Skip to content
Part 14 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Hudu

A wannan yinin aka kammala zaben dukkan wadanda za su yi waccan tafiya a ayari na biyu.  Bayan daukar lokaci Sarkin yana yi musu bayanai na karfafa gwiwa, Dila da Kahuhu suka bi bayan tasa da bayanan da suka shafi dabarun yaki da na sadaukarwa. Wadanda suke sa ran za su kai matuka wurin zaburar da rindunar. 

Daga baya su ma rundunar wadda take kunshi Karkanda da Mugun Dawa da Gwanki da Tsagagi da Beguwa da Murdiya da Dan Mitsu da Mujiya suka tashi suka rika gwada dabarun yaki iri-iri a gaban Sarki da mazauna fadar, har zuwa lokacin da yamma ta yi. Sai ya yi umarni cewa Sarkin Rumbu ya tabbabatar  ya samar musu da dukkan abubuwanan  da suke bukata tun daga kan makamai har zuwa abincin da za su bar wa iyalansu a gida, komai yawansu kuwa. Daga nan sai Sarkin ya koma gida, su ma suka koma nasu gidajen da zummar gobe za su fito cikin shiri, su rankaya.      

<< Yini Sittin Da Daya 13Yini Sittin Da Daya 15 >>

1 thought on “Yini Sittin Da Daya 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.