umaima na ƙoƙarin shigowa nasu gidan, murmushi suka sakarwa juna, Umaima ta ce, “Masoyiya muyi sauri lokaci ya ƙure kada muyi latti.”

“Aikam muka yi latti akwai mastala, yau ba shiga aji kenan sai dai mu dawo mu wuce College dan ba mai taɓa mini lafiyar jikina” na faɗa tare da riƙe hannun Umaima muna tafiya, muna hiranmu a haka har muka isa, Allah ya taimake mu ba’a fara tare lattin ba.

Mun yi karatun ranan mun gama har aka tashemu, mun fito muna tafiya ta hanyar da muke bi ta cikin anguwa, sai gani muka yi mutun ya tsaya stegege a gabanmu, ganin wanene dukkanmu sai muka haɗa fiska, Umaima ce ta buɗe baki tana hararansa ta ce, “Malam me damuwanka da mu? Yau kuma da me ka zo?”

Garba kallon sama da ƙasa ya yiwa Umaima ya ce, “ke mastalana da ke shishshigi ya miki yawa, ina ruwanki? Ko na miki magana? Na taɓa ƙiran sunanki? Dan Allah ki ƙyaleni nayi da wacce take gabana.”

A zuciye Umaima ta buɗe baki za tayi magana amma sai na dakatar da ita, kallon uku saura kwata na wásta masa sannan na riƙe hannun Umaima muka wuce, amma still Garba ya ƙara stayawa a gabanmu, a hasale na ce, “ka ɓace mana a hanya.”

Murmushi Garba yayi yana shafa suɗaɗɗen kansa da yaji askin tanƙwal ya ce, “stakani da Allah na kasa nistuwa, wallahi soyayyanki ta mini mugun kamu, ni ba ruwana da sana’ar babarki, dan Allah ki so ni, kiyi haƙuri da abinda na miki ranan.”

Hararansa nayi kawai naja Umaima muka wuce abinmu, duk magiyan Garba ko ta kansa ba mu bi ba.

Muna komawa kuma muka shirya shirin tafiya makaranta, Alhaji ne ya kai mu bayan ya gama jinjina mana na ƙoƙarin da muka yi, ya ce da Umaima ma ta dage nan gaba kada ta yi bracket, mudai cewa muka yi mun gode, yana sauƙe mu muka shige school, class da muke da shi sai wajan ƙarfe sha biyu, mun yi kuma, mu ne bamu bar makarantan ba sai wajan ƙarfe uku na yamma, muna dawowa Umaima ta shige gidansu na shige namu.

Mami da Alhaji na samu suna zaune suna hiransu da fara’a, gaishesu nayi sannan na shige ɗakina, wanka nayi tare da yin sallah, duk da yau ina jin wani yanayi hakan nan, marana ya fara ciwo-ciwo ga ƙafana ya fara kama mini, haka dai a daddafe nayi ayyukan da zan yi ma gida na shirya zuwa tahfiz na yamma, da Umaima muka tafi, yau bayan antashi Malam Abbo ya faɗa mini anjuma zai zo wajena akwai maganan da yake so muyi, nidai nasan ban aikata wani laifin ba, amma na amsa masa sai ya zo, muna komawa gida na samu Alhaji da Mamina za su fita, nima ta ce na shirya muje wanke kai, na ce a’a ni sai gobe, a dawo lafiya na musu, kallo na kunna kawai na kwanta amma inajin ciwon maran nawa na ƙaruwa.

Abbaa tunda Ya Danish ya zo jiya ba su zauna ba, sai yau ya faɗa masa da dare yana son magana da su shi da Ya Farooq, duk amsawa suka yi, dare nayi bayan sun yi sallahn isha’i suka amsa kiran Abbaa, a palournsa da ke cikin compound ɗin gidan suka zauna, ga Umma ga Ummu gasunan su ma, Abba gyaran murya yayi tare da mayar da kallonsa kan Umma ya ce, “Sabeera da ke zan fara, saboda kece babba kuma mahaifiya, duk turban da kika nunawa na ƙasa da ke, musamman yaranki to shi za su bi, duk da bansan me yarinyar nan Banafsha da mahaifiyarta suka tsare miki ba, amma na sha faɗa miki ki gyara halayyanki akan su, inason ki faɗa mini me mastalarki da su, dan duk abinda kuka yi ranan da matar kabeeru ya dawo kunnena.”

Umma Sabeera ɓata fiska tayi ta ce, “Ni ba abinda suka stare mini, halayyan mahaifiyarta ne kawai bana so, kuma ta dena shiga stabgan yarinyata kada ta lalata mini tarbiyaanta, gida kuma ka ce naka ne, dan haka ta shigo banda mastala.”

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, “Hakan yayi kyau tunda kinsan gida nawa ne, kuma sai wanda na bawa ikon shigowa zai shigo, dan haka kuma ina son ki sani ita Umaima ma yarinyata ce dan haka ni mastayina na mahaifinta na bata daman kula Banafsha da shiga gidansu, in kuma kin ce a’a sai ki nema mata wani uban bayan ni, lalacewa kuma idan Allah ya rubuto mata a ƙaddaranta to ko a ɗakin ki take akan gadonki to sai ta lalace, sannan akan abinda kuka yi ranan zan ɗau mataki ba shiru nayi da na ƙyale ba” Abbaa ya faɗa ransa a ɓace.

Umma dai fiskan nan a haɗe, Ummu kuwa kanta na ƙasa ma, Abbaa kallonsa ya kuma mayar wa kan yaransa ya ce, “Ku ma na dawo kanku, musamman kai Danish, kasan abinda ka aikata ba sai na faɗa ba, inason ka sani kai baka isa ka sani jin kunya ba, ni kuma ban haifi mara mutunci a cikina ba da yardan Allah, idan ka ƙara kuskuren aikata irin wannan abun ba iya ga Banafsha ba, wallahi ko a can wajan aikinka naji labari to ka tabbata zan cireka a cikin yarana, ka ji wallahi na ranste maka, bana son hauka da rashin hankali, ina ruwanku da rayuwar su? Haka Allah ya iyo su kuma haka Allah ya so ganinsu, kowa da ƙaddaransa da kuma jarabawansa, su wannan ne jarabawansu, ku zo a banza kuna uzzurawa kanku akan rayuwan mutanen da ba ruwansu da ku, kuma wataƙila a wajan Allah sun fi ku mastayi da komai, ni ba wanda ya bani mamaki sai kai Danish, da iliminka da tunaninka da tarbiyyanka da hankalinka, a bari ita mahaifiyarka da matar wanka su mata ne, kuma mata daman tunaninsu sai a hankali, amma kai za ka haɗa lissafinka da nasu kana na miji wanda ya isa ajiye iyali, to idan ka kuma gigin aikata irin wannan kuskuren ranka zai yi mugun ɓaci, yarinya da tarbiyyanta da komai ta fi wani wanda ya ke ɗan babban Malami nustuwa da komai amma kana neman aikata mata ba dai-dai ba, to wallahi kana ji na ka kiyaye, kuma daga kai har ɗan uwanka ina mai umurtanku da ku fito da matan aurenku akan lokaci dan ba zan ɗau wannan shirmen ba, tun kamun ku fara lalata yaran mutane gwanda na muku aure ku ɗin ma tunda duk kun kai riƙe iyali har kun kai zama iyaye ma, abinda ya sa nayi ƙiranku kenan, kuma duk wanda ya ɓata lokaci zai ga matakin da zan ɗauka, fatan kuna ji na Danish da Farooq?”

