Skip to content
Part 3 of 4 in the Series Ya'yanmu by Kabiru Yusuf Fagge

Kyakkyawar Rayuwa

Labarin Laure da kaninta Sadi

A tsaye idan ka ga Laure ba za ka iya kiyasin adadin shekarunta ba, amma dai yarinya ce ‘yar shekaru goma sha biyu da daidaikun kwanaki. Kyakkyawa ce, duk da ba ta karasa munzalin budurwa ba, saliha da ita, mai kamala saboda irin biyayya da taimaka wa mahaifiyarta ka’in da na’in da take. Ba ta shiga hayaniya da hargowar yaran kauyensu, shi ya sa ake ganin ta a matsayin salihar.

Tafe take, dauke da tulun ruwa, a bayanta kuwa kaninta ne, Sadi ke biye da ita. Sun gaji tikis, saboda tsananin nisan inda suka je, suka debo ruwan.

Sai dai ba gajiyar ba ce za ta sa ka damu da kallon Laure ba face yanayin da take ciki. Tana tafe, tana kuka, ba wai kukan ta je waje mai nisa ta debo ruwa ba ne, kuka ne na takaici da damuwa.

A cikin gidan Iya Marka tana tsugunne a bakin murhu, tana iza wuta, duk ta yi jibi, idanunta jawur saboda balbalin hayakin da ya balbale mata idanu, ga shi wutar ta ki ruruwa.

Laure da Sadi suka yi sallama kusan a tare. Iya Marka ta dago tana sharbe majina, ta dube su, ba ta amsa sallamar ba, ta tsaya tana kallon su, musamman saboda jin muryar da Laure ta yi sallamar da ita, muryar kuka.

Baki bude, cikin mamaki Iya Marka ta ce, “Allah mai iko, me ya faru, me ya sa ki kuka ‘yar nan?”

A yanzu ta mike, ta tarbe su, sai da ta sauke musu tulunan ruwan gabadaya, kana ta rungume Laure a jikinta, “Ke nake tambaya Laureta.”

Laure ta kuma fashewa da kuka, ta kankame ta.

Iya Marka ba ta son kukan ‘yarta, ta dago fuskarta tana cewa, “Kin san ba na son bacin ranku bare kukan nan naki mai sa ni kuka ni ma.”

Laure ta sassauta, ta ce, “Iya a da ne ba kya son kukanmu, amma a yanzu kina so, har fiye da kuka ma mu yi.”

Hankalin Iya Marka ya kara tashi, ta yi sauri, ta kalli Sadi, shi kam yana tsaye, yana kallon su, idanunsa jajur, yaro mai dakiya wanda ba karamin abu ke sa shi kuka ba.

Da Iya Marka ta dawo da hankalinta ga Laure sai ta fara share mata hawaye, tana lallashinta, “Zo mu je ku ci abinci ku nutsu, kya gaya min abin da ya faru. Amma fa ki yi shiru don Allah.”

Ta kama hannunta, suka nufi cikin daki.

Bayan da suka gama cin abincin, suka sha ruwa, abin ka da gajiya da yunwa, suna kammalawa barci ya debe su a wurin.

Iya Marka ta kalle su cikin tausayi, ta yi tagumi, hawaye yana biyo kan fuskarta. Tana son diyanta.

*

Bayan shudewar sa’a guda da ‘yan mintuna Iya Marka ce a zaune ita da Laure suna duban juna, amma Sadi har yanzu barci yake yi. Ita kuwa Laure ta jima da farkawa, sun yi jugum. Hawaye a fuskar Laure, damuwa da kwalla kuwa a idon Marka.

Daga bisani ta gyara murya, ta ce. “Babu yadda zan yi Laure, dole in amince da tafiyar ku birni. Ki yi hakuri ba son raina ba ne…” Muryarta tana rawa.

Laure ta katse ta, “Iya kin manta yadda ke da Baffa kuke gaya mana irin matsalolin da ke tattare da kai yara cikin birni, wasu ma ba sa dawowa har abada.”

Marka ta kalle ta, “Na gaya miki a yanzun ma dole ce ta sa na amince, kar ki manta Baffan naku fa guduwa ya yi ya bar mu cikin wannan hali, shi ya yi sanadiyyar da dole sai wannan abu ya faru.” Ta fara kuka, “Ban so kika yi min famin wannan ciwo ba Laure.”

Laure tana kuka, “Iya ki yi hakuri, amma maganar nan dole sai na yi ta.”

Marka ta durkusa ta fara share mata hawaye, “Na ji, haka ne, amma kin san ai laifin Baffanku ne ko.”

Laure ta ce, “Ta yaya ya zama laifin shi, shi da baya nan? Kuma na tabbatar da a ce yana nan haka ba za ta faru ba.”

Marka ta dan yi shiru, tana kallon ta, kafin ta ce, “Ya gudu ya bar mu cikin tsanani da kunci da fatara, dole in bayar da ku, ku je birni, ku yo aikatau da za mu sami abin da za mu yi rayuwa, mu sami kudin biyan haraji da biyan kudin magani da…sauran bukatunmu.”

