Skip to content
Part 25 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Ashirin Da Biyar

Kafin fitowar Zaki, fadar ta yi cikar kwari. Kuma babu abin da ake tattaunawa sai yadda juyowar wadancan dakaru da isowar Malam Kunkuru da ya tsare su za ta kasance. Su kansu Dila da Kahuhu sun cika da mamaki kwarai game da yadda har aka samu wata dabba da dadin bakinta ya sa dakarun yaki suka yi watsi da aiken Sarki, suka rungumi zancenta.

Ana cikin tattauna wannan batun ne kuma Basaraken ya fito. Wanda bayan kammala gaishe-gaihe shi ma ya kalli Kahuhu ba tare da magana ba, sai bayan ya juyo ya kalli Dila ya ce,

“Wane irin iya tsara zance ko girman ilimi kuke tunanin wancan Malami yana da shi, da har zai iya shasantar da wadanda muka yaba azancinsu muka tura su don su kare martaba da mutumcinmu?”

Dila ya ce. “Ba na zaton duk karatunsa zai kai Malam Kahuhu, balle ya dara shi. Kawai dai sun yaudaru ne saboda shi bakuwar fuska ne a wurinsu.”

Rufe bakinsa ke da wuya kuma shi ma Kahuhun ya ce. “Bana jin azanci ko hikimarsa za ta iya kai ta Dila, sai dai kawai sun rudu da zancensa kuma sun ba shi sama da kimar da ta kamace shi ne saboda ba su san shi ba.”

Zakin ya ce, “Abu daya dai kuka fada cikin mabambantan kalmomi ai.”

Dila ya ce. “Wato Rankashidade irin abin nan ne kawai da masu magana suke cewa ‘Ido wa ka raina?’”

Kahuhun ya ce. “Ya ce wai ‘wanda nake gani kullum’ ba.”

A daidai wannan lokaci ayarin wadancan kwari karkashin jagorancin kudan Zuma suka dawo daga waccan makaranta ta Kunkurun. Da ganinsu komai ya tsaya, aka mayar da hankali kansu. Bayan sun gurfana gaban Sarki sun yi gaisuwa, sai ya tambaye su,

“Mene ne sakamakon sakonmu?”

Kudan Zuman nan ya ce. “Ran Sarki ya dade mun isa, mun kuma sanar da wancan Malami sakonka kamar yadda ka yi umarni. Sai dai bayan gama sauraren mu, sai ya nuna dagawa ta hanyar cewa idan jangali Sarki yake neme, to shi ba makiyayi ba ne. Idan kuwa karatu Sarki yake son yi to sai dai ya je har can ya iske shi.”

Alamun bacin mai tsanani ya bayyana a fuskar Zakin yayin da yake cewa. “Su kuma yaya suka yi da shi, bayan isarsu?”

Kudan Zuman nan ya ce. “Sun same shi a cikin wannan hali, har ma wasu daga dalibansa sun fara dukan Zomo, saboda ya yi inkarin da’awarsa ta kin yin biyayya gare ka. Sai suka jaddada masa sakonka, shi ma ya maimaita musu irin amsar da ya ba mu.”

Zakin ya daka masa tsawa: “Kai, ka takaice mana zance ka ji. Ina yake yanzu?”

Kudan Zuman nan ya ce. “Tuba nake Rankayadade, yana nan sun daddauro shi, sun taho da shi gare ka.”

Da ya ji haka sai ya koma ya daidaitu bisa karagarsa ba tare da kara magana ba. 

Dila ya dubi Kahuhu ya ce. “Ka kuwa taba jin wani mai dagawa kamar wannan tsawon rayuwarka.”

Kahuhu ya ce. “Eh na sha ji, gani ne dai ban taba ba.”

Dila ya ce. “A tarihi ko?”

“A tarihi fa.” Kahuhu ya amsa masa.

“Wai shi tarihi komai akwai a cikinsa ne?” Dilan ya kara tambaya.

“Kwarai kuwa,” Ya amsa, sannan ya kara; “ida duniya dama ai ba wai mikewa ta yi take ta tafiya a guje ba, zagaye take yi.”

“Zagaye kuma?” In ji Dila.

“Zagaye fa.” Ya amsa masa.

“To kamar yaya kenan?”

“Babu wani abu da zai faru face in ka samu tsawon rai sai ka ga makamancinsa ya maimaitu.” Kahuhu ya amsa. “Don haka a wurin masana tarihi babu wani sabon abu da yake faruwa yanzu.”

“Iye?” Dila ya fada gami da karkata kai.

“Iye,” Kahuhun ya amsa masa cikin tasa siga, sannan ya kara; “Abubuwan baya ne kawai suke zagayowa kuma su kara wucewa.”

“To amma,” Dila ya ce. “ya aka yi wataran in wani abu ya faru, ko wani ya yi wata gwaninta ko rashin kirki, sai a ce duk duniya shi ne ya fi kowa a wannan fanni?”

“Idan an ce ya fi kowa, ai ambatar kowa din yana nufin akwai wasu da suka yi irin wannan ba shi kadai ba ne. Shi dai kawai fin kowa ake zaton ya yi.” Kahuhu ya fada cikin murmushi.

“Kai, wani lokacin ma akan ce  fa shi kadai ne a duniya ya taba yin kaza.” In ji Dila.

“Kai, duk lokacin da ka ji wannan, mai maganar yana magana ne kawai cikin iyakar guntun saninsa.” Kahuhu ya amsa cike da fara’a.

Yana daga cikin abin da ya sa suka kara dagewa da yin maganar, ganin yadda hankalin Basaraken ya dawo kansu, kamar yadda suka saba. Tsananin daure fuskar da a baya ya yi, tuni ya gushe yanzu. Wani murmushi ya fara shirin maye gurbinsa. Hucin da a baya yake yi saboda tsananin tunzura, ya yi kaura, wanda tuni nutsuwar da ta bakunci zuciyarsa ta fi galaba a kan sa.

Kafin lokacin da zaman fadar zai tike, tuni Basaraken ya saki rai, ya fara dariya shi ma. Kuma yana cikin wannan yanayi har yamma likis, lokacin da ya shiga gida.

<< Yini Sittin Da Daya 24Yini Sittin Da Daya 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×