Skip to content
Part 12 of 15 in the Series Zuciya by K_Shitu

Waziri ya isa Asibitin ya shiga Office ɗin Abdul, Dr Irfaan ya yi masa bayanin duk abin da ke faruwa da Ahmaad ɗin. Bai ɓata lokaci ba ya ɗaga waya ya kira Mai martaba ya faɗa masa halin da ake ciki. Sun jima sosai suna waya da shi, Kafin suka yi Sallama ya dubi Irfaan ya ce, “Ina Likitan da ya zo jiya??” Cikin girmamawa ya ce “Bari na kira shi Ranka ya daɗe.” Ya fice da sauri Ya nufi Emergency Room ɗin inda Doctor Danial yake, suka taho tare zuwa Office ɗin Abdul ɗin. Doctor Danial ɗin ya sake yi wa Waziri bayani a kan ciwon Ahmaad ɗin, Daga Ƙarshe suka yanke shawarar fitar da shi Ƙasar Malaysia a ranar suka tattauna da wani babban likita da ke chan wanda ya san Me martaba soaai.

Suna cikin Maganar asibitin da za a kai shi a ƙasar malaysia Abdul ya shigo ɗakin. Yanayin yanda ya shigo yana wata tafiya a hankali, ya sa duk suka zuba mishi ido ko wuni ba a yi ba amma har ya ɗan faɗa. Dr Irfaan ya sanar da shi Abin da waziri ya ce, Ya yi Na’am shi ma da batun Mahaifin nasa. Da kanshi ya ɗaga waya ya kira matuƙan Wani Private Jet ɗin Ahmaad ɗin Ya samu duk suna Cikin Garin Kano ɗin, Nan take Abdul ya tura masa kuɗi, ya ce su ɗauko Jirgin Su haɗu a Airport. Ana fitowa daga Sallar Azahar aka shirya Ahmaad ɗin wanda har lokacin yana a yanda yake. Aka saka shi cikin Ambulance Ammi da Imaan sai Abdul Su ma sun shiga wata mota driver ya ja motar Zuwa Airport ɗin. Dukansu sun yi shiru cikin Motar babu mai magana sun yi jugum-jigum, kowa ka kalla fuskarsa cikinsu za ka hango tsananin damuwa tattare da shi. Har suka Iso Airport ɗin Driver ya yi Parking babu wanda yai ko ƙwakƙwaran motsi, Sai da Drivern ya ce ma Abdul da ke gaban motar, “Ranka ya daɗe mun iso.” Bai ce komai ba sai ajiyar zuciya da ya sauke, kusan a tare su Ammi ma suka ankare suka buɗe motar suka fito. Jerowa suka yi suka sa Ammi tsakiya har bakin Inda jirgin ya tsaya za su hau, suna gani Likitoin Asibitin, suka shigar da shi cikin jirgin sannan suka Ammi da Abdul da Imaan kuma suka yi Sallama da ‘Yan’uwa da abokan arziƙi, su Akarsh da Dr Danial ma duk sun shiga suka tsaya kan Ahmaad ɗin, Aka rufe ƙofofi da Tagogi, jirgin ya fara ɗagawa A hankali.

Suna cikin jirgin har sun fara lulawa ciki Sararin samaniyar, Dr Akarsh da Abdul na ta ƙoƙarin saka masa Oxcygen Suna cikin kiciniyar sanya masa suka ga Murmushi mai kyau kan fuskarsa da kuma zufa sosai a goshinsa, Sai kuma bakinsa da ya ɗan motsa daga nan idanuwansa suka rufe ruf. Cikin murnarsu da tunanin ko ya samu barci ne Suka saki murmushi. Irfaan ne hankalinsa ya gaza kwanciya ya matso sosai Yana kallon Abdul ɗin Kuma ya ga yadda jikinsa ya sake ne Ya ruɗa shi, ya ɗauko Kayan aune-aune ya fara masa, Zuciyarsa ta daina bugawa Ya daina numfashi!

Hannuwansa ban da Kyarma babu abin da suke yi, Ya matsa ya yi wa Dr Danial magana ya matso ya dudduba sa. Sai kawai ya girgiza Kansa. Ya ce Musu ya mutu. Ba shi da aka shaƙe ake ma ihu ba har Matuƙan jirgin sai da suka razana da irin ihun da Abdul ɗin ke yi da Ammi suna sambatu, Irfaan ne ya matsa Idanuwansa na zubar da wasu zafafan hawaye ya ce ma matuƙan idan da hali a koma Kano Allah ya amshi Rayuwar Ahmaad ɗin.

