Yini Na Sha Daya
Wancan shi ne yini na farko da bakin mabambantan mazauna fadar ya hadu bisa ra’ayi guda, tun bayan raba zaman fadar: Wato bayan kananan dabbobin sun zauna da safe sun kuma yarda da cewa abu mafi dacewa shi ne a tura sabbin dakaru, su bi bayan wadancan. Haka ma a zaman manayan dabbobin na yamma suka cimma irin matsayar. Wanda kuma Basaraken ya nuna amincewarsa da hangen nasu, ya kuma yarda da fara shirin zaben wadanda za su kasance a cikin dakarun rindinar ta biyu. Kodayake dai, a wannan karon hanyar zaben. . .