“Iya kin sayar da mu…”

Marka ta yi saurin fiddo da idanu waje, ji ta yi kamar ta wanka wa Laure mari, amma ba za ta iya ba. Ta fara ba ta labarin yadda mahaifinsu ya gudu.

*

Karo na biyu Baffa Na’amadu ya sudado ya bi ta tsakanin ‘ya’yansa biyu Laure da Sadi ya wuce, sannan ya daga kafarsa a hankali ya tsallake Marka, yana haura daya kafar ya ji an rike ta.

Sannu a hankali don kar ya fadi, ya zauna a nutse, don ba ya son ‘ya’yan su farka. Marka da ta rike kafar, ta tashi zaune, suka sa juna a gaba suna kallon-kallo.

“Kana shirin jefa rayuwarmu a garari.”

Damuwar da ke fuskarsa ta fitar da hawaye, ya ce “Marka dole ne in gudu daga wannan kauye.”

“Za ka guje wa kunci, mu ka bar mu a ciki kenan?”

“Kuncin da nake ciki ya ninka wanda kuke ciki da wanda zan bar ku sau shurin masaki, don haka ki bar ni, in tafi, kar kaina ya fashe saboda bakin ciki.”

Duk da kokarin da ta yi wajen rike hawayen idonta don kar ya fito, domin ta nuna masa a wannan lokacin babu rauni a tare da ita, sai da ta gaza, hawayen ta silalo.

“Dukkanmu, mu ukun nan, ba mu kai ka karfin hali ba, muna da raunin da ba za mu iya irin juriyar da za ka yi ba, idan ka yi abin da kake kokarin yi, to ka yanke mana hukunci mafi muni da ka iya kai rayuwarmu gabar karshe.”

Na’amadu ya yi shiru, ya kasa furta komai.

“Ina rokon ka don Allah duk abin da zai faru kar ka tafi ka bar mu, Allah shi ne gatan kowanne bawa, amma kai ne katanga kuma majingina ga rayuwarmu.”

Ta fashe da kuka. Kukanta ya shiga zuciyarsa, ya tashi da sauri, ya koma inda yake kwanciya, ya kwanta shi ma yana kuka.

A nan ta ci gaba da kukan ta, har ta gaji, sannan ta ja shimfida, ta kwanta, nan da nan barci mai nauyi ya kwashe ta.

Kusan awa biyu da kwanciyar Marka, mafarki ya farkar da ita, kai tsaye inda mijinta Na’amadu ke kwance ta kalla. Gabanta ya yi saurin faduwa saboda rashin ganin shi a wajen, a hanzarce ta mike tsaye, ta fara dube-dube.

Kafin wani lokaci ta duba duk inda ya dace, tun daga cikin dakin ajiyar kaya da bayan rumbu zuwa bayan-gida, babu Na’amadu babu alamar sa.

Abin da ya kudira na guduwa sai da ya cimma nasara. A nan, a bakin bayan-gidan ta durkushe, ta fashe da kuka.

Wannan ita ce ranar da Baffa Na’amadu ya gudu, ya bar matarsa da ‘ya’yansa Laure da Sadi saboda halin kuncin rayuwa.

 “Kin ga ni a matsayina na mace babu abin da zan iya yi.” Cewar Marka tana duban Laure. A daidai wannan lokacin Sadi ya farka daga barcin da yake yi, suka kalli juna gabadayansu.

***

Dagaci, Bukar Maitsango na kauyen Mainar Wake shi ne jagoran aiwatar da wannan harka ta bayar da kananan yara zuwa birni don su yo aikatau, ko ma mai gabadaya, siyar da su.

Rayuwa irin ta bauta da bautarwa babu irin wacce ba a yi a kauyen Mainar Wake karkashin Dagaci Bukar Maitsango, domin ko a iya noma da yake sa yara kanana su yi da kuma debo ruwa ko kiwo ya isa a daga masa kara wajen zalunci.

Ban da wadanda yake sa yaran su yi masa a cikin kauyen, har kwangila yake karba daga wasu kauyuka, ya tura yara su yi ayyukan wahala, ayyukan kunci kuma ya karbi lada, ya soke a aljifansa. Kuma babu uban yaron da ya isa ya yi magana.

Duk lokacin da aka zo za a tafi da yara hudu ko biyar na wannan kauye, nunawa ake yi za a kai su karatu ne ko wata ziyara, daga haka kuma shikenan, wasu sun tafi kenan, wasu kuma sukan dawo amma da yawansu a wulakance.

A haka, aka tafi da Laure da kaninta Sadi. Rabuwa irin wadda babu tabbas ko za su sake ganin juna da mahaifiyarsu Marka.

*

A birni, a wani gida mai katotuwar haraba aka zube su Harira, akalla sun yi kusan mintuna arba’in, sun yi tsuru-tsuru da su wasu sai zare idanu suke, wasu kuma suna ta hamma saboda yunwa da gajiya, sun zuba idanu, suna jiran abin da zai faru.