Dukkansu ɗaga kai suka yi alaman sun amsa, sannan Abbaa ya ƙara musu faɗa sosai ya ce ya sallamesu, su tashi su basa waje, miƙewa suka yi suka fice, Danish fiskansa a haɗe, Farooq dai murmushi yake yi.

Bayan fitan su Danish Abbaa ya kalli Umma ya ce, “Sabeera na ƙara dawowa kan ki, ki sani kema abinda kika aikata zan ɗau mataki a kansa ba wai na yi shiru ba ne, matar dai da kika bi kika gallazawa kanki akan ta kuma bata san kina yi ba, to ina so ki sani ita zan auro, wataƙila idan na aureta to za ki dawo hanya ki koma hayyacinki, yarinyar ma nan za ta dawo da zama, kuma kika kuskura kika ce za ki aikata wani rashin hankalin to zan nuna miki abinda ke kai na ya fi naki, ai mutum ba shi yake yin kansa ba, dan mahaifiyarta na zaman kanta, ai ba yana nufin a staneta a stangwameta ba, ko akwai wanda yake zaɓawa kansa daga cikin iyayen da zai fito? Kowa da kike gani Allah ne ya riga ya gama stara komai a kansa tun fil’azal, dan haka ki dawo hayyacinki, bai kamata ke da za ki yiwa wasu faɗa, a ce ke da kanki kike aikata hakan ba, idan kuka tsamgwami yarinya kuka dinga kyamatarta, wani hali kuke tunanin za ta faɗa? Ai sai ta zaɓi ita ma ta shiga duniya tunda haka al’umma ke mata kallo, duk irin munin halin mutum, maganin zama da shi ake sha, sannan a ja shi a jiki a dinga nusar da shi gaskiya ana nuna masa abinda ya kamata, amma idan aka dinga ƙuntata masa to gaba-ɗaya ba za’a ribatu da mutum ba, yanzu idan yarinyar nan ta lalace kuma wani a yaranki ya bi ta shi ma ya lalace ya za ki ji? Kuma wa gari ta waya? Amma idan ta shiryu bata lalace ba ai ko ke hankalinki a kwance kinsan yaranki ba za su bita da ɓatanci ba idan ba maganan arziƙi ba, ba’a kyamar mutum ko ƙuntata masa ko da kafiri ne balle kuma musulmi wanda ya ke salla kai ma kake sallah, ya ambaci Allah da Manzonsa kai ma ka ambaci Allah da Manzonsa, akwai wani kissa na wani sahabin Manzon Allah SAW da ya kwanta mini, amma dai shi ma akwai wani abu da yake yi wanda ya zamana mutane na ƙyamatan shi, amma Annabi ya nusar da su hakan ba kyau ya ja bawan Allahn a jiki, daga ƙarshe sai da ya zama sahabi mayaƙin Annabi SAW wanda ake ji da shi, to ba’a rena ɗan Adam duk yanda ya je kuma ba’a ƙuntata masa, misalai dai da yawa akwai su kuma Annabi da kansa yayi magana akan hakan, dan Allah dan Annabi ki kiyaye Sabeera, wannan yarinya tamkar Umaima haka take a wajanki, Ummu-khultum ke ma abinda ya sa na ajiye ku, duk so nake ku gyara, mu gudu tare mu stira tare, duk da bantaɓa jin kin yi musu wani abun da ba dai-dai ba amma a kiyaye saboda zuciya watarana sai a hankali, kuma ku yi haƙuri amma zan ƙara aure, Insha Allahu dai ita Maman Banafsha zan aura, fatan za ku bani haɗin kai kuma ku ci gaba da tayani da addu’an alkairi.”

Ummu tana murmushi ta ce, “Allah taimaka ya kuma tabbatar da alkairi, Allah shige mana gaba ya sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu, Allah kuma ya baka ikon yin adalci.”

Murmushi Abbaa yayi ya amsa da Ameen, sannan ya dubi Umma ya ce, “Sabeera ke kuma ba ki da abin cewa ne?”

Umma cikin fushi ta miƙe fuuuu! zuciyanta na tafarfasa kaman za ta kifu akan Abbaa ta ce, “yanzu dan ka gama rena mana hankali ka rasa wa za ka auro sai gantalalliyar karuwa da ta gama yawon karuwancinta, wa ma ya sani ko tana ɗauke da ciwo, ka zo ka aurota ka raɓa mana, to wallahi ba da ni ba, kuma ban yarda ba ban amince ba, idan ma auren za ka yi jaraba na damunka ba ka godewa Allah da mata biyun ba, to sai dai ka auro wata amma banda wannan wastatstsiyar” tana gama faɗa ta fice.

Abbaa murmushi kawai yayi ya sallami Ummu, ya kwanta abinsa ba damuwan komai a zuciyansa, ransa wasai, sai addu’an fatan alkairi da yake yi, da kuma Allah haɗa yaransa da mata nagari.

Ya Farooq farinciki yake abinsa bai da damuwan komai, daman budurwansa ta faɗa masa an ce ya turo, yana niyan yiwa Abbaa magana kenan ya musu wannan magana, shi dai ya Danish cin rai kawai yake yi, shi yana da budurwan amma gaskiya ya rasa dalili tunda incident ɗin nan ya faru stakaninsa da Banafsha, sai ya fara jin haushin budurwansa haka kawai, ga shi tunda ya zo weekend ɗin nan, gobe Sunday zai koma amma ko kallonta bai yi ba balle ya mata wani mugunta, dan shi bai huce ba har yanzu, Ya Farooq na masa magana ma amma ko kula shi bai yi ba, kuma bai shiga cikin gida ba dan baya son surutun Umma.

Ina kwance na gaji da kwanciya na miƙe nayi ayyukan da ya kamata, wanka na shiga na gama na shirya, ina zaune shiru ni ɗaya a gida har nayi sallahn Magrib su Mamina ba su dawo ba storo ma ya bi ya cika ni, kaman nayi kuka haka nake ji, ga shi banda waya balle na ƙira Mamina, da ace ba weekend bane sai na shiga gidan su Umaima, amma weekend ne bana buƙatan haɗuwa da Ya Danish dan nasan yanzu haka ba zai wuce ma suna ƙofan gida ba, haka na daure na zauna cikin storo.

