Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Yasmeenah by Deejasmaah

“Ai ke baki da matsalar rashin saurayi sai dai mu mu koka” wata matashiyar budurwa wacce ba zata kimanin 21-23 ba, wankan tarwad’a ce haka tana da kyau dai-dai gwargwado  ta furta hakan tana zama a gefenta. Kallonta tayi da narkakkun idanuwanta masu hazo-hazo a cikinsu, fara ce amma ba shar ba irin farin nan mai ja a cikin shi. Tana da kyau ainun wanda ganin farko zaka shaida haka, sannan tana da d’an tsayo da jiki irin matan da ake kira full option wato komai ya ji.

Murmushin maganarta tayi tana cewa ” kin fiye zolaya Zuu”, ware idanu tayi tana cewa ” ai kema kin san gaskiya na fad’i, kina da samarin ki wanda ko yau aka ce ki fito da miji zaki iya fito da d’aya daga ciki ni fa?….ai sai dai zare idanu don banda takamaiman wanda zan tsayar” ta k’arashe maganar da d’an d’aci a harshenta. Dafa ta tayi cike da tausayi tace ” amma Zuu ai saurayi ba shi ne miji ba, sai ki ga ke da baki da kowa kin fara shiga daga ciki kin bar ni a nan”.

Dariya ta kwashe da shi tace ” imagination of the century!,,, wannan abu ne da baa zai tab’a faruwa ba ke dai ki godewa Allah kawai Yasmeenah”. Ta’be baki tayi tace ” baki san ikon Allah bane, yanzu dai tunda dai Baban bai motsa ba ai sai mu cigaba da addua Allah ya fito mana da nagari ko?”

Kafin ta kai ga cewa komai aka bud’e k’ofar aka shigo, doguwar mace ce mai jiki da tsayi duk maganar da sukayi a kunnenta suka yi shi. Sai dai ko a fuskarta bata nuna ba cewa tayi ” amma kun manta da aikar da akayi muku ne halan?, kun shige d’aki kun k’ule ko mai kuke tattaunawa ne da kullum baku gajiya oho “.

A tare suka mik’e suna cewa “yanzu zamu tafi Mama”, hijab Yasmeenah ta zara yayinda ita kuma Zubaidah ta yafa gyale akan doguwar rigarta sak’on suka amsa, kafin sukayi wa Maman sallama. Da idanu ta rakasu ta na mai cewa a dawo lafiya.

Dake gidan a nan unguwar su yake haka yasa suka tafi a k’afa cike da natsuwa, suna cigaba da hirar da basu gajiya da ita, yanda ka san ba gida d’aya zasu koma ba. Gidan Mama Ramatu suka shiga da sallama, da fara’a ta amsa tana cewa ” Aah ‘yan biyun Mama ne da ranar nan?, sannunku da zuwa “. Yauwa suka ce suna duk’awa, gaisheta sukayi ta amsa da fara’a tana tambayar su jamaar gida kowa lafiya suka bata amsa kafin suka k’arasa cikin parlorn.

Ruwa ta ajiye musu da abun motsa baki, sake gaisawa sukayi kafin ta zauna. Sak’on suka ajiye mata a gabanta, dubawa tayi sukayi mata bayanin sak’on. Amsa tayi tana bata nata sak’on da zasu kaiwa Maman, basu jima ba suka kamo hanyar tafiya gida.

Honk ake ta musu babu ko k’ak’kautawa, hakan ne ya sanya suka matsa daga kan titin don akan titi suke sosai. D’an wuce su motar tayi kad’an kafin akayi parking, na cikin motar bai fito ba sun d’an wuce kad’an aka bud’e k’ofar gaban motar. Sallama akayi musu cikin wata murya mai cikeda karsashi da aji, tsayawa sukayi ba tare da sun juyo ba suka amsa a hankali. “Nace ba…?”, ya furta da ya sanya suka waigo duka a tare ” Meenah bari inje, it might be my lucky day” ta furta in a whisper cikin tone d’in da tayi mata magana itama tace ” all the best”.