Bayan wucewar karin wasu mintuna wanda kamar an manta da su, sai ga wasu mutane su shida sun shigo, suna kallon su, kamar yadda su ma yaran suke bi su da kallo.

Biyu daga cikin mutane shidan mata ne, suka zo, suka tsattsaya a gaban yaran. Sai da suka rarraba su gida uku, suka ware su, Allah ya taimaki Laure tana tare da Sadi a rabon.

“Ku wadannan ku bi Alu.” Mai warewar ya nuna gajeren cikinsu, mai suna Alu.

Ya dawo da ganin sa ga rukunin su Laure.

“Ku kuma, za ku tafi tare da Hajiya Tala.” Ya nuna daya daga cikin mata biyun, fara, farin mai, mai ‘yar tsabar jiki.

“Ragowar kuma, sai ku biyo ni.”

Haka aka kasafta su, suna ji, suna gani ko uffan babu wanda ya ce a cikinsu. Babu abin da Laure take yi ban da addu’ar Allah ya sa duk rintsi kar a raba ta da kaninta.

Allah ya amshi addu’arta. Da aka tafi da su, ita da Sadi da wata yarinya mai suna ‘Yar’iya aka kai su wani babban gida, mai kyau; gidan Alhaji Namadi.

An ba su daki a harabar gidan kusa da dakin maigadi. Aka hada su da wata dattijuwa mai suna Mairo.

Mairo akwai ta da fadan tsiwa, ita ce ta yi musu bayani.

“Ku bude kunnuwanku ku ji abin da zan gaya muku don ba wasa ko iskanci a gidan nan. Da farko an kawo ku ne domin ku rinka yin shara ko wanke-wanke ko wankin bandaki ko rainon yara da sauransu. Kuma ba a son kazanta, ko yawan kallo bare uwa-uba sata, duk ‘yar iska ko dan iskan yaron da ya sami kansa a dayan wadannan abubuwa to zai dandana kudarsa, sai ya gwammace uwarsa ba ta aiko shi birni ba.” Ta yi kaki, ta tofar.

 “Ka ji kazama, tana yi mana fadan kar mu yi kazanta, ita tana yi.” Laure ta furta hakan a ranta.

“A nan gidan idan aka ce yi, to ana nufin a yi din, haka idan aka ce a bari, to barin ake yi kai tsaye, don haka duk wanda ya ji to ya huta. Ku je, ku ajiye kayanku, yanzun nan za ku fara share harabar gidan nan.”

Ta wuce, ta bar su, suna raba idanu.

Sadi ya kalli yayarsa, ya ce “Laure mun dawo nan da zama kenan, ba za mu koma gida ba?”

Ta nuna masa alamun ya yi shiru, ta hanyar sa hannunta a kan lebanta, “Za mu koma gida watarana, ka yi hakuri ka daina magana.”

“To.”

Washegari

Dan abincin da aka ba su Laure, bai taka kara ya karya ba, kuma suna gama ci aka hada su da tarin aiki, tun daga wankin bandaki zuwa wankin kaya da wanke tsakar gida.

Babu yadda za su yi, haka suka shiga aiki cikin damuwa.

Can wajen Azahar, Mairo ta sake kawo musu abinci; shinkafa da miya; su duka ukun a kwano daya, suka zauna a farfajiyar gidan suna ci.

“Laure yanzu shikenan ba za mu sake ganin Innarmu ba…” Muryar Sadi cike da damuwa, ya tambayi yayar tasa.

Cikin lallashi Laure ta ce.

“Ka daina fadar haka, za mu koma gida in sha Allahu, ko ‘Yar’iya?” Tana kallon ‘Yar’iya.

‘Yar’iya ta gyada kai, “Za mu koma gida idan muka samu kudi.”

Daidai wannan lokacin Isa ya danno kai farfajiyar gidan babu ko sallama. Yaro ne dan-bana-bakwai, mai dauke da shekaru ashirin da biyar a raye. Gafalalle ne da aka sangarta gami da shagwabawa. Ya bi su Laure da wani irin kallo, musamman ita Lauren.

Mairo ta dawo don kawo musu ruwa a kwano, ta dubi Isa, sannan ta daka wa su Laure tsawa.

“Ku ba za ku gaishe da shi ba. Kun ga mutum ya shigo, ko sai kun yi mana kauyancin…!”

A razane suka shiga gaishe da shi.

“Ina wuni…”

“Sannu da zuwa…”

“Ina kwana…”

Kowannensu da yadda ya yi gaisuwar, saboda rudewa.

Bai amsa musu ba, ya ce da Mairo.

“Wadannan almajirai ne ko ‘yan gudun hijira?”

“‘Yan aiki ne aka kawo.”

Ya sake duban su, sannan da zai wuce, ya ce da Mairo.

“Ki same ni a dakin Hajiya.”

