Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Zarina by K_Shitu


Bismillahir Rahmanir Rahim.

“Sultanmeeh Hayatieey!”

Ta faɗa cikin muryarta ma’abociyar tarin nutsuwa da taushi. Wata irin juyowa yayi da kyarmar jiki yana waige-waige bakin ruwan da yake zaune.

Yayi saurin tsame ƙafafuwansa daga cikin sweeming pool ɗin da ya sanya su ya miƙe tsaye yana dube-dube. Ya ɗan buɗe murya da alamun shauƙi da kuma nishaɗi ya ce, “kina ina..?”

Siririyar dariyarta mai daɗin sauraro ta sakar masa saitin kunne tana saka tafukan hannayenta masu laushi ta rufe mishi idanuwa.

Kiciniyar cire hannayenta ya hau yi cike da shauƙi ya zagayo da ita gabanshi ya zaunar da ita shi ma ya zauna yana lumshe idanuwa cike da tsantsar soyayyarta da ta gauraye masa ruhinsa,zuciyarsa,ƙwa-ƙwalwarsa da kuma gangar jikinsa.

“Ina fata kuma ina burin mu kasance da juna har ƙarshen rayuwarmu, Hayatieey ina tsoron na rasa ki ke ce Rayuwata gabad’aya”.

Wani irin kyakkyawan Murmushi ta sakar masa tana juya masa baya.

Maimakon Fararen ruwan da ke fita daga idanuwan kowane ɗanAdam a matsayin hawaye, ita ba su ke zubowa daga nata idanun ba jini ne mai duhu ya ke zubowa tana sharewa da farin mayafinta.

Jin ta yi shiru yana ta Magana ba amsa ne ya sanya shi juyo da ita gabanshi.

Ya kalli jinin da ya ɗan ɓata mata mayafi, Amma idanuwata babu jini Zuciyarsa tay wata irin bugawa Har hannunsa na kyarma ya riƙe mayafin yana jera mata tambayoyi.

“Hayatieey me ke damunki Ja`z kun chunboo, What’s Wrong..?” Tsabar yadda ya ruɗe lokaci ɗaya har yana haɗa mata da Yaren Soulj da turanci duk da ba ta jin turancin ita.

Ta ƙi yi mashi magana ta ƙi cewa komai sai dai Narkakkun idanuwanta masu kaifi da sheƙi da ta zuba masa ko ƙyaftawa ba ta yi.

“Kina so na je gun Abi na yi masa magana ko, Zan saka daga masatauta a nema mini aurenki, Gobe zan je da kaina ni ma Ki yi min magana Zarina..”

Har lokacin ba ta motsa ba, kuma ba ta ba shi amsa ba, Sai ƙwayar idanuwanta da su ke chanja launi daga kalar bula mai matsanacin duhu zuwa kalar bula Mai haske sosai da ke ƙoƙarin sajewa da launin idanuwanta.

Ruwan jinin hawaye masu duhu sosai su ka shiga zubowa daga Idanuwanta, Har lokacin ba ta motsa ba sai dai hawayen na ta ɗiga bisa fararen tufafinta.

Baƙin rawanin da ke sanye bisa kanshi ya ciro a hankali ya fara goge mata hawayen Shi ma Hawaye masu ɗumi na bin kuncinsa.

“Hayatieey!”

Ya kira sunan A hankali yana riƙo Yatsun hannayenta.

“Ki faɗa min me ke damunki ko kina so Zuciyata ta buga ne, Mi ya ke damunki ko Abi ne..?”

A hankali ta ƙwace Hannayenta, ta yi baya kaɗan, Sannan ta miƙe ta soma tafiya da bayaya har lokacin hawayen jini masu duhu na zuba daga idanuwanta har fararen tufafinta sun ɓaci sosai.

Tun ƙwayar idonsa na iya nuna masa hoton Zarina a idanunshi har ta ɓace ma ganinshi ba tare da ya sani ba.

Lokacin da tunaninsa ya fara dawowa Duniyar da yake ne ya fahimci Zarina ba ta tare da shi, Sai mayafinta da ke yashe a ƙasa da Baƙin rawaninsa.

Ya zube ƙasa bisa gwiwoyinsa yana dafe kansa da ke cike da yalwataccen gashi Launin Brawn colour mai duhu.

Yana da saurin Rikicewa da shiga yanayi na ruɗu sosai, Bai kuma iya fushi ba, Yana da Ji da kansa sosai da kuma kame kai da kowa, baya shiga sabgar da ba tashi ba, baya kula kowa sai Mahaifiyarsa da Mahaifinsa da ‘Yar’uwarsa, da kuma ahalinsa, Yana bawa Ahalinsa muhimmanci sosai da aikinsa, Ya ɗauki lokaci da muhimmanci sosai. Mutum ne mai wuyar sha’ani idan ba ka nazarce shi ba sosai, Baya magana sosai Izza, Ƙasaita duk da shi ake kwatanta su, Iko da mulki A jinin sa su ke kuma sarƙafe da numfashinsa.

