Skip to content
Part 2 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Biyu

Da gari ya waye Zaki da manyan mukarrabansa suka hallara a fada. Dukkan dabbobi suka zo suka yi gaisuwa, suka koma suka gurfana a geffensa. Sai ya fara, kamar yadda ya saba.

“Akwai wanda yake da wani koke ko korafi ko labari da yake son sanar da mu?’’ 

Haka nan dai shi ma Dilan nan ya maimaita karin hasken da ya saba yi.

Barewa ta daga hannu, tana mai alamta tana da magana. Nan take kuwa aka ba ta dama. Ta gyara zama ta ce. “Ubangiji Ya kara maka yawan rai, jiya cikin dare wani babban ayarin ‘yan karafka ya wuce ta kusa da makwancina. Kuma daga cikin labaran da suke yi a hirarsu, na ji suna labarta wa kansu cewa. An samu bullar wasu manyan karkuka masu kaho! Suna da tsananin gudu, da zafin nama kwarai. Domin a cikin kowane yini suna iya yin tafiyar farsaki maitan da daya, idan sun so! Sannan babu wani abu, bil’adama ko dabba da suke gani su razana! Kuma a iyakar sanin da suka yi musu, ba su taba taras da wani garke ba, ko na wadanne dabbobi ne face sun fatattake su! Kuma hiyyarmu suka nufo!’’

Da jin haka Zaki ya mike tsaye, ya yi gurnani! Nan da nan dukkan dabbobi suka mike tsaye, aka yi cirko-cirko. Kura ta ce, “Allah Ya taimake ka, daga jin wannan labarin ai ka san kitsattse ne, sam bai yi kama da gaskiya ba.”

Dage ya ce. “To ke malama ai duk  jikinki  ya karyata abin da bakinki yake fada.” A lokacin ne kuma sauran dabbobi suka lura da irin barin jiki da zawayin da Kurar taken faman yi. Kuma tare da tashin hankalin da suke ciki sai da suka dara.

Cikin ikon Allah kuwa wannan dariyar tamkar sauki da salama ta saukar a zukatansu. Sai Zaki ya zauna, sannan ya dubi Dila ya ce:

“Ku ne masana, shin wannan lamari zai iya faruwa?”   

Dila ya ce: “Ubangiji Ya kara maka yawan rai, ai rundinar Ubangiji yawa ne da ita. Babu kuma wanda ya san iyakarta sai Shi kadai. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa a baya akwai dabbobin da an san su, amma sannu-sannu yau duk sun kare.  Har an manta da sunansu. Kuma a yanzu akwai dabbobin da da can babu su, sai daga baya suka bayyana kuma har an saba da su.” Ya dan waiwaya gefensa, sannan ya ce. “Ga Beran-masar, shekaru dubu uku da suka wuce ba mu san su ba. kuma yanzu ina su Kambagi? Ba ko ire-irensu.”

Zaki ya gyada kai cikin sanyin jiki, sannan ya kalli hagu da damansa, ya tambaya: “Wai ina Kahuhu ne?”

“Ya yi  wani wurin, ka san shi da shegen yawo.” Inji Shaho

Cikin izza Zaki ya ce: “Duk yadda za a yi gobe a zo min da shi fada.”

“An gama, Rankashidade.” Inji Dila 

Sannan ya kara cewa:  “To yanzu me ne abin yi?” Ya ci gaba da bin  dabbobin da kallo daya bayan daya. Nan take yawancin dabbobi masu fika suka karkata kan cewa a yi takakkiya a tari wadannan dabbobi tun kafin su karaso. Yayin da maciya-ciyawa suka fi karkata a kan a yi kyakkyawan shirin ko-ta-kwana kawai, yadda in sun zo za a far musu.

Zaki ya waiwaya ya dubi Dila, “Ka ji fa sun kasa samun matsaya.” Dila ya risina ya ce. “Yalaboi ai dama shawarar sayen abinci, ba a yin ta da mai dakalallen ciki. Ba kum a yi da mai gyatsa.  Don haka ni ina ganin gara an ba wa kowa lokaci, ya je gida ya yi tunani a nitse, ya ga ya ya kamata mu tunkari lamarin.”

“Har zuwa yaushe kenan?” Zakin ya tambaya cikin tsare gida. “A kalla zuwa gobe. Ka ga wanda ya tunzura hankalinsa ya kwanta, nutsuwa ta zo masa. Haka ma wanda ya tsorata.”

Bayan amincewa a kan wannan matsaya, sai fada ta tashi, bisa sharadin gobe kowannen zai zo da tasa shawarar a kalla a kan mahanga biyu: Fitar za a yi? Kuma in fitar za a yi, su wane suka fi cancanta su fita? Ko jiran za a yi? Idan jiran ne kuma, su wa ne gwanayen ribadi da za a iya aminta da su?

Har wasu sun fara mikewa, Dila ya yi firgigit, ya dakatar da su. Yana sanar da su cewa: “Fada ta umarci in sanar da ku cewa, an sauya tsarin zama, saboda wannan kalubale da ya tunkaro mu. Don haka, daga gobe, fada za ta rika zama sau biyu ne a kowane yini. Inda dukkan dabbobi marasa fika, wadanda kuma ba su kai girman Gwanki ba, za su rika zuwa da safe. Yayin da su kuma manyan za su rika zuwa da yamma.” Ya dan yi shiru yana kallon yadda suke kallon-kallo a junansu. Sannan ya ci gaba: “Wannan tsarin shi ne zai fi ba wa kowa cikakkiyar dama da lokacin bayyana nasa hangen. Kuma shi zai fi yi wa fada saukin sauraren kowa.”

Bayan alamun gamsuwa sun bayyana a fuskokinsu, sai fada ta salami kowa suka juya.

<< Yini Sittin Da Daya 1Yini Sittin Da Daya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.