Skip to content
Part 1 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Farko

Bayan fada ta cika, kuma dukkanin mukarraban da ake tinkaho da su sun hallara ne, Zakin ya karaso, bisa rakiyar wani katon Giye da Bakane biyu da Damisa Daya da Mugun Dawa da sauran ‘yan’uwansa Zakuna. Ya zauna bisa karaga. Ya yi shiru, yana karbar gaisuwar sauran dabbobi ta hanyar gyada kai ba tare da sauti ba.

Zuwa wani dan lokaci, bayan an gama dukkan gaisuwa. Sai ya bude baki ya fara da tambaya, kamar yadda ya saba:

“Wa ne yake da wani labari muhimmi, ya ba mu?”

Kafin kuma kowa ya bude baki Dila ya ce: “Kar dai a manata, so ake labaranku su kasance dayan uku: Ko dai wata bushara, da za ta  sa mu farin ciki. Ko wani gyara kayanka, da zai sa mu ilmantu. Ko kuma wani kalubale, da zai iya zame mana barazana.  Mu tashi mu tunkare shi, tun kfin ya farga.”

Da rufe bakin Dila wasu suka daddaga hannaye sama, da zummar neman sahalewar fada. Bayan fada ta amince ya fara magana, Zomo ya gyra zama, ya ce.

“Allah Ya taimake ka, ni labarina albishir ne. Jiya cikin dare neman abinci ya kai ni har gefen gari. Sai na ji muryoyin bil’adama ana ta kaburburi. Na tsorata kwarai, amma sai na ki juyowa, na ce ni ma sai na ji me ake yi. Ko da na kara matsawa, sai na ji ashe wani mai wa’azi ne yake wa’azi. Daga cikin abin da yake fada ne kuma na ji yana cewa. ‘Nan gaba kadan aminci zai zo. Za a samu mulki na adalci a duk duniya. Dukkan halittu za su zama masu gaskiya. Adalcin kuma ba zai takaitu ga bil’adama kadai ba. hatta dabbar dake cikin dawa sai ya shafa. Har sai dabbobin dake cikin dawa su zo gefen gari su yi kiwo su koma ba tare da fargabar bil’adaman za su cutar da ita ba!’”

Zaki ya gyada kai cikin alamta farin ciki, sanna ya juyo ya kalli Dila.  Kafin su furta komai Kura ta daga hannu, tare da cewa. “Rankayadade ina da tsokaci.” Ba kuma tare da bata lokaci ba aka ba ta dama. Ta ce.

“Ina fata dai ba yarda da maganganun Zomo fada za ta yi ba. Saboda kafatanin dajin nan babu wanda  ya kai Zomo karya da fadin-rai da son a ce shi ne.”

Zomo ya kara tayar da kunnuwa suka fuskanci inda Kurar nan take, cikin tsananin bacin rai. Kamar yadda hankalin dukkan dabbobin ya koma kanta. Zaki ya ce.

“Me ya sa kika ce haka, shin kina da hujja ne, ko zato kike?”

Ta ce. “Rankayadade ko yanzu idan kana so ka tabbatar da karyarsa za  ka iya.”

“Ta yaya?” Ya tambaye ta.

“Ka tambaye shi wace ce matarsa a cikin dajin nan?”

Zaki kuwa ya juyo ya kalli Zomo. “Wai wace matarka ne?”

Zomo ya ce. “Giwa ce.”

Ai nan take Zaki ya tintsire da dariya, dukkan mazauna fada suka bi sahu. Babu abin da yake tashi a wurin sai sautukan dariya iri-iri. Sai dai tsawon wannan lokaci shi Zomo ransa a bace yake. Watakila ko don ba ya so ya yi dariya a zata karya yake yi ne, ko kuwa  tsorata ya yi da hararar da wancan katon Giyen na haunin Zakin yake ta faman galla masa.  Wanda shi ma tsawon lokacin da aka dauka ana dariya fuskarsa ba ta komai sai kara murtukewa!

Bayan wani dan lokaci, Zaki ya kara daidaita a kan karaga, ya ce. “Kai yanzu duk girman Giwa!”

Zomo ya ce. “Yallabai ai abin a zuci yake.”

Zakin nan ya kara yin dariya: “Lallai ko hakan ya nuna kana da karfin zuciya.”