Yana son Gaskiya baya son ƙarya Yana Rayuwar ‘Yanci baya takura ma kowa yana da tausayi fiye da tunani. Mutum ɗaya yake bawa muhimmancin da baya ba wa tashi Rayuwar ZARINA.

Zarina ta kasance Macce ta farko da ya fara ƙauna kamar ya zauce, Yana mata wani irin so sosai mai narke da Zallar ƙauna, Sai dai matsalarsu Ɗaya Abin Zarina.

Idan Ana neman Namiji mai Izza aka sami Abdulmaleek Muhammad bn Abdulmaleek Wanda ake ma Laƙabi da Sultaan dole a dakata domin da shi ake misalta izzar.

Kasancewarsa Ɗa na Uku da mahaifiyarsa ta haifa sauran tun suna jinjirai suka mutu shi kaɗai ne yay rai, Sai kuma Ƙanwarshi Nailah.

Shi ne Sarki mai jiran gado a Daulatul Najees wanda Naɗin sarautarsa ya rage kwanaki Goma Sha tara za a gabatar da Naɗin Mahaifinsa zai sauka daga Kujerar Mulkin Daulatul Najees shi kuma ya hau Kujerar mulkin Masarautar Najeessa A matsayin Sarki mai ji da cikakke kuma fitaccen iko

Idan Ana neman Namiji Mai Kwarjinin zallar kyawu da ji da Izza aka samu Sultaan Abdulmleek dole a ɗiga alamun dasa aya, Saboda yanda Allah ya yi masa Zubin halitta mai Nutsuwa da tsarin Yana da Idanuwa masu Kyawu sosai da fizgar Zuciya da gangar jiki..

A hankali kuma cikin Sanyin Jiki ya miƙe Hannunsa riƙe da Mayafinta, Ya nufi Ƙofar da ya fito daga ciki Ya bar Keɓantaccen wajen da shaƙatawarsa.

Har ya shige Cikin Ainahin Ƙayataccen Office ɗinsa da ke ƙawace tamkar ɗaki ko kuma Gida ya faɗa kan kujera bai aje mayafin ba.

Gaba ɗaya ya maida hankalinsa wajen tunanin abin da zuciyarsa ke kitsa masa kuma ya yanke shawarar Aikata shi…

Cikin Zafin nama irin na Mai ji da tashen Izza, Ƙuruciya da lafiya yake Tafiya Zuwa sashen Mahaifinsa Sarki Muhammad bn Abdulmaleek Yusuf.

Bayi da Hadimai da dogarai sai zubewar ban girma ta gaisuwa su ke yi saboda tsananin nuna girmamawarsu gare shi.

Bai iya samun Damar amsa gaisuwar kowa ba sai hannu da ya ke ɗaga musu har ya kai bakin ƙofar Shiga sashen Mahaifinsa da ya ƙawatu da gini mai azabar kyau na zamani da ƙyale-ƙyale mai tsari, Da ka gani za ka fahimci Irin yanda aka narka ainahin dukiya a Iya zubi da tsarin ginin.

An baza Dogarai sosai da kuma Fararen sojoji marasa Uniform da ke zagaye da sashen da ya kasance kamar wata unguwa guda.

Gaisuwa irin wadda ake yi ma Sarki suka yi mashi cike da tarin ban girma Yana ta amsawa da hannuwansa.
Duk sun sunkuyar da kawunansu ƙasa suna jiran umurninsa ganin ya tsaya bai bada damar a buɗe masa ya ƙarasa ciki ba.

Shi kaɗai ya san tunanin da yay kawai ya bada izinin a buɗe masa ƙofa, Dan ba shi da shamaki da Shiga Sashin Sarki.

Ƙamshi mai sanyi da daɗi ne ya doki hancinsa, Ya shige Ciki har zuwa Babban Parlourn Sarki ƙayatacce da ya sha ado mai jan hankali aka Narka mashi abin da ake kira ainahin Dukiya.

Duk wanda ya ga Yanayin yanda ya taho kanshi ba rawani yalwatccen gashinsa a bayyane sai ya sunkuyar da kansa don A tsarin al’adarsu rashin ɗa’a ne kallon Sarki a haka.

Kansa tsaye Shi kuma ya tunkari Ɗan Parlourn hutawar sarkin. Ya Isa bakin haɗɗiyar ƙofar Glass ɗin da yake da tabbacin Sarki yana ganin sa a halin yanzu, Ya latsa wasu abubuwa, sannan ƙofar glass ɗin ta rabe biyu Ya tura kai ya shige, Ta maida kanta ta rufe.

Yana gama shiga gaba ɗayansa ya sunkuyar da kansa ƙasa yana sarke damƙe mayafinta a hannunsa ya Duƙa har ƙasa saitin ƙafafiwan sarkin kamar zai Taɓa shi ya ce, “Barka da Hutawa Abbah”

Yay ɗan murmushi yana girgiza kai cikin Izzar da ta riga ta game masa jinin jiki ya ce, “Sultaan ka yi daidai ka ji ba zan yi mamaki ba idan haka ka ratso Bayi da kowa har nan sashen kad’an daga aikinka ne ni na sani”.