Malam Abbo sai da ya shirya zuwa wajan Banafsha abincin ruhinsa, sannan ya bi masallaci yayi sallahn Magrib, ana idarwa ya tashi ya kamo hanya cike da addu’an Allah bashi ikon furta mata soyayyansa, kuma Allah ya sa ta amsa, dan sosai take masa kwarjini, Malam Abbo ba ƙaramin kwalliya ya ci ba, ga wani ƙamshi da yake yi na musamman, Malam Abbo haɗaɗɗen matashin saurayi ne wanda ba macen da sa ta kallesa bata ji ya burgeta ba, cikin tafiyarsa na nistuwa yake taku har ya iso ƙofan gidan su Banafsha, kuma ya wuce su ya Danish a ƙofan gidansu, ya Danish kallo ɗaya ya masa ya ganesa, shi ne saurayin da yake ganinsu tare da Banafsha, tuni wani haushi ya rufesa da ya tuna abubuwan da ta ke masa, ga shi ranan bai samu ya koya mata hankali ba, ƙwafa yayi ya bi Malam Abbo da harara.

Dai-dai isowan Malam Abbo ƙofan gidan su Banafsha, dai-dai isowan motan Alhaji sun dawo daga anguwa da Mami, Alhaji da kansa ya sauƙa ya buɗe gate ya shige cikin gidan, Mami da yake ta kalli Malam Abbo, sai ta faɗawa Alhaji ai malamin su Banafsha ne ya masa iso, ta juya ta shige ciki shi kuma Alhaji ya fice waje, Malam Abbo yana ganinsa ya fara fara’a, cikin mutuntawa suka yi musabaha suka gaisa, sannan Alhaji ya masa iso suka shige cikin gidan.

Mami na shiga ta sameni zaune sturu-sturu da idanuwa kaman an tare kule a buta, duk a storace nake, murmushi tayi ta ce, “Sannu da gida ƴar Mami mai storo.”

Ina murmushi na tashi na rungume Mamina na ce, “sannunku da dawowa Mamina.”

“Yauwa Faɗiman Mami, ki shige ki sako hijabi dan naga malaminku ya zo” Mami ta faɗa tana nufan ɗakinta.

Ajiyan zuciya na sauƙe dan storo ya tafi tunda Mami ta dawo, ɗakina na wuce ina murmushi dan sai yanzu da Mami tayi magana sai na tuna Malam Abbo ya ce zai zo gidanmu, amma mamaki nake da zuwan da yayi da dare da kuma ko me ya kawo sa Allahu a’a lamun, nidai ya ce akwai maganan da za mu yi, addu’a nake Allah ya sa alkairi ne, kuma Allah yasa ba wani laifin na aikata ba.

Alhaji tare da Malam Abbo suka shigo palournmu, waje Malam Abbo ya samu ya zauna, Alhaji ya shige ɗakin Mamina ya faɗa mata malaminnamu ya shigo, Mami ta amsa shi kuma ya wuce ɗakinsa, Mami cikin kamala ta fito da hijabinta, Malam Abbo kuwa cikin ladabi ya durƙusa ya gaidata yana ya sunne kai, Mami amsawa tayi da fara’a bata ce komai ba ta dai ce bari ta ƙira masa faɗima, ya amsa yana mai sunkuyar da kai cikin kunya.

Ni kuwa ina shiga ɗakina haka kawai na stinci kai na da ɗan gyara fiska na, na shafa humrana sannan na ɗau hijabina na saka, ba ƙaramin kyau nayi ba ga shi har da man baki da kwalli na saka, Mamina ce ta shigo ɗakin da sallama, kallona tayi ta girgiza kai ganin har da kwalli na saka, murmushi kawai tayi ta ce, “Idan kin gama kwalliyan to yana jiranki” tana gama faɗa ta fice tana murmushi dan yanzu ta fara harbo jirgin abinda ke shirin faruwa, Banafsha har da kwalliya, shi kuma malamin nata sai sunne kai yake kaman mara gaskiya.

Mamina na fita na tsaya na gama dariyana sannan na tattaro nistuwata na fice palourn ina mai jin wani iri haka kawai, ina isa da sallama ya amsa mini, waje na samu na zauna a ƙasa, amma yau Malam Abbo ya dage firr! Sai na zauna a sama, haka ba dan naso ba na zauna a sama ina cusa fiskana a cikin hijabina, da hijabin a bakina na gaishe sa muryana yayi wani iri, shi kuma ya amsa yana kwaikwayon muryan nawa yanda yayi, sai abin ya bani dariya kawai na ɗan murmusa nayi shiru tare da yin ƙasa da kai na, ina wasa da yastuna.

Malam Abbo can da shirun yayi yawa sai yayi gyaran murya ya ce, “Malama Faɗima yau ba ruwan sha ne, abin rowa aka fara mini.”

Kunya na ji na miƙe da sauri, ni gaba-ɗaya na sha’afa ma, wucewa nayi kitchen na haɗa masa abin taɓawa har da tuwon dare da nayi, na ɗauko cikin nistuwa na zo na ajiye masa agabansa, murmushi Malam Abbo yayi ya ce, “ina godiya Malama Faɗima Allah ya yi albarka, sannu da ƙoƙari.”

Ina sunne kai na amsa da ba komai, sannan na ce, “ka taɓa abincin dai malam, ka ji girkin ɗalibarka.”

Malam Abbo cikin fara’an yanda na sake ya ce, “Masha Allah! Ai dole na taɓa Sayyadata” ya faɗa tare da kurɓan ruwa, sannan ya dube ni, cikin jarumta ya fara mini magana kaman haka, “Sayyada Faɗimah fatan dai ban takura ki ba da zuwan da nayi na dare?”

Jinjina kai nayi kawai alaman ba komai, murmushi Malam Abbo yayi ya ce, “To! Godiya nake Sayyadata, Allah ƙara lafiya.”

Murmushi nayi kawai, sai da muka gaisa ya tambayi karatu da boko duk na amsa masa, sannan ya ɗago yana bi na da wani irin kallo mai narkar da zuciyan abinda kakeso, ƙasa nayi da kai na, Malam Abbo ya numfasa ya ce, “Sayyadata ina mai fatan babu wanda ya rigani ko ya mini shigan sauri ya mini ƙafa?”

