Skip to content
Part 20 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin

Da gari ya waye sai wadannan dabbobi suka kara yin shirin karatu, suka riga kowa zuwa makaranta suka zauna, suna jira. Kodayake, har yanzu wasu masu zafin kai irin su Dan Mitsu da Gwanki suna ganin kamar ma za su iya kure Malamin, idan suka jeho masa wasu tambayoyin masu wahala. “Akwai bayanin da na taba ji an yi, zan yi masa tambaya a kansa. Kuma na san zai yi wuya ya iya amsawa. Idan ya kasa, sai in ba shi amsar. Sannan in tabbatar wa da dabbobin da suke wurin cewa dama duk maganganun nasa kame-kame ne.” In ji Dan Mitsu.

Da Malam Kunkuru ya fito, ya dan yi gajeten bayani, sai ya tsaya don jin ko wani yana bukatar karin haske game da batun. Amma da ya ba wa masu daga hannun dama, sai ya lura abubuwan da suke tambaya sam ba su da jibi da batun nasa. Hakan kuma ya sa shi ya sha jinin jikinsa shi ma. Don haka da ya ba su dama, sai ya tsaya ya kura musu idanu cikin nutsuwa. Duk wanda ya yi tambaya kuma ya ba shi amsa daidai.

Kusan dabbobi biyar suka yi tambaya kafin Dan Mitsun, watakila saboda tazarar girma da suka fi shi, wanda hakan ya sa ba za a iya gano nasa hannun sosai ba yayin da suka daga nasa. Yayin da damar ta zo kansa, sai ya ce.

“To Malam yanzu da a ce hankali da tunaninmu irin na bil’adama ne, yaya zamanmu zai kasance da su? Shin za mu yi zaman lafiya ne, ko rikici ne zai barke tsakani? Idan zaman lafiya za a yi, wane dabbobi ne za su fi abota ta kud da kud da bil’adama da kyakkyawar mu’amula da su. Idan kuma yaki ne zai barke tsakaninmu, wadanne dabbobi ne za su fi ba wa bil’adama wahala? Kuma saboda me?”

Aka dan yi kallon-kallo tsakanin dabbobin. Wasu suna ganin lallai wannan tambayar ta yi kama da ‘yar kure, yayin da wasu suke ganin tambaya kawai aka yi mai kyau, wadda za su sha karatu a cikinta.

Malam Kunkuru ya yi gayaran murya, ya ce.

“Bil’adama ba su wani kyakkyawan tsarin abota tsakaninsu da wadanda ba su sani ba, balle ma kuma wadanda suka zama kwata-kwata ba ma irin su ba. Ainishin rigimammu ne su, a junansu ma haka suke, balle kuma tsAkaninsu da bakin fuska. Don haka ina tabbatar maka cewa, da dai a ce hankali da tunaninmu iri daya ne da nasu, to da tabbas rikici ne gagarumi zai barke tsakaninmu.”

Dabbobi da dama suka ce. “Na’am.” Yayin da wasu kuma suka ce. “Da alama kam.”

 Kunkuru ya ci gaba: “Dabbar da za ta fi ba wa bil’adama wahala ita ce Biri. Kuma da shiri da zaman lafiyar za a yi ma su ne za su fi kowace dabba kyakkyawar alaka da su. Saboda su suka fi dukkan dabbobi kamanni da dabi’u irin na bil’adama.”

“Tabbas haka ne.” Dabbobi da dama suka hada baki.

Ya kara cewa. “Kuma ka tambayi saboda me? To babban dalilin da zai sa Birai su fi addabar bil’adama fiye da kowadanne dabbobi shi ne, su za su iya amfani da fasahar bil’adaman ta yaki, su yake su.”

“Tabbas.” In ji wani sashe na dabbobin. Sannan Malamin ya dora: “Duk wani abu kamar takobi da mashi da tsitaka da gariyo, har zuwa kan su kwari da baka da bindiga Birai za su iya sarrafa su. Idan wahala ta yi wahala ma, za su yi amfani da wani makamai masu ban mamaki fiye da wadannan.”

“Na’am.” Fiye da rabin jama’ar fadar suka hada baki.

Dan Mitsu ya girgiza kai a hankali cikin tsananin mamakin amsar, sannan ya ce.

“To tsakanin dabbobin da suka rayu a daji da wadanda suka rayu a hannun bil’adama, a sake ko a kange a wani wuri, wadanne ne suke fin jarumta?”

Malam Kunkuru ya ce. “Dabbobin da suka rayu a daji sai sun fi jarumta.” Ya dan yi shiru, sannan ya ce. “Domin dabbobin da suka rayu a tsakanin bil’adama komai ba su ake yi. Don haka da za su dawo cikin dawa da yawansu ma yunwa ce za ta kashe su. Saboda sam ba su da wasu dabarun farauta, sabanin wadanda suke nan, suke fara koyon farauta tun da kuruciya, har su zo su kware kafin girma ya kama su. Ka kuwa san rayuwar dawa ba rayuwa ce irin ta cima-zaune ba.”

Da aka kawo nan, sai kawai Dan Mitsu ya ce. “Na yarda, kuma na sallama.”

Malam Kunkuru ya yi dariya, sannan ya ce. “Har da su sallamawa kuma?”

Ya ce. “Kwarai kuwa.”

Kunkurun ya ce masa. “Ka yi kyan kai.”

Sai ya ce. “Wace shawara za ka ba ni?”

Kunkuru ya yi murmushi ya ce da shi. “Ka yarda cewa duk duniya babu wata baiwa kamar ilimi. Idan ka lura wata matsala ta zo ta raba tsakanin al’uma, kar ka rudu ka bi mai karfi ko mai babban rumbu, ka bi mai ilimi. Domin su dukkansu baiwarsu za ta iya gushewa, amma baiwar  ilimi tabbatacciya ce.” Ya dan dakata ya yi gajeriyar dariya, sannan ya ce. “Na san watakila za ka so in yi maganar zafin kanka da son fada, amma babu bukatar hakan. Domin duka a cikin ilimi za ka iya fahimtar wuraren da suka kamata a yi amfani da zafin kan, da kuma inda ba su kamata ba. Za kuma ka fahimci dabi’unka masu kyau, ka ci gaba da tafiya a kansu, da kuma  wadanda suke bukatar gyara, ka gyara su. Domin ilimi tamkar ruwa ne, wanda idan ka yi datti in ka shige shi sai ya wanke ka tas, ya gusar maka da muni, ya kuma bayyana kyawunka. Abu mafi muhimmanci kuma, ya gadar maka da nutsuwa.”

Jikin Dan Mitsu ya yi matukar la’asar, ya rasa abin cewa sai maimaita “Na gode, na gode.” Da ya rika yi.

Daga wannan zama, bayan makarantar ta tashi, Malamin ya tafi gida, sai suka dan kara tsayawa suka tattauna game da sha’anin Malamin. Inda dukkansu suka sallama, kuma suka yarda kan cewa lallai bai kamata su bar makarantar ba. Domin babu wani aiki da za su yi fiye da ita, idan ma sun tafi. Don haka suka yi sabuwar damarar zaman sai Baba ta gani a wurin.

<< Yini Sittin Da Daya 19Yini Sittin Da Daya 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×