Skip to content
Part 15 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)


Tun da safe da Ammi ta tashi suka shiga Kitchen ita da Imaan suka fara haɗa breakfast mai Aikin su Safiyya na kama musu, Around 8:30 suka gama komai, suka saka A Cooler, ko tsayawa karyawa ba su yi ba suka shiga mota Ammi ta tuƙa su zuwa Police station ɗin da Abdul yake, Su ka gaggaisa da ‘Yansandan da ke Duty sannan aka umurce su da su ci abincin da suka kawo suka ci, sannan aka fito da Abdul suka gaisa da Ammi ta ce Yawwa Abdul ga abinci na kawo maka, amma bari na roƙi DPO mu shiga Office ɗinsa sai ka ci, Aka yi musu iso ya ba su izinin shiga suka shige office ɗin, suka gaisa da Ammi Imaan ma ta gaida shi. Cikin Office ɗin ya ci Abincin Imaan ta tattara Cooler da ta fita ta koma mota. Ammi ta dubi DPO Ta ce “Yallaɓai ya ake ciki?” Ya numfasa sannan ya ce mata, “Hajiya abu mafi dacewa shi ne ku nemi Lawyer dan Abokinsa ma yana nan ya tabbatar mana Shi bai faɗa masa komai ba ya ce masa kawai akwai matsala ya zo gidan Akarsh da Police.” Ammi ta ce, “Hum! to idan haka ne Su ‘Yansandan ce mishi aka yi shashashu ne da zai kira su haka nan for no reason wallahi tun da ya ce haka na dasa masa alamar tambaya, Abdul’aziz ban taɓa tunanin Irfaan haka yake ba.” “Ni ma abin da Na yi tunani ke nan, kuma bayanin da ya min ya sha bamban da abin da ya faɗa wa Police ɗin da suka je gidan ya ce musu akwai matsala An Kashe Dr Akarsh wani likita aminin Dr Ahmaad Abubkar Ahmaad Lamiɗo da ya zo daga India.” Cewar DPO ya sake Faɗin, “Ranki ya daɗe ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda, da mun gama bincikenmu za mu sallama Case ɗin kotu, kawai ku samu ƙwararren lawyer da zai tsaya muku, dan na hango alamomin rashin gaskiya tattare da shi Abokin nasa.” “Shi ke nan na gode In sha Allah za mu san abin yi” Da haka Ammi ta yi Sallama da Abdul tana sake jera masa addu’o’i.

Har za ta fita ya yi mata magana ta tsaya ya ce “Ammi dan Allah ki min alfarma ki je Asibitinmu nan aka kwantar da Akarsh ki nemi bayanai a gunsa na allurar da aka ma Ahmaad da kuma wanda ya ziyarce su ki nemi Dr Saleem”.

Ta yi murmushi ta ce, “Ka wuce Neman alfarma wajena Abdul’aziz, in sha Allah chan zan wuce daga nan,” Ta sami imaan cikin mota suka bar Police station ɗin suka Nufi Asibitin Dr A. Ta shigo da motar cikin asibitin ta yi Parking suka fito tare da Imaan a dubi imaan ta ce, “Auta ke kika san kan asibitin nan da likitocin ciki, kin san inda zan ga Dr Saleem?” Ta yi Jim alamun tunani sai kuma ta ce, E, Mu je office ɗin sa na ƙasan benen na su Yaya Abdul. Suka shiga cikin asibitin har Admin Block ɗin, Ta nuna mata Office ɗin suka yi Knocking daga ciki ya bada izinin shiga, Ta tura ƙofar da sallama Ammi ta fara shiga, ita ma Imaan ɗin ta shiga.

Ya sallami Patient ɗin da ta shigo, yana ganin su Ammi ya faɗaɗa fara’arsa cikin girmamaw ya gaishe ta, Imaan ma ta gaida shi. Suka yi shiru, Ammi ta ce “Saleem wajenka na zo, Abdul’aziz ne ya ce Ka haɗa ni da Akarsh dan Allah” Cike da girmama zancenta ya ce, “To Ammi in sha Allah, Bari na kai ku inda yake amma da ƙyar idan zai iya magana, Dr Daniel kuma yana matury .’Yan’uwansa sun san da zancen mutuwarsa ne, Ƙaninsa ya kira ni yau da safe na ce, bana asibitin na yi tafiya wai sun kira wayarsa baya ɗagawa hakan ya sa suka tabbata yana Nigeria”.

