Kaicon Ilimi
Labarin Rayuwar Harira ‘Yar Talla
Alhaji Zakariyya, ya kamo dansa Sale mai kimanin shekaru goma sha daya a raye, tamau ya riko shi da hannun hagu, yayin da daya hannun nasa ke rike da bulala dorina, sai da suka shiga cikin gida, kana ya kwalla wa kanwar Salen mai shekaru tara da ‘yan watanni da haihuwa kira.
"Lantana! Lantana!! Zo nan."
Lantana ta iso a guje, ita din ma a tsorace take ta san halin mahaifinta da zafi da fushi, da ta iso, ta rakube a gefe guda. . .
Ma sha labari ya yi daɗi