Tamkar Abdul ɗin ya zare ya fara dukan Dr. Danial yana kuka yana sambatu, “Who are you?? Ƙarya kake yi ka ce min Ahmaad ya mutu, i can’t believe it, you are a mad man, i’ll Kill you!!” Imaan ma kukan ta shiga taya su cikin Karayewa da kuma sarewa da al’amarin ta durƙusa gaban Gawar Ahmaad ɗin tana kallonsa hawaye kawai ke zuba daga idanuwanta, Numfashinta na fita da sauri-sauri, ta kasa yarda ma. Audugar da aka sanya aka toshe hancinsa da ke jini da ita ce ta ga ta fara rinewa daga jini zuwa wani baƙin Abu. Cikin su kowa ya ruɗe an kasa samun mai rarrashin Wani Ba wanda ya iya bi ta kan Ammi, Irfaan na kuka idanuwansa sun yi ja fuskarsa ma haka sai jan majina yake, Ya ɗaga waya hannunsa na kyarma ya dannawa waziri kira da Lambar da ya Ba shi bugu biyu ya ɗaga kamar jira yake dama ya ce, “WE LOST HIM..DR AHMAAD ABUBAKAR LAMIƊO IS DIED!!!” Daga Chan Waziri ya saki wayarsa ta faɗi ƙasa ya ji jiri na neman ka da shi, ya faɗa kan kujera yana Ambaton sunayen Allah.

Lokacin da Jirgin ya sauka Airport Irfaan ne kawai yai Ƙarfin Halin fitowa da Akarsh, suka tari Amblance ɗin Asibitin, aka saka su su duka, suka Nufi Gidan Ammi. Kafin ƙarfe uku duk ‘Yan’uwa da abokan arziƙi sun haɗu, a nan gidan ana ta koke-koke har da masu suma, Ammi dai tun da Ta farka take zaune kamar butum-butumi kwata-kwata ta kasa Aikata komai ko motsi ta kasa yi.

Ƙarfe Biyar aka saka za a yi Jana’izar Dr A. Zuwa wannan lokacin Garin Kano ya ɗauka da Mutuwar Dr ɗin, An yi kukan rashinsa sosai. Huɗu da rabi aka gama shirya shi Aka sa shi cikin Mankara daga nan Aka fara kiran Makusantansu su zo su yi masa Addu’a. Hatta Sarkin Kano Sarki Usman Ahmaad Lamiɗo sai da ya zo Gaban gawar Ahmaad ɗin ya yi masa Addu’a sannan ‘Yan’uwa suka fara zuwa suna yin tasu. Tun da Ammi ta zo ta yi sujjada tana karanta addu’o’i kusan mintuna Arba’in ba ta ɗago ba, har An fara ba ta haƙuri ɗago tan da za a yi har ta siƙe. Da ƙyar aka mai da ta wani ɗaki da ke kusa da nata. An yi Jana’izar Ahmaad Abubakar Lamiɗon da Kowa ya fi sani da Dr. A An kai shi makwancinsa, wanda ya samu dubban jama’a na ban mamaki, Haƙiƙa idan ka ga irin mutanen da ya yi Tabbas za ka yi tsananin mamaki har aka rufo shi aka dawo gidan Ammi ba ta san inda kanta yake ba. Imaan ce ke Amsa gaisuwar waɗanda suka dawo daga maƙabarta sai kuma Umma Matar Waziri.

Har Aka yi sadakar Uku Ammi ba ta Um ba ta A’a magana ba ta daina yi kwata-kwata kullum cikin Addu’a take da kuka, ita da Imaan sun rame sosai gwanin ban tausayi ga ba wani makusancinsu, dan Duk dangin Ammin babu wanda ya zo Ita dai Imaan dama ba ta san kowa na Ammin ba shi ya sa ba ta damu ba. Abdul ne kawai ke tare da su, sai kuma Bayi uku da Mai martaba ya aiko musu da su, Kullum nan yake wuni. “Shi ke nan Rayuwa ba Tabbas Yanzu Abdul’aziz ɗana Ahmaad ya mutu??” Abin da Ammi ta faɗa ke nan, dan Sam ta daina magana sai dai ta ɗaga kai ta zuba wa mutum idanuwa. Abdul ya share Hawayen fuskarsa Yana ajiye wayar Ahmaad ɗin. “Ammi ki yi haƙuri dan Allah! Addu’a ya kamata a ci gaba da yi masa. Ni kaina na kasa yarda har yanzu, Mun rasa Ahmaad! Ya ilahi.”

