Yini Na Ashirin Da Hudu
Wannan ne yini na farko da dukkan dabbobin can da suka yi zango a makarantar na rundunonin biyu suka gagara hallara a makarantar da wuri. Tattaunawar da suke ta yi tun yammacin jiyan ce ta ki ci ta ki cinyewa; har yanzu kaso mai tsoka suna ganin zamansu a makarantar ne a’ala, yayin da a daya bangaren tsirarin suke ganin biyayya ga Sarkin ce ahakku.
A haka dai ganin lokaci ya ja suka kara rankayowa zuwa makarantar. Da isaru kuwa Kunkurun ya ce, “Na dauka busar sarewar ce za ta hore muku. . .