Ta amsa da to, ta ajiye musu ruwa daga inda take, ta juya, ta bi bayan shi.

Su Laure suka dauki ruwan don su sha.

A gaban Hajiyarsa, Isa cikin tsawa ya ce da Mairo.

“Ba ma son namijin, a mayar da shi. Su matan sun isa.”

Da uwar da Mairon babu wanda ya tanka masa, to kawai Mairo ta ce, ta yi waje.

Kamar da wasa, aka dauke Sadi, aka raba shi da ‘yar’uwarsa Laure, suna ji suna gani, sun sha kuka, sun koshi babu yadda za su yi, face fatan da Laure take yi shi ne, Allah ya sa kaninta ya fada hannu nagari.

Allah ya jinkirta karbar addu’ar Laure, don kuwa Sadi bai fada hannu nagarin ba, a hannun Hajiya Mala ya shiga, wata ‘yar kabilar Kanuri, fitacciya wajen safarar mutane; yara da manya zuwa kasashen Turai da Asiya don neman kudi. Takan fitar da yara kanana ko manya maza zuwa kasar Saudiyya da sauran kasashen Larabawa don yin bara ko aikin wahala bisa yarjejeniyar biyanta kudin da ta kashe musu, takan ci riba ninki-ba-ninki.

Tana fitar da yara ‘yanmatan masu shekaru sha uku zuwa sha takwas kasashe irin su Italiya da Jamus da sauransu, su sa su a karuwanci don su nemar mata kudi.

Tana yin harkokin nata bisa yarjejeniya ga mutanen da suka yarda ta fitar da su, su kuma irin su Laure da ba sa so, takan same su ne ta hanyar siyen su, kuma ta tilasta musu.

Ba sani ba sabo a harkarta, duk wanda ya karya mata yarjejeniya yakan gane kurensa, sannan babu wani tausayi ko kadan a lamuranta, muddin za ta samu kudi, to yaro ko yarinyar ko wahainiya ne su babu ruwanta za ta jefa su a miyagun harkokin da ke gabanta, da zarar ta tatsi kudinta ta ci riba, to kowa ya yi gaban kansa.

Akwai yakinin kaso mafi yawa na bakaken fatan karuwan da ke Italiya ko Jamus, musamman ‘yan Arewacin Najeriya, to ita ta yi sanadiyyar shigarsu Turai, masu so da wadanda ba sa so. Haka almajiran da ke Saudiyya da Dubai da sauran kasashen Larabawa, da yawansu ita ce silar kasancewar su mabarata.

Idan ka ga dan akuya na rawa a gaban kura to akwai abin da ya taka, Hajiya Mala tana da gagarumin daurin gindi a wajen ‘yan siyasa da jami’an tsaro na kasar nan, ta yadda tana jin babu wani da da zai kawo mata cikas a harkokinta, shi ya sa take rawar gaban hantsi abin ta.

Sadi da wasu yara su hudu, uku mata daya namiji mai suna Bala aka siyar mata. Ita kanta Laure don Isa ya ce a bar masa ita ne, amma da tare za a siyar da su ga Hajiya Mala.

Abu na gaba, shi ne safarar su Sadi zuwa kasar Saudiyya, sauran matan kuwa Turai.

Zaune a wani daki mai karancin haske, Sadi ya sha kuka har ya gaji, bayan rabuwa da mahaifiyar su Marka, tabbas rabuwa da yayarsa Laure ya kara daga masa hankali.

Sauran yaran, ‘yanmatan da ke gefe ya fara kallo kafin daga bisani ya dubi Bala da ke gefensa.

“Ina mutanen nan za su kai mu?”

Bala ya kalle shi da mamaki, “Kai ba ka san inda za a kai mu ba? Kuma ba ka ji suna fada ba?”

“Wallahi ban sani ba, kuma ban ji ba, ku kun sani?”

“E mana, Makka za a kai mu, mu yi bara, mu tara musu kudi da suka kashe a kanmu. Sun gaya wa babana kafin su kawo mu nan, ko ba ka son zuwa?”

Sadi ya yi shiru cikin damuwa. “Ni na fi so a mayar da ni wajen mahaifiyata…” Ya yi kamar zai fashe da kuka.

Kafin Bala ya yi magana, suka jiyo muryar su Hajiya Mala da wani mutum suna tattaunawa, sai suka yi shiru, suna sauraron su.

“Ba na son su dade a kasar nan, ka san zan yi tafiya.” Muryar Hajiya Mala.

Mutumin ya amsa mata, “Na sani Hajiya, kuma ba ki da damuwa a kan wannan, ki kwantar da hankalinki.”

“Ok, na san ba ka da matsala.”

Suka wuce, su Sadi suka yi ajiyar zuciya kamar a tare.

*

A can gidan Alhaji Namadi, Isa ya koma zama a gidan saboda Laure, har mutanen gidan sun fuskanci hakan. Wasu daga cikinsu sun san halin nasa zai nuna a kan Laure, wasu kuma ba su sani ba.

