Skip to content
Part 10 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Goma

Tamkar masu ramuwar biki, a wannan yinin da sanyin safiya Kahuhun ya riski Dila a gida shi ma. Ya fito, bayan an gaisa ya ce.

“Ba don kar mu tsaya mu shantake irin ta jiya ba, ai da na taso da ko guda ne daga batutuwan jiyan mun karasa shi.”

Kahuhun ya ce. “Haka ne, amma na san in dabarar taka ta motsa ai  kai kana iya tauna taura biyu lokacci guda.”

Dilan ya yi dariya gami da cewa.

“Ba masu zance sun ce ba a hada gudu da susa ba?”

Shi ma ya ce.

“Ga wanda bai iya susar ba ba.”

Bayan dukkansu sun yi dariya a lokaci guda, sai Dilan ya ce.

“To ina ganin abin da zai fi yi mana sauki shi ne mu tafi fadar, muna tafe muna tattaunawa a hanya.”

Kahuhun ya yi murmushi, ya ce.

“Ahaf, ai na san in ka so hanya ba ta bace maka.” Suka juya suka nufi fada.

Bayan tafiyar ta fara mikawa Dilan y ace masa. “A yammacin da ba ka samu uzurin zuwa fada ba, an yi maganar iyali, amma da na tambayi Sarki game da batun kokarinsu ga iyali, sai ya ki ban amsa. Haka a batun iyalin nasa, sai ya fadi bangaren kokarinsu kawai, tare da cewa kowa yana sane da mata ba a rasa su da ‘yar botsararsu ta al’ada. To abin da kuwa ya kara ban mamaki, kai ma da muka yi magana da kai sai na ga kamar kana nuna hakan kusan ita ne tsayayyiyar al’adar namiji.”

Kahuhu ya yi dan gajeren murmushi tare da cewa. “Na yi tunanin daga cikin maganganun da muka yi dama wannan za ka fara tasowa.”

Sai ya yi dariya: “Wato kai ma fa Malam na lura ka sa min ido, kamar yadda nake sa wa wasu.”

Kahuhu ya ce. “Ko dai da ka ambaci abin da sunan sa ido yanzu, na san wataran za ka ambace shi da sunansa na ainishi. Don haka sai in ce maka e din.”

Dukkanu suka tintsire da dariya, sannan Dilan ya ce. “To bari in ce, ni ina nazarin rayuwar wasu, kai  kuma kana nazarin tawan.”

Kahuhu ya ce, cikin sakin fuska: “Wato harka da mai wayo tana da matukar wahala idan ba ka iya ta ba. Domin shi idan ka tashi tsara wata magana da kake son gamsar da shi, sai ka sha wahala gaya, amma shi in shi ne nan take sai ka ji fit ya jeho makan zance tamkar wahayin sa ake yi masa. Sai dai dadinku, kuna iya fahimtar mai magana ko da kuwa a lokacin da ya kasa fito da shiryayyin kalmomin da za su iya bayyana ainishin sakon da ke cikin ransa ne.”

Dila ya ce. “Malam idan an ce min ina da baiwa ba na musu, amma ina mamakin taka baiwar. Domin mu ana haifar mu da ita ne, har ma mun yi shuhura  da haka. Amma ku da ba  ku aka sani da wannan baiwar hikimar ba, wataran in na ji takan har sai in rika raina tawa.”

Kahuhu ya ce. “Mu da ku ai Danjuma da Danjimmai ne Rankashidade; ku hikima kuka gada, mu kuma muka gaji ilimi. Ita hikima kuma wani kimtsattsen ilimi ne da Ubangiji yake sahalewa bawa ba tare da kowa ya koya masa ba. To banbancinsu kawai shi ne shi ilimi sai wani ya koyar da kai. Amma ko a cikin littafin Ubangiji Al Karim  ai akan ambaci hikima a inda ake nufin ilimi.”

Dila ya ce. “Wato mu ma tamu hikimar ilimi ce ashe?”

Kahuhu ya ce. “Ah, gangariyar ilimi kuwa Rankashidade. Ai duk abin da ya ba ka damar rarrabe kaykkyawa da mummuna, ko abin da ya kamata da wanda bai kamata ba, ilimi ne, ko ma in ce shi ne ilimi.”

