Skip to content
Part 11 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Daya

Wancan shi ne yini na farko da bakin mabambantan mazauna fadar ya hadu bisa ra’ayi guda, tun bayan raba zaman fadar: Wato bayan kananan dabbobin sun zauna da safe sun kuma yarda da cewa abu mafi dacewa shi ne a tura sabbin dakaru, su bi bayan wadancan. Haka ma a zaman manayan dabbobin na yamma suka cimma irin matsayar. Wanda kuma  Basaraken ya nuna amincewarsa da hangen nasu, ya kuma yarda da fara shirin zaben wadanda za su kasance a cikin dakarun rindinar ta biyu. Kodayake dai, a wannan karon hanyar zaben ta sha bamban da ta farko.

A can kuwa cikin kololuwar dajin da babu wasu dabbobi da suke rayuwa, waccan rundina tana ta faman tafiya da burin ganin wadancan dakaru da aka yi musu busharar sun durfafo matsugunin nasu. Tsawon lokacin da suka kwashe ba su ci karo da wani abu mai daukar hankali kamar wani duhu mai kama da cincirindon dabbobi da suka hango ba. Hangen waccan duhuwar ayarin ita ta tilastawa kowannensu gyara damara da kara yin kwarya-kwaryen atisayen dukkan wata bajintar yaki da suke tunanin suna da ita.

Sannan daga bisani aka fara tattauna yadda za a bi a afka musu. Abu na farko da suka fara yi shi ne amincewa a kan a aiki Mikiya ta yi leken asiri ta sama. Ita kuma Tururuwa ta  shiga ta karkashin kasa ta je ta yi nata leken. Bayan sun tafi sauran dakaru suka ci gaba da shirye-shiryensu, har zuwa lokacin da suka dawo.  Rahoton da dukkansu suka bayar sai ya zama akasin abin da mayakan suka zata. Domin kamar yadda Mikiyar wadda ta riga dawowa ta shaida musu cewa sansanin ba komai ba ne face majalisar hira ko ta zaman makoki. Haka ita ma Tururuwar da ta dawo ta shaida musu cewa majalisa ce kawai wadda wani jagora ko dai Sarki ko Malami yake da bayani, sauran kuma suna sauraren sa. Kodayake ita ma ta fi karkata a kan cewa mai maganar ya fi kamata Malami ba Basarake ba: “Cike maganganunsa suke da tausasawa da azanci kai ka ce Dila ne ko Kahuhu suke magana!” In ji Tururuwar.

Daga nan sai suka fara kwance damara, tare da fara lissafin yadda za su tunkari waccan majalisa. Da tunanin watakila su kara samun haske game da abin da ya fito da su. A karon farko sai a ka tura Birin Bika, kasancewarsa kwararre a fannin iya mu’amula da sauran dabbobi da ba kabilunsa na birai ba. Bayan ya je ya zauna ya saurari irin lafuzzan bakin Malam Kunkuru tare da nazarinsu da kyau. Sai kai tsaye ya nemi izininsa game da karasowar rundunarsu don zu zama dalibansa, kafin lokacin da za su kara gaba. Cikin kuma sa’a, ba tare da ko gizau ba Kunkurun ya amince wa bukatar tasa. Birin nan ya tafi cikin murna ya gayyato daukacin rundinar nan suka taho wannan katafariyar makaranta.

Da suka iso, kamar yadda Birin ya shawarce su, sai suka yi shiru dukkansu suna duban inda iskar take kadawa. Tambayar farko da suka ji daliban suna yi masa  bayan zuwansu, ita ce tambayar da Tsagagi ya yi, cewa:

“Da gaske ne dariya alamar hauka ce?”

Sai Kunkurun ya amsa masa cewa: “Hauka tana dariya, hankali ma yana yi.”

Ya ce. “To da yaya zan bambance?”

Malm Kunkuru ya ce masa. “Hauka tana yin dariya ne yayin da ta ga keta. Yayin da shi kuma hankali yake yin dariya yayin da ya ga abin farin ciki a tare da dan’uwansa.”  Ya dan yi shiru, sannan ya kara cewa: “A jikin dabba daya za a iya samun hauka da hankali, kowanne yana zaune a nasa sashen. Amma daya zai iya rinjayar daya bisa la’akari da muhalli ko yanayin da dabbar ta tsinci kanta.”

Tsagagi ya kara cewa.

“Kamar ya ya kenan?”

Ya ce masa.

