Yini Na Sittin
Da safe, sai Dila ya yi wa gidan Malam Kahuhu tsinke. Ya kuwa ci sa’a, yana kofar gida yana darasu. Bayan sun gaisa, sai ya samu wuri ya zauna har sai da ya sallami daliban, sannan ya matso suka gaisa. Ya ce.
“Alaramma kwanan nan biyu ba ma haduwa, shi ya sa ce yau dai kafin in wuce fada ya kamata in biyo mu dan zanta.”
Kahuhu ya yi murmushi sannan ya ce, “Ka kuwa yi dabara. Ya jikin Sarki?”
Dila ya ce, “Da sauki, wannan safiyar jakada ya ishe ni cewa. . .