Ba tare da na fahimci abinda yake nufi ba kawai na ɗaga kai, murmushi ya kuma yi ya ce, “Masha Allah! Alhamdulillahi ala kulli halin! Ni ɗin mai sa’a ne Insha Allah, Sayyadata abin da nake faɗa da gaske nake faɗansa tun daga ƙasan zuciyata, soyayyanki da ƙaunanki sun jima da yi mini mugun kamu, kuma ƙauna ce wacce aure za ta zama ribarta Insha Allah, ina fatan za’a amsheni hannu bibbiyu tunda an ce babu wanda ya rigani.”

Wani irin kunya ne ya rufe ni lokaci guda, kawai rufe fiskana nayi da hijabi ina ta murmushi, ba wannan bane karo na farko da namiji ke faɗa mini yana ƙaunata, amma wannan sai na ji sa daban, Malam Abbo ya kai maƙura duk inda ake buƙatar mijin aure ya kai, alhamdulillahi indai wannan ya zamo uba ga yarana to ina da tabbacin sun yi dacen uba, amma sai dai kashh! Ba wannan bane a gabana, ban da asali ban da kowa sai Mamina kawai, aure ba zai yiwu ba a gare ni, ba zan iya yaudaran bawan Allah ba na sa masa rai ba, ni na riga da na sani a ƙaddaran rayuwata babu aure, kowa na zagina da hantara ta akan ƙaddaran mahaifiyata, a yanzu zan iya jurewa amma ba zan iya jure hakan a gidan aure na ba, ko ga dangin miji ko kuma aje-aje har shi mijin da kansa, dole na haƙura da batun soyayya balle a kai ga aure, cikin sanyin jiki na ɗago shanyayyun idanuwana da ke neman zubar da ƙwalla na kalli Malam Abbo cikin ido, da duk sauran juriyata da jarumtata na ce, “ka yi haƙuri Malam, amma ni ba zan yi aure yanzu ba kada na bata maka lokaci.”

Daga yanayin Banafsha Malam Abbo ya fahimci ya samu karɓuwa, ko abinda take furtawa ma kokawa take da zuciyanta wajan faɗan hakan, cikin damuwa ya ce, “Sayyadata ko nan da shekara nawa ne na miki alƙawarin zan jira ki, nasan ba zai wuce kina son kammala karatunki ba, wallahi banda mastala da bokonki ni da kai na idan ina da hali sai iya inda rai ya stayar da ni akan iliminki, ina ƙaunanki Sayyadata, na jima ina dakon soyayyanki amma na kasa furta miki, wannan karo da na samu ƙwarin guiwan faɗa miki dan Allah kada ki juya mini ƙoƙon barana ba tare da kin cika mini shi ba.”

Zuwa yanzu hawayena ƙiris suke jira su kwalalo, a hankali na ce, “ka yi haƙuri Malam Abbo ba zan iya aurenka ba.”

Cikin damuwa yake kallona yanda nake kallonsa ya ce, “Saboda menene Malama Faɗima? Halinane bai miki ba? Ko nasaba na? Ko kuma menene ba dai-dai ba ki faɗa mini, na miki alƙawarin gyarawa yanda kike so in Allah ya yarda.”

Wannan karon muryana na rawa har hawaye sun fara bin kuncina na ce, “Malam nasan kasan gaskiya akan komai a rayuwata, nasan kasan duk abinda jama’a ke faɗa a kai na da mahaifiyata, Malam ba ta inda ka kasa, don babu macen da za ka nuna kana sonta ta ce baka mata ba, Malam ni kwata-kwata auren ne ba zan yi ba a rayuwata.”

Malam Abbo kallon Banafsha yake ba kifta ido ya ce, “Zan aureki a haka Faɗima, zan aureki a duk yanda kike, ni ke nake so ba komai da ya shafe ki ba, ko wanni bawa da irin ƙaddaransa da kuma jarabawansa, ina ƙaunanki a duk halin da kike ciki Sayyadata.”

Fashewa kawai nayi da kuka na ce, “Malam ko kana so na danginka ba za su aminta da ni ba na sani, dan Allah ka yi haƙuri Malam, Allah ya baka mace tagari wacce ta dace da kai”, ina gama faɗan haka na miƙe ina kukana na nufi tafiya ɗakina.

Malam Abbo ma miƙewa yayi ya fara magana wanda shi ya stayar da ni, “Malama Faɗima kaman yanda na faɗa miki ina sonki a duk yanda kike, to ina son ki sani ke ce dai-dai ni, kuma ni zan zauna da ke ba kowa nawa ba, ina sonki ina ƙaunanki ki saka wannan a ranki, in Allah ya yarda in har da rabo kuma da alkairi to Allah da kansa zai yi Allahnsa ki zama mallakina, amma ina roƙon ba za ki ɗau fushi da ni ba akan wannan magana.”

Ina gama sauraran Malam Abbo na wuce ɗakina da sauri ina kukana, ga samu ga kuma ráshi lokaci guda, Malam Abbo mijine da ko wacce mace tagari za ta yi addu’an samu, amma ni ga daman hakan ya sameni har gida sai dai babu hali, ƙaddaran mahaifiyata ya riga ya rusa mini komai nawa, ƙaddaran mahaifiyata ya sa na tashi banda kowa sai ita dan ina da tabbacin ƙaddaran rayuwanta ne ya rabata da kowa nata, ƙaddaran amsa sunan ƴar Karuwa da zamtowa ƴar Karuwa shi ne babban ƙalubale na a rayuwa, ɗaga hannayena sama nayi na ce, “Allah ga ni gare ka, Allah ka iya mini a lamurana, a yanda nake ina matuƙar son na ga nima na raya sunnan ma’aiki, amma mahaifiyata ta zama katanga a gareni tsakanina da aure, wa zai auri ƴar mace mara asali kuma ƴar karuwa? Banda Uba banda ƴan uwa banda kowa sai mahaifiya, ai ko a jikin bishiya na fito albarka, nasan babu ubanda zai amince ɗan sa ya auri ƴar mace mai zaman kanta, macen da maza daban-daban ke sintiri a wajanta” rushewa nayi da kuka mai ƙarfi saboda ciwon marana da ya ƙaru ya dawo mini sabo fill dan damuwan da nake ciki.

Malam Abbo kuwa Banafsha na shigewa kaman zai yi kuka ya koma ya zauna, sai da ya ƙara kurɓan ruwa ya dinga jera ajiyan zuciya sannan ya miƙe, ya juya zai fice sai ga Alhaji ya fito a ɗakinsa, Malam Abbo daurewa yayi ya shanye damuwarsa da murmushin yaƙe suka ƙara musabaha da Alhaji ya masa sai da safe, sai da ya rakasa har ƙofa sannan suka yi sallama ya tafi, Alhaji kuma ya rufe ƙofa ya dawo cikin gidan cike da tausayin wannan matashin, dan kusan maganansu na ƙarshe da Banafsha ya ɗan stinci saura, wannan jarabawa ce ga uwa da kuma ƴar ta, kuma Alhaji sam-sam bai ga laifin Banafsha ba saboda gaskiyanta ne, wasu iyayen sai a hankali ba lallai su amince ɗan su ya auri mara asali ba kuma ƴar mace, amma kuma yana tausayin saurayin dan ji yayi kaman yaronsa ne ya je neman aure aka masa haka, addu’an alkairi kawai yayi ya tura ƙofan Mami ya shiga, ganin tana bacci sai ya fice ya koma nasa ɗakin ya kwanta.

