Skip to content
Part 8 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Takwas

Wannan yini shi ya bude wani sabon shafi a fadar, kasancewar yanzu babu wasu shirye-shirye da suka rage musu masu daukar hankali, fiye da addu’a ga dakarunsu da suke tafe a kan hanya da nufin kare martabarsu. Kai tsaye bayan fadar ta dinke da Basaraken ya tashi magana sai ya ce.

“A can baya fa an taba ambatar kanun wasu labarai, amma har yanzu ba mu ji gundarin su ba. Ban sani ba ko ana sane da su.”

Nan take dabbobin suka fara kallon-kallo tsakaninsu, suna dariya. Wasu daga ciki suka ce. “Ana sane da su Rankashidade.”

Ya juya ya kalli damansa yana murmushi. Dila ya yi farat ya ce.

“Ubangiji Ya taimake ki Sarki, lallai wannan shi ne lokaci mafi dacewa na sauraren labaru.”

Sannan ya kara karkata maganan nasa ga Kahuhu. Wanda shi ma da ganin hakan ya ce.

“Ubangiji Ya ba ka yawan rai, ai a cikin kowane labari akwai karatu, shi ya sa ma ko addini bai hana sauraren labari ba. Domin labari yana da manyan tushe guda biyu ne rak; ko dai ya zama tarihi ko kuma labarun da manya kan kaga don isar da wani sako na musamman ga ‘yaya ko al’umarsu. Idan labarin ya zama tarihi; madalla da shi, domin babban darasi ne. Saboda duk abin da ya faru a tarihi to akwai yuwuwar zai iya kara faruwa a halin yanzu. Shi ya sa yana daga cikin muhimmancin tarihi; wanda duk ya san tarihi sosai, to zai yi wuya wata jarrabawar rayuwa ta same shi ka ga ya zauce.”

Dila ya ce. “Na’am.”

Kahuhun ya dora; “Da ilimin fikihu ake koyon ibada, amma ilimin tarihi shi ya fi tasiri wurin koya mana nutsuwa da darussan rayuwa.’’

Dila ya kara cewa. “Na ji dadin jin wannan sadarar.”

“Haka idan kirkirarren labari ne, to madalla da kirkirarren labari. Domin shi dama tun fil azal ana kitsa shi ne don cusa wani sako ga wasu mutane. Wanda zai kitsa shi yana fara shi da manufa, yana kuma daukar lokaci wurin cusawa da sakaya sakonninsa ta hanyar amfani da tsagoron azanci da hikima. Domin yana da yakinin idan bai kayata shi ba, kuma idan bai sanya wani sako a ciki ba, to babu inda labarin nasa zai je.”

Dila ya ce. “Tabbas.”

Sannan Malamin ya karasa: “Don haka dukkan wani tsohon labari, ko a kira shi tarihi ko tarihihi ko duk ma abin da za a kira shi. Da dukkan wani sabon labari da aka kirkira, ko a kira shi tatsuniya ko a kira shi almara, ko ma duk abin da za a kira shi. Kai dai in ka ji za a fade shi a kusa da kai, ka kasa kunne, domin tabbas ba a rasa sako a ciki. Idan kuwa ka ji wani ya ce babu sako a ciki, to shi ne bai gan shi ba.”

Tsawon wannan lokaci idanun Basaraken suna kan Malam Kahuhu, fuskarsa cike da walwala. Sai bayan ya kawo wannan gabar ya kuma dakata, ya ce masa.

“Idan za ka tafi gida ka biya ta rambu, ka ce wa Sarkin Hatsi ya bude maka da debi abin da kake so, da kanka.”

Dila ya riga shi bude baki:

“Yana godiya Rankashidade, Ubangiji Ya kara arziki.”

Zakin ya ce masa. “Kai ma kana da irin wannan damar, in ka so.”

Shi ma Kahuhun ya yi farat ya rama da biki:

“Ubangiji  Ya kara maka yawan rai, yana godiya. Allah Ya kara yalwa zahiri da badini.”  

