Skip to content
Part 7 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Bakwai

A  al’adar masarautar Gimatuwa suna haɗa bikin mutuwa ne da bikin naɗin sabuwar Sarauniya, saboda haka duk wani wanda ya kwana a masarautar ya bayyana gaban Dustin masarauta, inda suke jana’iza da kuma naɗin sarauta. Juhaina na tsaye daga gefe tana kuka, a ranta tana ƙara jin babu abunda ta tsana kamar Zinariya, saboda ita yau ta rasa Mahaifiyarta. Ruwan madara Juhaina ta ɗauka kamar yadda yake a al’adarsu ƴarka ta farko ke zuba maka ruwan madara, za ta zuba kenan Jamina ta ce “dakata!”, Juhaina ta juyo ta kalli Jamina, Jamina ta tako cikin ɓacin rai ta finciki robar madarar “ba zan bari gurɓattaciya irinki ta kusanci mahaifiyata ba, ke kika kashe ta” Juhaina ta ce “wannan ce ta kashe mana Mahaifiyar, duk wannan abun ya faru ne ta dalilinta ” ta nufi Zinariya tare da kama wuyanta ta ture ta, Jamina ta miƙawa Jahida robar madarar ta ce “ki tsarkake  jikin mama”, karɓar robar tayi ta fara zubawa, sannan Jamina ta yi, da Juhaina tayi yunƙurin zubawa a karo na biyu, Jamina ta hane ta. Saboda haka bata ƙara yunƙurin yin wani abu ba, har aka cika sharuɗɗun wanka. Bayan sun gama aka suturta mata jikinta da tufafi mafi tsada a cikin kayanta, sannan suka zagaye gangar jikinta da itace, suka kunna ashana, sannan mutanen masarautar suka juya kan naɗin sarauta. Duk wanda ya ɗaga tuta a ranar mutuwar Sarauniya shi ne magajinta, saboda haka aka naɗa Zinariya matsayin sabuwar Sarauniya.

Bayan wata ɗaya

Jahida na zaune gaban madubi, Juhaina ta shigo tana numfashi sama-sama ta zauna gefen gado, Jahida ta juyo ta kalle ta, sannan ta juya dan ita har yanzu haushin Juhaina take ji, numfashinta ya ci gaba da yin sama-sama kamar zai ɗauke, sai kuma ta fara tari jini na biyo hannunta, Jahida ta juya ta zuba mata ido tana karantar abunda ya same ta, ta numfasa ta ce “ke dai babu abunda kika sa ma gaba sai zalunci, ai ki mutu kowa ya huta “, Juhaina ta ɗago tana kallon Jahida, Jahida ta ce “e, yanzu ma ai zaluncin ne ya janyo kika sha gubar maciji, zan ga yadda za ki rayuwa”, Juhaina ta dafe ƙirjinta da take ji kamar zai buɗe ya raba kansa gida biyu ta ce “ki zo ki dawo min da ƙarfina yana ƙarewa “, Jahida ta taso abunka da ƴar’uwa, ta durƙusa gabanta tare da dafa tsakiyar kanta ta rufe idonta, ita ma Juhaina ta rufe ido har na tsawon mintuna biyar, Jahida ta buɗe ido da sauri jin ƙarfin baya tafiya, tana buɗe ido suka haɗa ido da Juhaina, “ko kin san dalilin haka, me ya sa ƙarfin baya dawowa gare ki”, “Saboda lokacin mutuwarta ya gabato “Jamina ta faɗa da shigowarta kenan, Jahida ta juya ta kalli Jamina cike da mamaki, Jamina ta gaɗa kai alamar e, Jahida ta ce “kenan kina da alaƙa da wannan ciwon?”, girgiza kai Jamina tayi ta ce “addinina ya haramta min kashe wata halitta ballanta ma ƴar’uwata, ita dai ta san inda ta ɗauko ciwonta”, Jahida ta ce “to ya za mu yi mu taimake ta domin ta samu ƙarfinta ya dawo “, Jamina ta riƙe hannun Juhaina tana murza, sai kuma ta saki ta ce “lokacin ya ƙure mana, dafin ya mamaye jikinta gabaɗaya”, Juhaina ta ce “ina Zinariya? “, Jamina ta ce “kin san inda take ai”, Jahida ta ce “gata nan zuwa ma, na hango ta tafe ” ko rufe baki Jahida ba ta yi ba Zinariya ta shigo ɗakin “Assalamu Alaikum” ta faɗa, Jamina ta ce “wa’alaikumus salamu warahmatullahi wabarakatuhu “, Zinariya ta ƙaasa shigo ɗakin da sauri ƙafarta har tana harɗewa, “me ya same ta?” ta tambaya, Juhaina ta miƙa hannunta ta riƙe hannun Zinariya tana faɗin “nayi yunƙurin kawar da ke, amma duk lokacin da na tunkare ki sai zafi ya dabaibaye min jiki, shi ya sa na hasala na yi yunƙurin kashe wata maciya sai ta sare ni”, Zinariya ta yi murmushi ta ce “Allah ke nan, Ubangiji Allah ne ya ba ni kariya, Alhamdulillahi ya Allah, na gode maka da ka kare ni “, Juhaina ta rufe ido, sannan ta buɗe a hankali dan zuwa yanzu ƙarfinta Gabaɗaya ya ƙare ta kalli Jahida da Jamina ta ce “ku yafe min, bani da sauran lokaci tare da ku, Jahida ki bi Zinariya kamar yadda ƙaramar cikinmu ke yi”,  Juhaina na jin yadda suke koke-koke amma Ina lokaci ya riga ya cika, ba mai iya ba bawa rayuwa, idan wa’adinka ya cika to tabbas ba makawa sai ka tafi, ko ka shirya ko baka shirya ba. Kamar yadda aka yi ma mahaifiyarta haka ita ma aka yi mata.