Ta yi shiru tana tunanin mece ce mafita ta dai san halin Turawa ba su ɗaukar ƙaddara wane mataki za su ɗauka shi ne matsalar. Jiki a sanyaye ta ce, “Kai na rasa yanda zan yi baki ɗaya amma za mu yi magana da Abdul’aziz ko me ke nan zan faɗa maka Imaan ki amshi Numbernsa.” Ya amsa yana miƙewa suka fice zuwa Wani ɓangare da ya kasance VIP cikin Asibitin. Ɗakunan ne masu kyau sosai da Banɗakuna a ciki, An ƙawata Wajen da glasses masu kyau ga Cameras na naɗar komai duk mai shiga da fita inda dai aka ajiye Ahmaad lokacin da aka kawo shi daga sashen Hajja daga masarauta.

Tura wata ƙofa Saleem ɗin ya yi, ya sa mukulli ya buɗe, sannan suka shiga ciki, wata ƙofa ce still, ya saka Wasu lambobi ta buɗe suka shiga cikin ɗakin ya maida ya kulle, Ɗakin akwai ɗumi sosai, ga kuma na’urorin da aka sanya masa suna ƙara kaɗan da oxcygen, yana kwance kan godon marasa lafiya ga ƙarin ruwa an saka masa sai dai Mutum ba zai iya gane idanuwansa buɗe, daga gefen gadon Kayan marmari ne ajiye da kuma flask ɗin ruwa sai takalma da kuma kujerun zama. Ya ce Ammi ga shi nan, ba zai iya magana mai tsawo ba kuma muryarsa ba ta fita da kyau. Ta jinjina kai ta zauna bisa kujera tana kallonsa, Ta fara masa sannu ta rasa ta yanda za ta fara tambayarsa, Ta yi ƙarfin halin fara magana da harshen turanci, “Ni Mahaifiyar Dr Ahmaad ce, Dr zan iya sanin wace allura ce kuka yi masa bayan maganin da aka ba shi wadda kuka ce ita kaɗai za a masa?” Ya fara ƙoƙarin magana hannayensa na motsawa, da ƙyar suka jiyo muryarsa “M…`dl” maganar ta yanke, na’urorin su ka ci gaba da ƙara. Saleem ya matso da sauri ya fito da ɗan ƙaramin littafi ya rubuta harufan da ya furta, -M…dl- Sannan ya ce “Ammi ya kamata ku bar shi, dan maganar ma da kuka ji ya yi Allah ne ya nufa kawai dan mu kanmu bamu zaci zai rayu ba, kuma har zai iya farfaɗowa ba da wuri ba, Idan ya sake yunƙurin magana ko wani abu akwai matsala, zan bincika sosai da waɗannan kalmomin da ya furta, dan Ni kaina ban manta Yadda allurar take ba, sunan ne ban sani ba”. Ta jinjina kai tana sa mishi albarka, suka fito daga Wajen gabaɗaya. Har Inda suka ajiye mota ya raka su, Imaan ta amshi numbernsa suka yi sallama, sa niyar ko me ke nan zai zo har gida ya yi mata Bayani..

Duk irin yanda mutum ke tunanin Mayyar hatsabibiya ce ta wuce nan, Tana ta kashe ƙananun yara, babu wanda yake da halin matsawa daga Rugar domin kashe shi za ta yi, sun rasa mai suka aikata mata ta ke kashe-kashen nan. Shi kanshi malam Iron yana tsananin taka tsan-tsan da ita saboda matarshi hawwa da ke ɗauke da ƙaramin ciki. Yana zaman-zamanshi Lohaj mayyar ta farmake sa, ya kasa jurewa da haƙuri, Domin Har da matarsa Hawwa abin ya shafa, duk yanda ya so haƙura ya kasa zuciya ta ɗebe sa, ya fara gwada wani baƙin magani, amma maganin akwai tsafi ciki dan ya saɓa ma dokar Addinin musulunci. Daga wannan lokacin ne suka fara Takun saƙa da Lohaj Daga ƙarshe har kashe jaririn da matarsa Hure ta haifa ta yi, Ransa ya ɓaci sosai sai dai Bai ɗauki wani mataki ba face ƙaura da yay aka daina jin sa kwata-kwata babu wanda ya san yana cikin Rugar Fago ne ko ya yi balaguro.