“Idan dabba ta tashi a wurin da babu mai saita mata hanya, sai ta zama mugunta kawai ta iya. Don haka dukkan dariyarta ta mugunta ce, ka ga a wannan yanayin dariya ta zama hauka. Amma idan ta tashi a inda aka saita mata lissafi sai dariyarta ta zama ta kauna. Don haka dariya a wurinta hankali ne.”

Kafatanin dabbobin da ke wurin suka gyada kai, tare da cewa “Na’am.” Kamar yadda suka saba.

Mazo ya daga hannu tare da cewa. “Malam ina da tambaya.”

Malum Kunkuru ya ba shi dama. Sai ya ce. “Wai wace uwa ce ta fi rashin tausayi a cikin iyaye?”

Sai Malam Kunkuru ya ce masa. “Kadangaruwa ce.”

Ya ce. “To me ya sa?’’

Ya ce masa. “Saboda ita ce tsakaninta da danta babu wata mu’amula, babu soyayya, ba sa ma ga maciji. Da zarar ya hango ta sai dai kafarsa ta kai shi, in ba haka ba kuwa ta cinye shi.”

Mazo ya bude baki cike da mamaki. “Cinyewa dungurungun  Malam?”

“Kwarai kuwa.” Kunkurun ya amsa masa.

Sannan ya kara cewa “To wadanne ‘ya’ya ne kuma marasa biyayya?”

Kunkuru ya yi wani gajeren murmushi, sannan ya ce. “Marasa biyayya daga ‘ya’yan dabbobi suna da yawa. Amma bari in ba ka labarin marasa biyayya kuma marasa tarbiyya, domin karatunka ya zama biyu a cikin daya.”

Mazo ya ce. “Na’am.”

Sai ya ce masa. “’Ya’yan Agwagwa ne. Ka san su ‘ya’yan Agwagwa ba sa bin bayan uwarsu, sai dai ita ta bi su a baya.”

Dabbobi da dama suka hada baki. “Kwarai kuwa haka suke yi.”

Kunkurun ya kara cewa. “Ka san abin da ya taimaka wurin habaka rashin biyayyarsu?”

Ya ce. “A’a.”

Ya ce. “Rashin azancinsu tun fil azal, domin a cikin ‘ya’yaye, ‘ya’yan Agwagwa ne kawai idan suka fito daga cikin kwanson kwansu ba sa gane uwarsu. Duk wani babban abu da suka ga ya fita daga cikinsu ya yi gaba, sawa’un Kare ne ko Mage kai ko ma mene ne, shi za su yi ta bi, a matsayin uwa. Babu wanda wata basira za ta zo wa daga cikinu ya yi tunanin ai wannan bai kama da jinsun su ba, don haka bai kamata ya zama uwarsu ba.”

Ganin yadda majalisar take da tsari kyakkyawa, da kuma yadda suka Malamin yake bayar da amsoshi cikin azanci, ya kayatar da kafatanin dabbobin da ke waccan runduna da Sarki ya aiko laluben abokan gaba. Don haka su ma nan da nan suka saki jiki, suka fara sakin nasu tambayoyin.  Birin Dungazau ya ce.

“Wai Malam me ya sa idan an kira ku da suna malamai, ku kuma sai ku rika cewa kanku almajirai?”

Kunkuru ya yi dariya tare da cewa. “Saboda kankantar da kai.”

Birin ya ce. “Haka ya kamata kowa ya zama kenan?”

Malam Kunkuru ya ce. “E kowa, amma ba kowa da kowa ba kuma.”

Birin ya ce. “To ai ni ka dan sa ni a duhu Malam, kamar yaya ba kowa da kowa ba?”

Ya yi ‘yar gajeriyar dariya, sannan ya ce. “To kana ganin kankantar da kai zai dace da Sarki ne?”

Birin ya ce. “Ina fa.”

Malam Kunkuru ya ce. “To kankan da kai abu ne mai kyau, amma fa ya fi kyau ga Malamai fiye da kowa.”

Ya kara cewa. “To kunya fa? Na ga kamar suna da ‘yar dangantaka.”

Kunkuru ya ce. “Kunya ma ta’ada ce mai kyau, amma ta fi kyau ga mata fiye da kowa.”

Mikiya da take can nesa ta dago murya. “To kyauta fa?”

Ya amsa. “Kyauta ta’ada ce mai kyau, amma ta fi kyau ga masu babban rumbu.”

Haka dai suka zage suna tambaya har yamma ta yi, lokacin da Malamin ya saba tattara komatsansa ya koma gida. Su kuwa suka koma gefe suka ya da zango.

<< Yini Sittin Da Daya 10Yini Sittin Da Daya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×