Yini Na Takwas
Wannan yini shi ya bude wani sabon shafi a fadar, kasancewar yanzu babu wasu shirye-shirye da suka rage musu masu daukar hankali, fiye da addu’a ga dakarunsu da suke tafe a kan hanya da nufin kare martabarsu. Kai tsaye bayan fadar ta dinke da Basaraken ya tashi magana sai ya ce.
“A can baya fa an taba ambatar kanun wasu labarai, amma har yanzu ba mu ji gundarin su ba. Ban sani ba ko ana sane da su.”
Nan take dabbobin suka fara kallon-kallo tsakaninsu, suna dariya. Wasu daga ciki suka ce. . .