Imaan da ke shigowa Parlourn ta zauna kusa da Abdul ɗin tana matse ƙwalla, duk ta yi sukuku ita ma. Abdul kanshi ko kallo ɗaya ka yi masa za ka fahimci tsan-tsar ramar da ya yi, da Alamun damuwa Tattare da shi. Ammi ta fashe da kuka mai raunata zuciya. “Abdul’aziz Ashe ya riga ya ji a jikinsa zai bar duniyar nan shi ya sa bai damu da duk abin da muka yi masa ba, Wallahi da ace na san Ɗana ba zai yi tsawon rai ba Ubangiji Zai amshi rayuwarsa da ban ƙuntata masa ba, Allah ya sani ba a son raina nake fushi da shi ba sai don lafiyarsa, Ashe shi ya sa ya sallami ma’aikatan gidan nan da albashi Shekara guda.

Tun bayan rasuwar Iyayena da Mijina ban taɓa jin Mutuwar da ta ruɗa ni ta gigita ni ba irin ta Ahmaad, ina ji a jikina ya riga ya san sai wani ikon na ubangiji ko zai rayu, Amma ina sa ran yadda ya ɗauko hanyar ganin bayan waɗanda suke ta kashe-kashen nan da Azzalumai jininsu ba zai ɓata tafiya a banza ba, Na sani ya riga ya yi wannan Alƙawarin da ZUCIYA…” Kuka ne ya ci ƙarfinta sosai ta kasa ƙarasa maganar, shi ma Abdul ɗin kuka yake yi sosai da Imaan an rasa mai Lallashin wani. Sai da ta zuƙe majina sannan ta ci gaba da Faɗin, “A da ban taɓa tunanin Alƙawarin da muka yi na kawo ƙarshen azzulumai zan tafi haka nan ba, Amma yanzu ko da ace ban aikata komai na kuma yi babban rashi ba zan sare ba akwai Ubangiji yana sane da mu, bai manta mu ba! Zuciya! Zuciya!! Kun ce Zuciyarsa ta buga ya mutu Mahaifinsa ma haka, Ya mutu ta dalilin bugawar Zuciya, Shi ke nan duk wani mai kyakkyawar Zuciya ba za a bar shi da ranshi ba?? Amma Abdul’aziz ka faɗa min Ahmaad ɗina ya chan-chanci a wahalar da rayuwarsa kafin a kashe sa Shekaru fiye da Uku yana ƙuntatacciyar Rayuwa daga ƙarshe ya mutu! Ka faɗa min miye laifinsa dan yana da Kyakkyawar Zuciya nagartacciya ya cancanchi a raba shi da wannan duniyar, Shi kaɗai nake da sai Ƙanwarsa haba wane irin rashin Adalci ne, Ni ma ina jin Zuciya..,” Saurin katse ta Abdul ya yi cikin sarƙewar Murya. “Kar ki kice haka Ammi ki yi Addu’a ni kaina na san Ahmaad ya san Abubuwa da dama amma yana riƙe su a Zuciya, Ammi na sani na ɓata masa rai gab da zai rasu a kan rashin sani, tun bayan da ya fita daga ɗakin na ji komai ya chanza mini, ina ta wasu abubuwa tamkar ba ni ne nake sarrafa kaina ba, Ya ubangiji ka sa Mutuwa ta zama hutu a gare sa ya ɗanɗani ƙuncin rayuwa sosai!” Ajiyar zuciyar kukan da ta sha kawai take yi. Wayar Ahmaad da Abdul ya ɗauko ce ta fara Ringing kamar ya share mai kiran dan ya yi tunanin Dubban mutanen da ke kira a kullum suna masa addu’a ne, sai kuma sunan mai kiran ya ja Hankalinsa. Sai kawai ya sa hannu ya ɗaga ya saka wayar Handsfree. Maimakon Sallama ko wani abu sai dariya Da aka fara ba ƙaƙƙautawa marar daɗin ji da murya mai amon sauti sosai. Abdul ya yi shiru bai ce komai sai da mai dariyar ya tsagaita sannan “Abdul ya ce Wa ke magana??” Sai da aka sake darawa kafin cikin Kausasshiyar aka fara magana “Izuwa yanzu na san cewa kun rufe babin Ɗan tsaurin ku ko, Mun gama da shi, Saura Kai muna nan juyowa kanka…Hahhhaha!!!” Kafin ya yi yunƙurin ba da Amsa an datse kiran. Ammi da Imaan da suka gama Sauraron komai suka yi zuru.Ammi ta nisa ta haɗe hannayen biyu alamun roƙo ta ce “Abdul’aziz dan Allah ka fita daga harkarmu, A halin yanzu ba na son na sake yin wani Rashin da zai Tarwatsa komai na, Ina jin Ƙaunarka cikin Zuciyata ban san ya zan yi ba idan har Aka ce ka rasa rayuwarka ba!” Abdul ya saki Wani murmushi mai tsananin ciwo ya ce “Ammi ina farinciki ko da a ce na rasa rayuwata ne, In dai ta dalilinku ne, Alhamdulillah Ubangiji na sane da mu, ban zan taɓa barinku ba In sha Allah sai ranar da na bar Numfashi.” Abdul da kanshi ya shiga Kitchen ya yi girki ya ɗauko magungunan Ammi ya tasa su gaba suka ci su duka sannan ya ce zai fita Asibiti ya dawo.

