Skip to content
Part 3 of 4 in the Series Yasmeenah by Deejasmaah

Da idanuwa ta rakata tana mai mamakin halayyar y’aruwarta kamar wata mai juju, kuna zaman lafiya zata juye tayi ta bala’i wani lokacin kuma bata son ko kusa a rab’eta. Duk k’wak’war ka baka isa sanin me take ciki ba, inda sabo ai ta saba da ganin wainnan abubuwan. Amma kuma har yanzu ta kasa sabawa don baa haka take ba, and bata da wadda ta fita a duniya duk ko da tarin k’awayen da take da su. Ajiyar zuciya ta sauke jin ana kiran sallah, tashi tayi zaune ta na mai kallon k’ofar.

Tada sallah a masallaci yayi dai-dai da fitowar ta daga toilet, bata tanka mata ba haka itama bayin da ta fito itama ta shiga. Tsarki tayi ta chanja pad d’in jikinta kafin ta d’auro alwala ta fito, dadduma ta shimfid’a ta sanya hijabinta gabas ta fuskanta tana zama cikeda nutsuwa carbi take ja. ( Yake ‘yaruwata a irin lokutan da baki da tsarki baki da halin ibada, ba zama zakiyi da najasa ba a duk lokutan sallah ki dinga k’ok’arta yin tsarki da alwala ki zauna a dadduma kina azkaran da zaki iya- tsari ne sosai ga dukkan abin k’i. Ba wai ki zauna kina hira ko chatting mara amfani ba Alwala kanta kariya ce mai k’arfi ga d’umbin lada Allah ya sa mu dace).

Tana zaune a wurin har aka kira isha’i, sai da aka idar ne tayi adduointa ta shafa kafin ta tashi maida komai wajen shi tayi. Tana shirin fita sai ga kira ya shigo wayarta, d’auka tayi duk da bak’uwar number ne tafi bada Sarham ne ya kira. Karawa tayi a kunnenta ta na mai lumshe idanu a d’an kamewar murya yace “I’m outside”.

Ajiye wayar tayi tana jin bugun k’irjinta yana mai matuk’ar tsananta, dafe k’irjinta tayi tana mai karanta ” laiha illa anta subhanka inni kuntu minaz zalimiin”. Sai da tayi kusan k’afa 20 kafin taji d’an dama, wani hijabi ta nemo white color mai d’an tsayi don ya wuce gwuiwarta da hannayen shi. Sanyawa tayi tana sa turare kad’an da lip gloss kafin ta fito parlor.

Duka suna zaune ana ta hada-hadar cin abincin dare, d’an gaban Mama ta k’arasa tana shaida mata da tayi bak’o. A dawo lafiya tayi mata, k’ofa ta nufa cikin tafiyar da ta nuna sanyin da gwuiwowinta sukayi da harara ta rakata tana mai jan tsaki k’asa-k’asa.

A tsaye ta same shi yana jingine da gate d’in, kan shi da yake sakaye da face cap bak’a a sunkuye take. Maana yana mai kallon k’asa, cikin sassanyar muryarta tayi masa sallama. Amsawa yayi yana d’ago kyawawan idanun shi, wani irin kallo yake mata mai cike da ma’anoni fuskar shi babu walwala ko ta sisi.

A take ta runtse idanu don bata son ya gane a firgice take, balle har yayi tunanin tana mugun tsoron shi ne. ” Ba zaki bar zuciyata ta huta ba ko?”, sune kalaman da ya fito daga bakin shi yana mai k’ureta da maganan shi. D’an dagowa tayi tana mai dubanshi da kyau, saurayi ne d’an matashi haka mai kyau da aji. Fari ne tas don har ya d’ara ta a haske haka za kyau, kana ganin shi kaga Fulani cikakke babu mix har a maganar shi ma kuwa.

A d’an shagwab’e tace ” ko gaisawa bamu yi ba zaka fara complain ko?” Girgiza kan shi yayi yana mai cewa ” ba k’orafi nake ba Meenah, kema kin san abinda kika aikata who is he?”. Shiru tayi ta tabbatar munafukan unguwa sun shaida masa da tsayuwar ta da wani, ta kuma san tsananin kishi irin na Nazeem abinda ma ya sata firgicewa tun da ya kirata kenan.

