Skip to content
Part 28 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Talatin Da Bakwai

A tsakiyar wannan yinin ne wasu Bakane suka tiso keyar wata bakuwar dabba, wadda da alama batan kai ta yi zuwa gaban Zakin. Ya kalle ta da kyau, ya kuma cika da mamakin kamanninta.

“Na yi mamakin ganin ashe akwai wata dabba da take rayuwa a kusa da mu ban san ta ba!”

Haka kuma dukkan wadanda ke zaune a fadar suka shiga irin halin da ya shiga, shi ya sa kusan dukkansu suka hadu wurin cewa, “Lallai wannan ya kaim abin mamaki kam.”

Zaki ya dubi Dila ya ce, “Sarkin Azanci ko ka san ta ne?”

Dilan ya ce. “Ina fa, ni ma ban san ta ba. Abin da kawai na iya fahimta a tare da ita, shi ne abin da kowa ya fahimta, cewa wata kabila ce daga kabilun jaki.”

Daya daga cikin Bakanen nan da suka rako dabbar ya ce. “Kwarai, mu ma dai abin da muka gane kenan, domin ga kansa nan irin na Jakin Gida da kuma zane-zanen jikinsa irin na Jakin Dawa.”

Zakin ya ce, “Ai fa shi ne,” sannan ya waiwaya ga Kahuhu ya ce, “To ko Malam ya san ta ne?”

Malam Kahuhu ya risina, ya ce, “Ubangiji Shi ne masani, ni ma kam ban san wannan dabba ba.”

Da zakin ya ji tasa amsar, sai kuma ya kara karkatawa ga Kunkuru, wanda yake zaune a can cikin ayarin ya-ku-bayi, ya ce, “Alaramma ko za a taimaka?”

Nan take sai Kunkuru ya ce, “Wannan ai shi ne Jakin Kagga, Rankashidade!”

Nan take kuwa sai hankalin kowa ya dawo kan Kunkuru yayin da yake ta bayani game da Jakin. Har sai da ya kai wata gaba ya tsaya, Zakin ya kara ce wa, “Abin mamaki, mu ka ga nan duk ba mu ko taba jin labarinsa balle ganin sa haka ba.” Kunkuru ya ce, “Ai ba a nan kusa da mu suke ba, dabbobi ne irin da dazukan Afurka ta Kudu. Kuma ba sa nisan kiwo saboda tsoron dabbobi masu fika da bil’adama masu farautarsu.”

Zaki ya ce, “Ka ga kuwa da kafafuwan nan nawa na je har wannan dajin da kake magana, tare da mahaifina yayin wani sulhu tsakanin manyan dabbobin duniya.”

Kahuhu ya ce, “Ba abin mamaki ba ne ka je har can kuma ba ka gan su ba. Domin baya ga tsoronsu, ba kuma su da yawa. Har ma dai ana ayyana su a cikin dabbobin da ake sa ran nan gaba kadan za su iya karewa a doron kasa.”

Cikin mamaki Zakin ya ce, “Ashe dai da gaske ne batun fargabar karewar wasu dabbobi a doron kasar nan da ake yi?”

“Kwarai ma kuwa,” In ji Kunkuru.

Sai ya ce, “To kamar wadanne dabbobi kenan ake wa wannan hasashen?”

Ganin ya samu rana, kowa shi kadai yake suararo, ga shi kuma Sarkin yau ma ya nuna yana tsananin son jin labari daga bakinsa, ya sa sai da ya nemi izinin dan matsawa kusa da Sarki. Wai a cewarsa, saboda muryarsa ba ta da karfi sosai, ai ya rika fadar wani abun Sarkin ba ji ba. Haka kuwa aka sahale ya kara matsawa. Sannan ya fara bayar da labarin:

Dalilai da dama ne suka haddasa rashin yawa da barazanar karewar wasu dabbobi a doron kasar nan. Wasu daga dalilan sun hada da: Yawan gine-gine da sare bishiyoyi da bil’adama suke yi, da gobarar daji ko sassabe shi don noma.  Har da yawan mafarautar wadanda kusan kullum cikin neman rayukan dabbobi suke. Wannan ya sa su kansu bil’adama suna lissafi cewa a kowace shekara dabbobi da tsirrai sama da dubu goma ne suke bacewa.    Wannan shi ya sa a yanzu aka nemi wasu dabbobi aka rasa, irin su:

Baturen Biri; wani kyakkyawan Biri mai nutsuwa kwarai da yawancinsu suna rayuwa ne a dazukan Zanzibar, wadanda su a can suke kiransa Jan Biri Na Kolobu. Daga kallo daya za ka iya fahimtar banbancinsu da sauran birar, ta hanyar wani dogon hanci da yake da shi kamar na Bature. Haka idan ya daga hannu ka dubi babban danyatsansa.

Akwai Kifin Baiji; wani katon kifi, ruwan toka da ya fi karfi a kogin Yangtz  na kasar Sin. Wand yawaitar jiragan ruwa da gurbacewar muhalli suka hana shi sakat, daga karshe dai har aka nemi ire-irensa aka rasa.

Akwai Beran Ayay; wani shu’umin Bera wanda a baya ba shi wata babbar daula kamar wani daji a Madagaska. Sabanin sauran baraye, shi Ayay ba shi da wani babban kalaci fiye da wasu tsotsotsi da yake bi yana kwakula a jikin bishiyoyi, da wani kakkarfan farce nasa.

Sai Kwadon Titikaka; wani katon Kwado mai tattaurar kuma tattararriyar fata. Amma duk da haka bil’adama sun takura wurin farautarsa, kamar wani kayan gabas. Duk da wani kokarinsa na buya tamkar ba ya tasiri. Domin yana iya shigewa can cikin tabo ya dauki lokaci mai tsayi ba tare da ya ko leko kan tudu ba, amma fitowarsan wataran sai ta zame masa barazana.  

Haka akwai wata Jabar Sintir, wata jarumar Jaba mai karancin gashi a jiki. Wadda masu dabbobin suke ce mata Zabiyar Jaba…”

“Lallai wannan malamin malam ne!” Zakin ya fada, tamkar wani mai subutar baki.

Daga wannan lokacin kuwa sai Kunkuru ya kara bude shafin sabuwar kafafa da iya-yi. A gefe guda kuwa Kahuhu da Dila suka shiga cikin damuwa, suna ganin wani ya zo yana neman danne nasu mukamin, wanda a baya babu wanda yake ko sansanar sa. Haka dai Malam Kunkuru ya gama sharafinsa a wannan rana, Zakin kuma yana ta nuna girman kayatuwar da yake yi da bayanan nasa, har zuwa lokacin tashin fadar.

<< Yini Sittin Da Daya 27Yini Sittin Da Daya 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×