Malam Abbo yana fitowa ya samu har lokacin su Ya Danish na zaune a ƙofan gida, duk da duhun dare amma Ya Danish yana ƙoƙarin hango wani abu daga yanayin Malam Abbo, kaman zai ji daɗi kuma sai ya taɓe baki irin me damuwansa da kashin su, shi kuwa Malam Abbo haka ya koma gida cikin damuwa da niyan zai bawa Banafsha lokaci ko da sati guda ne ya ji ko ta sauya shawara, idan kuma abun ya ƙi to gaskiya zai samu Ummanta da maganan, shi ba zai iya jure rashin Banafsha ba, Allah ya gani soyayyanta ya jima da masa mugun kamu.

Ya Danish har suka gama hiransu suka shige gida zuciyansa cike da son ganin giftawan mara kunyar, ya samu ya mata wani rashin kirkin ko zai ji daɗi, haka washegari da sassafe ya fito tun su Umaima ba su tafi makaranta ba ya zauna a ƙofan gida yana son kallon giftawanta dan ya yaɓa mata magana.

A ɓangaren Banafsha kuma da wani irin mugun zazzaɓi ta kwana da ciwon mara, kamun gari ya waye tuni ta fice a hayyacinta, daman ita idan ciwon maranta ya tashi ba ya mata ta sauƙi, duk wata na Allah sai ta ji a jikinta, balle kuma ga shi jiya abin ya haɗu mata biyu, ga damuwa ga ciwo, kwata-kwata ko sallahn asuba ta kasa tashi ta yi, ta galabaita sosai-sosai kuma har lokacin ba wai jinin ya zo ba ne.

Ko da safiya tayi, Mami jin shirun tayi yawa, sai ta ɗauka ko yau Banafsha rigimanta ne ya mosta, da kanta tayi ayyukanta ta yi wanka chass abinta, Alhaji kam ya koma bacci daman baisan me ake ciki ba, Mami ganin dai har lokacin ba mostin Banafsha kuma lokacin makaranta ya wuce, sai ta nufi ɗakinta tana surutu, tana tura ƙofan ɗakin ta shiga ta samu Banafsha yashe a stakar ɗakin a sume, salati Mami ta rafka dan sai yanzu ta tuno lokacin al’adan Banafsha ya yi, month nata ya zagayo, cikin damuwa ta fice ta ɗauko ruwan zafi, shafa mata a fiska Mami tayi, sannan ta sa mata a baki, ruwan na kai wa maƙoshinta ta sauƙe wani wawan ajiyan zuciya, a hankali ta buɗe idonta da suka rine saboda azaban ciwo, ruwan zafin Mami ta bata ta sha sosai kaman ba mai zafi ba ko cire baki bata yi ba sai da ta shanye tass, sannan ba jimawa ta dinga kwarara amai, sai lokacin ta samu salama dama-dama ta koma ta kwanta, Mami sai aikin jera mata sannu kawai take yi, a haka ta tashi ta gyara wajan aman da ta yi, ta cire mata kayanta suka shige toilet ta gyara mata jikinta, sanin ba lallai in tayi sallahn asuba ba, sai ta mata alwala, suna fitowa ta shiryata staff ta saka mata hijabinta, a haka a zaune ta ce tayi sallahn kamun taje ta taso Alhaji su tafi asibiti, Banafsha amsawa tayi da kai, Mami ta fice.

Ya Danish na zaune a ƙofan gida har su Umaima suka fito, yana tunanin ko za su biyawa Banafsha amma sai suka wuce abinsu, Ya Danish bai san idan yana ƙofa Umaima bata biyawa Banafsha ba, haka suka yi tafiyansu da Nana, sun je makaranta ana ta karatu Umaima ta zuba ido ta inda Banafsha za ta ɓullo amma shiru, haka malamai suka shigo har Malam Abbo ma aka musu darrusa har aka tashi ba Banafsha ba alamanta, Umaima duk ta bi ta damu dan tasan idan ba wani abun bane ya faru to Banafsha ba za ta ƙi zuwa makaranta ba.

Ɓangaren Malam Abbo ma bai ji daɗi ba dan gani yake shi ya ja mata rashin zuwa makaranta, sai duk abin ya bi ya damesa, ko da aka tashi ya daure dai bai tambayi Umaima ba yana tunanin zuwa yamma Banafsha za ta zo, dan Maminta ba za ta barta ta zauna a gida ba.

Ya Danish har ya gaji da zama ya shige gida, har su Umaima suka dawo, shiru ba giftawanta, Umaima ma ko da suka dawo ba ta shiga gidan su Banafsha ba, ta bari sai zuwa yamma dan tana tunanin ko wani abun ne ya kuma faruwa tsakanin Banafsha da mutanen Mami ya sanyata fushi taƙi zuwa, bata son taje dubo Banafshan kuma ta kalleta cikin damuwa, sai tayi zamanta cike da kewan ƙawarta aminiyarta.

Mami ɗakin Alhaji ta shiga da damuwa ta tashesa a baccin, faɗa masa abinda ke faruwa ta yi, Alhaji da yake shi ma yasan da ciwon Banafsha, cikin hanzari ya shige banɗaki ya wanke fiska, bai yi kowa wanka ba ya zura jallabiyansa ya fito, Mami ta shiga ta samu Banafsha ta idar da sallahn, kamota tayi suka shige motan Alhaji, shi kuma ya ja sai asibiti, duk da safiya ne amma Allah ya taimakesu da yake asibitin kuɗi ne kuma babban asibiti ne, likita yayi attending nasu an mata alluran da aka saba mata, aka basu magani sannan suka juyo gida, suna dawowa kuma ba jimawa jinin ya zo, nan ma ɗin wani ciwon maran ne dan sai Mami ne ta gyara mata jikinta staff, haka suka wuni cass! Alhaji daman sai Monday zai koma dan haka yana gida, Mami sai kula take da yarinyarta tana mata addu’an Allah ya yaye mata wannan ciwon maran jaraban.

Yamma na yi bayan ya Danish ya shirya tafiya ya fito ya staya a waje, nan ma dai shiru har su Umaima suka kuma wucewa yana wajan, saboda ganinsa Umaima bata yi gigin zuwa gidan su Banafsha ba, ya Danish gajiya yayi ganin su Umaima suna dawowa an tashe su ma, sai ya ja guntun tsaki ganin babu ita ya shige motansa yayi tafiyansa ko sauraran abokinsa IB bai yi ba.