Bayan yawan kallon ta da yake yi, har zuwa yake yi idan tana aiki ya dauki kujera, ya zauna, ya kura mata ido, sannu a hankali har ya fara yi mata magana cikin kulawa.

Ba a yi nisa ba, Laure ta fahimci manufarsa a kanta, don haka ta kara tsorata da shi, tana guje masa.

Da ya fuskanci hakan sai ya fara yi mata dole, nan ma Laure ta yi amfani da iyawar ta, ta guje shi.

Wani dare, Laure na kwance a dakin da aka ba ta, Isa ya shiga ba tare da ta sani ba, ya rufe mata baki, ya dauke ta cancak.

Kai tsaye, bangarensa ya nufa da ita, ya kai ta wani daki da ke loko a cikin dakunansa, ya kulle.

*

A kauyen Dandubga Iya Marka ta rasa sukuni a rayuwarta, da dare sai ta yi ta mafarki da ‘ya’yanta; Laure da Sadi, mafarki mummuna na tashin hankali.

Haka take wuni da rana cikin damuwa da zullumi da kuma tunanin halin da ‘ya’yanta ke ciki.

A karshe ta yanke shawarar tunkarar Dagaci.

Dagaci Bukar Maitsango na zaune da wasu ‘yan korensa guda biyu; Alu da Dangurgu suna hira, Marka ta iso gare su gami da yin gaisuwa.

“Me ke tafe da ke?” Alu ya tambaye ta.

Ta kara saddar da kai.

“Na zo neman alfarma ne gareka yallabai.”

Dagaci ya dube ta.

“Allah ya sa ba bashi ko kayan abinci za ki nema ba?”

“Ko kadan, so nake a taimake ni a dawo min da ‘ya’yana yallabai, wallahi kullum sai na yi mummunan mafarki da su.”

Dagaci da su Alu suka kwashe da dariya, har da buga kafa.

“Da alama kin haukace Marka.” Cewar Dagaci.

Ta girgiza kai.

“Lafiya ta kalau, ka taimake ni, ina son ganin ‘ya’yana.”

Suka sake shekewa da dariya.

“Tuburan kenan.” Alu ya fadi yana dariya.

Dagaci ya sha kunu.

“Ba zan iya dawo miki da su ba, sai dai ki je can, ki nemi hanyar da za ki komo da su…”

Marka ta yi kokarin yin magana, Dagaci ya daka mata tsawa.

“Tashi ki ban wuri, tun kafin ranki ya baci. Na ce miki ba zan iya ba, don haka ban son kara jin komai, bace min da gani.”

Ba yadda za ta yi, haka Marka ta mike a sanyaye, idanu cike da kwalla, ta bar wurin kamar wadda ruwa ya yi wa mugun duka.

Dangurgu ya dubi Dagaci, cikin muryar gulma ya ce.

“Yallabai akwai matsala fa.”

Dagaci ya dube shi.

“Wacce iri, kuma daga ina?”

“Daga wajen wannan matar mana. Ina tsoron tun da ta fara yin wannan maganar, to idan aka kyale ta, za ta iya kai maganar inda ba mu yi zato ba, kuma ta tona mana asiri.”

Suka yi shiru, suna tunani, jim kadan Dagaci ya girgiza kai.

“Kwarai kuwa, ka zo da hange. Yanzu ya za mu yi da ita?”

Suka kara yin shiru. Dangurgu ne dai ya sake korar shirun.

“Lallai ya kamata a yi maganin ta, ko da kuwa ta hanyar kawar da ita daga wannan kauyen ko duniyar ma gabadaya ne.”

Dagaci ya dube shi.

“Idan ka ce duniyar, kana nufin a kashe ta kenan fa?”

“Kwarai kuwa. Da ta tona maka asiri, ai gwara a yi hakan, don tonon asirin kamar kai ma ta kawar da kai ne, kuma kawar da makiyi kafin ya kawar da kai ai ibada…”

“Ni ma na goyi da baya.” Cewar Alu.

Dagaci ya ce, “Ka zo da shawara mai kyau, abin ba na wasa ba ne. Amma yanzu ya kake gani za a yi?”

Dangurgu ya ce, “A fara bibiyar ta don a tabbatar ta daina wannan tunanin nata, kuma a tabbatar ba za ta kai maganar ko’ina ba, idan ba ta ji ba, sai a dauki mataki na gaba.”

Ta hanyar girgiza kai Dagaci ya nuna amincewarsa. Sannan ya ce.

“Wa zai yi wannan aikin?”

Dangurgu ya yi caraf, ya ce, “Ka bar komai a hannuna yallabai.”

Dagaci ya ce, “Na damka maka, amma kar a samu akasi.”

“Ba za a samu ba.” Dangurgu ya amsa. A zucinsa kuma ya ce, “Alhamdulillahi, na samu damar yin ramuwar gayya.”

Jikakkiyar da ke tsakaninsa da Na’amadu mijin Marka yake so ya yi ramuwar gayya a kai. Na’amadu shi ne sanadin gurguncewarsa a wani fada da suka yi. Don haka wannan wata dama ce da Dangurgu ya dade yana nema ta samu don ya rama.