Mutuwa Juhaina ta taɓa zuciyar Zinariya sosai, saboda haka ta fara zaunar da Jahida tana nuna mata yadda addinin Musulunci yake, babban halarci da zata iya yiwa Marigayiya Mama Sarauniya shi ne ta inganta rayuwar ƴaƴanta akan turbar addinin Islama, dan kar ai haihuwar guzuma, ɗa ƙwace uwa kwance, ita ta mutu ba Shahada, Juhaina ma haka, kuma ita ma Jahida ta ƙare haka, kuma alhamdulillahi da taimako Hibshiyana da ta haɗa su da wata malama, sai Jahida ta kwaɗaitu da addinin Islama.

Zinariya na zaune a ɗakinta tana shiryawa domin zuwa fada, Jahida ta shigo cikin ɗakin, daga madubi ta hango shigowar Jahida, juyawa tayi tana kallonta, “na zo ne nayi miki bushara da na karɓi addinin kalmar shahada, kuma nayi imani da Allah da ranar lahira” Jahida ta faɗa tana murmushi, buɗe baki Zinariya tayi cikin tsananin farinciki ta tashi ta rungume Jahida ta ce “Alhamdulillahi. Allah abun godiya “, sannan ta sake ta cikin farinciki mara misaltuwa, Jahida ta ce “yanzu muka dawo daga gidan malama Faɗima”, Zinariya ta ce “ma sha Allah abu yayi, Allah ya ba mu ikon yi wa addinin Islama hidima “, Jahida ta ce “amin.”

Addinin musulunci ya samu babban rashe a masarauta, dan har makaranta aka ware domin karantarwa. Haka ya ragewa shaiɗanun aljunu ƙarfi, sun rage zalunci. Zinariya ba ta zaune, ba ta tsaye domin ganin addinin musulunci ya kafu.

Kamar kullum Zinariya takan hau mubari tayi kira zuwa ga addini musulunci. Yau ma ita ce tsaye saman mumbari tana kira zuwa ga ƴan cikin masarauta da su yi imani da Allah, su dawo zuwa ga addinin gaskiya, tana cikin jawabi aka fara buga ganga alamar lokacin sallar azahar, dama duk lokacin sallah ya zo sukan buga ganga a masarauta domin ayi kira zuwa masallaci, Zinariya na jin ƙarar gangar ta sauko daga saman munbari, kowa ya juya suka nufi masallaci.

<< Zinariya 6Zinariya 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×