*****
Kwana biyar ɗin da Nafi ta yi Gidan Hajiya Safeena babu abin da ke mata daɗi komai ya fita daga ranta dan ma Allah ya sa Hajiyar ba ta nan. Yau ma kamar kullum suna zaune A Parlourn Tala. Nafi ta lula duniyar Tunanin Baffanta da kuma Hamma ta sauke ajiyar zuciya lokacin da suka haɗa ido da Tala na ma Hannayenta Kallon ƙurilla wanda take yawan yi mata kwanakin nan. Suna Cikin Kallon TV suka fara jin Ƙarar shigowar motoci, Tala ta ja ta cikin Sauri suka fito Parlourn, Hajjaju ta gani ta fara shigowa sai wasu Manyan Hajiyoyi da Hajiya Safee, Suna ganin Nafi duk suka fara tururuwa wajen Rungumar ta.

Hajiya Safee duk ta riga su ta Rungume Nafi tsam a jikinta kamar za ta maida ita cikin cikinta. Bayan sun ci abinci Mutanen Hajiya su ka tafi ɗakinta dan Chan za su kwana, Ita kuma suka koma suka yi shiri suka kwanta ita da Tala. Har ta fara barci Tala ta tashe ta suka zauna ta fara magana A hankali cikin raɗa. “Kin san me su Hajjaju suka zo yi gidan nan?’ Nafi ta girgiza kai da sauri. Tala ta ci gaba da Magana “So take ta siye ki! tana so ki zama tata gobe za su yi shagalinsu daga nan kuma kin zama Mallakinta! Za ta yi yanda ta ga dama da ke ba ta da shamaki, ko me tuhumarta.” Nafi ta zaro idanuwa a ruɗe bakinta na motsi a hankali ta ce “Dama a binni a saida mutun??” Ta fashe da dariya sosai, Sai da ta yi mai isarta sannan ta ce “Lallai Nafi na sake yarda ke yarinya ce sosai, ai idan kika ji saidawa ɗaya ke nan, ke dai kawai ki kwana cikin shiri gobe, Kuma ki saki jikinki kar ki nuna kin san komai zan taimake ki ki bar Gidan nan duk da Aikata hakan abu ne mai matuƙar wahalar gaske amma zan ƙoƙarta.” Jiki a sanyaye ta kwanta tana jan bargo har kanta.

Ummi ta dubi Bilkisu ta ce ‘Tirr da ke! Gaskiya kin ba ni kunya yanzu kan mutuwar Maƙiyinmu kike damuwa Mts! Ni na rasa ke da Zubaida wa ya fi wani Sakarci da rashin sanin ciwon kai, ku rasa wanda za ku so duniya sai Yarima, ga Hisham nan da Adam masu jiran gado amma duk ba su yi maku ba dan lalaci sai Ahmaad.” “Haba Mammy ya za ki ce haka ni fa ba sakarya ba ce na san me nake yi” Bilkisu ta faɗa cikin ɓacin rai dan su Mammy suke ce ma Ummi. Ta harare ta cike da Rashin mutunci ta ce “Kin yi daidai bari na kira Ubanki sai ki faɗa masa haka, shashashar banza Mts!’ Tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin Hankalinta a tashe. Ta tura ma Galadima saƙo.

