Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Ya'yanmu by Kabiru Yusuf Fagge

Kaicon Ilimi

Labarin Rayuwar Harira ‘Yar Talla

Alhaji Zakariyya, ya kamo dansa Sale mai kimanin shekaru goma sha daya a raye, tamau ya riko shi da hannun hagu, yayin da daya hannun nasa ke rike da bulala dorina, sai da suka shiga cikin gida, kana ya kwalla wa kanwar Salen mai shekaru tara da ‘yan watanni da haihuwa kira.

“Lantana! Lantana!! Zo nan.”

Lantana ta iso a guje, ita din ma a tsorace take ta san halin mahaifinta da zafi da fushi, da ta iso, ta rakube a gefe guda, ta durkusa.

Alhaji Zakariyya ya daka mata tsawa, “Maimaita abin da kika gaya min.”

Cikin rawar murya da tsoro, ta ce “Uhm…uhm….Baba bai je makaranta ba, ….shi da su Yaroro….da Dan-ado ne… suka tafi garkar…Barau tsinko…..gob…ba.”

Kafin ta rufe baki, Alhaji Zakariyya ya tsula wa Sale bulala, wadda ta yi matukar shigar sa, ta dade masa baya.

Sale ya bankare, ya kurma wani wawan kuka “Wiiiiiwww, eyy….wawww! Wallahi na daina.  Wallahi ita ma idan ta je makaranta…..wayyo, wuwww!” Da saukar dorina da kukan suka katse abin da yake kokarin gaya wa mahaifin nasa. Mahaifin bai damu ba, ya ci gaba da zunbuda wa yaron dorina.

Da Sale ya ga babu sauki sai ya yi kokari da karfi ya ce “Wallahi Baba ita ma Lantana tana shiga ofishin Malaminmu ya dauke ta, ya dora a kan cinya…”

Dif! Alhaji Zakariyya ya tsaya da dukan, maganar yaron ta ja hankalinsa. Ya sake shi, ya ajiye bulalar a gefe, tsawon mintuna uku, har sai da ya ga Salen ya daina kuka, sannan ya dauki ruwan sanyi na leda ya mika masa.

“Sha ka wanke fuskarka.”

Yana kallon Sale ya aikata abin da ya sa shi, sannan ya ce, “Matso nan, na daina dukanka. Me ka ce Lantana tana yi?”

Sale ya kalli wurin da kanwarsa ke rakube, ya ce, “A makaranta ne kullum sai malaminmu ya kirawo ta ofishinsa, kuma idan aka tashi ma sai ya tsayar da mu, ya shigar da ita ofis, ya ce ni kar in shiga, kuma kar in fada a gida. Ran nan ma da na shiga cikin ofishin sai na gan shi ya dora ta a kan cinya….”

“Inna lillahi, wa inna ilaihi raji’un.” Haka Alhaji Zakariyya ke fada, a lokacin da ya yi duba zuwa ga Lantana, wadda ta kara tsorata, ta makale kanta.

Ya daka mata tsawa, “Dawo nan gabana.” A yanzu jikinsa bari yake yi kamar mazari.

Lantana ta dawo gaban mahaifin nata, tana kuka sosai.

Alhaji Zakariyya ya kara daka mata tsawa, “Yi min shiru, ba dukan ki zan yi ba. So nake ki  gaya min me malamin naku yake yi miki?”

Lantana da tsoro da muryar in’ina, ta fara cewa “Bayan… shi ne yake cewa in… zo… ofis zai ba ni alewa da kudin cincin, idan na je sai ya tube min kayana ya dora ni a kan shi, yana yi min wasa.” Ta yi shisshikar kuka, “Kuma, shi ma …Baba Liti abokinka yana yi min haka idan aka aike ni wurin shi.”

Baba Liti, abokin Alhaji Zakariyya ne, makobcinsa ne, yana sana’ar sayar da kayan yara irin su goriba da gawasa da tsamiyar biri da hallaka-kobo da sauransu.

Alhaji Zakariyya ya hada gumi yana bari, a ransa ya hada abubuwa guda biyu, kukan zuci da kuma sambatu, “Idan maganar yaran nan ta tabbata, lallai mutanen nan sun cuci rayuwata, sun gama da ni, sun cuci yarinyar nan. Allah ka sa ba gaske ba ne.”

Bai san maganar zucin ta shi ta fito fili ba, sai ji ya yi, Lantana cikin tsoro tana cewa “Wallahi da gaske ne Baba.”

Ya yi firgigit, ya dawo da hankalinsa garesu, ya dubi Sale a fusace, “Tashi maza ka je gidan Malam Lauwali ka kirawo min Harira.”

Sale ya falla da gudu, dan lokaci kadan ya dawo, tare da Harirar. Yarinya ce, makobciyarsu da suke makaranta daya, kuma ya san a wani lokaci sukan dawo tare da ‘ya’yan nasa, ta dan girme su, domin su suna aji biyu da uku ne, ita kuma tana aji hudu.

Ta gaishe da shi, ta kuma dubi Lantana.

Alhaji Zakariyya ya ce, “Harira me kika sani game da rayuwar Lantana a makaranta?”

Harira ta sake duban Lantana, ba ta fahimci tambayar ba, don haka ta ba da amsa da cewa, “Babu abin da na sani.”

Gaban Alhaji Zakariyya ya fadi, yanzu yake tunanin yana neman tonawa kansa asiri ne, tambayar Harira da yake yi tonon asirinsa ne. To amma yaya zai yi? Ya dubi Sale “Yaya sunan malamin?”

Sale ya ce “Sunan sa Malam Badau.”

Alhaji Zakariyya ya dubi Harira dake raba idanu a tsakanin ‘ya’ya biyu da mahaifinsu, ya ce mata “Wane hali kika sani game da Malam Badau?”

Gaban Harira ya fadi, a ranta ta ce, “Allah ya raba mu da Malam Badau.” Domin ya hana rayuwarta sakewa a makaranta, ya takura mata da son ya taba jikinta, ita kuma ta ki yarda. Kusan kullum sai ya sa ta yi shara ko gwale-gwale iri-iri, haka kawai ita ba fashi ba, ba latti ba, ba rashin kokari ba, ba surutu ko laifi ba. A yanzu ma zaman da ake ya ce a satin nan zai yi mata bulala talatin da biyar ya kore ta.

“Ke nake tambaya!” Alhaji Zakariyya ya daka mata tsawa.

Ta tsorata, ba za ta iya fada ba, tana ganin idan ta fada Malam Badau zai ji, za ta dandana kudarta. Tana rawar baki ta ce, “Ban…ban sani ba Baba.”

Alhaji Zakariyya ya kalle ta cikin tausayi a ransa ya ce, “Da alama ita ma Badau din ya yi mata tsiyar.”

“Tashi, je ki.” Ya ce da ita.

Farko abin da Alhaji Zakariyya ya fara yi, shi ne ya kai ‘yarsa asibiti aka duba ta, likita ya tabbatar da abin da yake zargi, don haka ya kuma bincikawa.

Abu na gaba da ya gano, ya kuma ba shi mamaki shi ne; ashe matarsa ta taba samun labarin faruwar hakan, ta ce a yi shiru, wai tonon asiri ne gare su.

“Ai yanzu ga tonon asiri nan ya bata rayuwar ‘yarki, kuma dole a sani. Amma da tuntuni an yi wa tufkar hanci da ba a kai ga haka ba,  komai dadewar karya sai ta bayyana karya ce.”

Abu na gaba da ya yi, shi ne ya kai kara ga hukumar ‘yansanda, ya yi bayanin cewar an yi wa ‘yarsa fyade. Ya kuma sanar da wadanda yake zargi da laifin, aka kamo su, aka kulle shi, don yin bincike.

*****

Ranar Litinin da safe, Harira ta shirya cikin kayan makaranta, tana rataye da jaka, sai dai kuma tana dauke da farantin robobin kokon siyarwa. Haka take yi kullum idan ta shirya zuwa makaranta sai ta dauki tallan koko, da yake hanya ce, idan ta je, ta sayar da kokon, sai ta bayar da ajiyar farantin da robobin ta wuce makaranta, idan ta taso kuma sai ta biyo ta amshi abinta, ta wuce gida.

Malam Lauwali shi ne mahaifin Harira, kamar yadda ‘yarsa ke son karatu, haka shi ma yake so mata. Sai dai rashin karfin da yake da shi da kuma abin da ba a rasa ba na rayuwa.

Yankan farce ne sana’arsa. Saboda rashin karfin tallafawa iyalinsa ne ya sa matarsa Indo ta zama mai sana’a goma maganin mai gasa, safe, rana, yamma da dare. Kuma duk Harira ce ke yin dabdalar daukar mata tallan don sayarwa.

Duk da zuwa talla da Harira ke yi, takan yi kokarin zuwa makaranta a kan lokaci, ba tare da ta yi latti ba, musamman a boko, saboda idan ta yi lattin ana yi musu hukunci mai tsanani, musamman ma a ce Malam Badau ne a kan aiki.

Ta isa gab da kofar shiga makarantar, a nan ta hadu da kawarta Mairo, suka gaisa, “Yau mun zo a tare.” In ji Mairo.

Harira ta yi dariya, “Na ci sa’a yau ba ki riga ni zuwa ba.”

Mairo ma tana da kokarin zuwa makaranta a kan lokaci, ga kuma kokari a aji.

Lokacin da suka shiga cikin makarantar, mai gadi suka tarar da zungureriyar tsabgarsa, kamar kullum yana zare idanu, wani tsamurmuri ne mai duguzuzum din gashin baki mai kama da shekar kurciya, wanda ya yi wa bakin da’ira, idanunsa jajaye ababen tsoro, ba shi da afkin jiki sai afkin bala’i da cin zalin yara. Yana daya daga cikin masu hukunta yara idan sun yi latti ko idan aka tashi bai ba su damar fita ba, suka yi kankanbar fita. Sau tari yara sun fi tsoron kamanninsa fiye da dorinarsa.

Yau Malam Badau ba ya wurin da ya saba zama. Daman duk a malaman makarantar tun daga shugaba har zuwa malamin aji daya, babu mai zuwa da wuri sai Malam Badau sai kuma maigadi, kuma su ake bari idan an tashi, yaran makaranta suna ganin suna zuwa da wuri ne domin su yi dukan latti.

Ragowar malaman ma idan suka zo ba sa shiga ajujuwan yaran har sai an je hutun cin abinci an dawo, sannan daidaiku ke shiga aji, wasu ba sa zuwa ma bare su shiga ajin, sai ko a lokacin karbar albashi za ka gansu.

Malama Rukayya, ita ce malamar ajin su Harira, bayan dawowa daga cin abincin yara ta shiga ajin. Kodayake wasu lokutan tana shiga da wuri, saboda dalilin; ko don ta yi cinikin ‘yan kayayyakin sayarwar ta na daure-daure kamar irin su garin bididis, alewar madara, majinar-Bature, dan tamatsitsi, tsamiyar biri da sauransu. Idan tana wannan kasuwancin, musamman idan kasuwa ta yi kyau, takan yi wa yaran ajin tatsuniyoyi da wasu labarun hikaya, idan kuwa ba su saya da yawa ba, sai ka ga ta cika ta batse da fushi, tana hararar su, duk yaron da ya yi magana kuwa sai ta tsula masa bulala.

Ta fara kiran sunayen yara daya bayan daya, duk yaron da ya zo sai ta rubuta masa ya zo a cikin rijistar ajin. Yara daidai har tamanin da biyu sun zo a cikin yara dari da  hudu na ajin.

Ta kammala, tana nishi, sannan tana kallon yaran daya bayan daya, can ta lura da Harira tana kallon ta, ta daka mata tsawa.

“Ke mene ne?”

Harira ta mike, tana daga hannu, ta ce “Malama ina da tambaya.”

Cikin fushi Malama Rukayya ta ce “Tambayi in ji.”

Harira ta ce, “Malama kamar yadda kika ce a rinka gaya miki matsalolinmu, to malama a wancan satin gabadaya malami daya ne kawai ya yi mana darasi, wato Malam Rufa’i; malamin Arabiyya sau biyu, daga shi babu wanda ya yi mana darasi, a malamai har ke.”

Ajin ya yi shiru, wannan ya kalli wancan, waccan ta kalli wannan, Malama Rukayya ta fahimci akwai masu son yin magana a cikin yaran, don haka ta ce.

“Akwai wani mai son yin magana kuma?”

Kafin ta rufe baki yara uku suka daga hannu. Ta kalle su daya bayan daya da idanun tsoratarwa, ta bai wa shugaban ajin dama “Rufa’i Bello ina jin ka.”

Rufa’i ya mike, ya ce “Kuma Malama wallahi tun da muka shiga aji hudu ba a yi mana darasi da yawa ba, har gara-gara aji uku.”

Ta dubi daya yarinyar da ita ma ta daga hannu don yin magana, ta ce “Saura ke Labila.”

Labila Aliyu Mustapha ta mike, “Aunty, kuma malaman ba sa zuwa da wuri, idan suka zo sai su rinka hira a sitafirum, ko a bakin ofishin hedimasta.”

Malama Rukayya ta girgiza kai, kamar ba za ta bai wa daya yaron dama ba, ko me ta gani sai dai ta ba shi.

Abubakar ya mike ya ce, “Kuma idan aka kirawo su ba sa zuwa aji.”

Malama Rukayya ta yi jim na dan lokaci, kana ta dago kanta, ta dube su, sun lura ranta ya baci, ta daka musu tsawa, “Wane ne ya gaya muku abubuwan da kuke tambaya ta?”

Suka yi shiru, kowa yana tsoro, “To, bari ku ji in gaya muku, duk yaron da ya kara yin wannan maganar sai na zane shi. Ko ba ni ba, ko wani Malami kuka yi karambanin gayawa sai na zane yaro ko yarinya, kuma na kore shi daga makarantar nan. To da kuke yin irin wannan maganar wane ne a cikinku ya taba kawo kudin makaranta? Dukkaninku fa kyauta ake koya muku karatun, ko….”

Wani dan figigin yaro mai muryar tsattsewala ya kutso da maganarsa tare da katse ta, “La! Aunty kin taba sa mun kawo miki naira acilin-acilin fa kudin caf (alli)…”

“Kaniyarka!” Ta katse shi ita ma, tana yi amsa dakuwa, “Taso nan.”

Ilu ya taso cikin tsoro, ya zo kusa da ita, ta rankwashe shi a kai, “Ja’iri mai kan goriba, ana magana kana magana. Tafi can ka zauna.” Ta dubi sauran yaran ajin, “Wallahi duk dan iskan yaron da na ji ya yi kyas da wannan magana sai ya dandana kudarsa, ja’irai kawai.”