Dila ya ce. “Na’am.” Sannan ya yi wa Kahuhu kallo irin na mamaki tare da bude baki: “Ai ka ga har mun zo fadar wani zancen bai bar mu mun yi wani ba.”

Kahuhu ya yi dariya: “Yo mu zantukanmu ai ba  sa karewa Yallabai, ma yi wani jikon.”

Bayan zamansu a matsugunansu na al’ada a fadar, dabbobin da suka riska a wurin suka matso suka gaishe su, suka koma matsugunansu. Sannan suka ci gaba da hirarsu. Kodayake lokaci bai tsawaita tsakanin zuwan nasu da fitowar Basaraken ba. Wanda wadanda ake gaisarwar suka fara gaida shi, sannan su ma sauran suka bi sahu. 

Gama gaishe-gaishen ke da wuya kuma, sabanin abin da suka zata Basaraken ya fara da tambayarsu:

“Wace hanya za mu bi don sanin halin da rundunomin  mayakanmu suke ciki ne?”

Aka dan yi jim babu wanda ya yi magana, har sai da ya kara cewa: “Wadannan rundunoni su ne mu, mu ne su. Don haka bai kamata mu shagaltu ga barin sha’aninsu ba.”

“Wannan gaskiya ne Rankashidade.” In ji wani shahe na mazauna fadar.

Sannan ya juya ya kalli inda Dila yake zaune ya ce.

“A fara nazari a kan wannan batun.”

“An gama Rankayadade.” Ya amsa yana mai risinawa.

Da ya waiwaya wurin Kahuhu kuwa sai ya ce.

“Akaramakallahu a yammacin da ba ka zo ba, abokinka ya yi tambayar da kai kadai za ka amsa masa, kuma ba ka nan. Ban sani ba, ya yi dai alwashin zai tayar da maganar wataran.”

Kahuhu ya dan risina yayin da yake bayar da amsa:

“Kwarai ya bunta min, ko yau mun so mu tattauna batun a kan hanyarmu ta zuwa nan. Sai kuma wani zancen ya dauke mana hankali.”

Ya juyo ya dubi Dilan cikin sakin fuska. Shi kuma ya dan sunkuyar da kai ya ce. “Ubangiji Ya kara maka yawan rai.”

Kahuhu ya ce. “Kodayake a lokacin da muka fara batun mu zame mana mai baki biyu ya yi: Wato bayan batun dabi’un mazajenku akwai kuma batun dabi’un gama-garin maza. Musamman game da dalilan da suka sa ba sa bayyana bangarori marasa dadin ji na gidajensu.”

Dilan ya ce. “Kwarai haka muka yi kam, ni har na so in manta wannan sashen.”

Kahuhun ya ce; “To da farko dai dama na fara kwatanta cewa wannan lamarin tamkar bayyana tsiraici ne.”

Ya ce. “Kwrai haka ka  ce min, kodayake ban san me ya sa ka ce hakan ba, wanda kuma watakila shi ne ma ainishin karatun.”

Ya ce. “Ai Ubangji Al Karim Ya bayayan abokan aure a matsayin sutura ga junansu a cikin littfinSa mai tsarki. Cewa su mazan sutura ne ga matan, kamar yadda matan ma  suke sutura ga mazan.”

Zakin ya ce. “Na taba jin wannan maganar.”

Ya ce. “Madallalah” ya kara da cewa: “to a takkaice dai yayin da duk  wani magidanci ya zo yana bayyana matalar ko barakar matarsa a waje cikin jama’a, tamkar yana yaga ko cire waccan tufafi ne da Ubangiji  Ya suturta shi

 da su.”

Dila ya ce. “Na’am.”

Ya ci gaba: “Haka kuma idan matar ce ta je take bayyana barakar mijin. Karshe dai za ta taras kanta kawai take kwance wa zane a kasuwa. Domin hakikanin lamarin shi ne, daga lokacin da mai rai ya yi aure to kuma babu wanda ya kai abokin raywar auren nasa muhimmamci a wurinsa. Ana auna nasararsa da nutsuwarsa da farin cikinsa har ma da arzikinsa bisa tasirin wannan abokin rayuwar auren nasa.”