Rana tsaka ya dawo cikin rugar da wani maciji, Maigari ya sa aka tara mutanen Fago ƙwansu da ƙwarƙwatarsu. Malam Iro ya zo ya tsaya ya fara wasu abubuwa irin na tsafi, ya buga macijinsa ƙasa, Sai ga Lohaj ta bayyana durƙushe, Yana ganin haka ya ɗebo wata baƙar hoda ya watsa mata, ta fara ihu, su dai Mutanen babu mai ganin ta domin a ainahin sufarta take sai ihu da suke ji mai amon sauti, Hawwa matar malam Iro ita kaɗai ce Allah ya ba ikon ganinta. Gabaɗaya Fulanin sun gama tsorata sosai dan da Ace wani ne ya faɗa musu abin da ya faru sam ba za su iya aminta da shi ba ko waye ma kuma ba za su sake ganin ƙimarsa ba za su ci gaba da ɗaukarsa Shahararren maƙaryaci mai lasisi, sai ga shi suna ganin abin da Malam iron ke yi da idanuwansu. Ya ci gaba da Watsa mata hodar yana Karanto wasu irin Ɗalasimai. Daga nan jikinta ya fara rugurgutsewa kamar ƙasa ƙafafuwanta suka gama narkewa suka zama ƙasa, ta yunƙura duk da irin illar da ya yi mata ta feso masa yawunta, a idanu. Ta fara magana cikin muryarta marar daɗin sauraro… “Ka janyo ma kanka bala’in duniya! Ni Lohaj za ka raba da wannan duniyar, Sai na dawo ɗaukar fansa! Saina ruguza rayuwarka kamar yanda ka ruguza ni!!” Za ta ci gaba da magana ya sake sakar mata macijin a jikinta, Dukanta ta zama baƙar ƙasa, Aka tattara cikin wani tulu aka yi rabi aka binne.

Har Bayan Kwana biyu Hankalin Fulanin bai kwanta ba duk da sun mugun samun sauƙi suna ɗan fitowa rafi da kasuwa, Amma kowa ya tsorata da maganart da ta yi, da kuma al’amarin malam iro da irin ƙarfin halinsa abin Kamar wasa ya kashe Lohaj sun jinjina masa sosai, ko ina ya samu Ƙarfin tsafi haka shi ne ba su sani ba, kuma kowa ya yi gum da bakinsa. Tun daga lokacin da Lohaj ta feso masa yawu a idanuwansa bai sake gani sosai ba, Ya yi magani abin ya ƙi ci, Sihirin da ya yi amfani da shi kuma ba zai iya zama mallakin nakasasshe ba. Hakan ya sa yay haƙuri su ka ci gaba da rayuwarsu. Hure Macce marar halaye masu kyau tana da baƙin ciki sosai da hasaada uwa uba tsananin son abin duniya da kwaɗayi da kuma Zalunci, ba ta dw maƙiyiya irin Hawwa amma ba ta taɓa nuna hakan ba saboda tsananin Shakkar Hawwar da tale bala’in ji ko haɗa idanu ba ta iya yi da ita tun bayan da aka kawo ta ranar farko idanunsu suka sarƙe da na juna, Sai da ta yi wata tana fama da bala’in ciwon idanu sun yi jajir sosai ta je wajen wani Malam Sama’ila ya tabbatar mata ta kallo ma kanta abin da ya fi ƙarfin rayuwarta ne kuma ta yi sa’a ba ta makance ba, ta haɗa Idanuwanta da na wani jinsi da ba na ‘Yan’Adam ba.

Ta nemi ƙari bayani ya dakatar da ita da faɗin tattaunawar da suke yi yanzu haka ana jin su, da haka ne ta shiga taitayinta ta sake tsorata sosai da Hawwa dan tunaninta ya fi karkata kan Kallon hawwa da ta yi ne, dan ita kanta ta gigita da kalar ƙwayar idanuwanta Golden ne kuma tsoro da fargaba sun hana ta bayyana ma kowa tana dai kiyaye kanta daga kallon ta. Haka suka ci gaba da rayuwa da daɗi ba daɗi, dan Malam iro ba mai wadata ba ne sam, amma tun da ya Auro Hawwa ya zamana ya fi kowa Arziƙi a rugarsu kaf, kuma yana taimako sosai shi da Hawwar bakin gwargwado, Hure dai ce ba ta sana’a amma Malam iro na ƙoƙari wajen ɗauke mata nauyi, Kuma yana ƙaunar Hassatu sosai ‘yar Shekaru Huɗu.