Ya sunkuyar da kansa alamun kunya yay Shiru kuma.

Ammah Ce ta ƙaraso cikin faɗa-faɗa tana mishi magana, “Sultaan ba dai haka ka shigo ba.?” Ya yi shiru dan ya san faɗanta.

Ta inda ta shiga ba ta fita ta nan tay masa tas.

Kai ɗin nan ko Allah ya shirya ka Tashi ka ɗauko (rawani) Houz cikin mang (Wardrobe) na naɗa makYa kalli kayan da ke jikinsa don Tunanin wane kala zai ɗauka daga ciki Golden nd Black Dress ne a jikinsa Wando mai baƙi mai ratsin Golden aikin jikin wandon ma Golden ne, Sai Rigar ita ma da tasha ƙayataccen ado aiki Golden da azurfar da aka ƙawata gaban Rigar da ita, Sannan Alkyabbarsa madaidaiciya mai kyau Baƙa, Sannan sarƙar wuyansa Mai sheƙi ta zallar Zinare marar kacau-kachau da yawa. Ya ɗauko Baƙin rawani mai kyau ya dawo inda ya tashi ya miƙa ma Mahaifiyar tasa.

Sarauniya Basima Ke nan, Macce mai ji da tsananin ƙarfin iko da na sarauta, Kaifi ɗaya ce tana da Izza da jin kanta, Ana matuƙar shakkarta ba ta ɗaukar raini idan tana ƙaunarka ka ji daɗi idan kau har ba ta yinka za ka fuskanci ƙalubale da wulaƙanci sosai wajenta, Ita ce Uwargidan Sarki sannan Sarauniya Najyla Ita ma matar sarki ce.

Tana naɗa masa tana ɓaɓɓata fuska kasancewarta macce mai faɗa da son Nuna isa akan kowa.
Ta kammala naɗa masa tsaf yay mata godiya. Ita kuma ta fice gaba ɗaya ta bar shi wajen Sarki.

Su ka yi shiru su biyun Babu wanda yay magana. Ajiye Faskekiyar Wayar hannunsa sarki ya yi yana maido hankalinsa kan Sultaan. Shi ɗin ma nutsuwa ya yi yana sake damƙe ɗan mayafin Zarina.

“Ko akwai abin da kake son fad’a ne, na ga ba ka saba rik’e magana ba Kai-tsaye kake komai Shinya sa na bar ka ka fad’i” Sarki ya ce yana sake kishingiɗa da tattausar kujerar da ke bayansa.

Ya haɗiye yawu Cikin dakiya ya ce, “Abbah dama maganar Zarina ce..”

Shiru Maimartaba ya yi na ‘yan wasu daƙiƙu yana ƙare masa kallo ba tare da ya ce komai ba yake nazartar yanayin nasa.

Cikin Kula da tsantsar tausayi da ƙaunar Ɗan nasa ya ce, “Abdulmaleek!’

Ya ɗago jin Yanda ya kira ainahin sunansa, Cikin yaren Soulj ya amsa masa, “Na’am”
“Ya kake so ayi?” Wani irin sanyin ƙaunar Abbahnsa ne ya ratsa sa, Wata irin murna na ta bayyana kan fusakarsa saboda tsananin farincikin da ya gaza ɓoyuwar masa.

“Abbah so na ke ka yarje min ka yi mini addu’a ina so na je da kaina na gana da Abin Zarina Gobe”.

Ya sakar masa murmushi mai kyau Tare da faɗin, “Go a head Wish you All the best”
Ya sunkuyar da kansa ƙasa Alamun girmamawa Kana ya ce “Shukraan Abbah Truly appreciated”.

Ya miƙe da saurinsa ya bar Sashen, Ya nufi nasa Ɓangaren Dogaransa suka buɗe masa Main Door ɗin tun kafin ya ƙarasa sun gaishe shi. Ya shige ciki zuciyarsa fal cike da Nishaɗi Ya shiga Bedroom ɗinsa yay ma kansa mazauni bisa Haɗaɗɗen gadonsa. Ta wani ɓangare yana cikin matsanancin farin ciki bisa ga Amincewar Mahaifinsa Fargabarsa Biyu ce A halin yanzu zuwa uku. Yana fargabar Abin Zarina da kuma Mahaifiyarsa, Sai kuma damuwa rashin sanin yanayin da ta ke ciki da kuma Abin da zai taras zuwansa wajen Abinta.

Wayarsa ya ɗauko ya fara danne-danne. Hadiminsa ya kira wanda yake kular masa da motocinsa da dawakai. “Ka shirya motoci biyu za mu fita gobe da safe.”

“To An gama ranka ya daɗe”. Ya faɗa shi ma ya kashe wayarsa.

Ya kwanta idanuwansa a rufe da tsananin Zumuɗi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Zarina 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×