Sauran mazauna fada suna da amshewa:

“Amin, amin.”

Sannan ya juyo gare su, ya ce.

“Wa zai fara?”

Suka dan yi kallon-kallo tsakaninsu, sannan wata Gafiya ta daga hannu.

“Wanne labarin za ki bayar?” Dila ya tambaya.

“Zuwa Tukubar Giwa.” Ta amsa.

Basaraken ya yi murmushi, sannan ya dubi Kahuhu ya ce.

“Wato gari ya yi lafiya.”

“Tabbas kuwa ran Sarki ya dade.” Shi ma cikin murmushi.

“To bisimillah.” Dila ya ce da ita.

Nan take kuwa ta kara dan muskutowa gaba, ta fara:

“A wani zamani da ya shude, an yi wani mutum gwanin iya wanki a Habasha. Wanda mutane suka yarda matuka da kwarewarsa a fannin wanki. Ya kasance idan ya yi wa mutane wanki sai kayansu su dade ba su yi datti ba, sabanin idan waninsa ne ya yi. Labarin kwarewarsa a wanki ta cika gari, har dai wataran Sarki Habasha Anas Gardaz ya aika aka gayyato masa shi, don ya dawo gidan sarauta ya zauna, ya ci gaba da yi wa shi da iyalansa wanki. Da kyar dai ya yarda, domin shi mutum ne mai matukar son ‘yanci.

Watarana yana cikin wankin kayan ‘yar sarki, sai ta zo ta tambaye shi:

‘Shin kana da wani sinadari da kake yin wanki da shi sabanin  na mutane ne, da ake ta yabon wankinka, ha rake cewa in ka wanke kaya ba sa yin datti da wuri?’

Ya ce. ‘Haka dai kawai ni ma na ji ana fada, amma tabbas babu wani sinadari da nake wanki da shi face irin sabulun da kowa yake yi.’

Ta ce. ‘To kamshin da kayan suke yi fa?’

Ya ce. ‘Shi ma dai ji na yi kawai ana fada, amma ban taba sa wani sanadari kuma da sunan abin da zai sa kaya kamshi ba.’

Sai ta bata rai, ta ce. ‘Wai kai ba ka san da wa kake yin magana ba ne?’

Ya ce. ‘Na san ke mutum ce.’

Ranta ya kara baci, ta Harare shi: ‘Amma dai ka san ni ba gama-garin mutane da ka saba gani ba ce ko?’

Ya ce. ‘Allah Ya kara miki yawan rai, dukkan dan’adam ya fito ne ta hanyoyin da kazanta take fitowa, kuma duk inda yake tafe shi ma yana tafe da kazanta a cikinsa. Don haka bai cancanci wani alfahari ba. Idan har zai ambaci wata falala tasa sai dai ya ambace ta da zummar godiya ga Ubangiji Al Karim, amma ba don kawai ya nuna shi isasshe ne ba.’

Yarinya dai da ta yunkura sai ta zabga masa mari, sannan ta ce masa:

‘Na yarda maganar da duk ka fada gaskiya ce, amma wannan marin da na yi maka na san ba ka isa ka rama ba. Idan kuma ka rama na san ba ka isa ka rayu ba. Idan kuwa dayan wadannan ta tabbata to yanzu ka tabbatar akwai bambanci tsakanin mutane kenan.’

Mai wanki ya daga hannu kamar zai rama, yarinya ta kara matso masa da kunci. Sai ya sauke hannu ya ce, ‘Na bar ki da Allah.’

Yarinya ta yi dariya sannan ta ce. ‘Lallai masu azanci sun yi gaskiya da suka ce ‘wanda duk kunnensa ya gaza yarda da gaskiya, to a fada wa jiknsa, zai tabbatar masa.’ Ta juya ta fara tafiya, sannan ta waiwayo ta kara cewa. ‘Ni ma ba burina in mare k aba, babban burina kawai ka fahimci lamarin, kuma ka gasganta maganata. Domin mu a gidanmu yana daga cikin manyan abin kunya mutum ya fadi magana kuma ya gaza samar da hujjar da za a tabbata gaskiya ce.’”