“Shirun ki yana nufin abubuwa da yawa Meenah, yana da kud’i ko? “. Kallon shi tayi yanzu kam da kyau cewa tayi ” ai da yake ni mayyar kud’i ce dole ka tambaye ni hakan”. A d’an hasale yace ” it’s just a question, na san yana da kud’i since he’s even riding a sport car.”

“And so?” A irin tone d’in da yayi magana ta so yi, amma kasancewar ta mai sanyi ya sanya ko kad’an bai fita a yanda tayi niyya ba. Rather it came out a bit sweeter than her normal voice ” Yasmeenah ki gaggauta sallamar shi, don bai da muhalli a rayuwar ki na sha gaya miki baki da miji sai NI!! ” ya furta cikin d’aci da umarni.

Amsa ta bashi da ” then prove it Nazeem, na gaji da gafara sa ban ga k’aho ba “. Bud’e ido yayi yana cewa ” soon Baibee, na kusa d’auke ki in killace ki a inda yafi dacewa dake but……” Katse shi tayi da ” sai ka samu kud’in da zaka gina min aljannar duniya and bathe me with wealth ko?, Nazeem when will you understand that arziki Allah ne ke bayarwa a duk lokacin da yaga dama ga kuma wanda ya ga dama? Me yasa ba zaka iya aurena a haka with the little that you have ba? I love you the way you are and zan iya zama da kai a duk yanda kake”.

Girgiza kai yayi yana cewa ” no way, ke d’in ba kalar matar gidan haya bace….” sake katse shi tayi da ” toh kafin ka farka daga baccinka, wanda yafi so na zai k’wace ni and don’t ever blame me”. Dariyar da ta k’ara masa kyau yayi ya bata amsa da ” that’ll be the mistake that person will do, ke mallakina ne and nobody dares take you away from me”. Wuce shi tayi zuwa gida tana mai cewa ” don’t say I didnt tell you so…” A ranta tana mai jin haushin attitude d’in shi, don kawai yaga tana son shi.

Ko da ta shiga gida Zuu ta riga taci abincinta, zama tayi ta d’an zuba kad’an taci itama. Kallo sukeyi ana tab’a hira kad’an, har lokacin bata sake ta dawo normal ba dama ta san may be sai da safe zasu tashi kamar basu bane. Mama da sai da ta sake wa Zubaidah nasiha kafin dawowarta sai da ta kalle su, bata son d’abiar ta ita da take babba in bata tarairayi y’anuwanta ba who will do so?. Allah ya kyauta ta furta a hankali suna cigaba da hirar su, a haka har Baba ya dawo.

Ita da su Khalifa suka fita gate ta taya su bud’ewa, Baba ya shigo da y’ar motar shi civic one door ( comot mek I enter) silver color. Maidawa sukayi suka rufe kafin ya gyara parking d’in shi, sannu da zuwa sukayi masa su Muhsin suka amshi ledar da ya fito da ita zuwa ciki yayinda shi da ita suka jera suna ‘yar maganar su cike da so da shak’uwa mai tsanani.

Bai wani zauna a parlorn ba Mama ta bishi da abincin shi zuwa d’akin shi, jim kad’an ta fito da tsiren da ya shigo dashi da fura. Zuu aka bawa ta raba musu ita kuma ta koma wurin mijin nata.

Rabawa tayi ta bawa kowa na shi, amsa tayi ta nufi fridge ajiye nata tayi don bata iya cin tsire da dare haka ma furan. In dai har taci sai cikinta ya b’aci, shiyasa ma ta daina ci gwara ta hak’ura taci da safe. Tana ajiyewa ta wuce d’aki, wayarta ta janyo wai ko Sarham ya kira amma babu ko miss call guda d’aya ajiyar zuciya ta sauke kawai tana kwanciya. Dama ita bata iya hira mai tsayi ba, hardly ta kai 10pm bata yi bacci ba amma da safe 4 am ta tashi sosai in ta samu dama take baccin rana.

Washegari lafiya suka tashi ita da Zuu suna ayyukan su da ‘yan hirarrakin su har suke firar Nazeem da haukar shi, dariya sukayi duka inda Zuu tace ” kema ai kin san halin mutumin naki indai a kanki ne”. Ajiyar zuciya ta sauke tana mai cewa ” ni ko na sani, shiyasa ma ban tanka masa yayi haukar shi ya gama duk da ina son shi ba zan iya jiran shi ba in ance in fito da miji a cikin tarin masu son turowar zan ba d’aya dama sai dai yaji a salansa”.

