Skip to content
Part 21 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin Da Daya

Da aka kawo wannan lokaci, Zaki ya ji har yau babu wani labarin runduna ta farko bare ta biyu, sai damuwarsa ta karu kwarai. Don haka sai ya fara tunanin daukar wani mataki da zai iya samun tabbacin shin kashe rundunar nan tasa ake yi ko kuwa dai batan kai suke. A karon farko sai ya aika aka kirawo masa Sarkin Ungulu. Ya tambaye shi,

“Shin a ‘yan lokutan nan, daga yini goma sha uku kawo yau, jama’arka sun yi karo da wasu tarin gawarwari a gabas?”

Sarkin Ungulu ya ce, “Wani labari mai kama da wannan bai zo mana ba, kuma tabbas da ya faru, da ya riske mu. Domin babu wata rikitiba da al’umarmu suke samu a kowane sashe take face sai labarinta ya riske mu a cikin wannan yini.”

Zaki ya gyada kai, ba tare da cewa uffan ba. Sarkin Ungulu ya ci gaba, “A cikin yini sittin da daya da suka shude, gawarwaki da aka gani mafiya yawa, na wasu jakan dawa ne guda goma sha daya, da ake tsammanin tsananin kishin ruwa ne ya kashe su, sakamakon mamaye gabobin kogi da manyan dabbobi   maciya nama suka yi.

Bayan su kam ba a kara samun rukunin gawarwaki fiye da uku ba, har zuwa wannan sa’a da nake magana da kai.”

Da Zaki ya ji haka, sai ya yi wa Sarkin Ungulu godiya, sannan ya ce, “Amma ku ta yaya kuke aika sako ne, da kake ayyana cewa dukkan abin da ya faru za ka iya samun labarinsa a cikin wuni guda?”

Sarkin Ungulu ya ce, “A kowace gunduma muna samun wasu jakadu zakakurai, masu karfi da juriyar tashi na zango mai nisa. Idan har babban labari  da ake so ya riske mu ya faru. Jakadu goma za su  taso daga inda wannan rikitiba take, kowannensu dauke da tsokar nama a bakinsa. Idan suka zo gunduma ta biyu, sai su ajiye wannan tsokoki, su sanar da labarin ga Hakimin Gunduma, su koma. Daga nan sai ya ajiye tsokoki hudu don  amfanin al’umar gundumarsa, ya kuma umarci jakadu shida su dauki tsokoki shidan su tafi da su gaba. Yayin da wadannan jakadun Hakimi su shida suka isa gunduma ta biyu, sai su sauko. Su ajiye tsokokin nan gaban Dagacin Gunduma , su labarta masa inda rikitibar nan take, daga nan sai su juyo. Sai shi ma Dagacin ya adana tsoka biyu, don amfanin jama’arsa. Sannan ya yi umarni ga jakadu su dauki tsokoki hudu su nufi gunduma ta gaba. Yayin da wadannan jakadu hudu kuwa suka isa ga Mai’unguwan  Gunduma, suka ajiye masa tsokoki hudu, to in ya dauki biyu sai ya aiko min da biyun har fadata, da cikakken bayanin inda abinn ya faru.”

Zaki ya girgiza kai cikin alamun kayatuwa da jin bayanan, sannan ya waiwaya ya dubi Dila. “Ka ji wani tsari mai kyau!”

Dila ya ce, “Ran Sarki ya dade, ni ai ina jin tun da nake ban taba jin wasu dabbobi masu kyakkyawan tsarin sadarwa kamar wannan ba.”

Zakin bai ce komai ba, ya kara duban Kahuhu. Kahuhu ya dan risina ya ce. “Ran Sarki ya dade, hakika wannan tsari yana da ban kaye kwarai. Samun irinsa sai an nitsa.”

Zakin ya ce. “Idan an nitsa din za a samu kenan?”

Kahuhu ya ce. “Kwarai ma kuwa.”

Sarkin Ungulu ya yi farat ya ce. “Kai Malam, a ina za a samu, kuma wadanne dabbobi ne wadannan?”

Nan take katuwar Damisar da ke tsaye kyam a bayan Zakin ta daka masa tsaya, tare da cewa. “Hattara dai.”

Sarkin Ungulu ya fadi ya yi birgima a kasa yana cewa. “Na tuba, a yi mini aikin gafara, ba zan kara ba.”

Kahuhu ya dubi  Damisar nan wadda murtuke fuskarta ya kai intaha, ya ce da ita.

“A yi masa afuwa, watakila rahin yawan zuwa fada ne ya sa bai san ladubbanta ba.”

Ta kara daka wa Sarkin Ungulu tsawa. “Tashi, ka yi mana shiru. Nan gaba kar ka kara irin wannan rashin ladabin a fada.”

Ya tashi yana karkarwa ya ce. “Godiya nake, ban kara komawa ga wannan mummunan laifi daga yau.”

Dila ya ce da shi. “To ka nutsu, Sarki bai gama magana da kai ba.”

Zaki ya dube shi cikin sakin fuska ya ce. “Yanzu idan muna son sanin inda al’umarmu suke a gabashin dajin nan, ya ya za mu yi?”

Sarkin Ungulu ya ce. “Ina godiya gare ka Sarki mai adalci, bisa tausasa min da ka yi. Duk da katobarar da na yi, fuskarka ta  kasance tamkar wata tattausar shimfida a gare ni.” Ya dan goge gefen idanu, kamar wanda kulla ta cika wa ido, sannan ya ce. “Idan ka so hakan, gobe war haka labarin halin da dakarunka suke ciki zai riske ka.”

