Skip to content
Part 16 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Sha Shida

A can kuwa makarantar Malam Kunkuru, tuni wadancan ayari na farko sun zama ‘yan gari. An saba da su, musamman saboda yadda suka dage da yin tambayoyi ba kakkautawa duk lokacin da makarantar ta zauna.

A wannan yinin ma, kamar kullum Kunkurun ya zo ya zauna yana ta faman bayar da fatawowi,  Zomo ya jeho tasa tambayar:

“Malam wai kuwa akwai dabbar da ta fi Dorinar Ruwa girman baki?”

Dorinar Ruwan da ke zaune a wurin ta waiwayo cikin bacin rai ta galla wa Zomon harara, ba tare da magana ba. Wani sashe na dabbobin suka tintsire da dariya. Abin da kuma ya zama silar kara murtukewar fuskar Dorinar Ruwan. Kunkuru ya yi murmushi, domin shi ma ya lura da waccan daure fuska da Dorinar ta yi. Sannan ya ce.

“Ai manyan halittu suna cikin ruwa. Duk ma girman wata halitta da za ka gani tana taka kasa, to  idan ta hadu da na cikin ruwa za ka taras ba a bakin komai take ba a girma.”

Zomo ya ce. “Ashe barazana ake yi mana, babban ma da babbansa.”

Kunkuru ya yi dariya, sauran dabbobi, musamman kanana suka shiga ayarin dariyar. Yayin da a gefe guda manyan irin ita Dorinar Ruwa da Giwa da Karkanta suka kara daure fuska. A can gefe kuma, tsakanin wadanda suke ayarin can da suka fito tare da Zomon, suka fara gunaguni. Alamun maganganun na Zomo ba su yi musu dadi ba.

Kunkuru ya ce. “To hakan.” Har yanzu shi ma akwai alamun dariyar maganar ta Zomo ba ta sake shi ba. Zomon ya kara cewa. “To Malam ai akwai sauran bayani, ba ka ambata mana dabbar da ta fi ta din ba.”

Malam Kunkuru ya ce. “Dabbobi masu manyan baki a cikin ruwa suna da yawa, amma daga cikinsu akwai Kifin Shak. Kifi ne mai katon baki matuka, kuma a cikin bakinsa ana samun hakora dai-dai har guda dari uku!”

Zomo ya ce. “Yauwa, ka ji manya-manya.”

Malam Kunkuru ya ce. “Ai duk girman bakinsa bai kai na Kifin Walle ba.”

“Kuma dai?” In ji Zomon.

Ya ce. “Kwarai kuwa.” Har ya dan yi shiru kamar ya gama, sai kuma ya zabura, kamar wanda ya tuno wani abu: “Kodayake shi ma Kifin Walle nau’i-nau’i ne. To daga cikinsu akwai wani mai sunkuyayyen kai. Wannan Kifin rankatakaf cikin dabbobi zai yi wuya ka hadu da  wanda ya kai shi girman baki. Kuma bakinsa babu hakori ko daya. Komai girman abin farauta in ya kama shi hadiyewa kawai yake yi.”

Daga nan Zomo ya dakata da tasa tambayar, sauran dabbobi suka ci gaba da tambayoyin. Har zuwa yammaci, lokacin da makarantar ta saba tashi. Bayan kuma an tashin ne, kafin Dorinar Ruwan ta tafi ta zo ta ce wa Zomon. “Ka iya bakinka.” Ta yi gaba.

Daga nan sai kuma  ‘yan’uwansa da yake tare da su a cikin ayari suka far masa da fada:

“Wace irin rayuwa ka zabar wa kanka ne haka kai kuwa?” In ji Kurege.

Zomo bai ce ku uffan ba, yana kallon su yana muzurai. Mikiya ta ce. “A can inda ya mu ya mu ne kana ta wannan tsokanar, ba ka bar manya ba balle kanana. Abin mamaki na yi zaton da muka zo nan inda bakin fuska ne a wurinmu za ka risina.”

Tururuwa ta ce. “Mai hali zai fasa ne?”

Zomo ya ce. “Rufe min baki ke kuma, ke ba sa’ata ba ce.”

Kafin duhun dare ya karade wurin dai sai da kowanne daga cikin wannan ayari ya tofa albarkacin bakinsa game da dabi’ar ta Zomo. Kuma dukkansu suka yi tarayya a cikin kushe ta. Amma gogan bai ko risina ba.

<< Yini Sittin Da Daya 15Yini Sittin Da Daya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×