Bayan ta dade tana yi musu muzurai da zare idanu, ta tattara kayanta, ta shuri takalmanta ta yi waje.

Yara dai suka yi jugum, sun rasa abin yi, kamar ruwa ya ci su. A wunin ranar nan, malamin Hausa ne kawai ya shiga ajin, ya yi musu darasin yadda ake yin gaisuwa a al’adance.

Bayan an tashi, Harira tana tafe da kawayenta, suna hira.

Harira ta ce, “Kun ga fa a sauran makarantun ba haka ake yi ba. A makarantar su Murja kullum sai ta nuna min an yi musu darasi guda biyar ko shida.”

Mairo ta ce, “Ai su ta kudi ce ko?”

“To in ta kudi ce, ai makarantar su Salame ba ta kudi ba ce, kuma ana yi musu karatu sosai. Kuma fa malaman nan gwamnati tana biyan su.” Ta dan yi shiru, kafin ta dora da cewa, “Gaskiya ni da Baba na zai mayar da ni can wallahi da na gaya masa.”

Samira ta ce, “Kuma ga yawan duka a wannan makarantar tamu.”

“Ita kuma, wannan Malama Rukayyar sai ta rinka kawo kaya da tsada ta ce ba za a sayi na kowa ba sai nata. Dubi wai dan-tamatsitsin da ake sayarwa hudu naira biyar ita daya da rabi take sayar wa naira biyar, har gwara Malama Talatu ko Malama Inno, ko Malam Mai-‘Yanyara, sun fi ta arahar kaya.” In ji Mairo.

Samira ta amshe da cewa, “Wai kuma fa a haka za mu je gasar karatu da sauran makarantu, ko me za mu yi idan mun je?”

Harira ta dube ta, ta ce “Haka za mu je, mu kokarta, ai ba su muka yi wa ba, kanmu za mu yi wa, kuma Allah shi zai shige mana gaba.”

Haka dai yaran suke tattauna matsalolin da ke kewaye da su a makaranta. Malaman nasu sun mayar da makarantar dandalin hira, kuma wurin kasa hajarsu don sayar wa yara, da sansanin zuwansu don su huta su yi hira. Ba su damu da su yi wa yaran darasi ba. Sai ka ga Malami a sati yana da shiga aji (period) a kalla sau takwas zuwa goma a mako, amma bai fi ya shiga sau uku ba, wasu malaman ma ba sa zuwa makarantar ma gabadaya.”

Abin ba dadin ji, wai wawa ya zagi uwar Dagaci. Masu kokarin shiga aji a kullum su ne masu zuwa don sayar da kayan kwalam da makulashe ga yara. A kalla duk wani kayan kwalam da makulashe, duk wani kayan ci da sha, to malaman nan suna sayar da su a ajujuwan yaran.

Wani lokaci siyen yakan zama dole ga yara, don malaman suna tilasta musu.

*****

A ranar Talata, kamar kullum, Harira a gaban kokonta sanye da kayan makaranta, tana ta hada-hadar sayarwa. Wani mutum a can gefe shi da abokinsa suna shan kokon da suka saya a wurinta.

“Allah sarki, ita fa yarinyar nan kullum, sai ta siyar da koko take tafiya makaranta. Gaskiya tana da kokari wallahi.” In ji daya.

Dayan shi ma ya dubi inda take, “Riba biyu take ci, sana’a da karatu, abin da ka rasa.”

“Me kake nufi?”

“E, kai dai kana sana’a, amma ba ka yi karatu ba. Ko ka taba yi? Ka taba tsugunno a gaban Malam, ko ka taba shiga aji?”

Ya yi shiru, don bai taba ba.

Allah ya taimaki Harira, ta gama sayar da kokonta, ta hada kaya, ta bayar ajiya. Sannan ta wuce makaranta.

Yau da wuri, bayan kwanaki masu yawa, da ya yi bai shiga ba, Malamin lissafi ya shiga ajin su Harira, ya yi musu darasin lissafi, a kan ‘tarawa (+)’. Ba shi da kwarewa ko kadan, don haka ba ya dadewa, ba ya wuce mintuna goma sha biyar ko sha shida yana yin darasi. Yana gama rubutawa, ya dubi yaran.

“Ita ‘tarawa’, ana yinta ne, a ba ka lamba ka gama ta da wata lambar da aka ba ka. Don haka kowa ya dauko littafinsa ya kwafa. Zan dawo in duba.” Ya fice.

Mairo ta dubi Harira, “Harira kin gane kuwa?”

Harira ta ce, “Ai bai yi bayanin yadda za a gane din ba. Ni dai na kwafa. Gaskiya ya kamata mu gaya wa shugaban makaranta halin da muke ciki.”

“Lalala, ba ruwana.” In ji Mairo.

“To mene ne na rashin ruwanki? Ni ina goyon baya.” Labila da ke gefe ta sa musu baki.

Mairo ta dube ta ta ce, “To idan shi ma hedimastan halin su daya fa?”

“To ai ba mu tabbatar ba, kawai idan aka fita cin abinci mu je, mu gaya masa.” Cewar Harira.

A wajen cin abincin, Harira da Mairo da Labila da Rufa’i da Loto da Rabi’u suna tattaunawa a kan za su je, su gaya wa hedmasta abin da ke faruwa. Bayan sun gama tattaunawar, sai aka nemi wane ne zai yi bayani a matsayin jagora, kowa yana tsoron abin da ka iya biyo baya, caraf Loto ya ce shi zai yi masa bayani.

Harira ta yi dariya, ta ce “Ai kai ka yi kankanta, ka bari ni zan yi masa.”

Suka yarda da cewar, Harira ce za ta yi magana idan suka je. Da suka gama abin da za su yi, sai suka dunguma zuwa ofishin hedmasta, suna gab da shiga sai ga Malama Rukayya ta zo fitowa daga ofishin, ta dube su. Sun razana da ganin ta, ta daka musu tsawa, “Kai ina za ku je?”

Suka yi cirko-cirko, suka kasa yin magana. Ta fara matsawa gare su, tana kokarin sake yi musu magana, ta ji an kwalla mata kira har sau biyu.

“Malama Rukayya! Malama Rukayya!!” Mai yin kiran ta yafito ta da hannu, da alamun tana gaggawar bidarta.

Malama Rukayya ta juya, “Ku tsaya ina zuwa.” Ta nufi wurin kawar tata Malama Shafa’atu. Yaran suka yi cirko-cirko. Daga cikin ofis, hedmasta ya hango su, ya kwalla musu kira shi ma.

“Kai, ku shigo mana, mene ne kuma kuka tsaya sai ka ce marasa gaskiya?”

Dukansu suka duru cikin ofishin a jere sai ka ce ‘ya’yan kaji.

“Mene ne?” Ya tambaye su bayan sun tsaya a gaban teburinsa.

Wannan ya kalli waccan, suka kasa magana, har sai da ya daka musu tsawa, “Idan ba za ku fada ba ku fice min daga ofis!”

Kamar za su fita din, sai Harira ta nisa, tana rawar murya ta ce, “Malam….malam, daman cewa muka yi….za mu zo mu gaya maka, ba a yi mana darasi a aji. Malamai ba sa shigowa sai kadan-kadan.”

Shugaban makaranta, Malam Tukur Buhari ya bi su da kallo daya bayan daya a nutse. Shakka babu abin da Harira ta fada gaskiya ne, ya san da faruwar hakan. To amma shi ina ruwansa, ko a koya musu, ko kar a koya musu, oho musu.

Ya yi wani tunani a ransa ya ce, “To amma fa tun da yaran suka fara ganewa, har suka fara magana to akwai matsala, domin za su iya sanarwa da kowa kenan.”

Ya kalli Harira da sauran yaran ransa a bace, ya ce, “Ku zauna a nan ina zuwa.”

Rawar dari suka fara yi da kyarmar jiki. Suka rakube cikin tsoro.

Har zai fita sai ga wani mutum ya shigo ofishin da ‘yarsa rike a hannu. Malam Tukur ya dube shi, ya ce “Yaya aka yi ka dawo bayan ka dade da tafiya?”

Mutumin, mahaifin yarinyar ya ce, “Dawowa na yi mu san abin yi, ko a fito da malamin da ya yi lalata da ‘yata ko kuma kai ka wakilce shi a ofishin ‘yansanda. Ni dai ba zan yarda ba, a ce makaranta ta zama matattarar bata yara da lalata musu rayuwa.”

Su Harira da ke zaune sun fahimci abin da ke faruwa. Wato wani malamin ne ya yi wa yarinyar da mutumin ke rike fyade.

Ganin su Harira suna sauraren su, ya sa Malam Tukur ya kore su.

“Ku tashi, ku koma aji zan zo in same ku.”

Bayan sun fita ya juya gurin mutumin, ya ce “Alhaji ka yi hakuri, ni fa na ce maka a yau din nan zan kawo maka malamin, bai zo makaranta ba ne, shi ya sa. Amma na san inda zan binciko maka shi.”

Mutumin ya cafe “Rainin wayon ne ya yi yawa, a ce malami kuna zaune da shi yana bata yara, shin kai a matsayin ka na shugaba kana ina?”

“Wannan abu fa tsautsayi ne, kuma ka san ba yawo nake da daliban a aljihu ba bare in san da faruwar sa. Za ta iya yiyuwa a can wajen makaranta ko kusa da gidanka abin ya faru, to kai kuma sai a ce maka kana ina hakan ta faru?”

A haka dai Malam Tukur ya  lallaba mutumin ya tafi da sharadin da yamma zai kawo masa Malam Badau da ake zargin ya yi fyade. Bai kuma komawa takan su Harira ba, har sai a lokacin da Malama Rukayya ta dawo ofis din.

*****

Karfe shida na yamma, yara ‘yanmata su takwas reras kowacce dauke da farantin talla, ire-iren su gyada ne, su gurjiya (dafaffu ko soyayyu) da fashen gurjiya, mangwaro, wasu dankali. Kamar kullum, haka suke jeruwa su tafi tallan kwararo-kwararo, lunguna, shaguna da kasuwanni, duk inda dai suke da tabbacin za su sayar da hajarsu, suna kurdawa su shiga, su siyar.

Harira tana daya daga cikin yaran, tana dauke da farantin gurjiya dafaffiya, tana tafiya a jere kafada-da-kafada da kawarta a wannan tallar ta yammaci, mai suna Jiddo, wata ‘yar shamilmilar yarinya mai siffar tsakuwa, tana da gulma kuma tana da shisshigewa mutane, ita ta shigewa Harira, suka zama kawaye.

“Ni fa ina zargin Karima, domin kullum idan muka biyo ta wurin nan sai ta shiga dakin wancan maigadin ta dade, wani lokacin ma sai dai fa ta same mu a bakin kasuwa.” In ji Jiddo.

Harira ta ce “A to, ita dai ta jiyo idan yin hakan shi ne dacewa a gurinta. Kuma ke me kike zargi?”

Jiddo ta ce “Ke kina ganin wani abu ba zai shiga tsakaninsu ba?”

Harira ta gyada kai alamun a’a “Ni dai na san malamin makarantar darenmu ya taba gaya mana hatsarin kebewar mace da namiji. Kuma ire-iren wadannan matsalolin a yawan yawon tallar da muke yi mun sha gani kuma mun sha jin abubuwan da suka faru a tsakanin ire-iren wadannan mutane da yara ‘yan talla ire-irenmu.”

“Uhmm. Ni wallahi ba zan iya yin abu idan mutum ya ce in yi ba.” Cewar Jiddo. Daga nan ta sauya zancen da fadin, “An ce yau babu makarantar dare, wai babar Malam Kabiru ce ta mutu?”

“E ni ma dazu ake gaya min a gida, kuma Baraka ma ta gaya min.” Harira ta amsa mata.

Jiddo ta ce, “Ke, na ji an ce kun kai malamar ku kara a makaranta, abin ya ba ni mamaki ashe dan makaranta yana iya kai malaminsa kara?”

“E mana.” Abin da Harira ta ce kenan, ta ci gaba da tafiya don kar ta dame ta.

*****

Kafin a kawo wa makarantar su Harira takardar cikewa don shiga gasa, da yawa daga mutanen gari sun ji sanarwar sanya gasar daga gwamnatin jihar Kano, karkashin gwamnan jihar. Shi kam hedmastan su Harira ko a jikinsa bai kawo cewar makarantarsa za ta shiga ba, domin mai daki shi ya san inda yake yi masa yoyo, haka su ma malaman daidai da rana guda ba su taba zaton dalibansu za su iya shiga gasar karatu ko ta ilimi ba.

Da aka kawo takarda, Malam Tukur hedmasta mamaki ya yi da sharadin da aka gindayawa gasar, amma da tuni ya jefa ta a kwandon shara, mataimakinsa mai suna Malam Hadi ya ba takardar.

“Ka ji wani zance, wato gasa sai ka ce ta Alkur’ani, wai dole sai makarantu sun shiga in dai ba akwai wata kwakkwarar hujja.”

Malam Hadi ya ce, “To ai sai mu nemo hujjar.”

Hedmasta ya harare shi “Karanta ka ji idan za mu iya samo hujjar mana.”

Ba zai iya karanta takardar ya fahimta ba don yana da matsala da Turanci, ya ce “Kana nufin ba mu da hujjar kenan?”

“To tana ina, kai ma da abin haushi.” Yana harararsa.

Malam Hadi ya ce, “To ai sai a dauki Dala ba tare da gammo ba.”

“Dole, tun da babu yadda za mu yi, ga shi tusa ta karewa bodari. Kawai dai idan ranar ta zo da malamin jarrabawa (edam officer) zan hada su. Wai kuwa a makarantar nan muna da malamin gasa (kuiz & debate teacher)?” Malam Tukur ya tambayi Malam Hadi.

Malam Hadi ya yi dariyar dolaye, “Wannan ai kai ka sani, ina zan san faduwar farashin bazawarar Kawuna?”

“Wallahi idan akwai ma na manta, bare ma ina ganin babu. Yanzu dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya.”

*****

Ranar Litinin ne za a gabatar da gasar mai taken: ‘Primary School Annual Debate’. Don haka malamin da aka wakilta, malamin jarrabawa, Malam Abdu Ado ya zabo yaran da yake sa ran za su tabuka wani abu. Yara biyar ya tantance, maza uku mata biyu, a cikin matan akwai Harira Lauwali, wadda shi kansa malamin ya fi yarda da wakilcinta fiye da na sauran, kuma ita ya zaba a matsayin ta farko a jagorancin.

