Waziri ya isa Asibitin ya shiga Office ɗin Abdul, Dr Irfaan ya yi masa bayanin duk abin da ke faruwa da Ahmaad ɗin. Bai ɓata lokaci ba ya ɗaga waya ya kira Mai martaba ya faɗa masa halin da ake ciki. Sun jima sosai suna waya da shi, Kafin suka yi Sallama ya dubi Irfaan ya ce, “Ina Likitan da ya zo jiya??” Cikin girmamawa ya ce “Bari na kira shi Ranka ya daɗe.” Ya fice da sauri Ya nufi Emergency Room ɗin inda Doctor Danial yake, suka taho tare zuwa Office ɗin Abdul ɗin. Doctor Danial ɗin. . .