A baya, ya sha dana tarko da fako amma bai samu dama ba sai yanzu.

*

Buda da Kaskali su ne fitinannu kuma tsagerun matasan kauyen Mainar-wake da sauran kauyukan da ke kewayensa, sun gagari kowa, abin da suka ga dama suke yi.

Kai tsaye su Dangurgu ya samu don ya ba su aikin gintse rayuwar Marka.

“Wa ya aiko ka da kwangilar nan?”

Buda ya tambayi Dangurgu.

“Yin kaina ne, ni na aiko kaina.” Cewar Dangurgu.

Kaskali da Buda suka kalle shi cikin mamaki.

“Me gare ka da za ka ba mu, don mu yi maka aikin?” Kaskali ya tambaye shi.

Dangurgu yana rawar kafa ya amsa.

“Shekaru biyu ina yin noma don in samu abin da zan bayar a yi min wannan aikin, kuma na samu. Zan ba ku buhun maiwa daya da tiyar alkama guda hudu.”

Suka jinjina abin.

Buda ya ce, “Ya aikin naka yake?”

“Wata tsohuwa nake so a kawar.”

“Tsohuwa? Tsohuwa kawai?”

“E, Marka ta kauyenmu nake so a kashe.”

Buda da Kaskali suka kalli juna.

“Ashe aikin ma karami ne, yaranmu ne ya kamata su yi aikin, amma tun da muna bukatar abin da ka bayar, gobe zan cika aiki. Bace mana da gani. Wato je ka kawo.”

Dangurgu ya dingisa, ya bar wurin. Buda ya ce da Kaskali.

“Ba mu kadai ba ne marasa imani ba, kowanne dan iska ba shi da imani sai dai idan bai samu dama ba.”

Suka yi dariya.

*****

Da tsakar dare, al’umma kowa na barci ciki har da Marka, Buda da Kaskali suka isa gidan Marka dauke da makeken buhun algarara, da yake ita kadai ce a gidan, kuma ga ta tsohuwa, su kuwa kartai guda biyu, ba su sha wahala wajen sankame ta ba.

Sun toshe mata baki, sannan suka daure bakin, suka cusa ta cikin buhun, suka yi kama-kama, suka tafi da ita.

Saboda tsantsar rashin imani, a can jejin da suka je, suka yi jifa da buhun, ba su kyale shi ba, suka sa sandunan da suka taho da su, suka dinga jibgar buhun, har sai da suka daina jin motsi. Sannan suka bar wurin.

*****

Duk lokacin da Isa ya ga dama, yakan je wa Laure, ya yi abin da ya so da ita, ya bar ta cikin tsananin kunci da bakin ciki.

A dakin da ya ajiye ta akwai komai na kayan alatu, gado, talabijin, firji da komai. Sannan ba ya bari kayan abinci da na sha su yanke, sai dai ba ya bari ta bar dakin, don ban da rufe ta, har daure ta yake yi, amma ba irin daurin da zai cutar da ita ba.

Wata ranar Juma’a da yamma Isa ya zo da abokinsa, Danmama. Bayan sun ci abinci, Isa ya kebe da Laure a cikin dakin da take, tsawon mintuna sannan ya fito, Danmama ya kalle shi.

“Gaskiya kai azzalumi ne.”

Isa ya harare shi, “Kai ma haka.”

“Ban kai ka ba, don kai naka ya wuce misali.”

“Duk zalunci da babba da karami daya suke.”

“Gaskiya, wallahi, wallahi sai na tona maka asiri, kuma ba a wajen kowa ba, a wajen Mamanka da ‘yan hisba.”

“Kai kuwa Allah ya tsine maka albarka.” Isa ya ce da Danmama.

Danmama ya ce, “Ko me za ka ce, sai dai ka fada.”

Isa ya san Danmama ba ya fadar magana irin wannan bai cika ba. Ya yi ta lallashin sa, amma ya yi fafur ya ki, haka suka rabu baram-baram dutse a hannun riga.

*****

Ganin babu yadda zai yi, washegari da daddare, Isa ya fita da Laure, ya kai ta gidan Hajiya Mala don siyar da ita.

Hajiya Mala ta kalli Laure sosai tana murmushi, “Gaskiya Isa ka yi min komai, duk cikin yaran da aka kawo min, ba a kawo min kyakkyawa irin wannan yarinya ba.”

Ta dubi yaranta.

“Ku kai ta daki.”

Cikin hanzari wata mace ta kama hannun Laure, ta fita da ita.

Dakin da aka kai Laure, babban daki ne, mai dauke da kafet da kujeru. A cikin dakin akwai yara maza da mata da Hajiya Mala ta siya wadanda take safarar su.

Bayan shigar da Laure, matar ta ja kofa, ta rufe. Laure ta sami gefe guda, ta takure.

“Yaya Laure.”