Dariya ta sanya mai k’ara tana cewa ” ai yanzu dama wanda ya shirya ake aure ba wanda ake so ba, amma ki dai bi a hankali tunda dai duk kuna son junanku” uhmmm kawai ta iya cewa tana juya juya k’ullun da zasu yi alalan breakfast dashi. Had’a komai tayi ta d’aura ba tareda ta sake magana ba, a zuciya kuma tana jujjuya maganar ta gaskiya ta fad’i tana son Nazeem amma a kullum in dai zatayi sabon saurayi toh sai ta kula shi ko da bata son shi, yayinda a k’asan rai da zuciya take adduar ta aure shi don yana da qualities d’in mazan da take son aure.

Kammala komai sukayi, suka ware na Baba da Mama a coolern su daban, sai nasu Muhsin sannan nasu. To 7 suka kammala komai, komawa d’aki suka yi aka hau shirin tafiya makaranta. Doguwar rigar atamfa ta sanya mai brown da blue, rigar A-line ce ta d’aura d’ankwalin kayan tana yafa madaidaicin gele blue da ya hau da kayan. Ita kuma Zuu jallabiya (gumama) bak’a ta sa da gyale bak’i. Fitowar su yayi dai-dai da fitowar Mama daga d’akinta gaisheta suka yi ta amsa da faraa tana mai kallon gidan da yayi tsaf dashi sai k’amshi yake tashi.

D’akin suka shiga Baba da yake kishingid’e suka gaisar ya amsa yana mai mik’o musu kud’in motar su, a natse suka amsa har da godiyan su kafin suka fito. A tsanake suka ci abincin kafin fito zuwa makaranta, school d’aya suke sai dai department da level na kowa daban ita Meenah criminology take 200l while ita Zuu take Pol Science 300l tare suke zuwa sai dai dawowan su ya kan sha bam-bam.

Tsawon 2 days bata kuma ji daga Sarham ba, ba zuwa ba kira gashi bata da numb shi balle ta kira taji ko lafiya. Tun tana d’an saka damuwa a ranta don ya shiga zuciyarta farat d’aya, har ta fara cire shi ta fuskanci harkokin gabanta.

A gajiye take tafiya sakamakon tests d’in da sukayi har guda biyu wainda sun wajiga gayu ainun, lumshe idanu takeyi burinta bai wuce ta ganta a gida ta watsa ruwa ba. Tura gate take niyyar yi a sanda ta iso gidan nasu, ta bayanta ta jiyo Masculine voice d’in shi yana cewa ” kyakkyawata!”.

A d’an tsorace ta waigo don bata san yaushe ya iso wajen ba, shi d’in ne kuwa yake fitowa daga motar shi sanye cikin Emirati jallabiya ash color kan shi babu hula sai k’afar shi cikin bak’ak’en crocs. Simple dressing ne amma a idanuwanta yayi wani mugun kyau da kwarjini, ware su kuwa tayi ta zube a kanshi kafin ta d’an lumshe tana jingina da bango ta fasa tura gidan ta shiga.

Hard’e hannayen shi da ta lura yana matuk’ar k’aunar yi yayi yana cewa “yanzu fa kyakkyawa inda mutuwa nayi shikenan ko?” A hankali tace ” ai ban san inda zan ganka bane” Murmushi yayi kana yace ” cigiya ai ake sakawa kije gidan TV or radio gama the most simplest one kije wurin Malamar aji ki sa cigiya”.

Dariya maganar shi ta bata wai cigiya, hakan yasa ta d’an dara cikin natsuwa tana cewa ” sai in ce musu mene tohm?” Lumshe idanunshi yayi ” sai kice mijina ya b’ata yau kwana biyu ban gan shi ko ji daga gareshi ba kuma mun rabu lafiya, in an ganshi a gaya masa matarshi tana neman shi don Allah ya dawo gida” ya furta yana d’age gira guda d’aya. Da sauri ta sa hannu tana mai rufe idanunta cikeda kunya, dariya ya saka dama abunda ya sanya shi fad’in hakan kenan don sosai yake kewar kunyarta.

“Wuce gida!!!” Shine zancen da ya katse musu moment d’in da suke ciki, da sauri ta bud’e idanun tana mai kallonshi. Shi ma kallon shi yake yi har yanzu fuskar shi da dariya. Sake matsowa gaban su yayi cikeda jin haushin kallon da suke masa ya sake bud’e murya yace

“I said get innnn!!!”