A lokacin da ya tara su yake ce musu, “Ku yi hakuri daidai ruwa daidai tsaki, daidai karatun da aka  koya muku da shi za mu je wurin gasar nan da shi za ku kara da kowacce makaranta da aka hada ku, komai karatunsu kuma komai kwarewar malamansu da kwazon dalibansu. Abin da ba a so shi ne tsoro. Yau Juma’a, gobe Asabar da jibi Lahadi, za ku rinka zuwa da safe, za mu rinka yin darasi da gwaji na fafatawar da za a yi, ina fatan kowa ya rinka zuwa.”

Ya kalli Harira “Ke za ki jagoranci ‘yan’uwanku dalibai, za ki rinka fara amsa kowacce irin tambaya ko kuma jagorantar yi idan an bukata, ko daga hannu idan ta daga hannu ce, kuma ke za ki rinka sanar da su abin da ya kamata su yi a lokacin da ban sanar da su ba. Ina fatan kun gane?”

“Mun gane.” Suka amsa. Sannan suka fara yi masa tambayoyi.

“Malam wadanne irin tambayoyi ake yi? Kuma yaya yanayin yawan mutanen da suke zuwa wurin yake?” Harira ta bukata.

Malam Abdu Ado ya ce, “Duk tambayoyin da ake yi, ana yi ne a kan darusan da ake yi muku (lessons) musamman Turanci (English) da Lissafi (Mathematics) sai a wani lokacin akwai al’amuran yau da gobe na zamantakewa da suka shafi (Social Studies) ko (Current Affairs) ko kuma lafiya da motsa jiki (Physical Health Education).

“Yawan mutane kuwa kin saba da ganin su, kawai iyaye ne da wasu shugabanni za su karu, amma ku da kuka saba da dalibai kuke karatu a cikinsu ai yawan mutanen ba zai dame ku ba, kuma ma abin burgewa ne a wurinku ku ga kuna amsa tambayoyi a gabansu.”

Daya yaron, mai suna Mamunu Aliko ya ce, “Malam wane ne zai ba mu abinci a can, ko ba dadewa za a yi ba?”

“Tabdijan!” Malam Abdu Ado ya ce yana duban sama “Gaskiya fa, amma a sani na ku za ku tafi da abincinku daga gida ko kuma kudin siyen abincin.”

Daga haka ba su kuma cewa komai ba, suka zuba wa juna idanu suna tunani.

*****

Ranar Litinin da safe, misalin karfe tara saura ‘yan mintuna Harira da Mamunu da sauran yara suka hallara a makaranta a gaban Malam Abdu Ado don tafiya wurin gasa.

Yaran sun yi wanki, sun yi wanka. Wasu dauke da abinci a roba, wasu kuma sun riko kudin abinci, me ya rage? Sai tafiya.

Sun bata mintuna ba tare da an waiwaye su don tafiyar ba, har sun fara tunanin ko an fasa, sai daga baya suka fahimci ba fasawa aka yi ba, Malam Abdu Ado ne yake can yana karma-karmar neman kudin motar da za su tafi a tsakanin wajen hedmasta da mataimakinsa, abin ya gagara.

“Wai ina kudaden bajo da testimoniyal da na satifiket da ake siyarwa suke ne?” Malam Hadi ya tuntuba.

Hedmasta ya bata rai, “Wa ya san inda suka shiga?”

Ran Malam Hadi ya baci, ya san an raina musu hankali, ya rasa me zai ce saboda haushi, kawai sai ya ce, “Ai sai su tafi a kasa ko su fasa zuwa.”

Malam Abdu Ado da Hedmasta da Malam Hadi suka yi shiru, kowa na yin numfashin takaici, kafin daga bisani Malam Abdu Ado ya fice daga ofis din ba tare da ya yi magana ba. Ya riski su Harira a inda ya bar su, yana zuwa wurinsu ya ce.

“Ku zo mu tafi.”

Yara suka bi shi yuuu, har suka fita daga makarantar, a tunanin su a nan za su hau mota, sai suka ga Malam Abdu ya dauki hanya a kasa, suka bi shi a baya kamar ‘ya’yan kaji, a cikin su akwai masu son yi masa tambayar su fa ba su gane ba wai an yi yamma da kare, amma suna tsoro. Suna cikin wannan hali ya juyo yana cewa.

“Ku yi hakuri fa, a kasa za mu je.”

Babu wanda ya tanka masa. Suka ci gaba da bin shi kawai. Sun yi tafiyar kilomita biyu a tsakani zuwa wurin taron gasar. A ka’ida a lokacin da suka isa, sun yi latti, amma Allah ya taimake su, an sami jinkirin zuwan gwamna da mukarrabansa. Don haka kafin a shiga dakin taron sai da suka zauna a farfajiyar wajen taron cikin sauran daliban makarantu suna hutawa.

Lallai gaba da gabanta aljani ya taka wuta, dalibai iri-iri su Harira suka gani, a tsammaninsu babu daliban makarantar da ba su fi su tsaruwa da sutturu ko yanayi na tsaf-tsaf ba.

Dalibai ne fes-fes, wasu sanye da sabbin kayan makaranta, wasu dauke da kayayyakin dalibai yara na debe kewa kamar su littafin roba ko biron roba da sauransu.

Da yawa a motocin makarantunsu suka zo yayin da su, suka zo a kasa duk kafafunsu sun yi budu-budu da kura.

Da yawa malamansu da iyayensu sun zo, sai tarairayarsu suke yi, yayin da su Harira suke zikau daga su sai malami guda daya, sun yi zuru kamar mujiyoyi. 

Da yawan daliban ana kara yi musu gwajin gasar a nan inda suke a zaune, yayin da su kuma su Harira ke tsaye suna kokawa da tunanin kwakwalensu na yadda za ta kaya idan yunwa ta matsa musu, kuma ga shi sun ga kamar babu wurin sayar da abinci bare su sayi abin sawa a baki ga wadanda suka zo da kudi.

Da yawa daliban akwai abincinsu a motocinsu, wasu suna ta shan ayis-kirim da siri-kanfo ko alewa mai zaki, su kuma ko oho. Kai lallai gidan kanari ba na dunbu ba.

Harira tana nan tsaye takure, jingine da wata bishiyar turare tana kallon ikon Allah, tana kallon bambanci, wata yarinya ‘yar shamilmila mai siffar belbelu, sanye cikin kayan makaranta masu dan banzan kyau da takalmin ta kwas-kwas, kanta ba dankwalin kirki, wanda hakan ya ba da damar ganin gyaran gashin da aka yi mata mai kyau, tana shan ayis-kirin, ta zo wucewa ta gaban Harira. Har ta wuce sai ta dawo, ta kalli Harira sama da kasa.

“Amma ke almajira ce ba ‘yar makaranta ba ko?” Tana magana da iyayi da kitifiri, “Kuma ai ba a ce almajirai su zo nan ba.”

Harira ta dukar da kai a sanyaye, “Mu ma daga makarantarmu muka zo yin gasa.”

Yarinyar ta dube ta da tsiwa, “Wai! Allah ya kiyaye mu yi gasa da ku talakawa.” Ta kuma dubanta daga kan fadenta zuwa fuskarta, “Ku ina kuke da kokari, Allah ya kiyaye, idan ma za ku tafi wallahi ku tafi na san ba za a bar ku, ku shiga ba, don ba irinku ne suke zuwa gaban gwamna gasa ba.”

Harira ta dukar da kanta cikin damuwa.

Gigiwar ‘yar shamilmilar yarinya ya sa ta tofa wa Harira yawu, ta jefa mata ayis-kirin a fuska, “Tun wuri ma ku fita kar ku ja wa mutane gwamna ya ce an fasa tun da almajirai sun fara shigowa. Na tsani ganin irinku a kusa da ni.” Ta wuce abin ta tana dariya.

Ba Harira da take hawaye ba, hatta sauran yaran da Malam Abdu da suka yi shiru, suna sauraron ta, ransu a bace yake, Malam Abdu Ado ya yi tunanin su yi tafiyar su, don kar wulakancin gaba ya ninka wannan, kawai sai suka ji jiniyar zuwan gwamna. Suka tsaya suna kallo. Suna gani gwamna da mukarrabansa suka fito daga motocinsu cikin hanzari, suka shiga dakin taron, sannan aka umarci wadanda suke waje kowa ya shiga.

“Yi hakuri, goge hawayen mu shiga, ba komai.” Malam Abdu Ado ya ce da Harira.

Lokacin da za su shiga sai da aka rinka kallon su, daya daga cikin masu gadin wajen ya tambayi Malam Abdu.

“Malam har da ku a taron ne?”

“Ga zahiri.” Malam Abdu ya ce da shi, sannan ya wuce, su Harira suka rufa masa baya suka shiga cikin dakin taron.

Dakin taron ya hadu sosai, bangaren alkalan gasa da wurin da ake gasar daban, bangaren gwamna da mukarrabansa da manyan baki daban, bangaren dalibai daban, bangaren malaman makarantu da iyayen yara ma haka.

A can gefe su Harira suka sami wuri, suka takure a kasa suka zazzauna suna raba idanu.

An fara bude taro da addu’a, sai kuma jawabin tuni na makasudin yin gasar, sannan sai jawabin gwamna, wanda a nasa jawabin ya yi bayanin yadda yawan makarantun ya koma ashirin maimakon goma ko takwas da aka saba, a cewar sa yin hakan zai kara bunkasa ilimi da baiwa wasu makarantun dama su ma a rinka damawa da su.

Daga nan mai gabatarwa ya bayyana sunayen makarantu ashirin da za su fafata a gasar, ciki har da Natsanbo Primary School; makarantar su Harira.

Mai gabatarwa ya yi bayanin karawar duka ta mintuna biyar-biyar ce a tsakanin makarantu bibbiyu, wanda a haka za a rinka tacewa har a samu makarantu biyun karshe da za su fafata a karshe a sami zakara a ciki.

Ya ci gaba da cewa, “Tsarin karawar har zuwa zagayen karshe za a yi shi ne kamar haka: Karawa biyar ce, wacce za ta kai makarantar ga zama zakara ta bana.

“Karawar farko a makarantu ashirin; goma ne za su kayar da goma, goma su tsallake zuwa zagaye na gaba kenan.

“Karawa ta biyu kuma biyar su kara da biyar, wanda za a sami biyar din da suka yi zarra. To a nan za a sami mutum daya dan-alfarma wanda aka kayar da maki kalilan sai a kara shi a kan biyar din can da suka yi nasara, wanda za su zamo su shida kenan, sai a yi karawa ta uku, inda a nan ma uku za su kayar da uku, a nan ma za a kara daukar dan-alfarma guda daya; wanda aka kayar da tsirar maki kadan, sai su zama su hudu, sai a shiga karawa ta hudu kenan, inda biyu za su kayar da biyu. Kuma biyun da suka yi nasara su ne za su yi karawar karshe wato karawa ta biyar inda za a sami gwarzuwar makaranta ta bana, wacce za ta lashe kyaututtuka…”

Mahalarta taro suka yi tafi da sowa. Da alama makarantu sun shirya, gaban su Harira sai faduwa yake, don su babu shiri, babu sabo.

Kaka-tsara-kasa, ga fili ga mai doki. Dalibai suka fara shiri, gaban wasu malaman yana faduwa, don ganin irin shirin da ake zaton kowacce makaranta ta yi, tare da tunanin mene ne sakamakon darusansu.

Darusan da za a yi tambayoyi a kansu guda uku ne, Turanci (English), sai Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Religion Knowledge),  da Lissafi (Mathematic), sannan Social Studies.

Wuyar aiki ba a fara ba. Nan aka fara gasar.

Sai  da makarantu bibbiyu suka kara, kafin a kira makarantar su Harira, inda ita Harirar ta mike, ta isa wurin karawar. Da kwarin guiwarta ta fita, domin Malam Abdu ya gaya musu kar su damu ko sun ci ko ba su ci ba babu damuwa a gare su, ita kuma Harira tana ganin to me zai hana su ci, su ba mutane ba ne?

A ka’ida duk yaron da aka kira akan yi tafi mai yawa, amma lokacin da aka kira Harira ta fita sai tafin ya zama raunanne. Ko don ita iyaye da malaman su ba su je da yawa ba ne? Oho. Da yake wasu makarantun har da ‘yan kallo dalibai suka zo. Ko kuma don yanayin kayanta na talakawa ne? Allah masani. Ta dai je gaban alkalan gasar.

Da mai gabatarwar ya lura dukkaninsu masu karawar, Harira da abokiyar karawarta Musulmai ne, sai ya fara yi musu tambaya a kan ilimin addinin Musulunci.

Harira aka fara tambaya. Nan da nan ta bayar da amsa, da yake ta sani a makarantar islamiyyarsu ta dare.

“Mene ne ma’anar Ubangiji? Da wane abu dan’adam ya san Ubangijinsa?”

Harira ta fara da cewa, “Ubangiji na nufin abin bautawa, mamallaki mai juya komai. Dan’adam yana sanin Ubangijinsa ta ayoyinSa da abubuwan halittarSa.”

Ya dubi abokiyar karawarta, “Da yaya ake bambance Annabi da Manzo?”

Ta kasa amsawa, ta tsaya tana duban wurin da malamansu suke.

Bayan an yi musu wadansu tambayoyin guda bibbiyu, sai aka umarce su, su zauna. Su kansu mahalarta taron sun san wadda ta yi nasara, bare alkalin gasar.

Bayan an karasa ragowar makarantun ne, aka kira sunayen goman da suka yi nasara a karo na farko, ciki har da Harira, wadda ‘yan makarantarsu, da malaminsu guda daya ne kawai suka taya ta murnar samun nasara. Sauran daliban makarantu taran kuwa ‘yan’uwansu, da malamansu da iyayensu kamar za su hadiye su don murna.

Allah sarki, a lokacin da Harira ta hango iyayen ‘yar shamilmilar yarinya mai suna Zabba’u suna taya ta murna sai ta tuno da nata iyayen, ta san mahaifinta na can wajen yankan farce, yana neman na abinci, mahaifiyarta kuwa a yanzu tana can gaban murhu tana yin abincin siyarwa, tana kuma fatan komawarta da wuri don ta daukar mata talla.

