Skip to content
Part 1 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Daya (Da Sake)

Da ƙyar take fitar da numfashi, tana juyi cikin tsananin azaba da raɗaɗi, ji take yi kaf ilahirin jikinta kamar an zuba mata ruwan batir tsabar zafi da raɗaɗin da take ji, wata ƙara ta saki tana ambaton Allah a bakinta, a hankali ta soma rufe idonta, tana jin fitar abunda ke cikinta, nan take kukan jaririyar da ta haifa ya karaɗe dajin, yayinda sautin kukan jinjirar yake ratsa jikinta, can ƙasa-ƙasa da murya ta ce “Alhamdulillahi.”

Tashi tayi dan yanzu har wani ƙarfi take ji ta sanya hannayenta ta ɗaga jaririyar, da ido ta kafe ta, hakan ya ba idaniyarta damar zubar da ƙwalla, “Ya Allah ba ni da wani zaɓi sai wannan, Allah ka ba Zinariya kariya cikin kariyarka, Allah ka raya ta, ka sanya mata albarka ” ta yi maganar tana share ƙwallar da ta zubo mata, ɗan kwalinta ta kwance yana da girma sosai ta naɗe Zinariya ciki, sannan ta aje ta, ba tare da ta damu da yadda jini ya ɓata mata jiki ba, Zinariya sai kuka take yi amma Mahaifiyarta bata ko waiwaya ba, jin kukan ƴar tata take yi kamar ana zuba mata ruwan dalma a kunne, a hankali ta ce “bani da wani zaɓi ne.”

Tayi tafiya ta tsawon awanni biyu, yunwa da ƙishirwa sun mata mugun riƙo, dan a halin yanzu tana gab da shiɗewa, ruwa ta fara nema ba ƙaƙƙautawa amma duk inda ta je ba alamar ruwa, daidai lokacin wata macijiya ta sulalo da sauri ta sare ta, nan take ta yanke jiki ta faɗi tana yarfi da hannu. Ta riƙe ƙafarta, take abubuwa da yawa suka shiga mata yawo a ƙwaƙwalwarta, ta tuna yadda gidansu ya ƙone suka rasa matsugunni, a hanya take bara dan ta samu abunda zata ci, ta tuna ranar da aka farmaki ƙauyensu wanda dalilin ne ya kawo ta zama daji, da ƙarfin gaske ta ɗaga muryarta cikin tsananin azaba ta fitar rai, muryarta na rawa jikinta na kakkarwa ta ce “ya Allah ka nisanta Zinariya da ƙauyenmu, ka mantar da ita duk abunda zai tuna mata da ƙauyenmu, ya Allah ka san garinmu ba zaman lafiya ka miƙa Zinariya wata duniyar da ba yankinmu ba” tana maganar tana kuka, tana tunda yadda aka kashe mata ƴanuwanta da duk wani makusancinta. A cikin wannan halin mutuwa ta ɗauki ran Hamida sanadiyyar wannan dafin da ratsa jijiyoyin jikinta.

*****

Zinariya na kwance cikin ɗan kwalin da mahaifiyarta ta naɗe ta da shi sai kuka take tsalawa, kukanta ya karaɗe gaba ɗaya dajin. Wata ƙatuwar Damisa baƙa ƙirin ta fito tana girgiza jikinta gashin jikinta yana wani warewa naman jikinta yana rawa tsabar girman da Allah ya mata, ta nufo Jaririyar da gudun gaske har tsalle take tana ciccira, Zinariya bata fasa kukan da take yi ba.

Damisar na gab da isowa kusa da Zinariya kawai ta yi wani mugun tsalle ta diro gaban Zinariya, nan take jikinta ya sauya zuwa halittar ɗan Adam cikin wasu kaya da suka sha ado, kaf ilahirin jikinta Zinare ne, hannu ta saka ta ɗauke Zinariya ta zuba mata ido, bayan wasu daƙiƙu ta ɓace tare da Zinariya.

Kogon Gimatuwa

Wani Babban kogo ne mai matuƙar girman gaske daga cikinsa, a cikin wannan kogon an danƙara wata ƙanƙararrar masarauta haɗaɗɗiya, matakin da ya wuce tunanin mai hasashe. An ƙawata ginin masarautar da Zinare, Wannan matar da ta ɗauki Zinariya ta bayyana ƙofar wannan fadar.

“Sarauniya Jahiyana ta dawo ” Binajita ta faɗa tana taɓa Akimita dake gefenta, kallon gefen da Binajita ta nuna mata tayi ta ce “har da wani abu a hannunta”, Sarauniyar Jahiyana ta ƙaraso kusa da su, nan take suka zube  ƙasa suna jinjina mata, alama ta musu da hannu cikin nuna isa ta ce “Binajita ki mata wanka da ruwan rijiyar Ziwale, sannan ki kawo min ita ” bata jira amsar da za su bata ba kawai ta juya baya tana tafiya. Binajita kuwa bata yi gardama ba ta ɗauki Zinariya zuwa gaban wannan rijiyar.