Zakin ya ce. “Ko shakka babu.”

Dilan ya yi wuf  ya ce.

“To Malam kar dai mu ja wannan da nisa mu manta daya gabar.”

Kahuhun ya ce. “To kuma fa haka ne, wasu su su….”

Zakin ya yi farat ya ce. “Su Zaki”

Fadar ta cika da dariya. Sannan ya kara cewa: “To ai na ji kana ta kame-kame ba ka san fadar sunan.”

Kahuhu ya yi dariya ya ce. “To ai sunan ne da nauyi Yallabai.”

Shi kuwa ya ce da shi. “To na dauke maka nauyin, ka fada kawai. Domin in ba fadar ake yi ba ai ba za a fahimci lamarin da kyau ba.”

Da yawa daga dabbobin suka ce. “Kwarai kuwa.”

Kahuhu ya gyara daurin rawanin da ke kansa ya kuma yi gyaran murya ya ce.

“A wurin mata, duk ta inda ka juya namijin Zaki, za ka taras gwani ne. Tun daga lokutan samarta har zuwa na tsufansa. Shi ya sa in ban da a wuri daya da wuya ka ji rikici tsakanin ma’auratansa. Mazansu suna da ainishin dabi’un da kusan kowadanne mata na kowace kabila suke so.  Kai ba ma matanmu kadai ba, har matan bil’adama sukan ayyana dabi’un mazan Zakuna a matsayin abin alfahari.”

“Na’am.” Wasu muryoyi kusan bakwai daga cikin majalisin suka hadu lokaci guda wurin furuci.

Ya ce. “Ai shi ya sa ma a cikin labarin Ummu Zar’in, da wasu mata goma sha daya suka hadu suna labarta wa junansu yadda zamantakewarsu da mazansu na aure take. Mai yabo tana yi, mai fallasa ma tana yi, wata da ta tashi yabon mijinta kawai sai ta danganta shi da cewa: Shi idan ya fita waje, kamar matashin zaki ne, kuma idan yana cikin gida kamar dattijon zaki ne a cikin iyali.”

Basaraken ya ce. “Na’am.” Gami da gyada kan da da zarar mai kallo ya kalla zai iya kardadon alamun gamsuwa ko kayatuwa a ciki.

Dila kuwa ya ce. “To ya ya lissafin yake ne?”

Kahuhu ya ce. “Wato shi matashin zaki yana da kwazo matuka wurin farauta. Kuma duk abin da ya farauto ya kawo wa iyalinsa, in ya ga dama daga nan sai ya yi tafiyarsa. Ba shi ba waiwayar wannan abin kuma. Ba zai ki kara kawowa ba, wai saboda ya san dazu ko jiya ya kawo mata ba, sannan in ya dawo ba zai taba tambayar ta:  ‘Ina abincin da na kawo dazu?’  ko jiya ba. Ba ruwansa da wannan, ita ya shafa.”

Basaraken ya yi wani faffadan murmushi, tamkar wanda ya tuno da tsohuwar masoyiya. Shi kuma Sarkin Azanci ya ce. “Ah, lallai mata sa so wannan.” Yana dariya.  Malamin ya dora: “Shi kuwa dattijon Zaki idan yana gida cikin iyali, za ta taras bayan tsaro da yake ba su, ba shi da wani aiki fiye da wasa da raha tsakanin iyali. Zai yi barkwanci da matar, kuma ‘ya’yan su hau kansa su yi ta kokawa da shi; ya ture wancan wannan ya ja shi can, ya waiwaya ya janyo wani, wani ya diro masa, aikin kenan, in dai ba farauta zai fita ba.”

Har yanzu Basaraken yana cikin wancan yanayi nasa mai matukar bayyana annashuwa. Sarkin Azancin kuwa ya kara cewa. “Tsarki ya tababbata ga Ubangiji Al Karim! Na rantse  ba a cikin dabbobi ba, ko cikin bil’adama idan magidanci zai zama haka sai mace ta yi alfahari da shi.”

Mafiya yawan mazauna fadar suka amshe: “Tabbas ma kuwa.”