Wurin shi ta k’arasa cikin yanga, matsawa Meenahn tayi izuwa k’ofar wani gida. Ko 2 mins ba a rufa ba ta dawo fuskarta da d’an murmushi. “White blood cells ke fa yake kira”, ta furta cike da tsokana. Wara idanunta tayi cikeda mamakin jin sunan da ta kirata dashi, cewa tayi ” wai white blood cells, ke dai Zuu baki rabo da tsokana”. Murmushi tayi tace ” Ai gaskiya ne, je ki yana jiranki”, ok tace tana nufar wurinshi cikeda natsuwa da aji kamar kullum.

Da sallama ta isa wurin kanta a k’asa, amsawa yayi yana cewa ” Hajiya Yasmeenah”. Da sauri ta kalle shi jin yadda ya kira sunanta, a take ta maida idanunta k’asa don mugun kwarjinin da yayi mata. Sake cewa yayi ” don’t tell me you are surprised da na san sunanki well, you shouldn’t be dearest”.

“Ina wuni”. Shine kalmar da ta iya furtawa kamar an k’wato daga bakinta, that’s how she is ta na da tsananin kunyan samari hakan ne ma yake k’ara masu sonta. Lumshe idanu yayi ya bud’e “well, lafiya lau tunda na ganki and I’m sure you too are doing well”.

Gyad’a kai tayi kawai d’an turo baki yayi yana cewa ” ku shiga mota mu k’arasa gidan don I can see you are not comfortable here and nazo da batutuwa a baki na”. Cewa tayi ” no ba sai mun shiga ba, zamu wuce daga gaba sai ka biyo mu da motar taka ai gidan ba nisa”.

“My queen a k’asa ni ina cikin mota, ai bai yi tsari ba if that’s the case sai dai mu jera a tare zuwa gidan kin yarda?” Okay tace kawai don ya rufe bakin, rufe motar yayi suka jero har izuwa inda Zuu d’in take tsaye. Murmushi tayi mata kawai tana mata nuni da su had’u a gida.

A bakin gate suka tsaya, k’ureta yayi da idanu yana mai aika mata da wani kallo mai shiga jiki da ya sanya ta jan hulan hijabinta tana rufe idanunta, ajiyar zuciya ya sauke yana cewa ” sai fa kin yi hak’uri dani Meenah! By the way I’m Sarham Ali Yakub a custom officer na kuma ganki ina so hope I’m accepted”.

Zaro idanu tayi he’s so direct and straight forward, shi ko d’an sakayawan nan babu?. Rufe idanunta tayi tana murmushi, jin tayi shiru ya sa shi cewa ” gwara ma ki sani tun yanzu don ki saba, thats how I am ba k’arya nazo in yi miki ba aurenki zanyi in shaa Allah am I accepted?”.

Ta ramin yatsunta take kallonshi he’s way handsome and classy, yanzu ita Yasmeenah ce wannan bawa yake so? Wow the lord is wonderful, in ba Allah ba wa ya isa?.

”Uhmm?” Ya furta cikin son maimaita mata last question d’in shi, a hankali tace ” ka d’an bani time zan yi tunani”. Hararar wasa yayi mata yana shagwab’e fuska yace ” hear yourself well, wai in baki time this thing na since our forefathers dem dey do am and we are in the 21st century just give me my answer kinji love”.

“Ya rabb! Thing man is driving me insane” ta furta a k’asan ranta a fili kuma kai kawai ta gyad’a mai. Murmushi yayi a karo na d’ari ba d’aya, kunyarta tana kashe shi and yana sa shi k’ara diving in the pool of her love.

Tun tana rufe idanu sai da ya sanya ta sakin jiki dashi, hira suka sha har da murmushi kafin su ankare sun cinye lokaci mai tsawo don sai gab da magrib lokacin har su Muhsin da Khalifa suka dawo daga islamiyya, gaishe su sukayi suna masu wucewa ciki. Sai da suka k’ara more than 10 mins kafin suka yi sallama ta shige gida kamar kar su rabu da juna.