Bayan Kwana Biyu.
Abdul da Irfaan suna cikin Cell ɗaya da aka sa su, tun bayan da aka kawo Irfaan shi ma ya daina ma Abdul ɗin magana kwata-kwata, kullum sai yayi kuka, Ƙanwarshi ta rasu tun ranar da aka kawo shi amma ya yi bakin ƙoƙari ya koma gida ayi Jana’izarta da shi amma an hana shi, kullum cikin kuka yake. Ya matso kusa da Abdul yana share hawayen fuskarsa Ya fara magana cikin rawar murya, “Dan Allah Abdul ku yafe mini na san ba zan rayu ba, Na ci amanarku amma ba laifina ba ne tursasa ni aka yi, aka ruɗe ni da wasu irin kuɗaɗe, daga ƙarshe kuma sun ci amanata Sun kashe Daniel da Ahmaad sun kashe mini ƙanwata na ji na tsani kaina bisa Butulci da na muku, na ci amnar Ahmaad..,”

Ya fashe da kuka Abdul ya yi mugun tsorata saboda tsananin mamaki Bakinsa har kyarma yake ya jera masa tambayoyi,“Cin amana kuma kai Irfaan! Su waye suka kashe Ahmaad ɗin kana nufin ka san wani abu ke nan??” Ya buɗe baki da Ƙyar ya ce, “Ban san wace Allura ba ce suka saka na karɓo ba amma tabbas ita ce silar mutuwar Ahmaad da mahaifinsa! Abdul dan Allah ka nema mini Afuwa wajen Mahaifiyar Ahmaad na san na ci amanarsu kaicona, Ni tawa ta ƙare ina da tabbacin ba zan rayu ba sun tabbatar mini duk ranar da bakina ya yi kuskuren bayyana ma wani abin da su ka aikata ko da wasa ba zan rayu ba” Hawaye na bin Fuskar Abdul ya ce, “Kai kuma Irfaan Why??” Cikin muryar kuka ya ce, “Tilasta min suka yi, kuma suka min barazana da Mahaifina da K’annena ‘yan biyu, sun Kashe Amra saura Amaal..” Cikin sauri Abdul ya ce, “Su waye ka faɗa mini Dan Allah ka fad’a min Irfaan” Ya buɗi baki ya ce, “Ban sani ba Abdul, amma wanda ya ba ni Allurar ogansu ne ya shiga Nigeria ba nan ƙasar yake zaune ba India yake, shi ma Akwai wani Babbansu, Duk waɗannan bayanan na same su ne ranar da Ahmaad ya rasu, tun daga ranar na yi nadama, sai dai Shi wataƙila ka san shi sunanshi Ab..,.”

Maƙoshinsa ya sarƙe, ya riƙe wuyansa yana wani irin kakari kamar zai shiɗe yana son yin magana ya kasa. Abdul ya fara jijjiga sa yana kururuwar faɗin, “Please Irfaan wake up say something..” Hawaye sun gama wanke masa Fuska. Idanuwan Irfaan ya ga suna chanza kala daga ja zuwa baƙaƙe. Ya kuma ihu, Police ɗin da suke nan suka matso da saurin ganin akwai haske ga kuma abin da ke faruwa ne ya sa Inspector Sada garzayawa Office ɗin DPO ya faɗa masa abin da ke faruwa. Aka buɗe su, aka fito da Irfaan sai hawaye yake Ransa duk a jagule, Yana gani aka tafi da Irfaan asibiti, DPO ya tambaye sa duk abin da ya faru ya faɗa masa. Ya sake nutsuwa sannan ya ce, “Abdul’aziz ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu mun gama tattara dukkan bayanai akan mutuwar Drn Za mu miƙa case ɗin kotu, sannan Hajiya Asiya (Ammi) Za ta zo da Lawyer anjima, idan an samu yanda ake so zai iya Beilling ɗinka, sai Monday a zauna kotu, Amma ka yi ƙoƙari idan ka fita ka sanar da Mahaifinka waziri abin da ke faruwa dan Zai iya bada gudummuwa.”

Ya amsa masa sannan Aka maida shi Cell. Yana zaune ya yi jigum tunanin duniya kawai yake da tsoro Mutane da ya ɗarsu a ransa.

<< Zuciya 14

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×