Ba tare da bata lokaci ba aka shiga zagaye na biyu, wanda kiran farko aka kira su Harira, ita da wani dan kabilar Igbo mai suna Chinedu Obu, wanda da a ce alkalan gasar za su dubi Chinedu sosai, da sun gano badda-bamin da aka yi musu, aka kawo musu wadan mutum dan shekaru ashirin da takwas a matsayin dan firamare. Ya kwalkwale fuskarsa kamar bayan kwarya, a dole shi yaro ne. Ba su lura da hakan ba suka hada shi da yarinya karama, Harira.

A kan darasin Turanci a ka fara yi musu tambayoyin. Babu tangarda Chinedu ya amsa tambayoyinsa guda uku daidai, ita kuwa Harira da kyar ta iya amsa biyu a cikin uku. Aka hada musu da darasin lissafi, a nan ne ta yi kokarin amsa nata ukun ita ma.

A wannan zagayen da aka gama, aka kira sunan biyar din da suka yi nasara, a ciki babu Harira, Chinedu ya kada ta, amma saboda makinta na da yawa, sai ta sami shiga alfarma inda suka zama su shida, ciki har da Zabba’u wadda ta yi wa abokan karawar ta zarra.

Harira ta gamsu da cewar dole Zabba’u ta yi musu gorin karatu, ashe kokari gare ta. Allah ya taimaki Harira ta sami alfarma da ta ji kunya, musamman irin kallon tsanar da Zabba’u da sauran mutane ke yi mata.

A zagaye na gaba, zagayen mutum shida Harira ta samu nasara babu tangarda, ta shiga cikin mutum uku da suka yi nasara. Zabba’u ma haka, domin ita ta kayar da Chinedu a wannan lokaci, sai dai da yake da kyar ta kayar da shi, shi ma sai ya samu nasarar shiga alfarma.

A zagaye na gaba, zagayen kusa da karshe, zagayen ragowar mutane hudu da suka hadar da Zabba’u, Chinedu, Harira da wata yarinya mai suna Surayya. Da aka fara kiran wadanda aka hada, sai ga shi an sake hada Chinedu da Harira, sai da gabanta da na abokan tafiyarta ya fadi, sun san shi kenan ta su ta kare. Shi kuwa Chinedu murmushi ya yi, ya fakaici idon mutane ya yi wa Harira gwalo, don ya san shi zai yi nasara. Ita ma Zabba’u dariyar keta ta yi mata.

Su Zabba’u ne suka fara, inda suka amsa tambayoyi a kan Turanci, suna gamawa kowa ya san Zabba’u ta lashe Surayya. Lokacin da Zabba’u ta tafi za ta zauna, ta kalli Harira ta yi mata gwalo, ta nuna da hannu cewar idan ta isa ta lashe nata abokin karawar.

Harira da Chinedu suka fara da Lissafi. Chinedu aka fara tambaya, yana da matsala da lissafi, nan ya rikice, ya yi zaton da Turanci za a fara, sai ya kasa bayar da amsa yadda ya kamata, aka maido da tambayar ga Harira.

“Fibe times twenty, dibide 2” (biyar sau ashirin a raba gida biyu. 5 d 20 ÷ 2=)

Nan da nan lissafi ya fado ran Harira, ta tuno wata rana za ta tafi talla mahaifiyarta ta aike ta, ta tuno da abin da ya faru a aiken.

“Kwano ashirin ne na kokon idan kika sayar Naira biyar-biyar ya zama Naira dari kenan. Ki raba kudin biyu zai zama Naira hamsin, ki yi cefane da rabi ki kawo min rabin, wato Naira hamsin.”

Nan take Harira ta ce “Is ekual to fifty 50 (ya zama hamsin 50)”

Su Malam Abdu suka yi tafi da sowa.

Aka yi wa Chinedu tambaya ta biyu. Ya yi jim, wanda har sai da ya fita daga lokacinsa sannan ya bayar da amsa.

Ita ma Harira aka yi mata tambaya ta biyu, ta amsa daidai. Tambaya ta uku, kuma ta karshe a kan Turanci ce, Chinedu ya amsa daidai, ita ma Harira ta amsa daidai. Kana aka sallame su, Chinedu yana hawaye ya tafi mazauninsa, ya san Harira ta kayar da shi, kuma ya gaza abin da aka sa shi yi, bai ci kwangilar da aka dauko shi ba, wadda ya yi kurin zai ci.

Ita kuwa Harira tana murmushi da murna ta isa wurin abokan tafiyarta ta zauna. A nata bangaren Zabba’u kamar ita aka lashe don bakin ciki, sai cika take tana batsewa, wai ita tana jin haushin nasarar da Harira ta samu.

Alkalin gasa ya bayyana sunan Harira da Zabba’u a matsayin wadanda suka yi nasara, kuma wadanda za su yi karawar karshe don fitar da gwarzuwar shekara ta bana.

Kaka-tsara-kaka. Babban takaicin Zabba’u shi ne; a ce da Harira za ta kara, wadda ta raina, take gani ba a bakin komai ba. Ta kudurce a ranta bayan ta kayar da ita, sai kuma ta yi mata wulakanci, don ta nuna mata ita ba sa’arta ba ce.

Ta dubi malamarsu da ke kusa da ita, ta ce, “Auntie ku yi murna don na lashe waccar kazamar yarinya, ba ta iya Turanci ba, kuma na fi ta iya lissafi. Kuma I swear idan na lashe ta sai na yi mata wulakanci a gaban kowa. Wallahi na tsane ta, ‘yar matsiyata ce kuma kazama.”

Malamar ta yi dariya, “Kin yi min daidai, ni ma ganin farko da na yi mata na ji na ba na son ta, ki wulakanta ta, ki nuna mata ke ba sa’ar yin ta ba ce.”

Bayan an dan yi hutun rabin lokaci, alkalai sun tattauna a tsakaninsu, sai aka yi kiran su Harira don yin karon karshe. Zabba’u ta taso cikin kasaita da kinibibi tana wani taku daidai, tana ta murna, tana dagawa masu yi mata tafi hannu.

Ita kuwa Harira lokacin da ta taso addu’a ta tsaya, ta yi, babu mai yi mata tafi, bayan ta shafa, ta tafi a hankali, wurin ya yi tsit, har sai da mai gabatarwa ya fara magana.

“To, komai ya yi farko, zai yi karshe, gasa ta zo karshe, ga gwarazan karshe nan za su yi karo na karshe da za a samu gwana kuma gwarzuwa a cikinsu, kuma a gaban gwamna da mukarrabansa.” Ya nuna Harira, “A haguna akwai Harira Lauwali ta makarantar Maitsango Primary School.”

Babu wanda ya tafa, sai su Malam Ado da daliban makarantarsu. Ya ci gaba da cewa, “A dama kuma akwai Zabba’u Dr. Bukar ta Successful Academy…”

Bai rufe baki ba sai da tafi da sowa na mahalarta taro suka cika wurin. Wannan ya nuna kamar akwai jari hujja a cikin al’amarin.

Da aka sarara, ya ci gaba “Za su kara a kan darussan Islamic Religion Knowledge da Turanci (English), da kuma Lissafi (Mathematics). Sai kuma ‘yan tambayoyin da suka danganci al’amuran da ke wanzuwa a yanzu (Social Studies/Current Affairs). A bisa tambayoyi bibbiyu kowannensu. Sai mu ce Allah ya ba gwani sa’a.”

Aka kuma yin sowa da tafi.

Zabba’u ta dubi Harira, tana magana a hankali “Dube ki kazama, matsiyaciya. Yau za ki gane bambancin mai shakar kyakkyawar iska da mai shakar iskar kwatami, bambancin mai cin mai kyau da mai cin mara kyau, mai sa suturar alfarma da mai sa tsumma. Bambancin mai karatu da isassun littattafai na rubutu da na karatu da kuma mai zuwa makaranta da yagaggen littafin eksasayes (edercise) babu littafin karatu (tedt book)”

Duk batun da Zabba’u take yi mai gabatarwar yana jin su amma bai hana ta ba, sai da ta gama don son ranta. A karshe ya mika abin magana ga alkalan gasar don su fara yin tambayoyin ga su Harira da Zabba’u.

Alkali na farko, ya fara da cewa, “Za mu fara da Turanci, sai I.R.K. sai kuma Lissafi, sannan kuma al’amuran yau da kullum da zai zo a karshe. Kowanne darasi akwai tambayoyi guda biyu, duk tambaya daya maki daya, idan aka hada tambaya takwas kenan. Don haka idan gwanaye sun shirya sun ja damara to zan fara.”

Ya yi shiru don ba su dama. Da ya dube su, sai ya ga alamar sun shirya din, sai ya ci gaba da cewa cikin harshen Turanci.

“Tambaya ta farko, kowacce daliba za ta kawo mana jumla (sentence) mai nuna umarni (direct speech).”

Zabba’u ya umarta a matsayin wadda za ta fara don haka cikin ji da kai ta amshi abar maganar, bayan ta yi gaisuwa ga gwamna, manyan baki da alkalai da sauran mahalarta taron, sai kuma ta gabatar da kanta da makarantar da take wakilta sannan ta bayar da amsa.

“I said, “I don’t understand you.” (ma’ana, na ce “Ban fahimce ka ba.” Kai tsaye ta fada ba gargada.

Mai gabatarwar ya ce, “Ya yi kyau.”

Mahalarta taro suka rude da sowa saboda yadda ta burge su wajen bayar da amsa, amma ban da Malam Abdu wanda shi kam haushin ta yake.

Aka dawo da abin magana ga Harira, ta karba hannu na rawa, sannan idanu da kwalla. Sai da ta yi dakiku tana tunani kafin ta ce bakinta na rawa, “The boy going to school.”

Dakin taron ya yi shiru domin babu labari, sai ‘yan guna-guni da ake. Zabba’u ta yi mata dariya.

Alkali na farko ya ci gaba da magana, “To yanzu sai tambaya ta gaba ita ce; a karkashin suna (noun) akwai suna na jinsi (gender) kashi hudu, kowacce daliba za ta fadi guda daya. Zan fara da Harira Lauwali.” Ya mika mata amsa-kuwwa.

Harira gani ta yi kamar yana sane ya fara da ita don ta fadi, kwallar dake cikin idanunta ta digo kasa, take tunanin ta ya tafi wani waje. Watarana suna hira da wata malamar makarantar sakandire dake unguwarsu, hirar ta kawo su kan suna (noun) da kashe-kashensa, har ta fado yi mata bayanin sunan jinsi (gender) ta tuno abin da ta ce mata a lokacin.

Daf da lokacin da ‘yan kallo suka fara ‘yan maganganu na ganin ta yi shiru, Harira ta ji bakinta na fadin da Turanci;

“Na daya boy (yaro) a karkashin jinsin da ke wakiltar sunan namiji (masculine gender). Na biyu akwai girl (yarinya) a jinsi mai wakiltar sunan mace (feminine gender). Na uku teachers (malamai) a karkashin common gender (gama-garin jinsi). Na hudu tree (bishiya) a neuter gender (mara mace ko namiji)…”

Tun kafin ta karasa wani bangare na taron suka yi tafi don ta burge su, ba su yi zaton za ta iya fadar komai ba a wannan tambayar sai ga shi ta bayar da amsa daidai. Su Malam Abdu da dalibai ‘yan’uwan Harira har da tsallen farin ciki da murna.

Bayan an nutsu ne aka bai wa Zabba’u dama. Cikin fushi, rai a bace wadda ba ta ji dadin amsar da Harira ta bayar ba, ta amsa tata tambayar da sauri ba tare da bata lokaci ba, aka yi mata babban tafi.

Karo na gaba, a bangaren I.R.K. ne, wani alkalin ne ya amsa a matsayin mai yin tambayoyin. Kai tsaye tambayoyi biyu ya yo a jere, inda ya fara da tambayar Zabba’u. Ya ce.

“Tambaya ta farko (1) sharuddan sallah guda nawa ne? Tambaya ta biyu (2) Me ya sa ake yin addu’a?”

Kowa a wurin ya yi shiru, har Zabba’un da ake jira ta amsa, wadda take amsa tambayoyinta cikin sauri, amma wannan lokacin shiru kake ji malam ya ci shirwa. Ita a islamiyyarsu, karatun Alkur’ani kawai ake koya musu, ba sauran littattafai.

Tsawon lokacin da aka yanka mata ya cika ba ta bayar da amsa ba, har aka kara mata, amma shiru, ranta sai kara baci yake yi. Alkalin gasar ya yi murmushi, ya kada kararrawa, yana cewa.

“To Zabba’u Dr. Bukar ta gaza, yanzu za mu mika tambayoyin ga Harira Lauwali.” Ya mika mata amsa-kuwwar.

Tuni Harira ta kissima yadda tambayoyin suke a ranta. Ta yi jira ne da fatan idan Zabba’un ta amsa nata tambayoyin, ita ma a yi mata masu sauki kamar haka. Sai ga tambayoyin sun dawo gareta, ta amshi amsa-kuwwar ta fara amsawa.

“Amsar tambaya ta farko ita ce; sharuddan sallah guda biyar ne, su ne; (1) Musulunci (2) Hankali (3) Balaga (4) Tsarki da samun dama (5) Shigar lokaci.

“Amsa ta biyu, ana yin addu’a ne domin dukkan halittu matalauta ne a wurin Allah (S.W.T.), mabukata ne ga abin da yake wajensa (Allah), shi ya wadatu daga su, ba ya bukatar komai daga wurinsu, Allah da kansa ya wajabta wa bayinsa yin addu’a, inda ya ce “Ku roke ni zan amsa muku… a karshen ayar “Lallai wadanda suke girman kai game da ibada ta (addu’a) za su shiga wutar Jahannama suna madawwama. Kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya ce “Dukkan wanda ba ya rokon Allah, to Allah yana fushi da shi.”

Ustazan da suke wurin da sauran mutane suka yi kabbara ga Harira. Zabba’u kuwa kamar ta fashe don bakin ciki.

Bayan an gama da karawa a kan I.R.K. sai alkali mai tambaya a kan Lissafi (Maths) ya karbi abin maganar, domin yin ta shi tambayar. Bayan gaisuwa, ya fara da cewa cikin Turanci.

“Tambaya ta farko za a bayar da amsa ne da baki, tambaya ta biyu kuwa za a rubuta ne a allo.” Ya nuna allon da ke tsaye a gefensa, akwai maka (marker) a wurin. Kana ya dora da cewa, “A nan zan fara da Harira Lauwali ta makarantar Maitsango. Tambayar ita ce; ‘8 ÷ 2 d 4 + 7 – 5 = ’

Tab, dakin taron ya yi shiru, Harira ta yi kuri tana kifta idanu, ta rinka maimaita tambayar a zuciyarta. A can bangaren ‘yan makarantarsu, ragowar daliban murna suke yi da ba su suka wakilci makarantar su ba, domin da an ji kunya, Harira ta fi su kokari, su ma sun yi mamakin ta.