Umaima kuwa suna zuwa makaranta nan ma babu Banafsha har aka tashi, cikin damuwa dai Malam Abbo ya tambayeta ƙawarta ko lafiya bata zo ba, Umaima ta faɗa masa bata sani ba dan bata dubo ta ba, amma za ta duba ta, amsawa Malam Abbo yayi yana addu’an Allah ya sa lafiya, Umaima suna komawa suka samu sai lokacin ya Danish zai tafi, shigewa gida suka yi, ta ce sai ya tafi da anjima za ta je ta dubo masoyiyarta.

Sai da suka yi sallahn Magrib sannan Umaima ta samu Ummu ta ce, “Ummu zan je wajan masoyiya Banafsha, yau kwata-kwata safe da yamma du bata je makaranta ba bansan me ya faru ba.”

Jinjina kai Ummu tayi cikin damuwa ta ce, “To Allah ya sa dai ba wani abun ba ne ya faru kuma, wannan yarinya Allah bata miji nagari inda za ta huta, Allah dai-daita mata lamuran mahaifiyarta.”

“Ameen Ummu ba na je, sai na dawo.”

“To ki dawo lafiya, ki ce ina gaisheta, idan ba komai ki dawo da wuri saboda Abbaa kada yayi faɗa kin fita da Magrib, idan kuma wani abun ne ki kwana can zan faɗa masa, Allah muki albarka dukanku ko” faɗin Ummu.

Umaima ta miƙe tare da cewa, “Ameen Ummuna” ta fice a ɗakin, tana ƙoƙarin fita a ƙofan palourn su ta jiyo muryan Umma na faɗin, “Ina za ki je da daren nan bayan anyi Magrib? Abbaanku bai hana ku fita da dare ba?”

Umaima tura baki tayi ta ce, “Na faɗawa Ummu fa, kuma wajan Banafsha zan je ni, yau bata je makaranta ba kwata-kwata bansan ko bata da lafiya ba.”

Wani kallo Umma ta mata ta ce, “Ita wacce kika faɗawa ita ce uwarki ko ubanki? Umaima zan yi mugun saɓa miki fa, wallahi ki fita a idona na kulle, na ce sannu Uwar Banafsha, ke ce karuwa uwar Banafsha ƙarshenta kenan, to maza ki juya ki koma ɗakinki, idan kika fita a gidan nan yau ba wanda ya isa ya hanani karyaki, ba dai kinga Danish ya tafi ba ko? Shi ne za ki stiro da wani hali, kullum na miki magana bakyaji, to ni nan zan karyaki, wuce ki koma kamun na taso” Umma ta ƙarishe maganan da mugun stawan da sai da Umaima ta ɗan firgita, tura baki tayi ta wuce ɗakinta tana kuka an hanata dubo Banafsha, Umma kuwa ƙwafa tayi ta koma ta zauna ta ga ta inda Umaima za ta fita, duk abinda ya faru Ummu ta jiyo amma sai ta yi shiru, ko ba komai ba’a shiga tsakanin uwa da ƴa, da gaskiyanta ita ce mahaifiyarta ta fi ta iko da Umaima, jan baki Ummu tayi ta yi shiru akan zuwa gobe Insha Allahu ita da kanta za ta je ta dubo Banafsha ɗin.

Washegari Monday bayan Umaima ta shirya tafiya makaranta kasancewan Monday ne suna da class na safe, sai Umma ta fito, mugun kallo ta bita da shi sannan ta ce, “Umaima kina fita ki wuce makaranta, idan kika kuskura kika bi gidansu yarinyar nan wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, bana son shashanci, idan mutuwa ta yi ma ina ruwanki? Ko akwai wanda aka ce ba zai mutu ba ne?”

Umaima yanzu ma tura baki tayi haka ta fice, tana kallon gidan su Banafsha tana son zuwa amma tana storon Umma, haka ta wuce ta tafi makaranta, kaman yanda ta yi tsammani kuwa ba ta ga Banafsha a boko ba har suka gama class nasu wajan ƙarfe huɗu ta dawo gida, nan ma dai ba daman zuwa tana storon Umma haka ta shige gida, tana shiga kuwa ta samu Umma a palour, wani kallo Umma ta mata ko amsa gaisuwan da take mata bata yi ba ta ce, “kinje gidan ƙanwar uwartaki ko?”

Umaima girgiza kai tayi ta wuce kawai, Umma ta yi ƙwafa ta ce, “Ya fi miki, ai da kinje wallahi sai na kusa karyaki, kuma ki gama abinda za kiyi maza ki fito ki shirya ki tafi tahfiz, kuma kika sake kika bi gidansu sai na miki baki.”

Umaima haka ta ci abinci ta yi sallah ta wasta ruwa, sannan ta shirya ta wuce islamiyya, yau ma shiru ba Banafsha ba alamanta, Malam Abbo duk ya bi ya damu, ga shi yana son ya bata sato guda tukunna ya kuma komawa, bayan an tashi ya tambayi Umaima lafiya kuwa ko akwai wani abun da ya hana ƙawarta zuwa makaranta, Umaima kaman za ta yi kuka ta ce bata samu zuwa ba, amma Insha Allah anjuma za ta je.

Malam Abbo cikin damuwa ya ce, “Allah ya kai mu anjuman, ki faɗa mata ina gaidata, na yi kewanta” yana gama faɗa ya wuce.

Umaima da kallo ta bi Malam Abbo, duk mamaki take yanda ya bi ya damu haka shi ma, duk da dai tasan masoyiyarta tana da shiga ran duk wanda ya zauna da ita saboda halinta masu kyau, haka Umaima ta juyo gida ita kaɗai da aka tashi, nan ma Umma ta kuma faɗa mata kada ta kuskura ta ce za ta je gidan su Banafsha, Umaima ko Ummu bata yi wa magana ba taja bakinta tayi shiru, sai da Abbaa ya dawo wajan isha’i sannan ta miƙe saɗaf-saɗaf ta tafi sashinsa, da sallama ta shiga.

Abbaa yana murmushi ya amsa mata ya ce, “shigo ko Umaimatun Abbaa.”

Umaima shiga tayi ta samu waje ta zauna, gaishe da Abbaa tayi ya amsa, ta amsa sannu da dawowa.

Abbaa ya ce, “Ya aka yi Ummul-khultum kaman akwai magana a bakinki? Wa ya taɓa mini ke?”

Umaima sarkin taɓara, tura baki tayi cikin shagwaɓa ta ce, “Umma ce Abbaa.”

