Zango Na Tara - Karshe
Duka masarauta ta cika taƙil da ƴan masarautar Bishtimal da ƴan masarautar Gimatuwa, kowa ya hau kan doki, daga ɓangaren Zinariya kuwa tana tsaye daga gefen dokinta ta sha ado cikin wata doguwar riga ta ƙarfe wadda aka ƙawata da duwatsu masu matuƙar ƙyalli, dafa dokin tayi ta hau, ƴan ayarin Sarauniya Hamiyya wato Sarauniyar Bishtimal suka tunkaro su, Zinariya ta ɗaga takobinta ta ce “Allahu akbar ", nan duk sauran mabiyanta suka ce “Allahu akbar", suka tunkare su ga da ga da, yaƙi ya kaceme tsakaninsu.
Jamina tayi kukan kura ta. . .