Harira tana cikin tunani ta ji alkalin gasar yana cewa “Kina da ragowar mintuna uku da sakanni kafin a kada kararrawa.”

Tunaninta ya zurfafa ga yadda take yin kasuwancinta a wurin talla, ta tuno yadda take raba takwas gida biyu, ta tuno yadda biyu take kasancewa sau hudu, ta tuno yadda take tara hudu da bakwai da yadda take debe biyar a cikin bakwai ta bayar da canji idan ta kama.

Daidai lokacin da mintunanta ke kokarin cika, aka ji muryarta cikin rawa tana ba da amsa da cewa.

“Eighteen ‘18’’ (sha takwas).

“Correct’”(kin yi daidai) in ji alkalin gasar.

Aka rude da tafi. Wasu daga masu yin tafin suna yi don dole, saboda kokarin da Harira ke nunawa na bayar da amsa da ba su zaci za ta iya bayarwa ba.

“Yanzu saura Zabba’u Dr. Bukar. Tambayar ki ita ce; 2 d 8 ÷ 8 + 5 – 4 = “

Minti daya tsakani ta bayar da amsa cikin kwarewa ta ce; ‘is ekual to three ‘3’’ (amsar ita ce uku ‘3’)

Kafin ta rufe baki an rude da sowa da tafi. Ita kanta Harira ta ji wani abu a ranta na yadda babu gargada Zabba’ur ta bayar da amsa.

Alkalin ya ce “Edcellent” Ya ci gaba “Tambaya ta gaba, ita ce zan rubuta a allo, a amsa min a rubuce. Zan fara da Zabba’u Dr. Bukar.” Ya matsa wurin allon, ya sa alli ya rubuta tambayar kamar haka;

Common factors

Solbe  K = ad – ay

                          2a + 3a2

“Bismilla.” Ya ce da Zabba’u.

Gaban Harira ya fadi, ita ba ta taba ganin irin wannan lissafin ba, bare a ce an yi musu, haka ma ‘yan’uwanta. Ta zuba wa Zabba’u idanu, domin ganin yadda za ta bayar da amsa.

Zabba’u ta isa wurin, ta amshi makar, a kasan tambayar ta fara amsawa kamar haka;

Solution:

= a( d – y)    =        d – y

   a(2 + 3a)   2 + 3a.

Tana gamawa alkalin ya jinjina mata, mahalarta taro ma suka tafa mata. Saura Harira wacce ta yi dif. Ita ma ya rubuta mata tata tambayar. Yana rubutawa, tana nazarin amsar da Zabba’u ta bayar da yadda ta bayar da amsar, da yadda lissafin yake, ta nutsu tsaf, tana addu’ar Allah ya sa nata bai kai na Zabba’u wahala ba. Da ya gama rubutawa ta dubi tambayar.

Solbe

K = 2m2 + 16mn

          9mn2 – 8m2

“Tashin hankali! Mun fadi. Ai ko ni ba zan iya amsa wannan tambayar ba.” Malam Abdu ya fada a ransa. Ya dubi Harira da yadda ta amshi abin rubutun, da kuma lura da ya yi tana cikin wani hali na tunani, tana kuma addu’a, a ransa ya ce “Allah sarki yarinya kin yi kokari ai.” Yana kallon ta, ta fara rubuta amsa, kamar haka;

Solution

= 2m(m + 8n) = 2(m + 8n)

   m(9n2 – 8m)     (9n2 – 8m)

Dif aka yi a wurin, ana tunanin me ya faru, ta rubuta daidai ne ko kuwa? Wadanda suka san ta rubuta daidai ciki har da alkalin tunani suke yi ko dai yarinyar nan da aljanu take aiki ne? Da kyar alkalin ya iya cewa.

“Edcellent, it is correct.” (da kyau kwarai, kin yi daidai)

Ai kuwa sai ihu da tafi da sowa. Wadda ake tunanin za ta kasa amsa 1 + 1 amma ita ta amsa wannan, lallai akwai abin mamaki.

Zabba’u kamar ta mutu don haushi, tana ji tana gani dinkin hula na neman kai ta tsakar dare.

Alkali na karshe, wanda zai yi tambayar a kan al’amuran yau da kullum, ya mike. Bayan sallama sai da ya yi dan sharhi kadan kana ya fara da tambaya.

“Tambayoyi guda biyu za su isa kai tsaye ga Harira. Tambaya ta farko ita ce; (1) A wacce shekara aka fara bude makarantar gaba da firamare (sakandire) a kasar nan, kuma a wacce jiha ce? (2) Tambaya ta biyu; A wacce shekara aka kirkiri yin bautar kasa? (wato N.Y.S.C.)”

Aka yi shiru na mintuna biyu, kafin a kaure da ‘yan surutai. Kowa ya san Harira ba za ta iya bayar da wannan amsar ba, musamman idan aka yi la’akari da makarantar da ta fito, makarantar da darasi bai ishe su ba bare su rinka samun ire-iren wadannan bayanai.

Ita kanta Harira ba ta da wannan amsar. Haka ta shiga raba idanu tsakanin alkalan gasa da mahalar taro, tuni ta saduda, a tunanin ta kafin a kada kararrawar cewar ta kasa, kawai za ta ce ba ta sani ba.

A cikin baza idanun da take yi ne, ta tsayar da ganinta ga wasu manyan mutane guda biyu, da alama malaman wata makaranta ne, abin da ta karanta a zancensu ne ya tsayar da hankalinta gare su, domin ba za ta iya jiyo abin da suke cewa ba, tana iya karanto maganganunsu dai.

Daya ne a cikin su, dogon ya ce “Ja’ira, ba za ta iya amsawa ba.”

Gajeren ya ce, “Ai ko ni sai na duba littafi.”

Dogon ya yi dariya, “Ka ga ni kuwa na rike. A 1859 aka kirkiri makarantar gaba da firamare mai suna Grammar School a jihar Ikko. Bautar kasa kuwa a 1973 aka kirkiro yin ta.”

Kamar a littafi haka Harira ta karanci kalaman dogon mutumin nan, da taimakon Allah ta rike abin da ya fada din. Kawai ta kara amsa-kuwwa a bakinta tana cewa.

“A 1859 aka kirkiri makarantar gaba da firamare a jihar Ikko mai suna Grammar School. Ita kuwa bautar kasa an kirkire ta ne a 1973.”

Mamaki ya wadatu ainun a dakin taron, kafin kuma a dole kanwar na ki ta sa a rude da tafi da sowar gamsuwa da amsar da Harira ta bayar. To a yanzu fa wasu sun fara tunanin Harira tana aiki ne da aljanu da suke fada mata amsar, don haka suka shiga matukar mamakin ta, ciki har da dogo da gajeren mutanen nan da suka tattauna kafin Harira ta bayar da amsa.

Sai da aka yi kusan mintuna shida sannan alkalin ya yi ajiyar zuciya, shi ma yana da tunani irin na sauran jama’a, sannan ya ci gaba da tambaya ga Zabba’u, wadda ta zama kamar sokuwa a tsaye.

“Mai ba da amsa tambaya ta biyu, za ta amsa tambayoyi kamar haka; (1) A wacce shekara aka canja wa ‘yansanda kakinsu (uniform) ya koma baki? (2) A wacce shekara aka dawo da babban birnin tarayyar Nijeriya daga Lagos zuwa Abuja.”

Zabba’u ta karbi amsa-kuwwa, ta san amsar, ta ce. “A 1988 aka sauyawa ‘yansanda uniform daga baki da ruwan toka (mai duhu) zuwa baki. (2) Amsa ta biyu a 1991 babbar birnin Nijeriya ya taso daga Lagos zuwa Abuja.”

An yi mata tafi sosai, saboda ba ta yi gargada ba ta bayar da amsa.

Bayan an nutsu ne aka ba da damar dan shakatawa da sauraron wasu wakokin dalibai na rediyo, kafin a fadi amsar wadda ta lashe gasar. An shafe mintuna bakwai, sannan babban alkalin gasa ya sa aka yi shiru, ya mike, ya yi gaisuwa ga gwamna da manyan baki da mahalarta taro, sannan ya ci gaba da fadin sakamako.

“A sakamakon karawa da aka yi, ga yadda sakamako na karshe ya kasance.

“Da farko, Zabba’u Dr. Bukar a sakamakon ta, a Turanci tana da maki 2, I.R.K. 0, Lissafi 2, Current Affairs tana da baki 2 idan aka hada sun zama 6.”

Ba a yi tafi mai yawa ba a dakin taron saboda an fara tunanin inda aka dosa, wato wacce ta lashe gasa.

Ya ci gaba “Sai kuma Harira, sakamakonta ya nuna a Turanci tana da maki 1, a I.R.K. maki 2, sai Lissafi maki 2, Current Affairs ma maki 2 gabadaya ya kama maki 7. Don haka Harira Lauwali daga Maitsango Primary ita ce ta daya kuma zakara a gasa ta bana da maki 7….”

Tafi ya hana shi ci gaba, dole ta sa mutane ke tafawa Harira don yadda ta amsa tambayoyin sun burge su.

Ya ci gaba da cewa, “Sai kuma Zabba’u Dr. Bukar wadda ta yi ta biyu da maki 6.”

Zabba’u zubewa ta yi a kasa tana kukan bakin ciki. Harira ta isa gare ta, ta yi kokarin dago ta, tana cewa, “Ki yi hakuri yarinya ita kwakwalwa ko ilimi ko nasara ko kokari ba sa tare da mai kudi, kuma ba sa siyuwa da kudi da kin siya. Mamallakin arziki da mai arziki da talaka da saraki shi ke ba da su ga wanda ya so ba don an ba shi komai ba, don babu abin da za a ba shi din sai don buwayarSa, shi ne wandara gagara misali…” Ta mike, ta nufi wurin abokan tafiyar ta.

Jim kadan mai gabatarwa ya sanar cewa, tsakanin zakara Harira da mai bi mata Zabba’u za su yi jawabin gamsuwa ko hangen su game da gasa.

Zabba’u da tawagarsu sun dan ji dadin wannan abu, don sun san da wuya idan Harira za ta iya yin wani jawabi mai gamsarwa.

“Kin samu damar da za ki yi fata-fata da ita da kalamai da habaici.” Auntie din su Zabba’u ta ce da ita.

Zabba’u ta yi murmushin mugunta tana gyada kai, duk da har yanzu tana cikin matukar damuwa, idanunta jawur.

Sannan karin jin dadin su Zabba’u shi ne da suka ji Harira ce za ta fara gabatar da nata jawabin. Don haka ta samu damar da idan za ta yi nata ta yi wa Harirar tatas. Ta kulle a zuciyarta za ta yi jawabin da za ta nuna ya kamata a rinka bambance tsakanin makarantun talakawa da masu kudi.

Lokacin da aka gabatar da Harira, wurin taron ya yi tsit, ba ka jin motsin komai sai na takun sawayenta, ta isa wajen da za ta yi magana, ta tsaya cikin rissina da biyayya, ta gaishe da duk wadanda suka dace, sannan ta fara gabatar da jawabinta.

“Na gode wa Allah da a rayuwata na samu wannan damar a gaban wadanda suka dace zan yi bayanin abin da ya dace.” Fadin hakan da ta yi da nutsattsiyar murya ya sa mahalarta taron suka kara nutsuwa. Ta ci gaba.

“Idan gwamnati tana son ta gyara ilimi, to dole sai ta gyara ilimin firamare, kuma hanyoyi uku zuwa hudu kacal ake da bukata a gyara, ilimin ya gyaru.” Aka kuma nutsuwa, “Dalibai yara suna kwashe shekaru biyar zuwa shida har ma zuwa bakwai suna karatu a firamare, kuma a lokacin ne na rayuwar dan’adam ilimi da tunani da tsarin rayuwa yake shigar kwakwalwar dan’adam, don haka wannan lokacin ne mafi tsada da muhimmanci a rayuwar mutum da zai ginu ko a gina shi ta yadda zai amfana kuma ya amfanar da kasa da al’ummar da ke cikinta. A wannan lokacin ne za a kimsawa yara so da kishin kasa, za a raini masu hidimtawa kasa ba masu ruguza kasa ba. Wadannan abubuwa guda uku, ilimi, kishin kasa da hidimtawa kasa kawai idan aka bai wa yara shi zai sa a sami ci gaba a kasa.

“To amma sai ya zamana gidajen holewa da dandulan wasanni sun fi makarantu daraja a wurin gwamnati da al’umma, sannan kuma sai a rinka tura mutanen da ko kadan ba su cancanta ba wai a matsayin malaman da za su koyar da karatu da ilimi da tarbiyya a makarantu.”

Gwamna ya kalli Kwamishinan Ilimi da ke gefensa, suka yi wa juna kallon-kallo.

Harira ta ci gaba, “Wadannan abubuwa su ne suka yi katutu a makarantunmu na firamare, wanda zan yi amfani da wannan damar in yi roko ga masu ruwa da tsaki da su taimaka su ceto rayuwar kananan yara su ceto kasarmu. Allah ya yi mana jagoranci, na gode.”

Mahalarta suka kwashe da tafi suna jinjina mata, da yawa sun tausayawa jawaban Harira, har da masu zub da hawaye, kuma sun yaba da karfin halin ta, da ta fadi wannan gaskiya mai daci a gaban gwamna.

Wannan dalilin ne ya sa zuciyar Zabba’u ta yi sanyi, ta ji wani abu na ratsa ta, da ta tashi yin nata jawabin maimakon ta fadi abin da ta kullace a ranta, sai ta yaba da irin jajircewa da gwarzantakar Harira. Wannan ya sa da yawan mutane suka tausaya mata, su ma suka yaba mata.

Mai girma gwamna ne ya yi jawabin karshe na godiya da kuma jinjina wa kalaman da Harira ta yi.

“Hakika na yaba, kuma na jinjina fadar gaskiya da wannan gwarzuwa ta yi, kuma ta cancanci lashe wannan gasa, domin ba kowa ne zai iya tsayawa a gaban irinmu ya fadi gaskiya kamar yadda ta fada ba.”

Ya dan yi shiru, cikin damuwa, “Kuma in sha Allahu za mu duba abin da ta ce, za mu yi gwargwadon kokarinmu wajen magance matsalar.”