*****

Tun da Abdul ya shiga motarsa ya fara tafiya kan titi zuwa Asibitin Dr. A yake jin gabaɗaya duniyar ta yi masa zafi, ya kasa ci gaba da tuƙin da yake yi, ya yi Parking ɗin Motar gefen titi ya duƙar da kansa yana jin ɗaci a ransa. Bai taɓa sa ran zai Rasa Ahmaad nan kusa ba, Ashe ba shi da tsawon rai, Kai ya ma kasa gasgatawa har lokacin Ahmaad ya bar duniya. Ya fesar da huci mai zafi wasu hawaye na bin kuncinsa. Lokaci ɗaya kuma Rayuwarsu ta baya da suka yi shi da Ahmaad ɗin ta soma dawo masa tamkar a wasan kwai-kwayo ya lumshe idanuwansa Yana tunane-tunane. Ya ɓata lokacin a nan ba tare da ya taɓuka komai ba, Da ƙyar ya ja motar ya ƙarasa Asibitin. Ya yi Parking ɗin motar ya fito ya shiga ciki ya nufi hanyar Office ɗinsu, Ya wuce Office ɗin Ahmaad ɗin ya tsaya ya Kalla sannan ya wuce tuna fitar da suka yi ta ƙarshe yake yi. Ya kasa shiga nasa Office ɗin ya nufi na Irfaan duk da ya san ba lallai ba ne ya same sa ba. Ya buɗe Ƙofar a hankali cikin Rashin kuzari ya shiga.

Ga mamakinsa sai ganin Irfaan ɗin ya yi, yana harhaɗa abubuwansa Cikin wata jaka da Alama fita zai yi, Ya yi sallama a hankali suka gaisa tare da yi ma juna ta’aziya Sannan Abdul ya zauna yana faɗin “Lafiya dai Irfaan Ina za ka je ne?” Ya numfasa cikin nuna damuwarsa ya ce “A gaskiya Abdul ba zan iya zaman Hospital ɗin nan ba, Komai ya fice daga raina ina son komawa gida ne.” Ya dafa kafaɗarsa cikin dakiya ya ce “Ka yi haƙuri ka ji! Komai yai farko yana da ƙarshe in Allah ya yarda ka ƙara haƙuri dan Alkah kar ka ce za ka bar asibitin nan” Ya numfasa ya zauna sannan shi ma ya fara magana a hankali, “Wallahi Abdul gabaɗaya zaman Asibitin ya gundure ni ne”. “Ka yi haƙuri duk da haka Dan Allah”. Ya ce “Shi ke nan ba matsala. Ka zauna mana”. Ya zauna ya fuskace sa sosai Sanna ya fara magana, “Na ce Irfaan wai yaushe Akarsh ya tafi ne da Dr Daniel sun yi maka bankwana ba a sallame su ba fa??” Ya yi masa kallo irin na rashin fahimta sannan ya ce “Kana nufin sun tafi ke nan? To ni gaskiya tun washe garin rasuwar ban sake ganin su ba.” Ya kalle sa cike da tsananin mamaki ya ce “Kana nufin ba ka san sun tafi ba sai yanzu da nake faɗa maka?” Ya jinjina kansa don tabbatarwa ya ce “Gaskiya sai yanzu da ka faɗa na sani, amma akwai wata matsala ne?” Ya ɗan zaro idanu ya ce “Hum! tambaya ma kake yi, Wallahi sam hankali bai kwanta da Daniel ɗin nan ba daga baya haka nan nake jin tsanarsu har Akarsh ɗin, kai ba ka ga alamomin rashin gaskiyar da suka bayyana ba tattare da su lokacin da Ahmaad ya rasu??” Irfaan ya sauke numfashi ya ce “Ni kaina tuntuni na dasa musu alamar tambaya, sai dai tun da na ga har kai ka aminta da su ne ya sa kawai na share. Amma ka tabbatar Sun bar Ƙasar nan kuma ka kira layinsa na India da na Nija??” Ya girgiza kansa a hankali ya ce, “Duk na ruɗe ne, ban yi wannan tunanin ba bari na kira shi. Yai saurin riƙe masa hannu da yake ƙoƙarin kiran Akarsh ɗin ya ce, “Ba buƙatar ka kira sa, ka bari mu je gidan Kawai mu ganewa idanunmu.” Ya miƙe tsaye yana faɗin “To mu je ga mota chan a parking lot.” Suka shiga Motar Abdul ya tuƙa su ya ɗauki hanyar Gidan Akarsh. Suka ƙarasa gidan ya yi Parking daga waje suka Yi Knocking ɗin Main Door ɗin amma ba a buɗe ba, sun fi mintuna goma nan ba su haƙura ba, suka ci gaba da bugawar, suna ta jin hayaniya. Maigadin ya buɗe a fusace dan ganin su waye, Ganin Abdul da ya yi da wani ya sa, ya ɗan sassauta fuskarsa ya ce “Sannu Yallaɓai” Abdul ya amsa yana ƙaƙaro murmushi sannan Ya ce, “Dan Akarsh fa yana nan??’ Sai da ya ɗan yi jim kafin ya ce “To ban dai sani ba gaskiya ku dai shiga ku duba. Yallaɓai Ashe abin da ya faru ke nan da Dakta Ahmaad, Duk waɗanda suke da hannu a kan mutuwarsa Allah ya gaggauta tona musu Asiri, Allah kuma ka rabamu da zaluncin nasara! Duk yadda kake ƙaunar kafuri baƙin kafurci ba zai taɓa bari ya ƙaunace ka ba, kullum cikin yunƙurin ganin bayanka zai kasance, Allah ya kunyata su a mika mini ta’aziya ga ‘yan’uwansa”. Da ‘Amin’ Abdul ya amsa suna shiga cikin gidan, Ƙwaƙwalwarsa sai juya maganganun Kamal Maigadi take yi, Ya yi shiru har suka ƙarasa cikin gidan sai dai A mamakinsu suka ji tsit saɓanin da, da suke ta jin hayaniya sosai. Lokaci ɗaya gidan ya yi tsit, suka nufi Main parlourn suka yi, Knocking suka ga ƙofar a buɗe take suka shiga ciki. Shiru Parlourn babu kowa sai dai Waren takalmi da suka gani tsakar parlourn, sai kuma abinci da aka zuzzuba a dinning da ƙamshin girkin da ke tashi an fara ci. Ga kuma Tv kunne amma kan kashe ƙara, sun dudduba ko ina sun ƙwala kiransa amma babu Akarsh babu dalilinsa. Cike da ƙuluwa Abdul ya ɗaga waya ya kira sa, Ringining biyu suka fara jin ƙarar waya, sai kuma suka daina ji, Miscalls Bakwai ya yi masa amma bai ɗaga ba, kawai Abdul ya girgiza kai ya kalli Irfaan suka fice.