Kahuhu ya ce. “Mafi yawansu kam, amma daga cikin matan bil’adama akwai wani rukuni na mata masu wuyar sha’ani. Idan hali ya yi wataran zan ba ka labarin wasu mata.”

Basaraken ya magantu a daidai wannan gaba: “Wato ina ganin duk duniya babu wani abin mamaki kamar ilimi.?”

Malamin ya rakwafa: “Rankashidade”

Shi kuwa ya dora: “Saboda ilimi ne kana nan, wani yana  can wata duniya zai ba da labarinka tsaf, kamar da shi ake yanke maka cibiya!”

Malamin ya ce. “Haka ne Rankashidade.”

Sannan ya kara ce masa: “To ina jin nan gaba kadan ya kamata mu fara nazarin yadda za a bude makarantu a dajin nan.”

Malamin ya kara risinawa tare da cewa. “Ran Sarki ya dade, wannan daidai ne.”

A daidai lokacin kuma suka lura da yadda lokaci ya ja kwarai. Don haka ya yi bankwana da su ya shiga gida. Har dabbobin sun fara mikewa Dila ya ce. “Kowa ya zauna a inda yake.” Bayan sun daidaitu ya ce da su: “Ina fatan dai kun ji kuma ba ku manta me Sarki ya fada game da dakarunmu kafin fara wannan labarin ba.?”

Da yawa suka ce. “E muna sane.” Yayin da wasu kuma suka yi kasake suna kokarin tunowa. Ya ce. “To don haka, ku ma ku tafi da wannan tunani a ranku, cewa za mu lalubi mafitar da ta fi dacewa.” Suka nuna sun fahimta, sannan aka rabu kowa ya kamma hanyar nasa gidan.

Da yamma ta yi fada ta kara zama da manyan dabbobi kamar yadda aka saba. Sarki ya fito, su ma bayan karbar gaisuwa ta al’ada ya kara sanar da su damuwarsa game da wadanda suka tafi fafatawa domin kare martabar dajin. Sannan ya roki kar a manta da su a cikin addu’o’i. Su ma ya bayyana musu bakatarsa ta sanin halin da mayakan suke ciki ko ta hakinn ka’ka. Bayan daukar lokaci yana magana game da batun mayakan sannan  ya juyo ga Dila ba tare da furta komai ba. Irin kallon da shi Dilan daga ganin sa ya san inda ya nufa. Sai dai kafin ya buda baki  wata Dorinar ruwa ta bude naka:

“Ran Sarki ya dade, ni ina da magana.”

Dil ya daure, kodayake ba hakan ya so ba, ya ce. “Me ce maganarki?”

Ta ce. “Wadancan dakarun da ake magana ni ina ganin kawai kamata ta yi dama tun da wuri a tura wasu, su kuma in an gan su a hanya a ce su dawo.”

Mafi yawan mazauna fadar maganar ba ta yi musu dadi ba, bisa alamun da suka bayyana a tare da su. Dilan ya daure ya kara ce mata. “Yi mana bayani, me ya sa?”

Ta ce.

“Idan fa magana ake ta fada ko yaki, to magana ce ta karfi da makamai. Don haka ba dalilin da kananun dabbobi raunana za su fi manya karfaffa dacewar tafiya irin wannan fafatawa.”

Gwanki ya ce mata.

“Ke kam kin cika wauta,” sannan ya dan matsa daga kusa da ita yayin da zai ci gaba; “in ba haka ba, duk irin bayanin da Dila ya yi mana na dalilan da suka sa a ka tura wadancan har yau kwakwalwarki ba ta bude kin fahimta ba.”

Tana ta faman galla masa harara, ta ji Zakin ya ce. “A toh.” Sai kuma ta gaggauta shiga hankalinta.

Bayan daukar wani lokaci ana tattauna batun, Basaraken ya yi musu umarni irin wanda ya yi wa mazauna fadar da suka gabace su. Sannan ya koma gida, abin da ya kawo karshen zaman na wannan yinin.

<< Yini Sittin Da Daya 9Yini Sittin Da Daya 11 >>

2 thoughts on “Yini Sittin Da Daya 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.