Murmushi Abbaa yayi ya girgiza kai dan yasan za’a rina, yana kallonta ya ce, “ya aka yi? Me Ummanki kuma ta miki?”

Umaima ta ce, “Abbaa wai fa Banafsha ce tun ranan asabar rabona da ita, ranan Lahadi har yau litin kwata-kwata bata je boko ba, kuma ba ta je tahfiz ba, shi ne nace zan je dubota na faɗawa Ummu, har ta barni naje kuma ta ce za ta faɗa maka, amma sai Umma ta hanani, kuma ta ce idan na tafi makaranta na bi gidansu bata yafe mini ba…….”, Umaima ta faɗawa Abbaa duk yanda aka yi, kaman za ta yi kuka.”

Girgiza kai Abbaa yayi ya ce, “Mai hali ba ya fasa halinsa, Allah ya kyauta, ki yi haƙuri ko, yanzu ki je ki jirani ina zuwa sai mu shiga gidan nasu tare, Allah ya sa tana lafiya, ki ƙyale Ummanki kar ki ce mata komai, duk abinda dai ta ce miki kiyi ko kar kiyi, idan bai saɓa addini ba kiji magananta, ita mahaifiyarki ce, kuma sai an anrabu da iyaye lafiya ake dacewa.”

Umaima jinjina kai tayi sannan ta tashi ta fice ta koma cikin gida, Abbaa kuwa wasta ruwa yayi ya saka jallabiyansa ya feshe jikinsa da turare sannan ya shiga cikin gidan, duk matan sannu suka masa ya amsa, sannan ya ƙira Umaima ya saka ta a gaba suka fice, suka nufi gidansu Banafsha.

Ɓangaren Banafsha haka ta kwana ranan Lahadi da ciwonta, Mami sai tattalinta take yi, Alhaji ma dai tausayin yarinyar yake yi, har washe gari Litinin haka suka wuni, Banafsha zuciyanta cike da kewan Umaimatynta ga shi bata shigo ta duba ta ba, amma ta mata uzuri tasan ba zai wuce ya Danish ba ne ya hanata zuwa, sai bayan azahar Alhaji ya sallami Mami, bayan ya ajiye mata kuɗi masu yawa dan jinyan Banafsha, Allah ƙara sauƙi ya mata sannan ya fito ya shige motansa, ya nufi Yola daga nan kuma sai Kano Kanawan dabo.

Sai da Mami tayi Magrib sannan ta Lallaɓa Banafsha ta yi wankanta da kanta a daddafe ta gyara jikinta chass da ita, abinci ma da lallami ta ci Mami na bata a baki, ana ƙiran isha’i Mami taje tayi sallah, Banafsha kuma tana kwance a palourn idanuwanta akan TV amma hankalinta ba ya kan TV, hankalinta na can yana tunano mata Malam Abbo nata, har Mami ta idar ta fito bata sani ba, sai da ta taɓa ta ta ce, “shalelen Mami me kike tunani haka?”

Murmushi na sakarwa Mamina na ƙarfin hali na ce, “bakomai Mamina.”

Mami ta ce, “Ban yarda ba, amma dai ina son ki daina saka damuwa a ranki, komai na duniya mai wucewa ne, watarana ciwon nan zai barki kaman ba kiyi ba, Allah dai ya baki miji nagari Banafsha wanda zai kula mini da ke sosai fiye da ni.”

Ajiyan zuciya kawai na sauƙe tuna maganganun Malam Abbo, kawar da tunanin nayi tunda nasan ba mai yiwuwa bane na ce, “Mamina bansan me ya hana Umaima shigowa ba kwata-kwata, Allah ya sa ita ma lafiya.”

Murmushi Mami tayi ta ce, “Insha Allah! Lafiya lau take, may be wani abun ne, karki damu za ta shigo, kinsan dai Umaima na ƙaunarki.”

Murmushin nima na yi da na tuno Umaima, na yi shiru tare da ɗaura kai na a cinyan Mamina da ta sha nata wankan muna kallo, ba jimawa kuwa muka jiyo sallamana Umaima, daga ni har Mamina da murmushi muka amsa, hannuwana na buɗe na ce, “oyoyo Umaimatyna.”

Umaima rungumeni ta yi ta ce, “afuwan masoyiya.”

Hararanta nayi na ce, “Na janye oyoyon ma fushi nake da ke.”

Umaima gaishe da Mami tayi ta ce, “Tare Da Abbaa muke Mami.”

Washe baki Mami tayi ta ce, “To shi ne kika bar Abbaan naku a waje Umaima saboda yaranta? Ki ce ya shigo mana.”

Umaima miƙewa tayi ta fice, tana murmushi ta ce, “Abba ka shigo inji Maminmu.”

Abbaa na murmushi ya biyo Umaima da sallama suka shigo, duk amsawa muka yi, na miƙe daga kwanciyan da nayi ina murna na ce, “Sannu da shigowa Abbaanmu.”

Murmushi shi ma Abbaa yayi ya ce, “Sannu Faɗima.”

Mamina da mayafinta ita ma ta yiwa Abbaa sannu da shigowa ya amsa yana fara’a bayan ya zauna, gaishe da Abbaa nayi ya amsa, sannan na miƙe cikin dauriya, muka shige ɗakina da Umaima muka bar Abbaa da Mamina a palourn.

Muna shiga ɗaki Umaima ta ce, “ki yafe mini masoyiya, na yi kewanki sosai.”

Murmushi na sakar mata na ce, “Nima haka Umaimatyna, wallahi kekam marana ke ciwo tun ranan asabar da dare shiyasa, kuma nasan ba zai wuce ya Danish ne ya hanaki shigowa ba, bakomai wallahi, ya karatu? Fatan dai ba’a ba da assignment ko presentation ba? Tahfiz ma normal ko?”

Umaima murmushi tayi ta ce, “Nasan ai babu dalili ba za ki ƙi zuwa makaranta ba, mayyar karatu, kina fama da kanki kina tambayan wani presentation ɗin buhun uba, ni fa na stani presentation ɗin nan wallahi, amma normal ba’a ba da komai ba, tahfiz ma lafiya, Malam Abbo ya ce na ce yana gaisheki kuma yayi kewanki” ta faɗa tana kyalkyalewa da dariya.

Murmushin yaƙe kawai nayi a nawa ɓangaren na ce, “Masha Allah! Ina amsawa, amma tunda ya Danish ya koma jiya Sunday, me ya hanaki shigowa da safe yau Monday?”

Tura baki Umaima tayi ta faɗa mini yanda suka yi da Umma, murmushi kawai na kuma yi na ce, “Allah ya kyauta, bakomai, Allah raba mu da su lafiya.”

“Ameen masoyiya Banafsha” faɗin Umaima tana kwanciya a kan gadon.”

