Yini Na Ashirin
Da gari ya waye sai wadannan dabbobi suka kara yin shirin karatu, suka riga kowa zuwa makaranta suka zauna, suna jira. Kodayake, har yanzu wasu masu zafin kai irin su Dan Mitsu da Gwanki suna ganin kamar ma za su iya kure Malamin, idan suka jeho masa wasu tambayoyin masu wahala. “Akwai bayanin da na taba ji an yi, zan yi masa tambaya a kansa. Kuma na san zai yi wuya ya iya amsawa. Idan ya kasa, sai in ba shi amsar. Sannan in tabbatar wa da dabbobin da suke wurin cewa dama duk maganganun. . .