Zaki ya ce. “Zan so hakan kuwa. Amma zan kuma so in ji yadda za a yi hakan ta samu.”

Sarkin Ungulu ya ce. “Idan al’umata suka tashi neman bayanai, suna yin aiki sadaukarwa ne, wanda yakan bukaci jama’a masu yawa fiye da wadanda suke isar da sakon samuwar rikitiba. Kuma a cikin duk wadanda suka shiga wannan neman bayanan, babu wanda yake komawa gida ya kwana a cikin iyalansa a ranar. Sai ko washegari ko ma bayan ‘yan kwanaki.”

Zaki ya ce. “Na’am.” Tare da dan tura kai gaba, cikin alamun tsananin sha’awar jin labarin.”

Sarkin Ungulu ya ci gaba, “Sabanin waccan hanyar isar da sakon, wannan tana farawa ne daga Mai’unguwar  Gunduma. Wanda idan aka sanar da shi yanayin bayanan da ake nema, sai ya tura jakadu shida su nufi gunduma ta gaba. Amma biyu ne daga ciki za su nufi gundumar kai tsaye, sauran hudun za su rabu dukkan bangarori hudu, su yi t faman lalube. Tare da haka, duk Ungulun da suka gani a kan hanya sai sun sanar da ita irin bayanan da suka fito nema, don ita ma ta sa ido in ta ga ko ta ji labarin ta sanar da shugaban gunduma mafi kusa.”

“Na’am.” In ji Malam Kahuhu.

Sarkin Ungulu ya kara samun nutsuwa, ganin cewa har wanda ya yi wa laifi a fadar ya sakankance shi yake sauraro. Ya dora, “To yayin da biyun can da suka nufi gundumar kai tsaye suka karasa, sai su sanar da Dagacin Gunduma bayanan da Mai’unguwa yake nema, a madadin Sarki. Daga nan, kafin sauran jakadu hudun can su karaso, sai shi ma Dagacin ya tura dakaru goma sha biyu zuwa gunduma ta gaba. A cikinsu hudu ne kawai za su nufi gundumar kai tsaye. Sauran jakadu takwas kuwa sai hudu daga ciki su nufi banagarori hudu; kudu da arewa da gabas da yamma. Hudu kuma su nufi kusurwoyin wadancan bangarori hudun; kudu maso gabas da kudu maso yamma da yamma maso arewa da arewa maso gabas. Su ci gaba da lalube, da kuma shelanta abin cigiyar ga dukkan Ungulun da suka ci karo da ita a kan hanya.”

Dila ya ce, “Ikon Ubangiji Al Karim!”

Sarkin Ungulu ya ci gaba, “Yayin da wadancan jakadu hudu suka isa gunduma ta gaba, sai su sanar da Hakimin Gunduma cigiyar da muke yi. Ba tare da ya saurari zuwan sauran jakadu takwas da suka bazama sasanni ba, sai kawai shi ma ya tashi nasa jakadun. Shi kuma zai tashi jakada ashirin ne, gaba daya. Guda shida daga cikinsu kai tsaye fadata za su nufo. Suna tafe suna bin dukkan gundumomin can, suna tambayar ko an samu labarin da Sarki yake bida. Har su karaso gare ni. Yayin da su kuma wadancan goma sha shidan sukan kara bazama dukkan gaffen daji, suna bibiyar jama’armu ko sun samu irin wancan labarin. Su ma kuma sukan fuskanto inda fadata take ne.”

Da ya kawo wannan gabar sai Zakin ya ce da shi, “Duk wannan aiki yini nawa zai dauke su?”

Sarkin Ungulu ya ce. “Idan ba a samu labarin ba ne har sai da aka kai ga Hakimi, to dawowar amsar gare mu za ta iya kasancewa a cikin yini biyu. Amma idan aka samu a wata gunduma kafin kaiwa ga ta Hakimin, ko kuma ma wadanda suke bin kusurwoyi ne suka samu bayanan, to cikin wuni guda amsa za ta ishe mu.”

Zaki ya kara waiwayar dama da hauninsa zuwa ga Dila da Kahuhu, sannan ya ce. “Yanzu wannan ba abin mamaki ba ne?”

“Na gaske ma kuma Rankayadade.” Suka hada baki.

“Kodayake,” Zakin ya fada yana duban Kahuhu, “ku idan an bibiyi tarihi ba mamaki ku bayar da labarin wani tsari mai kaye kamar wannan.” 

Kahuhu ya ce, “Ai tarihi ya kunshi dukkan wata gwaninta da za a iya bayaninta a yanzu Rankayadade.”

Ya ce. “Idan kuwa haka ne, to lallai ya kamata mu samu lokacin sauraren tarihi, maimakon na labarai da muke yi yanzu.”

Kahuhun ya risina kadan ya ce, “Hakan ma daidai ne Rankayadade.”

Zakin ya ce, “To Ubangiji Ya ara mana rai da lafiya.”

Ilahirin al’umar fadar suka hada baki, “Amin.”

Daga wannan lokacin sai ya kara duban Sarkin Ungulu, ya ce. “Muna so a samo mana labarin inda dakarunmu suke daga nan zuwa kowane lokaci mafi sauri.”

Sarkin Ungulu ya ce, “An gama Rankayadade.”

Daga wannan lokaci sai Sarkin ya  tashi, ya shiga gida, sannu a hankali kuma kowa ya fashe.

<< Yini Sittin Da Daya 20 Yini Sittin Da Daya 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×