Kamar daga sama Laure ta ji muryar kaninta Sadi yana ambatar sunanta.

Da sauri ta juya, ta tabbatar shi ne, ta rungume shi, suka sa kuka. Suka yi mai isar su, sannan suka sake duban juna.

“Ke ma an kawo ki nan?”

“E.” Ta amsa a takaice.

“Na ji an ce sayar da mu aka yi, za a kai mu wasu kasashen a sayar a can.” Cewar Sadi.

“Wa ya gaya maka?”

“Wadancan yaran ne na ji suna labari.” Ya nuna su. “Su, suna so ma a kai su.”

Suka sake fashewa da kuka. Wata yarinyar da ke gefe ta ce.

“Kwa yi, kwa gama, domin ko kukan jini za ku yi ba za a kyale ku ba.”

Kallon ta kawai suka yi.

*****

Sadi yana cikin yara goma sha uku da aka kai kasar Saudiyya don yin bara. Wani rashin sa’a da ya kara yi, shi ne; yaran Hajiya Mala sun fuskanci yanayin samun abin sadaka a Makka ya yi karanci in har ba wata tawaya yaro gare shi ba, ma’ana idan yaro ko yarinya ba gurgu ko marasa hannu ba, to ba a cika ba su sadaka ba.

Hakan ya sa suka ware su Sadi su takwas, kiri-kiri suka sa aka yanke wa wasu daga cikinsu hannu daidai, wasu kuma kafafu, har da yara biyu da suka cirewa ido daidai. Suka yi jinyar su na ‘yan kwanaki, kana suka zuba su a kan hanyoyi na biranen Makka domin su samar musu da kudaden da suka kawo su nema.

Tabbas yaran sun ga rashin imani, haka siddan saboda neman abin duniya an nakasa musu rayuwa.

*****

A nata bangaren Laure ita ma babu sauki, kasar Italiya aka kai su, ta hanyar Libiya zuwa cikin ruwa, har suka haure zuwa Italiya, wato ta kasa kenan.

Dukkansu, tun a cikin Libiya suka fahimci inda aka nufa da su, wato karuwanci za a kai su.

Wani gida ne da Turawan Italiya ke zuwa su sheke ayarsu aka kai su. Ba’italiye ya sha giyarsa ya yi tatul, ya afka wa yarinya karama.

Bayan mummunan wannan aikin da ke faruwa da su Laure, abin da ya fi muni shi ne, rashin ‘yancin yin ibada, domin wadanda suka tarar a wurin duk Musulman an hana su yin salla bare sauran ibadun addini. Wasu daga cikin yaran sun hadiyi zuciya, sun mutu. Ita ma Laure ta so hakan ya faru da ita, amma ba ta samu ba.

Haka rayuwar su Laure ta zama injin buga kudi. Kullum a kan samu Turawa mashaya su sadu da su, su biya su, kudin kuma sai a bai wa yaran Hajiya Mala.

Suna samun abinci da abin sha da makwanci mai kyau, da walwalar rayuwa idan sun so.

*****

A tsammanin su Buda da Kaskali, tuni Marka ta mutu a inda suka jefar da ita, sai dai ba su suke da rayuwar ba, domin Marka ba ta mutu ba, amma ta samu tabuwar hankali saboda bugu da ta sha a ka.

Haka, ta tashi a matsayin mahaukaciya, ta shiga gararamba tana neman ‘ya’yanta. Takan sami abin da za ta ci a bola ko a sadaka, sannan takan kwana a duk inda ta sami kanta komai ruwa ko sanyi ko zafi.

Ba ta san wace ce ita ba, bare inda ta nufa, kawai dai ta san tana neman ‘ya’yanta, lallai tsakanin ‘ya’ya da mahaifiyarsu, sai Allah.

Watarana a irin wannan gararambar, Allah ya watsa Marka garin Gumel a ke jihar Jigawa, ta kwana a kofar wani katafaren gida na Alhaji Ahmad. Har gari ya waye, rana ta fito tana kwance, tana barci a kofar gidan.

Misalin karfe sha daya mai gidan da ‘yan korensa suka fito a motoci don su yi masa rakiya filin jirgi, a hanyarsa ta zuwa France.

Har sun wuce, sun hau babban titi, Alhaji Ahmadu ya tsayar da direbansa.

“Mu koma kofar gida.”

Direba ya duba agogo, “Alhaji lokaci ya kure fa, za ka iya rasa jirgin wannan lokaci.”

“Kar ka damu, mu koma.”

Direba ya juya mota, suka dauki hanyar komawa.

Har yanzu Marka na kwance tana barci. Motocin suka yi fakin a daf da inda take kamar yadda Alhaji Ahmad ya ba da umarni.

Shi da kansa ya bude kofar motar, ya fita, ya je gabanta, ya bi ta da kallo sosai. Cikin gaggawa kawai sai ya durkusa a gabanta.

Yaransa suka matso.

“Alhaji lafiya?”

Ya dube su, “Matata ce.”

