Tsabar jin daɗi da ya yi musu yawa barci Nafi kanta ta fara ji, ta Kalli Hinde ta marairaice fuska cikin harshen Fillaci ta ce “Hinde barci” Hinde za ta yi magana Hajjaju ta buɗe ƙofa ta shigo, ta kalli Nafi tana murmushi ta ce, “Abincin ya ishe ku Nafeesa?” Sunne kai ƙasa Nafi ta yi ta amsa. “Good! Hinde Na sa an gyara muku ɗakin ki ku je ku yi wanka ku kwanta idan kuna buƙatar wani abu ku faɗa wa Asma'u za ta kawo muku”. Bakinta a washe ta ce “Hajjaju mun gode. . .
Mungode Allah