Wani abu na faɗa mini na faɗawa Umaima yanda muka yi da Malam Abbo, amma wani abu na ce mini a’a, sai kawai na ƙyale nayi shiru, nima kwanciyan nayi, muna hiranmu da yake ciwon maran da sauƙi.

Mamina bayan mun shige ɗaki sai ta kawo wa Abbaa ruwa, bayan ya sha suka gaisa, ya ce, “kwana biyu bana ganin giftawan Faɗima fatan dai lafiya?”

Mami ta ce, “Lafiya Alhamdulillahi Abbaansu, dama bata ji dad’i bane amma da sauƙi.”

“To Masha Allah! Haka ake so, Allah ƙara afuwa, Umaima duk ta bi ta ishi mutane da rigima shi ne nace bari mu taho tare ma.”

Mami dariya ta ɗan yi ta ce, “Yaran nan ai rigimansu ya fi ƙarfinsu, ita Banafsha ma tana kwance tana fama amma sai mita take wai Umaima bata shigo ba yanzu ma mun gama maganan kenan sai ga sallamanta.”

Abbaa murmushi yayi ya ce, “Masha Allah! Ai haka ake so, Allah ƙara haɗa kawunansu, kinga sai a bar miki su ki haɗa duka biyu.”

Mami ta ce, “Waii! Wane ni, ai Ummu ba za ta bar mini yarinyarta ba, da dai za’a ce a haɗa mata su ne ita za ta yarda.”

Dariya Abbaa yayi suka ɗan taɓa hira da Mami sosai da yake daman can sun ɗan mutunci, Abbaa mutum ne da bai da damuwa sam-sam, da yayi tunanin baje wa Mami sirrin ƙalbinsa amma sai ya fasa ya bari zuwa gobe, tunda yanzu dubiyan Banafsha suka zo.

Sai da suka ɗan ɗau lokaci sannan Abbaa yayi ƙiran Umaima ta zo su koma, amma rigima ta saka ita za ta kwana, ba musu Abbaa ya ce su kwana lafiya ya juya yayi tafiyansa bayan sun yi sai da safe da Mami, Umaima da farinciki suka fito da Banafsha suna kallo duka da Mami har dare tayi suka wuce suka kwanta, Mami ma tayi nata ɗakin ta kira Alhajinta suna wayansu cikin soyayya tana masa sannu da hanya dan ya koma gida.

Abbaa yana komawa dai Umma sai zubawa bayansa ido ta ke ta ga ɓullowan Umaima amma shiru, daganan ya fahimci inda suka je, wato Umaima faɗawa mahaifinta tayi shi ne suka je tare, daman mai neman kuka ne aka jefe sa da kashin akuya, ya ce zai auro karuwa ga shi ya samu daman zuwa zance ma dan cin fuska, ƙwafa Umma ta yi ta ce, “Idan na kamaki Umaima sai ɗan buzunki.”

Ummu kuwa ta tambayi ina Umaima ya faɗa mata ya baro ta gidansu Faɗima, Ummu ta tambayi ya jikin nata, ya amsa da sauƙi, ta ce ita ma gobe za ta je dubo ta, Abbaa ya ce, “Ba damuwa Allah ya kai mu, Kinga sai ki raka ni zance mu dai-daita, tasan da amincewnki, dan inaga idan ba ki ce kin amince ba, zai yi wuya ta yarda saboda kar ta ci amanan ƙawance.”

Dariya Ummu tayi ta ce, “Allah ya kai mu Abbaansu.”

Sai da safe ya yiwa Ummu ya wuce ɗakin Umma da yake ita ce da girki.

Washe-gari da safe Umaima daga gidan Mami ta shirya ta je tahfiz, bayan anyi karatu an tashi Malam Abbo ya kuma tambayanta, ta faɗa masa bata jin daɗi ne amma da sauƙi, hamdala yayi tare da yi mata addu’an samun sauƙi, sai yanzu hankalinsa ya kwanta, kuma yana kan lissafi sati guda ranan asabar nayi zai koma ya kuma jin hukuncin da ta yanke, Umaima kuwa tana dawowa ta kuma shiryawa daga gidan Mami ta wuce school ta saka uniform na Banafsha, ko da ta dawo bata tafi gida ba har sai da Ummu ta shigo, bayan sun gaisa da Mami ta tambayi jikin Banafsha Mami ta amsa da sauƙi, sannan ta saka Umaima a gaba suka koma gida, bata haɗu da Umma ba daga nan ta shirya ta koma tahfiz na yamma.

Abbaa yau ma bayan ya dawo ya shirya tsaff ya nufi gidan Mami dan ya sanar da ita abinda ke ransa.

Alhaji Mukhtar ya koma gida lafiya, ya samu Hajiya ta tafi Dubai akan business nata, gaba-ɗaya ya ji ba daɗi amma yayi haƙuri yana addu’an Allah sa ta gyara halinta, Allah kuma ya mallaka masa Ramla.

Yana zaune a palourn sama yana ayyukansa a system nasa, Majeeder ta shigo da sallama, amsawa yayi yana murmushi ya ce, “zauna Maman babanta.”

Majeeder zama tayi ta gaishe da Alhaji sannan cikin shagwaɓa ta ce, “Papi ni wallahi na gaji, gida kullum shiru, dan Allah nima a mayar da ni gidan Affa General.”

Alhaji barin abinda yake yi yayi ya shafa kanta tare da kamo hannunta ta zauna a kusa da shi, yana murmushi ya ce, “Mai jiddan babanta kina so idan kika tafi na zauna ni ɗaya ne nima? Kina son damuwa ya yiwa babanki yawa? Ke nake gani a gidan nan naji sanyi a rai na, ki yi haƙuri ko, in Allah ya yarda komai zai wuce, na kusa kawo miki Aunty da kuma ƙawa abokiyar hira, ba dai kina son ƙawa ba?”

Gyaɗa kai Majeeder tayo ta ce, “Eh Papi ina so.”

Murmushi yayi ya ce, “yauwá na kusa kawo miki ƙawa, kuma auntynki har da ƙanne za ta haifa muku, Mami za ki dinga ƙiranta ma, ƙawarki kuma sunanta Faɗima amma ana ce mata Banafsha, ita ma ta sanki, kuma tana son ƙawance da ke, su ma da suka yi musabaƙa a makarantar su ita ce ta zo ta ɗaya kaman yanda kika zo ta ɗaya.”

Majeeder da murna da farin ciki ta ce, “Wayyo Papi ina sonta sosai, dan Allah a kawo su da wuri, nima a mini ƙanne, ka ga sister Ramla ma da ƙannenta, Suhaila da Nabeela.”

Alhaji dariya yayi ya ce, “kinsan me Maman babanta?”

*****

<< Yar Karuwa 9Yar Karuwa 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.