Zaki ya dubi Dila ya ce. “Wai ba labarin Giwa na ji an ce za a bayar ba ne dazu?”

Dila ya ce. “Sake-saken da nake ta yi kenan tun dazu Yallabai.” Sannan ya juya ya kalli Gafiyar ya ce. “Ina fatan dai ba manta sunan labarin da kika ce za ki bayar ki ka yi ba.”

Ta ce. “E ban manta ba Yallabai.”

Ya ce. “To ai ji muka yi har yanzu ba inda Giwar ta fito ne.”

Ta ce. “To bari dai in takaice maka zancen Yallabai.”

Suka yi dariya.

Ta ci gaba: “Daga karshe dai, an kori Mawanki daga gidan sarauta. Ya koma can wani kauye a kusa da iyakar kasar. To bayan ya koma kauyen ne kullum sai ya tsuma kayan wankinsa, ya bar su su kwana. Ta yadda washegari yana zuwa da safe nan da nan sai ya wanke su cikin sauki. To kafin ya tafi sai ya karkada sabolu, kumfa ta taru har ta yi tsiri a cikin kwatarniyarsa.

Ashe bai sani ba, kullum bayan ya tashi sai wata Giwa ta zo ta yi wasa da kumfar nan. Sai ta rika zira hancinta cikin kumfar ta rika debowa, ta hura ta yi ta tashi sama, tamkar balanbalan. A hankali tn haka har sai kumfar nan ta kare don kanta.

Watarana sai aka yi bakon Mahauci, ya zo shi ma ya gina tukuba, ya ci gaba da gasa nawa a wurin. A rana ta farko, da ya ga nan da nan wuri ya zama saura shi kadai, bayan Mawankin nan da abokan hirarsa sun waste, sai shi ma nan da nan ya tarkata komatsansa ya tashi. jin kadan wutar tukubar nan ta rufe ido; babu abin da za ka hanga in ka nufi wurin sai farar toka ta yi tudu, a tsakiyar tukuba.

Da Giwarka ta zo, sai kawai ta cika da murna, tana ganin yau kumfa har kashi biyu. Ta nufi tukubar nan da sauri, tana zuwa ba ta yi wata-wata ba ta turbuda hancinta cikin farar tokar nan. Ashe a can tsakiyar tokar nan garwashi ne jawur. Ba shiri ta zaro hancinta, ta daga kai sama ta yi wata irin kara mai tsanani, har sai da dukkan giwayen dajin suka firgita. Tun daga wancan lokaci Giwa ba ta kara yarda da wani farin abu mai kama da kumfa ba.”

Fada ta yi tsit, a lokacin Sarki yana kokarin gimte dariyarsa. Zuwa wani dan lokaci kuma, bayan ta gagara rikewa ya sake ta. Nan take kuwa fada ta cika da dariya. Kahuhu ya ce, cikin murmushi. “Eh to lallai wannan labari ba zai yuwu a bayar da shi a gaban manyan dabbobin dawan nan ba.” Sannan ya dubi Zaki ya ce. “Hakika ba karamin azanci aka yi ba wurin raba zaman fadar nan, tsakanin manya da kananan dabbobi.”

Shi kuma ya nuna Dila da baki yana cewa. “Ga kanwa uwar-gamin nan, duk shi ya tsara hakan.”

Suka yi dariya dukkansu. Daga bisani Dila ya kara sanar da mahalarta fadar, musamman wadanda suke daga hannu da neman a lamunce musu su ma su bayar da nasu labarin cewa, labari daya kawai fada za ta iya saurara, sai dai gobe ma a kara ba wa wani dama ya yi nasa.

Bayan dabbobi sun gama tafiya Sarki ya koma gida. Su kuma Dila da Kahuhu suka nufi rumbu, wurin Sarkin Hatsi.

