Gudu sosai Ɗansahun ke yi da Nafi. Lokacin da ta Ankare da ta yarda Wayar da Tala ta ba ta sai ta dafe kai cike da Takaici. Ta maida hankalinta kan Hanyar da suke bi, kamar za a bar garin, hanyar wajen gari ya ɗauka samɓal, ita dai sai zare idanuwa take yi jikinta a sanyaye, Ga manyan gidaje masu kyau da suke ta wucewa amma ko ina tsit. Bakin wani ƙaton gida ya yi Parking, Ya ce, “Yawwa Baiwar Allah, nan ne inda aka ce na kawo ki, za ki sauka.” Ta zaro idanuwa ta ce “Nan kuma. . .