Yini Na Hamsin Da Tara
Kamar yadda suka saba a kowace rana tun bayan kwanciya jiyyar da Sarkin ya yi, mafiya yawan wadanda suke lazumtar fadar sukan zo su shiga cikin gidan, su dube shi, sannan su dawo fadar su zauna. A yau ma kamar kullum suna zaune jigum-jigum a fadar tamkar masu zaman makoki, sai kawai Kunkuru ya tashi ya dare kujerar sarautar nan!
Nan take kuwa hankalin dabbobin da ke zaune a wurin ya kai matukar tashi, wasu suka harzuka suka fara gurnani! Da ya lura da wannan alama sai ya yi farat ya mike. . .