Rijiyar Ziwale

Rijiya ce mai matuƙar mahimmanci a Masarautar Gimatuwa, Sarauniya Jahiyana takan yi amfani da ruwan a kowace ranar Lahadi domin tsarkake su, kamar yadda suka yarda idan tayi amfani da su to abar bauta Bizani ta albarkaci waɗannan ruwan. Guga Binajita ta saka ta jawo ruwan sannan ta warware naɗin dake jikin Zinariya ta jefar ta fara kwarara mata ruwan a jiki, Zinariya ta fashe da kuka jin saukar ruwan a jikinta, ruwa ne masu matuƙar sanyi da ratsa gaɓɓan jiki , sai da ta tabbatar ta wanke mata jikinta tas sannan ta lulluɓeta da farin ƙyallen da ta gani gefen rijiyar yana danja alamar Sarauniya Jahiyana ta aiko da shi. Naɗe mata jikinta tayi da wannan ƙyallen ta juya ta nufi yankin Sarauniya.

Wata ƙatuwar Mage ta shigo ɗakin Sarauniya idonta na fitar da wasu launuka na kaloli (ja, kore, ɗorowa da fari), Sarauniya ta aje wata takobi kan madubin da take kallo ta ce “Me ya faru da masoyiyar ƴata take tsananin fushi haka “, “Wace ce yarinyar nan” Magen ta tambaya, “wace yarinya kenan? ” Sarauniya Jahiyana ta tambaya, “Zinariya?” magen ta tambaya. Sarauniya ta juyo ta ce “Oh! Shi ya sa kika zo nan kenan. To na tsinto ta ne. Kuma na ji a raina ta kwanta min shi yasa na kawo ta nan ” ta faɗa tare da juyowa ta kafe magen da ido, “Mama bazan yarda ta zauna gidan nan ba ” ta faɗa, “zaki aminci Juhaina” sarauniya ta faɗa, daidai lokacin Binajita ta shigo ɗakin. “Ranki ya daɗe  an gama ” Binajita ta faɗa , Hannu Sarauniya Jahiyana ta sa ta karɓi Zinariya, sannan ta juya ta aje ta kan gado, tana faɗin “zaki iya tafiya.”

Magen da Sarauniya ta kira da Juhaina ta ce “Mama taya kike tunanin zata iya rayuwa a inuwa ɗaya da mu?” Sarauniya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce “zan bata ƙarfin da zata iya rayuwa a cikinmu ba tare da ta wahala ba.”

Juhaina ta juya baya cikin tsananin fushi ta maƙe jikinta wuri ɗaya nan take ta rikiɗa zuwa halittar bil’adam, ta wuce ba tare da ta juya ba idonta yana fitar da haske. Girgiza kai kawai sarauniyar tayi.

Jahida na zaune gaban madubi tana kallon fuskarta Juhaina ta shigo cikin ɗakin rai ɓace. Jahida ta zuba ido cikin madubin tana kallon yadda fatar jikin yayarta ta takure duk jijiyoyin jikinta sun fito, “Abar bauta ta taimake ki yaya, ke da Mama ne ko? ” ta faɗa tana juyiwa, Juhaina ta juyar da fuska ta ce “ni bana sonta”, “wace ce wannan ɗin wadda kike fushi ta dalilinta? ” ta tambaya tana kallonta, “ki daina yawan tambaya bana cikin yanayi mai kyau” ta bata amsa, sannan ta faɗa kan gado tana huce  ta ce “DA SAKE”, Jahida ta ce “an bai wa mai kaza kai.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.9 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Zinariya 2 >>

5 thoughts on “Zinariya 1”

  1. Abba Abubakar Yakubu

    Zinariya ta ɗauki saitikuma babu shakka wannan salon zai tafi da tunanin mutane da dama, ba ni kaɗai ba. Nasmah Liman, Allah ya ƙara basira da ɗaukaka. Muna zuba ido a cigaba da zazzago labari!!!

  2. Ibrahim Adam Dan Sarauta

    Maa Shaa Allah

    Labarin

    Zinariya, Juhaina d Jihada ya tafi da Zallar tunanin Dan Sarauta.

    Tabbas da shi za’a ƙarara labarin nan, don ya ƙagu ya ji yadda Jaririya Zinariya za ta kasance watakila ma ta zamo ita ce mai mulkin Masarauta kamar yadda Sarauniyar Masautar ce ta samo ta daji.

    Muna tsumaye.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×