Banafsha na ci gaba da kukanta, cikin kukan ta ke faɗin, "Me yasa sai ni? Komai ni? Daga wannan sai wannan, ina farin cikin komai ya zo ƙarshe mahaifiyata ta yi aure, nima na yi, ashe ba haka ba ne, Allah idan wani abun na aikata, na tuba ka yafe mini" ta faɗa tana sakin kuka mai tsanani, ga wani irin sarawan da kan ta ke yi, kaman ta cire kan ta huta.
Mami cikin damuwa ta ce, "Banafsha meyasa bakyason aiki da karatunki ne? Sau tari idan kika yi abu ina dukanki ne dan haushin da kike. . .