Lokacin da suka fito Maigadin bai nan, suka buɗe gate kawai suka fice. Abdul Yana Driving ya kalli gefen titi kaɗan ya ce “Ka san me Irfaan?” Irfaan ya girgiza kai alamar A’ah. “Me ka fahimta, ka kuma gane da zuwanmu Gidan Akarsh!” Yay jim kaɗan kafin ya ce “Kamar yana cikin gidan bai bar ƙasar ba kuma baya son haɗuwa da mu”. Abdul ya ɗan yi murmushi sannan ya fara magana. “Hum! Irfaan. Kafin mu shigo Cikin Parlourn muna magana da Kamal na ji Hayaniya sosai da sautin kiɗa da ke tashi, sannan A Maganganun Kamal ɗin baka hango abin da yake nufi ba, kuma Yanayin Parlourn da yadda yake ka hararo wani abu??” Ya girgiza kai da sauri ya ce “Ka ɗan ƙara mini haske Please kana nufin Akarsh ba ya son ya haɗu da mu shi da Daniel ne??” ya ce “Good Ka fara ɗaukar hanya, Ina zargin Akarsh akan abubuwa da dama, gobe za mu yi magana bari na yi droping ɗinka nan zan shiga Masarauta.” Ya shiga cikin asibitin ya ajiye sa, sannan ya Juya ya ɗauki hanyar masarauta. Tun da ya shiga yay Parking ya fito, mutane da yawa ake ta gaishe shi da yi masa ta’aziyar mutuwar Abokinsa, yana ta amsawa, Ya ɗauki hanyar ɓangaren Waziri mahaifinsa, Ya shiga Parlourn mahaifiyarsa, ta sallami Hadimanta suka gaisa tana ma Ahmaad addu’a. Ya miƙe ya shiga ɗakinsa da ke cikin Parlourn dan ya yi Wanka. Ko mintuna goma bai yi ba da shiga ba, Bilkisu ta faɗo Parlourn mahaifiyarsa tana wani tattauna cingum cike da tsageranci da rashin Kunya. Ta zo ta tsaya kan Mama ta fara surfa mata tijara da tsantsar rashin mutunci har tana jijjiga jiki. “Wai me ya sa kike wasu abubuwa kamar ma ke ce sarauniya matar Sarki Mts! Wallahi idan ba ki kama kanki ba za ki sha mamakin rashin mutuncin da zan miki, sai kawai ki je ki kai ƙara ta wajen Mammy tsabar wulaƙanci Mts…,”.