Da maraice manyan dabbobi suka hallara a fada a kan lokaci. Bayan wani dan lokaci Dila ya isa shi ma. Da gama gaisawarsu suka tambaye shi.

“Ina kuma abokin naka?”

Ya ce.

“Ai na yi tsammanin risker sa a nan ni ma, amma dai ina sa ran duk inda yake yana kan hanya.”

Ana cikin wannan tattaunawa Zaki ya fito. Shi ma da zamansa, bayan an gama gaisawa ya dubi Dilan cikin sakin fuska ya ce.

“Yau ga Wata ba Zara.”

Dilan ya yi dariya, ya ce.

“Maganar da muke yi kenan ran Sarki ya dade.”

Zakin ya ce.

“Kuma na ji an ce ku gwanayen zance kuna cewa wai ‘Kowa ya ga Zara zai ga Wata.’”

Ya ce. “To Rankayadade ai ka ga ko yanzu mun kara samun wani ilimin kenan.”

Ya ce masa. “Ban gane ba.”

Ya ce. “Yanzu mun fahimta kenan; ashe abubuwan da masu azancin zancen suke fada, sukan kasance ne a lokuta da dama, ko kuma mafiya yawan lokuta, amma dai ba kullum ba. Kamar dai yadda mukan kasance kusan kullum da shi Alaramma, amma ga shi yau ba ma taren.”

Zakin ya ce.

“Kwarai haka ne, wannan ma karatu ne.” Ya dan daga kai ya kalli mazauna fadar, sannan ya kara juyowa a zabure ya ce wa Dilan. “Ka tuna min maganar karatun nan ko na manta, in mun kadaita.”

Shi kuma ya gyada kai tare da cewa.

“An gama Mai Nasara.”

Ya juyo ya kara fuskanta mazauna fadar, yana cewa.

“’Yan’uwanmu suna kan hanya, a tafiya ta kare mutumcinmu. Ina fatan ba a manta su a cikin addu’o’i.”

Muryoyin kusan dukkansu suka yi tarayya a cikin cewa. “Ba a mantawa Rankashidade.”

Sannan ya ce.

“Madallah, ina kuma fatan ku ma ba ku manta da zama cikin shiri, kamar yadda tun a ranar muka sanar da ku ba?”

Nan ma suka hada baki.

“Ba mu manta ba Rankashidade.”

Ya kara maimaita “Madallah.” Sannan ya dubi Dila ba tare da magana ba. Da ganin haka Dilan ya dauka:

“To kun san dai yanzu alhamdulillahi hankali ya dan kwanta, tun da mun gama shiri mun tura dakarunmu. Wadanda kuma muna da kyakkyawan faton za su iya aikin da muke so, da yardarm Ubangiji Al Kahhar. Don haka yanzu ya kamata kuma mu samu wata hanya da za ta dawo da mu cikin hayyacinmu. Kamar dai yadda a baya kuka sani, idan Sarki ya fito, bayan gaisuwa, sau da yawa mukan bude wannan zama namu da wani labari da ya shafe mu. Sawa’un ya shafi wani ko wata daga cikin wannan al’umar ne ko kuwa masarautar a karan-kanta ya shafa kai tsaye.”

“Haka ne.” Da yawa daga cikinsu suka amsa:

“Amma yanzu,” Ya ci gaba: “dayake so muke a dan gyagije, ina ganin labarai da suka shafi raha ya kamata mu fi mayar da hankali. Kodayake, babu laifi idan akwai mai wani labari da yake dauke da darasi ya ba mu, ko da kuwa babu rahar a ciki.”

Jim kadan bayan sauke numfashinsa Kura da daga hannu, tare da cewa.

“Ni ina da labari.”

Giwa ta katsi numfashinta: “Maimakon ki bar wadanda za a ji muryarsu kar-kar su fara, ke kuwa?”

Kura ta hada girar kasa da ta sama, ta ce.

“Wanda ya raina tsaiwar wata ba sai ya hau sama ya gyara shi ba.”

Dila ya ce.

“Babu laifi Kura, mu je labarin.”