Aka tafa masa. Sannan ya gabatar da kyaututtukan da Harira ta lashe a matsayin ta na gwarzuwar shekara. Ita ma Zabba’u ya ba ta tata kyautar, da sauran dalibai da makarantun da suka cancanta.

A kunnenta Harira ta ji an ba ta kyautar kujerar Makka, an ba ta kyautar kudi dubu dari, sannan an bai wa makarantarsu kujeru masu hade da tebur guda dari biyu da kofi na nasarar gasa da littattafan karatu da rubutu.

Kowa a wurin taron sai da ya kuma bin su da kallo a lokacin da za su tafi, suka tafi suna murna.

Sai dai kuma abin haushi, abin takaici, kwanaki biyu da yin gasar hedimasta ya sa aka bai wa Harira dubu uku da dari biyar da littattafan rubutu guda goma sha biyu, su kuma sauran yaran littattafan rubutu guda goma-goma da kudi Naira dari biyar-biyar, wai a matsayin kasonsu.

Kujerar Makka da sauran kudin da littattafai su hedimasta da su Malam Abdu sun yi kashe-mu-raba da su.

Allah sarki, dole yara suka saduda, suka yi kuncinsu a zuci, suka bar wa Allah, babu wanda ya binciki yadda aka yi, daman iyayensu ba su damu da zuwa duba yanayin karatunsu ba bare wasu al’amura na makaranta, bare su yi bincike.

*****

A bakin bishiya, malamai ne su hudu tsaye cirko-cirko kamar zakaru, a lokaci guda suka zo makarantar, misalin karfe tara da mintuna sha biyar suka fara zuwa, suka gama haduwa dukkaninsu zuwa tara da mintuna hamsin daidai.

Tsayuwar da suka yi, sun tsaya ne domin jiran tabarma.

Malamin lissafi, mai suna Malam Akilu ya dubi ragowar malaman ya ce “Wai su yaran nan kullum sai su dauke mana tabarma, sai mun zo muna zuwa mu karbo.”

“E to, ai ka san ba su da kujerun zama ne shi ya sa suke dauka, kuma su ya kamata su rinka amfani da ita maimakon mu. Tun da dai ka ga hira muke zama mu yi a nan din, su kuwa fa, karatu suke yi.” In ji Malam Mamman, malamin Arabiyya. Ya dora da fadin, “Ai mu muna da ofis, bai ma kamata mu rinka zuwa muna gaje musu abin zama ba.”

Malamin Social Studies, Malam Muntari ya tsoma musu baki, “Ka fadi haka mana, tun da kai ba zama kake yi a wurin sosai ba.”

Malam Mamman ya yi murmushi ya ce, “Daman bai kamata in zauna din ba, kamata ya yi in rinka yin abin da ya kawo ni makarantar. Kai ba ni ba, har ku ma bai dace ku rinka zuwa kuna zama ba, kuna kin shiga aji ku koya wa yara karatu, alhalin abin da ya kawo mu kenan, kuma sai lokacin karbar albashi ya yi a ga mun fi kowa yin zugun kamar beraye a gaban mage. Ya dace a ce, gasar nan da aka yi ta zama darasi garemu.”

Malam Akilu ya dube shi sosai, “To mai gaskiya, sannu agogo sarkin aiki. Da kake maganar abin da ya kawo mu makaranta, da maganar gasa, da kuma maganar albashi da kake yi, shin albashin namu nawa ne? Abin da bai taka kara ya karya ba, bai fi a cinye su a rana daya ba. Kuma, malam bai kamata ka dora laifin a kanmu ba, idan ka duba tsaf, za ka ga wannan kangon da muke ciki bai yi kama da makaranta ba. Misali a hujjance, tun da inda ba kasa nan ake gardamar kokawa.

“Da farko, ga dai ginin makarantar, gini irin na ‘yan siyasa, gini da tubalin toka, duk ya zama kango. Sannan kana sane cewar idan ana ruwa, to babu damar yin karatu sai dai neman wajen rakubewa tsakanin malamai da dalibai, da kuma fatan Allah ya sa a gama ba tare da an yi rusau ba.

“Sannan ka san mu, muke sayo alli da magogi (dasta) da kudinmu, gwamnati ba ta kawo mana. Haka nan ka san duk yaran da kake koyarwa a kasa suke zama a haka kake koyar da su. Haka mu ma malamai, yanzu mu hudun nan wane ne mai kujera da tebur masu kyau a cikinmu? Ka san babu.” Ya dan nisa, sannan ya ci gaba da cewa.

“Shin a tsawon shekarun da kake koyarwa ka san walwalar malamai, kafin in ce komai?”

Malam Mamman ya girgiza kai alamun bai sani ba. Malam Akilu ya guntse baki ya ce “Uhum, ai ka ji, wato ba ka san da ita ba, saboda babu ita din. Ni fa nan da ka gan ni idan zan shigo makarantar nan gabana faduwa yake yi, haka nan raina kan baci har sai an tashi. Abubuwa ga su nan iri-iri na koma-baya da nakasu a makarantu irin wadannan…”

Malam Mamman ya karba da cewa, “Ka so fadar gaskiya, amma ka hada da karya domin ni dai na san alli ana kawowa, sai dai a ce ba yadda ya kamata ba, sai kuma yara da suke sayowa su kawo…”

“To ka ce babu gaskiyar mana.” Shi ma ya katse shi.

*****

A cikin aji, a yanzu Malama Rukayya ta gama yi wa yaran ajin bulala biyar-biyar. Bulalar da ta sha alwashin sai kowanne yaro ya yi kuka kafin ta gama yi musu. Ranta a bace ta yi bulalar, duk dakiyar yaro sai ya yi kuka, idan ma a cikin bulala biyar bai yi ba takan kara masa har sai fitar da hawaye.

Da ta kammala, sai ta biyo tsakiyar ajin tana taku daidai har ta isa bakin allon ajin, ta dube su iya inda idonta suka kai.

“Magulmata, daga yau in sake jin kun yi wani kes na fadin wani abu a kaina, kai ba ma a kaina ba, ko wani malami ne a makaranta ko a gida. Musamman ke ‘yar banza, matsiyaci.” Ta nuna Harira. “Ja’ira mai fuskar munafukai, sai ka ce mutuniyar kirki. Ni ba ruwana da wani kokarin ki, jibgar ki zan yi, har sai kin raina kanki.”

Yaran, wasu kuka suke yi muraran, wasu kuma suna shisshika, haka nan masu ajiyar zuciya ma suna yi. Ta daka musu tsawa, “Ku yi min shiru na ce, ko sai na kara muku! Har wani zuwa kuke ku gaya wa Hedmasta, kuna tsammanin ba zan ji ba, to ya gaya min duk abubuwan da kuka fada a kaina, daga yau kwa kara.”

Ta koma wurin zamanta, kan wani dogon teburi inda take kasa kayan siyarwarta, ta zauna. Daga haka sai duk ajin ya yi shiru, ba ka jin duriyar kowa, sai ‘yan kananun ajiyar zuciya. Babu wanda bai yi kukan ba a cikinsu.

‘Yan dakiku a tsakani, mutane biyu suka shigo ajin. Hankalin Malama Rukayya a tashe, ta kifar da teburin da kayan siye da siyarwar ke kai, Allah ya taimake ta, ya yi yadda take so, teburin ya kife a kan kayan dan-tamatsitsin, ta dubi yaran cikin basarwa ta ce, “Tun da babu mai tambaya, zan ci gaba.” Ta sa tafin hannunta, ta shiga goge rubutun da ta yi, wato kalmar HAUSA, a gefe kuma ta rubuta kwanan wata, sai a tsakiya kuma ta rubuta TARBIYA, wanda a zahiri kullum ta shigo ajin wannan rubutun kawai take yi, idan ta ci sa’a yaran ba su goge ba shi kenan ba sai ta sake rubutawa ba, idan sun goge sai ta kara rubutawa. Ba karantawa take yi ba, face ta zauna, ta shiga yin kasuwancinta, na siyar da abubuwan lashe-lashe da tande-tande.

Yaran har sun saba da ganin rubutun, sun gane shi, sun san yadda take rubutawa, kai tun ita da kanta ma ba ta iya rubutawa daidai ba har ta iya, su ma kuma sun san yadda za su rubuta ko karanta shi duk da ba karanta musu take yi ba.

Malama Rukayya ta dawo da ganinta ga mutanen da suka shigo. Biyu, daga masu duba aikin malamai ne, dayan kuma Hedmasta ne. Ta yi musu barka da zuwa, sannan su ma dalibai suka yi abin da aka koyar da su na gaisuwa ga wadanda suka shigo din.

Da alama ukun da suka shigo sun fahimci abin da ya faru na wayancewa da Malama Rukayya ta yi kokarin yi da nuna wai darasi take koya wa yaran.

Daya daga cikin masu duba malaman ne ya yi tsai, ya nazarci yaran ajin da kuma yanayinsu da yadda suke zaune, da yanayin ita Malama Rukayyar, zuciyarsa ta zargi cewar akwai wani abu a kasa, wanda malamar ta boye.

Ya dube ta, ya shiga yi mata tambayoyi. A cikin amsoshin da take ba shi ne ya tabbatar da zargin da yake. Ko amsa daya ba ta ba shi daidai ba, a haka ma ya fahimci ba ta dace da zama malamar makaranta ba, ya kuma gane, tana saye da siyarwa a makarantar, wanda wannan haramun ne a tsarin aikin.

A waje a lokacin fita hutun rabin dakika, Mista Rabe (daya daga masu duba malamai) yana tsaye da abokin aikinsa suna magana.

“Ita ma wannan makarantar tana da matsalolin the same (daidai yake) da ragowar makarantun. Akwai siyar da kayan kwalam da makulashe, akwai rashin darasi, rashin sanin aiki da sauransu. Wannan malamar, a bincike na is not deserbed (ba ta cancanta ba) kwata-kwata, watakila  daurin gindi gare ta, tana cikin ire-iren malaman da ‘yan siyasa ke bai wa aikin koyarwa, wai a matsayin sun samar wa al’umma aiki. Za ka yi mamaki idan na gaya maka cewar ba ta iya rubuta sunan makarantar nan daidai ba.

“A haka za mu ci gaba da rayuwar kenan? jahilai suna koyar da ‘ya’yanmu? Likitocin dabbobi sun zama likitocin mutane? Injiniyan ruwa a ba shi aikin akanta? Kawai saboda daurin gindi, ya za mu yi da wannan kwamacala?”

“Abin dai ba a cewa komai. Kuma wannan abu a gaskiya ya yi yawa, shege da hauka.” In ji Malam Aliyu.

Mista Rabe ya ce “Gaskiya ba don ina da nufin yi domin Allah da taimakon kasa ba da na hakura da wannan aiki mai kama da bakin bunu bata baibaya, kullum abin kara baci yake. Ita fa matar nan nunawa take yi abin ko a jikinta an yakushi kakkausa. Yadda take kidahuma me kake tsammani zai faru da take koyarwa yanzu? Ai kai daga ji ka san daurin gwarmai za a yi…”

Yaran da suka nufo shi ne ya sa, ya yi shiru daga abin da yake fada. Harira ce da ‘yan tawagarta. Ba su daddara ba, tun da sun ga, sun kai kara wajen Hedmasta reshe ya juye da mujiya, sai suka ga alamar wadannan mutane suna da matsayin da za su iya share musu hawaye, musamman da suka lura ita kanta Malam  Rukayya tana tsoron su.

Kafin su zo, Harira ce ta ja ra’ayinsu, ta ce musu. “To, yanzu idan ba mu gaya musu mun samu mafita ba, ta yaya za mu yi nasara a karatunmu? Daga cikin duk abubuwan da muke tsoro mene ne a ciki ba a yi mana ba? Kullum fa duka take yi mana, kuma babu karatun. Ai gwara mu samu mafita.”

Suka yi shiru, kafin can daga baya su yarda da batun ta, kana suka taho gare su.

Bayan sun yi musu sallama, suka gaishe da su. Harira ce ta yi bayani dalla-dalla, a kan rashin darasi da cin zali, da sayar musu abubuwan sayarwar malamai suna so ko ba sa so.

Mista Rabe ya dubi abokin aikin sa, ya ce “Ka ji ko. Ka ji yara kanana suna fadar abin da muke zargi ko.”  Ya dubi su Harira, yana fadin,  “Ku yi hakuri, in Allah ya yarda komai ya zo karshe, za mu sa a yi maganin abin, ku kuma, Allah ya yi muku albarka, Allah ya ba ku abin da kuke nema na ilimi. Ku je ba komai.”

Suka juya, suka tafi. Mista Rabe ya bi su da kallo cikin tausayawa.

“Wannan yarinyar fa ita ta yi zarra a gasar makarantu da aka gabatar…” In ji Mista Rabe.

“Allah sarki, da a ce tana da galihu da ba a wannan makarantar za ta yi karatu ba. Kuma da iliminta ya inganta, amma yanzu ina da tabbacin kokarin ta ko neman ilimin ta na iya zama yankakke.” Malam Aliyu ya fada da muryar tausayawa.

Duk wani kokari da ya kamata Mista Rabe ya yi da abokan aikinsa don fito da illar da ke tattare da malaman makarantar su Hajara don a gyara sun yi, har ma da sauran makarantu masu irin wadannan matsaloli. To amma, an sami akasi, domin Malama Rukayya da sauran malaman makarantar suna cikin malamai ‘yan alfarmar ‘yan siyasa, kuma shugabanni.

Irin ‘yan siyasar nan, wadanda don a ce suna samar wa mutane aiki sai su debi kowane irin mutum, wasu ba su yi makaranta ba, wasu ba su gama karatun ba aka kore su ko suka daina zuwa, wasu ‘yan kwaya ne, wasu ma suna taba halin beraye da sauran ire-iren wadannan halayya, su ba su aiki a makarantun gwamnati a matsayin malamai.

Ka ji bata dubu daya ba ta gyaru ba, makaranta irin ta firamare, inda ake son a dasa wa yara tushe na karatu, an kawo marasa tushen. Inda ake son a tarbiyyantar da yara an kawo malamai marasa tarbiyya. Inda ake so a bai wa yaro nagartaccen ilimi an kawo malamai marasa ilimin, munin wannan al’amari har ya yi yawa.

Da yawa malamai ire-iren su Malama Rukayya duk da rashin iyawarsu da dacewarsu, babu wani hedmasta ko mai kula da malamai da ya isa ya kawo musu barazanar kora ko dakatarwa.

