Skip to content
Part 24 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin Da Hudu

Wannan ne yini na farko da dukkan dabbobin can da suka yi zango a makarantar na rundunonin biyu suka gagara hallara a makarantar da wuri. Tattaunawar da suke ta yi tun yammacin jiyan ce ta ki ci ta ki cinyewa; har yanzu kaso mai tsoka suna ganin zamansu a makarantar ne a’ala, yayin da a daya bangaren tsirarin suke ganin biyayya ga Sarkin ce ahakku.

A haka dai ganin lokaci ya ja suka kara rankayowa zuwa makarantar. Da isaru kuwa Kunkurun ya ce, “Na dauka busar sarewar ce za ta hore muku kunne ai, ku bar aikin da ya fi komai muhimmanci, ko koma koma-bayan ayyuka.” Wani daga cikinsu bai ko iya bude baki ba, ya kara cewa, “Domin duk wani aiki da za ka yi bauta ce ko bautarwa, amma aiki na ‘yanci kawai shin ne wanda ake yinsa da ilimi, ko wanda ilimi ya gina.”

Mafi yawansu suka hada baki yayin cewa, “Na’am.”

Sannan ya kara cewa, “Don haka duk wani wanda ma zai ture ka daga kan turbar karatu, ba masoyinka ba ne, ko wane kuma.”

Wasu suka kara cewa. “Haka yake.” Wasu kuma suka yi kasake cikin rashin tabbatacciyar matsaya.

Zomo ya kara mikewa ya ce, “Alaramma ko da iyaye ne?”

Ya ce, “Ko da iyaye ne.”

Ya kara cewa, “Alaramma ko da malamai ne?”

Kunkuru ya dan yi jim, sabanin yanayin amsawarsa ta farko, sannan ya ce, “Ko da malamai ne.”

Sai ya ce, “To amma in haka ne, me ya sa kwanaki ka tura jakunan nan biyu gidanka, don su ci gaba da jigilar kayan abincinka? Ka tura Dage da Damisa rumbunka suna gadi, alhali duk neman karatun suka zo? Kenan ma iya cewa kai ma ba masoyinsu ba ne?”

Alamomin bacin rai suka mamaye fuskar Malam Kunkuru, amma duk da haka ya daure ya yi wani yake. “Ai ita biyayya ga malami ita kanta ibada ce mai girma.”

“Ita biyayya ga Sarki fa?” In ji Zomo.

Kunkuru ya ce, “Wai tsaya, wai hujjatayya kake son yi da ni ne?”

Zomo ya bude baki zai yi magana wata fusatacciyar Giwa ta sharba masa hancin nan nasa. Nan take kuwa ta yi wurgi da shi can gefe.

Fadawar Zomon nan a kasa tik ke da wuya, su kuma wadancan jakadun Sarki na biyu sun kawo kai. Suka dakata suka daga Zomo, suka yayyafa masa ruwa, aka kuma yi sa’a ya farfado. Ba tare da tambayar sa komai ba kuma suka karasa inda Malam Kunkurun yake zaune kan wani buzu, kuma zagaye da dimbun dabbobin dawa.  Damisar nan da take jagorantar rundunar ta ce da shi.

“Shin ba a sanar da kai sakon Sarki ba ne?”

Ya ce, “To banda abinku kwa shigo cikin jama’a ko sallama babu?”

Ta kara maimaita masa waccan magana, a wannan karon cikin mafi tsananin daurewar fuska, kuma daf da shi. 

“An sanar da ni.” Ya amsa mata.

“Kuma sai ka ki bayar da amsa ko?” Ta kara tambaya.

“Na ce idan jangali ne, ni ba ni da kiwo, idan kuwa karatu ne, to shi ya fi kamata ya zo.”

Da Damisar nan ta ji wannan lafazin daga bakinsa, ba ta yi ko jinkirin daidai da dakika ba, sai kawai ta sa kafar nan tata mai manyan farata ta take masa kai. Sannan ta juya ta ce, “Ku kawo igiya ku daure min shi, ku sa a buhu.” Nan take kuwa  dakaru suka fara cika umarnin.

Da sauran dabbobin da ke makarantar suka ga wannan lamari, sai dukkansu tsoro ya cika zukatansu, musamman saboda sanin izzar Sarkin da ya turo jakadun, suka fara darewa. Daga karshe wannan tawaga ta daure Malam Kunkuru ta dauko shi, suka nufo fadar Sarki.

<< Yini Sittin Da Daya 23Yini Sittin Da Daya 25  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×