Kura ta matso gaba ta fara:

“Watarana a cikin wata damuna, abinci ya yi matukar wuya…”

Dila ya ce.

“Afuwan ke ba ki fadi sunan naki labarin ba.”

Ta ce.

“Au, haka ne fa. Sunansa Bikon Bodari.”

Dila ya yi dariya: “Au to to, wancan labari da aka taba ambatawa kwanaki a fada kenan.”

Ta ce. “Kwarai an taba ambatar kanun nasa, amma ba a bayar da labarin ba.”

Ya ce.

“Haka ne, to muna jin ki.”

Ta ci gaba: “Abinci ya zama sai gidan wane da wane, domin a lokacin wanda ma bai yi da gaske ba sai iyalansa su yi ta mutuwa don yunwa. Haka ma kuma manya wadanda ba su da ‘ya’yan da za su rika doguwar tafiya su yo musu farauta. Domin in dai a kusa ne abinci sai dai masu tsananin rabo.

“To akwai wani burgun Gafiya, malalaci ne kwarai sabanin sauran tawarorinsa. Daga ya fita kiwo bini-bini sai ya koma gida ya cewa matarsa bai samo komai ba. Sau da dama sai matar ta fito, ta yi wannan doguwar tafiya, ta samo musu abinci. Amma daga baya sai ta kasa fita, saboda tana da tsohon ciki. Burgun nan duk ya shiga damuwa, ba ya iya samo mata komai sai in ya ji ta dame shi da azalzala da yawan korafi. In kuma ya je ya samo mata abin da bai kai ya kawo ba, ya kawo sai ya tsaya ya dame ta da yawan tambaya, a kan wai yaushe za ta haihu, kuma me za ta haifa. Ranar da ya fahimci nakuda take yi sai ya zauna ya rika addu’ar ta haifi ‘ya’ya maza. Amma da ta haihu sai ga akasin abin da ya roka, ta haifi ‘ya’ya mata har guda bakwai.

“Daga nan da ya fita daga gidan nan bai kara waiwayarta ba, sai ya aika mata da sakon cewa shi fa ya sake ta. Saboda ba zai iya daukar dawainiyar rayuka har takwas, wadanda kuma babu wani amfani da za su tsinana masa ba. Gafiyar nan kuwa ta yi kukanta son rai ta goge hawaye. Sai ta tattara ‘ya’yanta ta nufi gidansu. Bayan kusan makonni uku, Burgun nan yana wata maciya ana labari, sai ya ga wasu ‘yanmatan Gafiyoyi sun dawo daga farauta, sun dauko kaya niki-niki, sun nufi gidajensu. Ya tambayi daga ina suke, aka ce masa ai farauta suka je. Ya tambayi dama kananan Gafiyoyi kuma mata suna iya zuwa farauta. Aka ce masa ai har sun fi maza kokari a farauta. Sai kuwa ya kama hanya ya tafi neman biko gidan surikansa.

“Ya je ya yi yin duniya ko sauraren sa ba su yi ba. Daga baya sai ya zo ya nemi Bodari, ya lallaba shi don ya je ya yo masa bikon matarsa. Bodari ya amince, ya je kuwa aka gan shi fes-fes ya sha shirbace, don haka iyayenta suka ce to su dai sun hakura, amma ya je ya lallabe ta, in ta hakura shikenan. Bodari ya sami Gafiyar nan ya yi mata dadin baki har dai ta hakura. Amma daga bisani, bayan ya ga ta yarda sai ya ce. ‘Ni ina ganin ma za ki fi dacewa da ni, domin yadda kike kaykkyawar nan ba ki dace da malalacin namiji ba.’  Gajiya ta duba jikinta ta ce. ‘Ko?’ Ya ce. “Kwarai kuwa.” Daga nan sai labari ya sauya.