Wannan ce ta faru ga lamarin irin su Malama Rukayya, wanda a karshe reshe ya juye da mujiya su Malama Rukayyar suka shiga, suka fita, suka sa aka kori su Harira da sauran yara bakwai, wai sun yi rashin tarbiyya da cin mutuncin malamai da kirkirar laifuka iri-iri na sharri suka dora musu, wanda ya sa aka kore su din. To ita dai wannan rayuwar kowa ka ga ya numfasa to yana da sauran numfashin ne.

*****

Malam Lauwali ya damu matuka da hukuncin korar da aka yi wa ‘yarsa Harira, bai yi kasa a guiwa ba, da misalin karfe bakwai na safe ya tashi, ya tafi makarantar. Hausawa kan ce sa’a tafi sammako, to amma shi dai Malam Lauwali bai yi sa’ar ba, domin bai riski wanda ya je nema ba, wato hedmasta. Haka ya yi ta zama har tsawon awanni uku, wato har zuwa karfe goma, amma babu Malam Tukur hedmasta babu alamar sa. Da ya gaji da zama sai ya matsa wurin masinja, ya ce.

“Malam, ko shugaban makarantar nan zai zo kuwa?”

Masinja, Malam Lukuman ya kalle shi, ya ce, “Wayyo bawan Allah, ashe hedmasta kake jira, ai yau da wuya ya zo, don yana zuwa kasuwa a yau din.”

Malam Lauwali ya dube shi cikin mamakin abin da ya fada ya ce, “Kasuwa, kamar yaya?”

“E, yana dan taba kasuwanci, don haka ba kowacce rana yake zuwa makaranta ba.”

Takaici ya kama Malam Lauwali ya rasa abin da zai ce, kawai sai ya ce, “Na gode Malam.” Ya juya, ya tafi cikin takaici da bakin cikin ga shi shi bai tafi neman kudi ba, ga ba biyan bukata.

Washegari ma da ya koma makarantar haka abin yake, labarin dai irin na jiya ne. Haka ya rinka jele na tsawon kwanaki hudu yana zuwa bai sami ganin hedmasta ba, wata rana idan ya je, a ce suna taro, ko kuma ya tarar ya yi baki ko kuma ya tarar ba ya nan.

A cikin kwana na biyar ne ya taki sa’ar yin kicibis da shi, yana zuwa kofar ofis din, sai ga hedmastan shi ma ya zo, suka gaisa. A nan suka tsaya. A yadda hedmasta ya nuna a nan din za su tattauna abin da ya kawo shi, su rabu, don bai ga alamun ya zo da wani abin da za a so ba.

Malam Lauwali ya dube shi, ya ce, “Na zo ne a kan maganar korar yaran nan da aka yi, wadda ciki har da ‘yata.”

Malam Tukur ya yi masa kallon biyu ahu, ya ce “Ka zo da magana mara amfani, wadda ta dade da wucewa.”

Da mamaki Malam Lauwali ya ce masa “Kamar yaya magana mara amfani?”

“Kamar dai yadda na gaya maka tun farko, ko ba ka fahimtar abin da nake fada?” In ji hedmasta, ya dora da cewa, “Kawai fadi abin da ya kawo ka in ji. Kai baban wane ne ko wace ce a cikin korarrun yaran?” Yana magana da yanayin gajiyawa.

Malam Lauwali ya yi jim, ransa a bace, kamar ya fasa magana, ya tafi, sai ya dan yi tunani, ya ce “Ni ne mahaifin Harira, na zo in ji takamaiman dalilin korar su da kuma neman mafita.”

“Tabdijan! Lallai, ashe kai ne baban babbar ja’irar. Sannu malam. To kar mu bata wa juna lokaci, kar mu bata yawan kalamanmu, abin da ya wuce, ya wuce, hannun agogo ba zai taba dawowa baya ba. An kore su kuma ba za a saurari batun kowa ba, bare a dawo da daya daga cikinsu, ka tafi kawai shi ne abin da zan iya ce maka.” Ya juya, ya nufi cikin ofis dinsa, yana magana, “Kar ka yi zaton wai don ‘yarka ta ciwo mana gasa, za mu saurare ka, mu wannan bai dame mu ba.” Ya bar Malam Lauwali a nan.

Malam Lauwali ya bi shi da kallo kawai, yana mamakin irin wannan wulakanci da hedmasta ya yi masa, hawaye ne ya rinka fita daga idanunsa, ransa ya yi kuna. A nan da yake tsaye ya kasa motsawa, kawai kallon ofishin hedmastan yake, yana tunanin irin cin zarafin da ya yi masa.

A karshe dole Malam Lauwali ya hakura, ya nemi wata makarantar Islamiyya ya sa Harirar, wadda ake zuwa da rana, kafin ya sami husufin sama mata wata makarantar firamaren.

Da yake da wuri ake tasowa daga Islamiyyar sai Indo mahaifiyar Harira, ta sake samun damar kara kasko na abin talla da take dorawa ‘yar tata.

A ka’ida, tallan safen na nan, wato tallan koko. Da misalin karfe goma sha daya da rabi na rana kuwa idan ta taso daga makarantar Islamiyya, sai ta dora mata tallan kunun tsamiya da na kanwa a faranti guda, sai kuma wanda ake bin ta da shi zuwa bakin kasuwar, wajen sayarwar. Idan mutum yana bukatar kunun kanwa sai ya siya, idan na tsamiya yake bukata shi ma akwai a wurin Harira.

Idan ta dawo, da yake ba ta zuwa makarantar yamma sai ta dare, ta ci abinci, sai kuma ta dauki tallan wake da shinkafa, ko shinkafa da salat ko shinkafa da taliya wanda wani lokacin sai bayan karfe hudu na yamma take dawowa.

Idan ta dawo, shi ne take daukar tallan gyada ko gurjiyya dafaffu ko soyayyu, su rankaya da kawayenta. Dawowar su kuwa sai abin da hali ya yi. Amma sun fi dawowa bayan sallar magariba. A wannan lokacin ne kuma take sake daukar wani tallan kafin lokacin shiga makarantar dare.

Kwanci tashi, ba wuya a wurin Allah da yau da gobe karar kwanaki ga mai rai, sai ga shi an yi watanni uku da korar su Harira daga makaranta.

A wannan lokacin ne wani al’amari mai ban mamaki ya faru, musamman ga ire-iren su Harira masu daukar talla. Wata yarinya, mai suna Karima, kawar su Harirar da suke tafiya tallan gyada ko gurjiya da yamma tare, suke tafiya tallan kunu da rana, suke haduwa a wurin sayar da wake da shinkafa, alhalin ita Karima tana siyar da alala wani lokacin danwake, to ita ce ta yi ciki a wajen yawon talla. Yarinya shekarunta goma sha uku da watanni a raye.

Abin ya bayar da mamaki matuka, ya kuma razana iyaye. Su kuma ‘yan gaza-gani suka ci gaba da bayyana zatonsu da son ransu. Wasu da yawa ma cewa suke kamar yadda aka bata Karima haka su ma kawayenta an bata su, ciki har da Harira, a ganin su kawai ciki ne bai bayyana a gare su ba.

“Da yawa yaran daman neman su ake yi, shi ya sa za ka ga suna samun kudi, ko kuma ka ga sun sayar da abubuwan da suke talla cikin kankanin lokaci. Amma fa wasu da karfi ake yi musu, wato fyade ake yi musu, wasu kuma yaudarar su ake yi da kudi.” Cewar Malam Sabo mai kanti, yayin da suke hira da Nata’ala a kan maganar.

Nata’ala, ya ce “Ire-iren wadannan abubuwa su ne ke faruwa, yawan yin mu’amala da yara mata kanana, musamman ‘yan talla, sun saba mu’amala da maza, sun saba yin furuci marasa kyau, wasu kuma su koyi maitar son kudi, wanda komai ma za su iya yi da su a kan kudi. Ni na rasa mene ne mafitar wannan bakin al’amari da muke ciki?”

Malam Sabo ya yi murmushi, ya ce, “Da wuya, gaskiya a tunani na babu mafita, domin idan ka lura da ire-iren wadannan tallace-tallacen yawanci iyayen yaran suke samun dan rufin asiri, su samu na abinci da sutura da kudin haya da kuma sauran lamuran rike rayuwa. Ka san manyan abubuwan da talaka ke bukata don ya rayu ba yawa gare su ba. Ka ga wutar lantarki da ruwan sha da kyawun hanyoyi da  magunguna a asibitoci da tsadar abubuwan masarufi da sauransu su suka haifar da tsadar rayuwar…”

“Duk da haka.” Malam Nata’ala ya katse shi, “Iyaye maza ne ya kamata su dauki ragama mai yawa a kan al’amuran rayuwarsu, su zamo masu neman na kansu, masu neman ilimi. Ba wai su mike kafa, su kashe zukatansu, su saki bakuna su kyale wai ‘ya’ya ne za su jagoranci rayuwarsu da kansu ba.”

“E to, haka ne, Allah ya sa mu gane.” In ji Malam Sabo.

*****

Saboda faruwar wannan abu, ya sa Malam Lauwali, ya fitar da lokacin yi wa ‘yarsa Harira aure, a ganin shi gara ya yi wa tufkar hanci, ya shafa wa gemunsa ruwa tun da na dan’uwansa ya kama da wuta.

Kana taka Allah na tasa. A ra’ayin Malam Lauwali ba yanzu ya yi niyyar yi wa Harira aure ba, ya so a ce sai ta gama sauka ko haddar Alkur’ani, da wasu littattafan, sannan kuma ya so a ce sai ta kammala karatun sakandire, to amma dole a yanzu ya yi mata aure don ya guje wa surutu da maganganun mutane.

Yaron da yake neman ta da aure, sunan shi Balele, dan Malam Tanimu Magini, yaron kirki ne, ya yi saukar karatun Alkur’ani da littattafan addini kuma ya kammala karatunsa na sakandire, yana matukar son ci gaba da karatun boko amma saboda halin yau da gobe bai samu yin hakan ba, sai dai ya kudiri aniyar idan ya sami faraga zai ci gaba da karatun nan gaba.

A saba’ar watan cin jela aka daura auren Balele Magini da Harira Lauwali, aka yi daurin aure kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, aka yi biki irin na al’adun Hausawa.

Allah ya taimaki Harira, Balele shi ma mutum ne mai son karatu, don ya bai wa jama’a mamaki a lokacin da suka ga ya sama wa Harira wata makarantar firamare don ta ci gaba da karatunta.

*****

Da yake saura shekaru biyu Harira ta kammala firamare a lokacin da mijinta Balele ya samar mata wata makarantar, kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau da gobe asarar mai rai, Harira ta kammala makarantar firamare cikin kwazo da hazaka. Daga nan Balela bai yi kasa a guiwa ba, ya bar ta, ta ci gaba da karatun sakandire.

Mutane ba su yi tsammanin haka ba, shi da kansa ya yi mata duk cike-ciken da ake bukata, da saya mata littattafai da sauran kayan karatu.

Kwazon Harira ya kara karfafa Balele guiwar lamunce mata ta ci gaba da karatu, a ganin shi katse mata karatun na iya zama nakasu a gare ta.

Haka kuma da yake akwai ‘yar tazara daga gidansu Balelen zuwa makarantar su Harira lokacin da ta fara karatun shi yake kai ta makarantar a kan kekensa, sannan kuma idan lokacin tashi ya yi, ya je ya dauko ta.

Duk ranar da ka ga bai je, ya dauko ta ba, to ka tabbatar ya yi nisa zuwa wajen aikinsa.

Ranar wata Laraba, bayan an tashi su Harira daga makaranta, Balele yana tsaye a kofar makarantar a bisa kekensa rali (raleigh), yana jiran ta, bayan dan lokaci ta fito dauke da robar abinci da jakarta goye a baya, tana zuwa gare shi, ta dane kan kariya, in da ta saba hawa, ya tuka suka fara tafiya, suna hira.

“Ni ma fa na yanke shawarar zan siyo takardar shiga jami’a,  in ci gaba da karatuna.” Balale ya ce da Harira.

Harira ta ce, “I wallahi, yadda takardunka suka yi kyau tabbas ya kamata ka ci gaba da karatu, gaskiya na yi farin ciki da jin wannan magana.”

Balele ya yi murmushi, “Kuma kin san me zan karanta?”

“Sai ka fada.” Ta ce ita ma tana murmushi.

“Cibil Engineering zan karanta.” Ya ba ta amsa.

Cikin zumudi ta ce, “Ai kuwa ya yi wallahi.”

Suka dan yi shiru kafin Balele ya dora da cewa, “Ke ma idan kina bukata, zan so ki zarce da karatunki har jami’a…”

“Allah?” Cikin doki ta tambaye shi da mamaki gami da jin dadi.

“Tabbas.” Ya ce mata.

“Ina bukata mana. Gaskiya na gode, Allah ya saka da alkairi.” Ta ce da shi cikin murna.

Harira tana son karatu, tana da burin ta yi  karatu don ta taimakawa al’ummarta.

“Kin san wani abu?” Balele ya kuma cewa da ita yana dariya.

“A’a sai ka fada.” In ji Harira.

“Harira kina da kokari sosai, Allah ya kara buda kwakwalwa.”

“Amin.” Tana murmushi.

*

Harira ta kara kyau da nutsuwa da kwanciyar hankali. A yanzu ba ta zuwa talla.

Kafin a daura mata aure mahaifiyarta Indo ta dage a kan ita ba ta yarda da wannan auren ba, don zai hana ‘yar tata ta yi mata talla. Malam Lauwali ya ki yarda, saboda ga halin da suka samu kansu ana yi wa ‘ya’yansu kagen da neman maza. Da Indo ta ga ba mafita sai ta shimfida masa sharadin wai dole ne idan an yi mata auren sai Harirar ta rinka daukar mata talla, ka ji wani mulki gyartai da bai wa sarki umarni.

“To wannan kuma ai sai ki bari sai an daura auren.” A lokacin Malam Lauwali ya ce da ita cikin gatse.

Da aka daura auren, ko komawa ta kanta bai yi ba, domin daman in ban da abin Indo ina ta taba ganin an yi haka, a daura wa yarinya aure ta dawo tana yin talla a gidansu?

Haka ta dame shi da mita da naci, ta matsa masa idan har bai bi sharadin da ta gindaya a baya ba, to sai dai a cikin ‘ya’yan ‘yan’uwansa ya samo mata mai yi mata talla. Idan ba haka ba, to ita za ta rinka fita tallan da kanta.