A firgice suka dube ta, sannan suka sake kallon shi. Daya ya ce.

“Alhaji wannan mahaukaciyar ce matarka?”

A fusace Alhaji Ahmad ya kalle shi, “Uwarka ce mahaukaciya. Ku yi sauri, a saka ta a mota mu tafi asibiti. Na soke tafiyar da zan yi.” Take al’amura suka sauya, maimakon tafiya filin jirgin sama, suka dauke ta sai asibitin da Alhaji Ahmad yake mu’amala da su.

Ba jira, aka karbe su, aka ba su daki na musamman. Duk irin abubuwan da ke faruwa Marka barcinta take yi, ko da ta tashi a lokacin an kai ta asibiti, an kwantar a gado, da ta ji, ta bisa katifa, sai ta kara yin likimo.

Likitoci suka shiga aiki a kanta, tension da depression ne da duka da su Kaskali suka yi mata, amma abin ya zo da sauki, liktoci suka shawo kan al’amarin.

Sai bayan kwanaki uku Marka ta dawo hayyacinta, a ranar ta hadu da mijinta, ta sake rikicewa, da farko kin yarda ta yi da shi saboda fushi sai da kyar ya shawo kanta da uzururruka irin na shi. Abin ka da mace ta yarda da shi.

“Ina ‘ya’yana?”

Tambayar farko da ya fara yi mata kenan. Ta ba shi labarin abin da ya faru da ita da Dagaci da ‘ya’yansu.

Alhaji Ahmad ya harzuka, a ranar ya sa yaransa suka bazama zuwa kauyensu don samo labarin inda ‘ya’yansa suke. A ranar kuwa suka kawo masa sakamako.

“Bayan an kai su birni aikatau, an siyar da su ga wata mace mai safarar yara, sannan an kai Sadi kasar Saudiyya, yana can, yana bara, kuma…”

Dan aiken ya yi shiru. Alhaji ya daka masa tsawa.

“Kuma me?”

“An cire masa hannu daya don ya yi barar…”

Alhaji ya zube a kasa, ya fashe da kuka kamar yaro, haka ita ma Markar kuka take yi.

“Laure fa, tana ina ita?”

“Laure tana Italiya, a gidan mata masu zaman kansu.”

“Masu zaman kansu? Kana nufin Laure ta zama karuwa?”

“Ba zama ta yi ba, mayar da ita aka yi da karfin tsiya don ta nemar musu kudi. Wannan shi ne aikin da Hajiyar da ta siye su take yi, ta sayi yara ta mayar da su karuwai da almajirai a ciki da wajen kasar nan don su samar mata da kudi…” Cewar yaron Alhaji.

Zumbur Alhaji ya mike.

“Ku zo mu je, ba zan dawo ba sai da ‘ya’yana.”

Yana kuka, ya fita, yaransa suka rufa masa baya.

*****

Duk abin da Alhaji Ahmadu zai yi shi da yaransa, sun yi, amma sun sha bakar wahala sai bayan kwanaki arba’in da hudu suka samo su, aka dawo da su gida.

Tun daga lokacin da Alhaji Ahmad ya hadu da ‘ya’yansa bai iya magana da yawa ba, sai kuka. Bai tashi ganin tashin hankali ba sai lokacin da aka kawo su gaban mahaifiyarsu, Marka, ta sa wani irin kuka mai tsuma zuciya, sannan ta fadi, ciwon zuciyarta ya tashi.

An kai ta asibiti, ko awa biyu ba ta yi ba, ta ce ga garinku nan, ta mutu.

Abubuwa goma da ashirin na takaici suka hadar wa Alhaji Ahmad, ya rasa inda zai sa kansa, ya zama kamar zautacce. Sai da kyar ya samu kansa.

A lokacin ya sa abubuwa guda biyu a gabansa, na farko zakulo su Dagaci da su Dangurgu da Hajiya Mala da sauran masu harkokin safarar yara, ya sa aka hukunta su ta hayar doka da oda.

Sannan ya shiga lallashi da ban hakuri ga ‘ya’yansa. Tashin farko Sadi ya yafe masa.

“Baba ai ba kai ka yi mana haka ba. Na yafe maka.”

Amma ita Laure ta cije.

“Amma shi ne sila, ba don ya gudu ya bar mu ba, ai ba za mu zama haka ba, ni dai ban yafe ba, Allah ya isa…”

Sadi ya yi saurin rufe mata baki da hannu. Akwai tasirin zama da Turawa a tare da ita.

“Kar ki yi haka Laure, mahaifinmu ne fa, kuma ya nemi afuwarki.”

“Don yana mahaifinmu ai ba a ce ya watsar da mu ba, da ya san ba zai iya rike mu ba, ai da sai ya ki haifar mu.” Ta mike, “Ni a mayar da ni Italiya, na fi son zama a can.” Ta bar wurin da gudu tana kuka.

Alhaji Ahmadu ya fashe da kuka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< ‘Ya’yanmu 2‘Ya’yanmu 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×