Da Zomo ya ji haka, sai ya kara samun kuzari. Ya karkace, tare da kara gyara murya, yana cewa. “To Rankayadade ka duba fa yadda muke yi da karnuna. Karnuka hudu za su bi ni, ni kadai. Ina sane da cewa sun fi ni girma, sun fi ni karfi, sun kuma fi ni gudun ma. Amma hakan ba ya sawa in sare. Sai mu dauke sa’a duga muna zubawa, har dai Ubangiji Ya kawo min dauki, in tsira da kyar. Da karayayye ni ni irin su……” Ya dan yi shiru, ya kalle gefensa na hagu. Sannan ya juyo ya ce. “Ai da tuni babu ko dan buzuna.” 

Zakin nan da mafiya yawan mukarrabansa suka kara tuntsirewa da dariya. Yayin da shi ma Zomo a wannan karon yake cikin dariya tare da kallon su cikin nishadi, har zuwa lokacin da idonsa ya kai ga wancan katon Giye da ke tsaye fuskarsa tamkar an aiko masa da manzon mutuwa!  Ai nan da nan sai shi ma tasa dariyar da dauke!

Bayan wani dan lokaci, Zaki ya kara cewa. “Akwai wani kuma da yake da wani labarin?”

Kafin kowa ya kara bude baki shi ma Giye ya yi farat, ya ce. “Ina fatan dai ba yarda Shugaba ya yi da wannan labarin karyar da aka gama bayarwa ba?’’

Zaki ya waiwaye ya kalle shi, tare da cewa. “Da alama dai kana da ja game da batun kenan?’’

Giyen nan ya ce. “Ai Rankashidade, akwai labaran da daga ji ma, ba sa bukatar wani dogon sharhi, labarai ne irin na kanzon Kureje.”

Da jin haka, shi ma Kurege wanda yake zaune cikin ayari, ya mike ya ce. “Rankayadade, ya kamata adalcinka ya waiwayi yadda manyan dabbobi suke gwada mana fin karfi, hatta a zaman fada. Kwanaki ana so a bayyana wauta, wai sai aka ce “Zuwa bikon Bodari.” Sannan aka dawo “Zuwa Jujin Bushiya.” Da “Cin Hanjin Hankaka” da sauransu. Wadannan fa duk cin fuska ne.”

Gafiya ta yi caraf, ta ce. “Ubangiji  dai Ya yi maka albarka Kurege. Kuma kar su manta idan fa irin wannan tone-tonen za a yi, kowa da irin nasa labarin.”

Zomo da jin haka, bai bari Gafiyar nan ta kara bude baki ba, ya dora: “Kwarai kuwa, tunda akwai ‘Zuwa Tukubar  Giwa’ da ‘Cin Sabulun Damisa’ da ‘Angoncin Farin Kure’ da sauransu.”

Nan da nan fuskoki suka fara sauyawa, gurnani iri-iri ya fara yawaita a fadar. Take kuwa hantocin kananan dabbobi suka hau rawa. Sai da Zaki ya mike ya yi wani kuka mai sanya firgici, sannan kowa ya koma hayyacinsa. Aka yi shiru lokaci mai tsayi ba tare da kara furta komai ba. Sannan Zakin ya juya ya kalli Dila, wanda shi kuma da ganin hakan ya dauki haske. Sai ya ce. “Zaman fada na wannan rana ya tashi a daidai wannan lokaci. Amma akwai wadanda Sarki yake so su tsaya don ya ja musu kunne da kansa. Da farko dai dukkan dabbobi da tsuntsaye masu kafa biyu, in dai ba Jimina ba ce, to su tafi. Dukkan wata dabba ma-ja-ciki, indai ba Kada ba ce, to su je an sallame su.”  Zaki dai ya yi saroro yana kallon ikon Allah. Zuwa wani dan lokaci kuma ya kara cewa. “Dukkan wata dabba wadda ta san ma-ci-ciyawa ce, ko mara fika, to an sallame ta, komai girmanta kuwa.”

Cikin daurewar kai,  su Gada da Barewa, manyan dawa irin su Jakin-dawa da  Rakumin-dawa da Giwa  da dangoginsu duk suka bar wurin. Aka bar sauran manyan dabbobi masu fika kadai, cikin zulumi. Sanna ya kalle su, ya ce.

“Kun san an ce wai ‘wata kusan ta fi wata’. Na san kuna sane da cewa duk fadin dajin nan babu wadanda suka kai daraja da kusancinku a wurin Zaki. Saboda ku ne kuke da halitta da dabi’a iri daya da nasa. Kuma asalinku duk yana tikewa ne a dangi guda. Don haka, Zaki ba zai juri wata karamar dabba ta rika kawo muku raini ba.”

