"Ai ke baki da matsalar rashin saurayi sai dai mu mu koka" wata matashiyar budurwa wacce ba zata kimanin 21-23 ba, wankan tarwad'a ce haka tana da kyau dai-dai gwargwado ta furta hakan tana zama a gefenta. Kallonta tayi da narkakkun idanuwanta masu hazo-hazo a cikinsu, fara ce amma ba shar ba irin farin nan mai ja a cikin shi. Tana da kyau ainun wanda ganin farko zaka shaida haka, sannan tana da d'an tsayo da jiki irin matan da ake kira full option wato komai ya ji.
Murmushin maganarta tayi tana cewa " kin. . .