Yini Na Ashirin Da Biyar
Kafin fitowar Zaki, fadar ta yi cikar kwari. Kuma babu abin da ake tattaunawa sai yadda juyowar wadancan dakaru da isowar Malam Kunkuru da ya tsare su za ta kasance. Su kansu Dila da Kahuhu sun cika da mamaki kwarai game da yadda har aka samu wata dabba da dadin bakinta ya sa dakarun yaki suka yi watsi da aiken Sarki, suka rungumi zancenta.
Ana cikin tattauna wannan batun ne kuma Basaraken ya fito. Wanda bayan kammala gaishe-gaihe shi ma ya kalli Kahuhu ba tare da magana ba, sai bayan ya juyo. . .