“Duk lokacin da Burgun nan ya tambaye shi. ‘Ya labarin bikona?’ Sai ya ce. ‘Ai wadannan surikai naka ba su da mutumci ko kadan. Kamata ya yi ka hakura da ita kawai.’ Har dai daga baya Burgun nan ya gano zagon kasan da Bodari yake yi masa, aka yi baram-baram, aka rabu dutse a hannun riga. Shi kuwa ya ci gaba daga inda ya tsaya.

“Watarana bayan sun gama shiryawa za a daura musu aure har Bodari ya gama kai dukkan kayayyaki da kudade da amarya take bukata don ‘yan gyare-gyare da hidindimun biki, sai angon ya je wata ganawa ta karshe, don tabbatar mata da cewa shi ma ya shirya mata masauki tsaf. Tsawon lokacin da Bodari yake zuwa bai taba yin tusa ba, abin da kawai Gafiyar nan ta sani shi ne Bodari wata kyakkyawar halitta ce mai kyan gani. Wanda za ta so nuna shi a cikin dangi da kawaye. Don haka, dayake ‘yan biki sun fara hallara, sai ta taro kawaye da dangi tana nuna musu ango, cike da alfahari. Cikin rashin sa’a ashe dai nuku-nukun da yake ta yi, wanda ita ta dauka kunyar dangin nata yake ji, ashe tusar ce take ta tahowa yana danne ta. Ai kuwa can ta da kubuce ta ce darrr, nan take amarya da wasu daga cikin dangi suka fadi sumammu!”

Yayin da ta kawo wannan gabar sai kusan dukkan mazauna fadar suka barke da dariya. Aka dauki lokaci ana dariya ita ma tana yi. Sannan daga baya Dila ya  ce mata.

“To auren nan zai yuwu kuwa a hakan?”

Ta yi dariya: “Yo Yallabai ina kuwa aure zai yiwu ango yana sumar da amarya da tusa” Ta dan kara yin dariya, sannan ta ce. “Ai daga nan da ya lura da yanayin da suke ciki ya samu hanya ya sulale bai kara nufo hanyar gidan ba.” 

Zaki ya dan gyara murya, sannan ya ce.

“Wato irin wannan takan faru a cikin dabbobi da dama, amma da wahala ka ji ta a cikin Zakuna.”

Dila ya wasu daga mazauna fadar uka hada baki wurin cewa. “Na’am.”

Ya ce. “Mu a cikinmu babu ma wanda yake raina mata. Mata suna da tasiri fiye da duk tsamanin wanda ba a cikin kabilar yake ba. Domin kaso sama da sittin na farautar abincinmu matan ne suke yi. Matanmu sun fi mu gudu, domin jikinsu bai cika nauyi kamar namu ba. Sannan suna da juriya gayar juriya wurin bin abin farauta, harwayau dukkan aikin da za su yi suna yi ne da tsananin kishin iyali da burin ganin asirinsu ya rufu.”

Suka kara cewa. “Na’am.”

Ya ce. “Wannan fa wai abubuwan da suka kamata in fada a nan na fada, amma tasirinsu yana da yawa. To shi ya sa kuma da wuya ka ga maza suna wulakanta mata ko gudun su da sunan kar su zamar musu wahala.”

Dila ya ce. “Yallabai ai kuwa ku ma fa na ji ana yabon ku wurin kula da iyali.”

Zakin ya yi murmushi, ya ce.

“To ni ba a bakina za a ji wannan ba.”

Shi ma Dila ya yi dariya ya ce.

“To ma tambaya a cikin gidan.”

Da yawa suka yi dariya ganin yadda Zakin yake yi. Sannan da kansa ya kara cewa. “Ka ga ranar abokinka kenan.”

Ya ce. “Wato Yallabai abin da ni ma yanzu nake tunani  a raina kenan. Ubangiji dai Ya sa lafiya. Amma in sha Allahu in dai ba mantawa na yi ba, sai na tayar da maganar nan.”

Haka aka yi ta zantuka cikin raha har zuwa lokacin komawar Sarki gida, wadda ta kawo karshen zaman fadar.

<< Yini Sittin Da Daya 7Yini Sittin Da Daya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×