Ƙarar saukar marin da ta ji da zafinsa ne suka hana ta ƙarasawa, cikin Zafin nama ya ingiza ta ta faɗi. Mama ta yi saurin miƙewa tana faɗin “Hum ai da ka ƙyale ta, ni nan da ta ganni a yanzu daidai nake da kowane shege mai jin kansa na masa tururin tsageranci, Maza ki fice mini dga sashe tun kafin nasa bayi su yi miki korar karya sakaryar banza, shashasha marar Tarbiyya.” Cike da tsananin mamakin da ya kasa barin kan fuskarta ta ce, “Ni kuka maka haka?? Wallahi ku sani sai na tozarta Rayuwarku Ni Bilkisu!!” Ta fice tana sakin wani zazzafan huci da sake jin wata muguwar tsanar Abdul da Mama. Ta nufi Ɓangaren Mammy a fusace. Ko iso ba ta jira an yi mata ba ta faɗa Parlourn tana ƙwala mata kira, “Mammy! Mammy! Kina ina??” Tsabar rufewar da idanuwanta suka yi ba ta ma hango su ita da Galadima ba a Dinning ba. Ta ƙarasa fuu.. Cike da Rashin Tarbiya, “Wai Mammy dama kin san tozarci da za a min ke nan, shi ya sa kika tura ni wajenta?” Galadima ne yay saurin fadin “Calm Down my daughter! I’ll explain everything for yuh so that you’ll understand what i’m trying to do, Please have a seat” “I Cant! Dad you said I should calm down! Do you know what they have done to me she nd her Son?? i can’t even repeat this kind of shameless to anybody, just keep waiting i’ll surely suprise them”. Tana gama faɗar haka ta wuce cikin zafin nama ta faɗa ɗakinta. Mammy ta dubi galadima cike da son jin ƙarshen maganar da suka fara. “Kana faɗin min” ta ce tana gyara zama. “Ai ina tabbatar miki da Ahmaad ya daɗe da mutuwa, Dan kuwa..,” Ta yi saurin faɗin ‘Shh! Ya ɗan yi ‘yar dariya zai yi magana ta yi saurin katse sa. “Wallahi na kasa yarda ya mutu, kullum ina tunanin Asirinmu ne zai tonu, ina jin tsoro sosai fiye da zatonka, na kasa aminta da zance mutuwarsa. Na kasa samun salama kullum cikin fargaba nake da Ruɗani” Ya numfasa ya ce, “Hum! ba ke kaɗai ba Malika Ni kaina haka take ban taɓa tunanin al’amarin zai dame ni ba, Shi ya sa na yanke shawarar bin umurnin …A… mu kawar da Likitocin nan kafin barinsu ƙasar dan Alamominsu sun nuna akwai wani abu da suke shirin aikatawa tun kafin mu kwashi abin kunya. Kin ga bara na je, da dare ma ƙarasa tattaunawar.”

Sai wajen Ƙarfe bakwai na dare sannan Abdul ya ɗauki Hanyar zuwa wajensu Ammi. Ya Parking ɗin motarsa yay Knocking ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga jin door ɗin a buɗe. Zaune ya samu Ammi na karatun Alqur’ani ya ƙarasa yana ɗan murmushi ya zauna. Wayarsa ce ta fara Ringing ya kalli sunan Akarsh yay saurin ɗagawa. “Hello.. Akarsh” Ya fada a hankali. Muryar Wani ya ji ya fara magana. “Ba likita Akarsh ɗin ba ne, Jami’an tsaro ne, Yanzu haka an kashe Ɗayan likita da suke tare, shi kuma yana cikin wani irin yanayi, shi da Maigadin gidansa, Ko za mu iya samun ganinka yanzu.!” Wata irin faɗuwa gabansa ya yi, cikin Rawar murya ya ce “E.” Ya ajiye wayar jikinsa a matuƙar sanyaye. Ammi ce ta dube shi ta ce “Lafiya?” Ya ja numfashi A hankali ya faɗa mata komai. Sosai hankalinta ya tashi ta ce “Innalillahi Wa’inna ilaihi raji’un ka san Nasaran nan ba su da imani azzalumai ne basa ƙaunar musulmi kullum cikin nemanmu da sharri suke yi ba mu yi musu komai ba, ina ga an kashe musu Ɗanƙasarsu Ya ilahi. yanzu tashi ka je da sauri” Ya miƙe cikin kyarmar jiki, sai kuma aka sake kiran wayar, ya ga Private number ya ɗaga ya sa Handsfree dariya aka dinga yi ba ƙaƙautawa sannan aka ce a daƙile. “Ka duba whatsApp ɗinka akwai saƙonmu.’ Yaraf ya faɗa kan kujera yana dafe kai Ammi ta ce ya shiga su gani. Saƙonni na cikin shigowa ya ga wata baƙuwar number an turo masa photo, Yana buɗewa hoton suka ƙura mishi ido. Hoto na farko na Mariganyi Sarki Abubakar Ahmaad Lamiɗo ne, wanda aka yi ticking ɗinsa, sai kuma na Tsohon galadima da ya rasu shi ma aka yi ticking ɗinsa, Na uku kuma Ammi ce ba a yi ticking ba sai kuma Imaan, sannan Ahmaad shi ma an yi ticking, sannan waziri ba a yi ticking ba, sai kuma, Matar sarki ta yanzu Halimatu ba a yi ticking ba, sai kuma na Akarsh da Daniel da aka yi Ticking suma. Hankalinsu ya yi mugun Tashi suka shiga nazarin Hotunan, ba wanda ya iya furta ko da kalma ɗaya ce.