Da sallama ta shiga gidan fuska babu walwala ko kad’an, Mama dake kitchen ne ta fito tana amsawa ganinta ita d’aya ya sa ta cewa ” a’ah ina kika baro Yasmeenahn?”. Tunzura baki tayi sama tana cewa ” sarkin samari tana can tsaye da wani, Allah Mama na gaji zan daina fita da ita kawai ba zai yiwu duk inda na fita in dai tare da ita ne sai ta disashe haskena ba…”

A fusace ta katse ta da cewa ” kulll na sake jin wannan maganar daga bakin ki, ‘yaruwarki kikewa bak’in ciki?” Tunzura bakin ta sake yi tana cewa ” ni ba wai bak’in ciki nake ba Mama but try to understand me, duk fa inda zamu shiga tare ba a tab’a noticing d’ina ba hatta k’awayena sun koma nata har fa Saif ya rabu dani ne akanta haba Mama!”.

Ta k’are maganar da k’walla mai zafi, yayinda k’asan mak’oshinta ke mata d’aci Allah ne shaida bata bak’in ciki da ‘yaruwarta but ta gaji da kad’aici da rashin tsayayyen saurayi. Meenah is her younger sister but tafi ta da komai na rayuwa, haka za tunda ta girma ta dusashe duk wani haske da take tak’amar tana dashi.

Kallonta Maman tayi tana mamakin kalamanta, ba tun yau take hankalce da ita ba sai dai bata tab’a b’ara ta fad’i halinda take ciki ba sai yau. Dafata tayi cikin lallashi don bata k’aunar abun yayi nisa, domin in har ya wuce haka toh tabbas zata kawo matsala mai girma a cikin gidanta which is the last thing da za tai fatan ya ziyarce su.

She built her house ta raini yaran da soyayya, da kuma had’in kai. Rarrabewar kansu akan petty thing is a disaster cewa tayi ” haba Zubaidahn Baba, shi fa yawan samari da kike gani bashi ne ke nuna auren wuri ba Aa wannan farin jini ne daga Allah kuma dama kowacce mace da kalar k’arfi da tasirin nata.  Meenah da kike gani k’arfin jini take da shi kuma yarinya ce mai matuk’ar shiga rai shi ba komai ba, ki kwantar da hankalinki. Ban son kina sa damuwa akan wainnan k’ananun abubuwan ki sani wani hanin ga Allah hausawa suka ce wai baiwa ne kuma wani jinkirin alkhairi ne kin ji Mamana?”.

Lumshe idanu tayi kawai a hankali ta furta ‘toh Mama’ tana mai mik’ewa zuwa d’aki, tun ba yau ba ta san Mama ta fi son Meenah akan ta. Ko ta fad’i ko bata fad’I ba her kind gestures towards her says it all and she’s not complaining about that ita kawai damuwarta rashin mashinshini wanda bata raba d’ayan biyu akwai influence na k’anwarta a ciki.

Da idanu ta rakata tana mai sauke ajiyar zuciya, a fili ta furta ” Allah kar ka bawa shaid’an dama ya watsa min gida, ka san k’ok’arina da fad’i tashi na akan su ya Allah “. Tana a zaune har su Muhsin suka dawo daga islamiyya, basu dad’e da shigowa ba ne Yasmeenah itama ta shigo da murmushi a fuskarta.

Sannu da gida kawai tayi ma Maman tareda tambayarta Zuu ” tana ciki kamar ta kwanta ne” ta bata amsa cike da kulawa. Cikeda zak’uwa ta nufi d’akin nasu burinta ta zazzaga mata kanun labaran da ta kwaso, a kwance ta sameta tayi ruf da ciki. Fad’awa gadon tayi har tana bigeta ” sissy tashi kiji…..”

Idanunta da ta sha kuka ta d’ago tana kallonta, kamar sauna bata ko lura da canjin su ba ta fara rattafo mata zance kamar mai cutar magana. Sai da ta kai k’arshe da cewa ” yanzu kam ina ji a jikina kamar na samu Mr. Right d’ina, Allah ya kawo maki kema duk a had’amu mu tafi “, tab’e baki tayi cikeda k’unci tana cewa ” you should be thanking your stars……” Tana mai komawa same position d’in da take before.

Lakato tayi da baki tana kallonta don ita kam bata gane mai take nufi da kalamanta ba, sake dafata tayi tana cewa ” siss…..y” katse ta tayi ta hanyar jan dogon tsaki tana mai cewa ” you are disturbing..!” Daga haka ta wuce izuwa toilet murmuring some words under her breathe…

<< Yasmeenah 1Yasmeenah 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.