Skip to content
Part 9 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Tara – Karshe

Duka masarauta ta cika taƙil da ƴan masarautar Bishtimal da ƴan masarautar Gimatuwa, kowa ya hau kan doki, daga ɓangaren Zinariya kuwa tana tsaye daga gefen dokinta ta sha ado cikin wata doguwar riga ta ƙarfe wadda aka ƙawata da duwatsu masu matuƙar ƙyalli, dafa dokin tayi ta hau, ƴan ayarin Sarauniya Hamiyya wato Sarauniyar Bishtimal suka tunkaro su, Zinariya ta ɗaga takobinta ta ce “Allahu akbar “, nan duk sauran mabiyanta suka ce “Allahu akbar”, suka tunkare su ga da ga da, yaƙi ya kaceme tsakaninsu.

Jamina tayi kukan kura ta cira sama ta tare kibiyar da ke shirin shiga daidai saitin cikin Zinariya, cikin tsanin fushi ta riƙe kibiyar idonta na sakin wani haske mai matuƙar ƙarfi, ta buɗe hannayenta da ke riƙe da kibiyar , nan take kibiyar ta cira sama ta juya tayi saiti daidai da ƙirjin Sarauniya Hamiyya ta nufi ta gadan-gadan.

Sarauniya Hamiyya ta ɗaga takobinta zata kai ma Zaliha ɗaya daga cikin ƴan masarautar Gimatuwa, kawai ta ji shigar kibiya ta ƙirjinta, nan take idonta suka fiffito waje, jini ya fara fitowa daga bikinta, nan take yake ta faɗo ƙasa daga kan dokinta. Wannan ne karo na farko da Sarauniyar masarautar Bishtimal ta faɗi ƙasa, tarihi ya nuna tsawon shekaru dubu biyu da ashirin da biyu kenan da hawanta bisa karagar mulki, amma a duk tsawon shekarun nan ko da launin fatarta ne bai taɓa canzawa ba, a taƙaice ko ciwon farce bata taɓa yi ba, wannan dalilin ne yasa ƴan masarautar suka mayar da ita abar bautarsu.

A ɓangaren Jahida tana zaune gaban madubi ta dafe ƙirjinta, tana faɗin “abunda nake gudu ya faru “, sai kuma ta rufe ido zuciyarta na bugawa, sai wani ƙara daddafe ta take yi, dan yadda take jin tana buguwa, kamar za ta faɗo ƙasa. Jin ihu ya hautsine masarautar tayi saurin buɗe idonta ta sauke su cikin mudubin, ganin yadda aka sare kan ƴan masarautar Gimatuwa ya matuƙar ɗaga mata hankali, su huɗu kawai suka rage a wurin, Zinariya, Jamina, Zaliha, da Zulzul, Taya wannan yaƙin zai yuwu tsakaninsu, bayan a ɓangaren masarautar Gimatuwa su huɗu kawai suka rage cikin Aljanu ɗari da aka ware saura huɗu kawai.

Kukan kura ƴan masarautar Bishtimal suka yi suka ƙara yin cikin su Zinariya suna faɗin “Rayuwarku Fansar zaluncin da kuka ma Sarauniyarmu “, ɗaya daga cikinsu mai suna Altuna ta ɗaga takobi daidai tsakiyar kan Zinariya zata Sara, Jamina tayi iya ƙoƙarinta tayi amfani da ƙarfin sihirinta amma abun ya faskara, duk sun rufe ido, har Zinariya ta cire rai da zata kai, kawai suka ji ihun Altuna ta saki takobinta ta zube ƙasa, Zinariya ta buɗe ido, cikin mamakin ganin Jahida ta juya ta kalli Jamina da ita ma ɗin mamakin duniya ya kamata.

Jahida ta sauke takobin da ta sara ma Altuna, sannan ta buɗe Bakinta ta saki wuta ta musu tsakani da ƴan masarautar Bishtimal, sannan ta kalle su ta ce “ku tsallake wutar nan yanzu zamu fara sabon yaƙi “, hannunta ta miƙar wuƙa guda hudu suka bayyana, ta jefa ma Zinariya ɗaya, ta jefa ma Jamina ɗaya, Zaliha ɗaya, Zulzul ɗaya, sannan ta ɗaga sama, ita ba ba sama ba ita ba ƙasa ba, ta zira hannunta zuwa gefen Jamina ta ce “ƴar’uwa ki dafa ni ƙarfin da kika rasa zai dawo miki “, Jamina ta ɗago ta riƙe hannunta, sannan ta sauke hannunta, ta juya cikin tsananin fushi ta cira sama kamar yadda Jahida tayi, Zaliha da Zulzul ma suka yi kamar yadda suka yi, Zinariya kuma ta tsaya ƙasa riƙe da takobinta, Wutar da Jahida ta ja mu su layi da ita sai ci take yi balbalbal, Ƴan masarautar Bishtimal da tun ɗazu suka juya suna shawara suka juyo suka nufi su Jahida, sunan zuwa daidai inda wutar suka tashi sama sannan suka dire gaban Zinariya, takobin dake hannunta kawai ta ɗaga ta rufe idonta tana juyawa, a haka suka yi nasara kashe duka rundunar masarautar Bishtimal.

Rungume juna Jamina, Zinariya da Jahida suka yi suka ce “Alhamdulillahi “, Zinariya ta ɗago ta kalli Jahida ta ce “dama ashe zaki iya faɗa?”, Jahida tayi murmushi ta ce “ceton rai nayi “, Jamina ta ce “mun gode da kika cece mu, a yau da ba ki zo da an shafe labarinmu daga yau”, Zinariya ta ce “ƙwarai kuwa da gaske, muna godiya da ceton rai da kika yi. Amma ta ya kika san halin da muke ciki? “, “Madubina” Jahida ta faɗa, Zinariya ta ce “Allah abun godiya “, Jamina ta ce “dama kukan da Jahida ke yi kenan, ganin za a kashe ki idan har bata ceci rayuwarki ba”, Zinariya ta ce “kenan ta san haka zai faru “, Jahida ta ce “an nuna min haka a madubi tun ba yau ba, yau saboda rayuwarki na riƙe takobi. Kuma daga yau na fara riƙa takobi kenan har abada”, suka sake rungume juna.

Tun daga wannan ranar, duk wani yaƙi da za a yi Jahida tana shiga. Sun yaƙi masarautu da dama, daga cikin akwai Bishtimal wanda ta kasance masarauta ta farko da ta fara yaƙar su bayan Zinariya ta karɓi sarauta, sai Masarautar Jahimta, sannan Jaznin, sannan Miktibal, sannan masarautar Fikirar da dai sauransu, sun yaƙi masarautu a ƙalla ashirin, sun yi nasara akan masarautu sha shida cikin ashirin. Wannan dalilin yasa aka yi ma Zinariya naɗin sarauta zuwa Sarauniyar Aljanun yankin Briktamal. Wato babban reshe na yankin sarautar Aljanu.

ALHAMDULILLAHI!

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI DA YA BANI IKON KAMMALA LITTAFIN NAN.

<< Zinariya 8

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×