Kyakkyawar Rayuwa
Labarin Laure da kaninta Sadi
A tsaye idan ka ga Laure ba za ka iya kiyasin adadin shekarunta ba, amma dai yarinya ce 'yar shekaru goma sha biyu da daidaikun kwanaki. Kyakkyawa ce, duk da ba ta karasa munzalin budurwa ba, saliha da ita, mai kamala saboda irin biyayya da taimaka wa mahaifiyarta ka'in da na'in da take. Ba ta shiga hayaniya da hargowar yaran kauyensu, shi ya sa ake ganin ta a matsayin salihar.
Tafe take, dauke da tulun ruwa, a bayanta kuwa kaninta ne. . .