Dabbobin nan babu abin da suke yi sai faman gyida kawuna, cikin bayyana amincewa da kalaman da suke surnana  kunnuwansu. Ya ci gaba. “Na san ku ba ku lura ba, amma lokacin da aka fara maganar manya da kananan dabbobi, saura kadan Zaki ya tunzura ya sa ku daka musu wawa. Allah Ya taimake su, ya tuna da wata wasiyar Kakansa. Albarkacinta ne ya sassauta musu. Amma lallai yau da sun san sun taba masa dangi!”

Nan da nan fuskokin dabbobin nan suka washe. Suka ci gaba da murmushi da annashuwa. Zaki dai bai ce komai ba, sai dai shi ma ya yi tarayya da su  cikin           yin murmushi. Kodayake dai shi ma abin da ya kayatar da shi da ban. “Don haka,” Ya ci gaba; “ya nemi ku dakata ne yanzu,  don ku taushi juna. Kuma yana umartar ku, cikin tausassar murya, cewa ku dauke kai, ku ja girmanku, kar ku saurare su.”

Nan take kuwa duk wani alamun bacin rai ya gushe daga fuskakonsu. Suka yi wa Zaki godiya da gaisuwar bankwana cikin girmamawa. Suka kama hanya suka tafi.

Bayan wani dan lokaci, Zaki ya dube shi, ya ce. “Lallai Dila ka cika mai hikima. Tsawon lokacin da kake maganar nan, kallonka kawai nake ta yi cikin mamaki, amma sam ban fahimci mafi yawan abubuwan da kake yi ba, sai dai na yarda cewa ba za ka ba mu kunya ba.”

Dila ya dan rankwafa ya ce. “Ubangiji Ya kara maka nasara.”

Za ki ya kara cewa. “Amma fa ka dan yi min laifi, saboda ka ja lokaci fiye da wanda na so zama a fadar.”

Ya ce. “Tuba nake Rankashidade, amma na yi hakan ne don tabbatar da dorewar zaman lafiya a wannan dajin.”

Zaki ya ce. “Ban gane ba?”

Ya ce. “Na fara sallamar kananan ne saboda na tabbata idan har za su tafi tare da manyan, to fa komai  zai iya faruwa a hanyar nan. Bisa la’akari da yadda  suka harzuka. Sannan daga baya na sallami manya masu cin ciyawa, saboda su ma idan an hada su da wadancan za su iya zalumtar su, kuma idan an bar su da wadannan masu fikar, sai a ci zalin su, su ma.”

Zaki ya gyada kai gami da murmushi, cikin alamun kayatuwa da abin da Dilan ya yi. Kafin ya bude baki ya kara cewa. “Kuma ni ma yanzu tun da na tabbata sun yi nisa, sai in kama tawa hanyar. Saboda tsaro, ba don tsoro ba.”

Zaki ya tintsire da dariya a wannan karon, sannan ya ce. “Wai dama kai ma duk irin kusancin da yake tsakaninmu da kai, kana tsoron wata dabba  dajin nan?”

Dila ya ce. “Rankashidade, daga cikinn wasiyoyin da kakana yake yi min ya taba ce min. ‘Daga karfi zuwa arziki, daga dabara  zuwa ilimi, tafi-tafi har zuwa mulki. Tare da cewa sune abubuwa mafiya rinjaya, su ma wataran rinjaye su ake yi! Kuma a ranar da aka tashi rinjayarsu, ana yi musu mafi munin rinjaya ne, saboda da gamayyar hannaye ko kunan-bakin-wake akan far musu.”

Zaki ya gida kai yana murmushi gami da cewa. “Dila sarkin wayo!”

Shi ko ya dan kara risinawa lokacin da zai ce. “Zaki manyan dawa.” Sannan ya kara: “ni dai na bar ka lafiya.”

Har ya yunkura zai tashi, Zakin ya kara cewa. “To ai da sauran zance.” Dila ya koma ya kara gurfana. “Allah shi dafa maka, wanne kenan?”

Zaki ya ce. “An yi maganar zuwa tukubar  Giye, da zuwa jujin Bushiya da sauransu.”

Dila ya gida kai cikin alamun kokonto, sannan ya ce. “Rankashidade, tabbas na ji tsoron za ka iya bin ba’asin batun nan, saboda na san ka da son jin labarai. Amma ina tsoron in dai za a bayar da labarun  a fadar nan, to fa dajin nan zai hargitse. Domin manyan dabbobin za su sauke fushinsu a kan kananan.’’

Zaki ya hada girar sama da ta kasa, ya ce masa “To wannan kuma ya rage naka. Ni dai kawai ina son jin labaran.” Ya tashi ya tafi. Dila ya rintse idanu kimanin dakika hamsin a wurin, can ya girgiza kai shi ma ya yi nasa wuri.

Yini Sittin Da Daya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×