Da tsawa a harshen shi haka yanayin shi ya nuna babu sauk’i ko na sisin kwabo, gimtse dariyar da yake yi yayi yana kallonta don so yake yaga iya gudun ruwan su daga ita har shi d’in.

Kasa motsi tayi yayinda fargaba ya cika zuciyarta, tana tsoron fushin shi amma baza ta tab’a bin umurnin shi a wannan karon ba. Dan haka ta tsaya k’ik’am tana kallon k’asa, tana jin yawon da idanuwan su suke yi akanta amma bata kalli ko d’aya daga cikin su ba sai rik’e jakarta da take jin ta mata nauyi tayi tam kamar za’a k’wace mata.

“Meenah don’t let me repeat myself! Ki wuce gida nace”. Ya sake jaddadawa yana mai matsowa gabanta, kyarma jikinta ya fara sai dai ta daure bata nuna ba all thanks to her brown hijab. Yanzu kam ran shi ya fara b’aci ba zai d’auki rainin hankalin gayen nan ba , ya za a yi ya fad’o musu haka babu sallama kamar an jeho shi bai kuma tsaya a nan ba sai ya musu hauka.

“It’s you that’ll get outta here, so ka duba hanyar da ta kawo ka nan and follow that straight!” Ya furta cikin authorative and coarse tone. Waigowa yayi ya tsaya a gabanshi ” Malam ai ban zo kan ka ba tukunna, and ko baa fad’i ba kai ne zaka bar nan wajen don baka da muhalli a nan!”

Dariyar rainin hankali yayi yana d’age girar shi yace ” ohhh really, I can see you gat some nerves well let’s see ” yana mai gyara tsayuwar shi. Yanda yayi d’in ba k’aramin hasala shi yayi ba, dama ga yanda ta kalle shi ta watsar. Hannu ya kai da niyyar ya janyo ta, hijab d’in ta ya tab’a ji kake tass ya d’auke shi da wata arniyar mari.

Da sauri ya saketa don tabbas marin ya shige shi ainun, gashi yazo mai a bazata. Dafe kuncin shi yayi yana mai kallon shi. “Ko a mafarki ka sake gigin tab’ata da k’azamin hannunka sai na datse shi, na lura da haukan ka magani yake nema.” Ya k’arashe yana nuna mai yatsar shi alamun gargad’i, sauke hannun da ya dafe kuncin yayi yana kallonshi, lallai ma gayen nan ya lura bai san ko shi waye ba.

“Ni ka mara?” Ya tambaya cikin son tabbatarwa, gyad’a masa kai yayi in affirmation. Kafin yace ” yes na mareka, ko yanzu ka kuma kwatanta abunda kayi niyya sai na kuma and you have nothing to do”. Hannu ya d’aga kamar zai rama sai kuma ya sauke hannun yana mai cewa ” just because kana da kud’i?” murmushin dake k’aramai kyau yayi yace ” Eh ina da kud’i” yana mai juyawa kanta da take rakub’e jikinta na mugun rawa jin yanda suke shirin tara mutane, da alamun tsoro a bayyane a fuskarta jira take ace ” arrr” ta arce.

Kallon tsaf yayi mata yana cewa “wuce ciki!!” A take kamar wacce aka sawa remote ta nufi gidan ko waiwaye babu, da sauri ya sha gabanta yana cewa ” dake zaa wulak’anta ni saboda ban da kud’i ko Meenah?”. Hawaye ne ya cika idonta cikeda tausayin shi, ta san duk wannan abunda yakeyi akan ta ne amma kuma ya kamata ya san annabi ya faku don haka ratse shi tayi baa tare da ta tanka ba.

Hakan ya sake tunzura shi ya isa gabanshi ya furta ” ka bar murna karenka ya kama zomo, aikin banza kake yi ba kuma zaka tab’a aurenta ba, domin Yasmeenah bata da mijin da ya wuce ni d’in nan!”. Kallon ka-ci-kai yai masa yana mai cewa ” mu zuba mu gani!” Daga haka ya fad’a motar shi yana janta cikin wani mahaukacin gudu yana mai b’ulale shi da hayak’i….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Yasmeenah 2Yasmeenah 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×