Da matsin ya yi yawa, dole ya hakura, ya bar ta, ta rinka fita tallan da kanta. Haka kuwa ta rinka yi, tana dauka tana fita safe da rana da yamma.

Ita dai Harira, Allah ya taimake ta, ta sami ‘yancin kawar da talla a babin rayuwarta, ta yi dace da miji mai goyon bayanta a wajen yin karatu na Islamiyya da na boko.

Suna tafe, a hanyar su ta zuwa gida, Balele yana tuka keken sannu a hankali, suna hira. Ta kofar tsohuwar makarantar su Harira suke wucewa idan suka dawo, suna tafe kamar kullum, har sun gifta makarantar, sai Harira ta tsayar da shi.

Balele ya tsaya, ya juyo, ya kalle ta, ya ce, “Mene ne ya faru, amarya?”

Harira ta ce, “Wani abin mamaki nake gani mijina.” Ta nuna masa abin da ta gani din da yatsa.

Malama Rukayya ce take dauke da kayan siye da sayarwa a kanta na kulle-kullen yara, irin su dan-tamatsitsi da garin-bududus da tsamiyar-biri da sauransu. Kuma tana cikin wani hali da yanayi da yake nuna rayuwarta ta jigata, rayuwa ta sauya mata, rayuwarta ta munana.

“Malama Rukayya ce, malamar da ta sa aka kore mu daga makaranta.” Harira ta gaya wa mijinta cikin muryar tausayawa.

“To yanzu me za ki yi mata da kika sa na tsaya?” Balele ya tuntube ta.

“Zuwa zan yi in gaishe ta. Ka ba ni dama.” Harira ta nemi izinin shi.

Balele ya yi murmushi ya ce, “Idan kika yi hakan kin kyauta. Haka rayuwa take, abin da ya ba ka tsoro wata rana shi zai ba ka tausayi. Kuma macucinka ko makiyinka dole wata rana sai ya ba ka tausayi.”

Harira, ta karasa gurinta da sauri, a inda take kokarin zama a bakin kofar makarantar kafin a ba su damar shiga don sayarwa da daliban yamman abubuwan siyarwar tasu.

“Salamu alaikum.” Harira ta yi mata sallama.

Malama Rukayya ta amsa tana kallon ta da idanun mamaki. Ta santa, ba ta mance da ita ba, musamman a dan wannan lokaci, domin dalilai da yawa. Kawai dai abin da ya ba ta mamaki, shi ne sauyawar da yarinyar ta yi, ta yi haske, ta nuna alamun nutsuwa da alamun kwanciyar hankalin da ta samu, ga shi kuma sanye da kayan makaranta na sakandire masu kyau, ga takalmi ga jaka duk masu kyau, haka yanayi na zaman karatu a tare da ita. Ta dai kokarta ta amsa mata “Maraba, Harira ce ko?”

“E ni ce Malama. Yaya makaranta da gida?”

Malama Rukayya ta dube ta a nutse a tunanin ta ko shakiyanci take yi mata, amma ba ta ga alamu ba, don haka ta amsa mata. “To makaranta dai sai a tambayi masu yin ta, don mu, ta fi karfinmu.”

Harira da tausayi a tare da ita, ta dube ta sosai ta ce “Malama me ya faru?”

Malama Rukayya ta fara fitar da hawaye, can dai ta fashe da kuka, sai da ta yi gwagwardon mai isar ta, kana ta share hawaye, ta kama hannun Harira, ta ja ta gefe, ta zaunar da ita, ta fara da cewa, “Harira, daman ina neman ku, don in nemi gafarar ku a kan abin da ya faru, ki yafe ni Harira.”

Duk abin da ake yi, Balele na can gefe a inuwa, a rakube yana jira matarsa, ya zauna a kan wani tubali na kasa.

Malama Rukayya ta ci gaba, “Ki yafe ni Harira, idan kika yafe ni shi zai ba ni damar samun nutsuwar sanar da ke abin da ya faru da rayuwa ta a dan lokacin nan.”

Harira da hawaye ta ce, “Na yafe miki Malama, babu komai wallahi.”

Sai da Malama Rukayya ta sake casar kuka na dan lokaci, kana ta dora da cewa.

“Harira, ita rayuwar da kika gan ta tana da wani abu, da idan ta dauki mutum ta dora shi a can kololuwar sama, sai ka ga kowa shi yake hangowa, yake gani, shi kuma da yake yana kallon tsakiyar kan kowa, sai ya rinka ganin ya fi kowa, ya rinka ganin sama yake da kowa.

“To haka duniyar ta yi da ni…” Ta dan tsaya, na alamar karayar zuciya, “Na zamo ina ganin babu wanda ya isa da ni a cikin makarantar, ba Hedmasta ba, har masu zuwa duba malamai ma. Saboda…” Ta sake yin shiru kafin ta dora da cewa.

“Harira, an ba ni aiki a makarantar nan taku ba don na cancanta ba, ba don iyawa ta ba, ba don komai na dacewa ba, sai don siyasa. Mijin kanwata shi ne abokin wani kansila, na gaya masa ni dai ina zaune babu hanyar shigowar kudi, shi ne ya ce kar in damu akwai hanyar da zai samo min, to shi ne ya samo min koyarwa a makarantar taku. A zahiri nan da kika ganni, ko firamare ban gama ba, firamaren ma da na fara ba kokari gare ni ba. Su kuma ‘yan siyasa, a kan siyasarsu ba su dauki ilimi a bakin komai ba, shi ne suke yi masa karen-tsaye.

“Misali, dan siyasa, shugaba za ki ga ya dauki wanda ya yi karatun Injiniya ya kware a wannan fanni, ya ba shi shugabancin asibiti. Ko ya dauki mai ilimin aikin gona ya ba shi shugabancin ma’aikatar wuta da sauransu. Kin ga a nan ai sam babu hadin kifi da kaska, amma an hada su.

“To a kasa, ga makarantun firamare na gwamnati abin ya fi muni, inda nan ne tushen ilimin, kuma mafari, su wadannan shugabannin a nan suke yi musu mummunar illa. Misali, kawai shugaba dan siyasa don a ce ya samarwa mutane aiki, sai ya hada sunayen ‘yan jagaliya, ‘yan kwaya da irinmu, wadanda ma ba su san mene ne ilimin ba, kawai su ba su aikin koyarwa, su koma jaridu da mujallu da kafafen watsa labarai suna ikirarin sun samar da aiki ga matasa.

“Za ki tarar da mu din ba ma amfana wa yaran komai, sai dusashe kwakwalensu da jefa su cikin duhu. Shin ta yaya jahili zai koya wa yaro ilimi?” Ta yi shiru ba don sauraron amsa daga Harira ba, ta dora da cewa “To a wannan kasar jahilai ake dauka a tura makarantun yara na gwamnati a matsayin malamai, wai masu koya musu ilimi. Ke kanki za ki shaide ni, idan na ce miki duk tsawon lokacin da na yi da ku ban amfanar da ku da komai ba. To ire-irenmu muna da yawa a makarantu irin naku da ma na sama da su. Kuma aiki iri daya ne, babu bambanci, cutar da yara manyan gobe, a matsayin ba su ilimi.

“Na zamo bakar bunu bata baibaya a makarantar ku, kuma bakar fura dakan ibilisai, ta yadda babu ceto sai cutarwa, babu bayar da ilimi sai bata ilimi. Haka kawai nake sa a kori yara idan na ga za su kawo min barazana, alhalin suna da gaskiyarsu, kamar yadda na sa aka kore ku din ba a kan hakkinku ba.

“Dukkan abin da dan’adam ke yi, idan gaskiya ne, ya san gaskiya ne, idan karya ne ma haka. Ni da kaina na san barna nake yi, kuma na san ko ba dade ko ba jima sai gaskiya ta yi halin ta, to ga shi ta yi din, su kansu wadanda suke daure mana gindin an binciko almundahana da barnar su, aka yi hukuncin da ya raba su da mukamansu wanda dole ya shafe mu. Abin da ban taba zato ba, ban taba tsammata ba, shi ya faru. Aka raba ni da aikin koyarwar da nake yin yadda na ga dama, ni da ire-irena. Kin dai ga abin da ya faru da ni.” Ta ci gaba da hawaye abinta.

Zuciyar Harira ta karye saboda tausayi, ita ma kukan ne ya kubuce mata, ta rinka fitar da hawaye.

“Na yi wa yara da yawa rashin adalci, na sa an kore su daga makaranta, na hana su karatu.” Kuka ya hanata ci gaba.

Da Malama Rukayya da Harira kuka suke yi, a ran Harira ta tabbatar dukkanin abin da Malam Rukayya take fada gaskiya ne, kuma tana fatan Allah ya sa ragowar su gane kamar yadda ta gane. Idan haka ta faru, al’amura za su gyaru.

“Allah ya sa su gyaru din.” Harira ta fada a ranta. Kuma tana tunanin irin gudunmawar da za ta bayar a kai.

Bayan sun gama, Harira ta dauko wasu kudade, ta bai wa Malama Rukayya. Ta karba tana kuka, sannan ta koma wurin mijinta a sanyaye cikin damuwa.

Yana kallon ta yake cewa.

“Wadannan matsalolin da ta gaya miki, su ne matsalolin da suke addabar makarantun firamare.”

Ya hau keken, ita ma ta hau, suka tafi. Suka ci gaba da tattaunawa. Balele ya ce.

“A ka’ida, kuma a inda aka san darajar ilimi, ake son talakawa su yi ilimi, za ki tarar malamai suna cikin walwala da ingantaccen albashi, don ilimi shi ne ginshikin rayuwar al’umma, da shi ake zama komai, ake zama shugaba, ake zama likita, ake zama injiniya, ke ake zama duk wani abu da kika sani na ci gaba, da shi kasa ke ci gaba. Amma a wannan kasa tamu, malami ya zama wulakantacce, albashin sa ya zama nakasasshe. A lokacin da malamai ke rainon yaran, don su zama masu ilimi, wasu su zama shugabanni ko ‘yansandan, a lokacin wasu bata-gari ke shiga aikin dansandan. A lokacin da malamai ke rainon yaran don su zama masu biyayya ga doka da kishin kasa, a lokacin wasu ‘yansandan ke zama baragurbi. Me kike tsammani idan a ce a makarantun nan, mummunar tarbiyya ta bijirewa shugabanni ake koya musu, shin kasar za ta zauna lafiya?

“A bangaren ciyar wa gaba, za ki tarar ana ciyar da ma’aikata gaba, amma malamai ko oho? Malamai ba su da walwala a kasar nan?

“Daliban da suke zuwa makarantar firamare ta gwamnati, dukkansu dai kin san ‘ya’yan talakawa ne, hatta kansila a yanzu ba ya kai dansa irin makarantun nan, don haka babu batun wani kulawa daga wadancan wakilai na al’umma. Idan ana neman yara su siyo littattafai da wuya za ki samu yara biyu a cikin dari sun siyo, iyayensu suna ta abin da za su ci ba za su iya siya ba. Hatta kudin bajo, ko na jarrabawa ko na wasu takarda, sai dai iyayen yaran su biya, kin ga dole a samu harkar karma-karma wajen biya, ta yadda a irin haka wasu ke rasa ingancin karatun nasu, wasu kuma sai ki ga sun hakura.

“Makarantun sun zama kangwaye, sun zama matattarar kadangaru da wurin wasan kwallon yara. Babu teburan da kujerun zama na yara sai dai su zauna a kasa, har su ma malaman ba su da wurin zama, sai dai kan  tabarmi. Ba a maganar dakin karatu (library) bare dakin taro.

“Bangaren al’amuran da suka shafi wasanni, babu su a ire-iren wadannan makarantu, kokari guda da yaran ke yi wa kansu, shi ne, su samo kwallon su (ball), su zo, suna yi, amma duk wani wasa ba dai shugabanni su kawo shi makarantun ba, har a samu yara suna yi, su motsa jikinsu, ya kuma ja hankulansu su je makaranta, su yi karatu.

“Hakika, ba a damu da ilimin ‘ya’yan talakawa ba, kuma babu alamun za a damu da shi din. To amma da su talakawan za su yi wani abu, su damu da yin karatun nasu, masu ilimi a cikinsu, su sadaukar da kansu, su bai wa kannensu na baya ilimi kyauta, sannan su nuna musu muhimmancin ilimin, kuma su tallafa musu su yi karatun, haka, masu dan karfin su, su tallafa da abin da suke da shi, to da an rage, an sami rangwame daga abin da aka rasa.”

Harira ta amsa, “Wadannan abubuwa da ka lissafa, duk su ne matsalar, kuma su ne mawarwara, ina ma za mu gane, mu gyara. Ni dai, in sha Allahu, ina da burin taimaka wa al’ummata ta fuskar ilimi.”

Balele ya yi murmushi, “Ni ma ina da wannan ra’ayi naki, fatanmu Allah ya ba mu iko.”

“Amin.”

Da yake Harira tana da buri da manufa a rayuwarta, haka mijinta Balale, tana zaune a gidan aurenta, ta kammala karatun sakandare, ta shiga jami’a, inda take karanta tsimi da tanadi (economics). A lokacin shi Balelen ya kammala karatunta na jami’a, har ya samu aiki a ma’aikatar tsara birane ta jiha.

Bayan ta kammala, ta yi nisa wajen aikin al’umma, ta hanyar wayar da kai, da kuma jan ragama a yi abin da ya dace a tsakanin al’umma, tun daga unguwarsu, har ta kai matakin jiharta da jihohin arewa.

Harkokinta suna tasiri ga al’umma, saboda tana yi don Allah, kuma halayyarta da amanarta ya ja mata farin jini da karbuwa.

Kafin wasu shekaru, unguwar da Harira take, ta karbi tunanin ta, na bai wa kananan yara mata da maza dama su yi karatu, da kuma inganta harkokin karatu daga tushe.

“Allah cikin ikonsa, ita Harira Allah ya taimake ta, ta samu mafita.” Cewar daya daga cikin masu saurarona.

“Kwarai kuwa.” Na amsa masa, “Allah ya taimake ta mahaifinta yana kula da rayuwar ta, amma su Laure da kaninta Sadi, su mahaifin su, guduwa ya yi, ya bar su, ya yi sanadiyyar jefa rayukansu cikin mawuyacin hali.”

“Kamar yaya?”

“Kamar yadda zan gaya muku labarin Laure da kaninta Sadi.”

“To ba mu, muna sauraronka.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< ‘Ya’yanmu 1‘Ya’yanmu 3 >>

1 thought on “‘Ya’yanmu 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×