Washe Gari Nafi na cikin Barci Hinde ta tashe ta, ta ce ta shiga ta yi wanka, ta yi, ta ba ta wasu kaya masu kyau ta saka suka fito Parlour dan ba Maganar sallah. Hajiya Safeena da baƙinta duk sun hallara a dinning. Ta gaishe da su suka amsa suna sakar mata murmushi tare da tukwicin kallon ƙurilla da ya saɓa ma addinnin musulci mai cike da zallar Sha’awarta da Kwaɗayinta. Suna gama cin Abinci Hajiya Safee ta ce ma Tala ta sake shirya ta da wuri za su fita Shopping yanzu. Suka koma ɗaki ita da ,Tala, suka shige Toilet tare ta kamo ta ta ce, “Ki natsu ki saurare ni da kyau, karki aikata abinda zai halaka ki mutu Bakiɗaya dan da Alamu aurenki hajiya za ta yi.” Ta raɗa ma Nafi wasu maganganu, sannan ta fito da waya Ta miƙe mata ta ce “ki ɓoye ta har sai kun je, Akwai Ɗansahun da zai ɗauke ki indan kika fito daga Shopping Mall ɗin wanna shi ne hallacin da zan iya miki a matsayinki na mai ƙananun shekaru,”. Ta sake ɗaukar wanka cikin wata Arniyar Gown mai tsananin kyau Army green da veil Milk color sannan ta ba ta takalma da ‘yar purse. Ta fito Parlourn da ita Hajiya Safee har ta shirya. Ta kamo hannunta suka fara takawa har Zuwa Parking Lot ɗin gidan. Ta buɗe wata ƙatuwar mota ƙirar Lexus baƙa siɗik, har glasses ɗin tinted. Ta ja su da mugun gudu Gate man ya buɗe musu ta fara tafiya. Nafi sai kalle-kalle take zuciyarta cike da tsananin tsoro tana ta tunane-tunane har suka iso Bata sani ba, sai da ta ji hannun Hajiyar a jikinta sannan ta yi firgit ta dawo hayyacinta, ta sakar mata wani makirin murmushi ta ce “Nafeesa mun iso fito mu shiga ki zaɓi duk abin da kike so”. Ta ɗaga kai sannan ta buɗe motar suka fito.

Haɗaɗɗiyar S Mall mai kyau ta kawo su, Suka shiga Nafi na ta kalle-kalle irin na ƙauyanci, ta bata Basket ta ce ta jidi duk abin da take so, ita dai haka nan take zagayawa tana ɗaukar abubuwa waɗanda ba ta ma san amfaninsu ba kwata-kwata. Ta shiga jerin inda kayan sawa suke ta ɗauki wata riga ta ce ma Hajiya bari ta gwada, daɗi ya kama hajiyar ta ce to ta mata kwatancen inda ake gwadawar, Tana shiga ɗakin ta kashe fitila ta yarda rigar ta fara kallon ɗakin Ƙofar da ta sake gani ce ta sa ta murɗawa, ta ga banɗaki ne, ta shiga ta yi sauri ta kulle, ta fara leƙen tagar banɗakin, Ta ga wani Ɗansahu daga waje ya yi Parking sai dube-dubae yake, ta gyara yadda zata diro duk da kuwa tsananin tsayin ginin. Amma ta rufe idanuwa kawai babu ko ɗar a ranta ta faɗo ƙasa wajen Shoping Mall ɗin daga baya. Sai kuma ta tsaya tana kallon tsananin Tsayin inda ta faɗo kuma ba abin da ya same ta ko ƙwarzane, ta faɗa cikin Napep ya ja ta da gudu, suka fara tafiya, Sai nishi take yi da sauke Ajiyar zuciya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Zuciya 11Zuciya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×