Skip to content
Part 5 of 15 in the Series Zuciya by K_Shitu

Tsabar jin daɗi da ya yi musu yawa barci Nafi kanta ta fara ji, ta Kalli Hinde ta marairaice fuska cikin harshen Fillaci ta ce “Hinde barci” Hinde za ta yi magana Hajjaju ta buɗe ƙofa ta shigo, ta kalli Nafi tana murmushi ta ce, “Abincin ya ishe ku Nafeesa?” Sunne kai ƙasa Nafi ta yi ta amsa. “Good! Hinde Na sa an gyara muku ɗakin ki ku je ku yi wanka ku kwanta idan kuna buƙatar wani abu ku faɗa wa Asma’u za ta kawo muku”. Bakinta a washe ta ce “Hajjaju mun gode ƙwarai Allah Ya biya”.

Suka miƙe ita da Nafi suka bar ɗakin, daga ƙasan benen hannun dama jerin ɗakuna ne masu kyau sosai da lambobi, na biyun ƙarshen Hinde ta buɗe suka shiga.

Lumshe idanuwa kawai Nafi ke yi saboda sanyin da ta ji. Ɗakin Ciki da Parlour ne me kyau sai Banɗaki. Ƙuryar Hinde ta ce su shiga, zuwa lokacin Nafi ta ma manta da wata damuwa burinta kawai ta kwanta.

Ƙaton gado ne me kyau sosai cikin ƙuryar sai kujera ɗaya da dress mirrow da bedsides masu kyau, Hinde ta nuna Mata gadon ta ce ta kwanta. Ta kwanta ta yi ɗai-ɗaya ta baje sosai, ta ji wani mugun taushin gadon ga ƙamshi me daɗi da ke tashi ko ina, sai Barcin da take ji ma ya sake cika idanuwanta ta yi hamma ta kwanta tana latsa katifar tana dariya ƙasa-ƙasa. Sai da Barci ya ɗauke ta sannan Hinde ta fito daga wanka ta rufe ta da bargo ta gyara mata kwanciya.

Zaune Dr A yake a office ɗin shi, yana wani aiki, ba neman izini ko wani abu Abdul ya faɗo yana masa faɗa, “Yanzu wai daga Noor ta kira ni shi ne za ka tafi office ka kyale ni, kuma na faɗi maka Akarsh ya ce kar mu daɗe mu same shi amma ka yi tafowarka ka yi daidai.” Yamutse fuskarsa ya yi, ya harare sa, ya nuna masa ƙofa da hannu alamun ya bar masa office ɗinsa. Bai kula shi ba ya zauna yana faɗin, “Za mu iya tafiya wajen Akarsh din yanzu?” Ɗaga masa kai kawai ya yi, dan kwata-kwata ba ya son yin magana yau.

Tare suka fice daga office ɗin Suka nufi Parking lot ɗin asibitin, Dr ya buɗe ƙofar ya zauna seat ɗin driver shi ma Abdul ya shigo, ya ja motar a hankali suka fice daga asibitin.

Cikin nutsuwa yake driving ɗin, a hankali kuma cikin ƙosawa da shirun Abdul ya ce “ni fa bakina ciwo yake min idan ban yi surutu ba”. Yanayin yadda ya yi maganar dan ya sanya shi dariya ne ya sanya shi sakin murmushi ya kalle shi kaɗan ya ci gaba da tuƙi bai tanka masa ba.

“Ni kau doctor na tambaye ka man?” Abdul ɗin ya sake faɗi yana ƙunshe dariya “Ina jin ka” ya faɗa ƙasa-ƙasa, Abdul ya ce, doctor wai kallon mace kake mini ko namiji?” Duk yadda ya so ya ƙi dariya sai da ya murmusa sosai har haƙoransa suka bayyana masu kyau. Ya ce “Baby girl.” Dariya Abdul ɗin fashe da ita yana ta ƙyalƙyatawa cike da shaƙiyanci ya sake tambayarsa “Oh! Really?” Ya gyaɗa masa kai daidai yana karyo kwanar da za ta sada su da layin da Akarsh ɗin yake zaune. Ya yi parking ƙofar gidan alamun ba shi da ra’ayin shiga ciki. Suka fito tare suka ƙwanƙwansa, Maigadi ya buɗe musu suka gaisa, ya bar suka shiga dan ya san su. Knocking ɗin ƙofar Parlourn suka yi, Akarsh ya taso fuskarsa cike da fara’a ya buɗe musu, suka yi hugging ɗin juna suna barkwanci shi dai Dr A iyakarsa murmushi bai tanka ba sai Abdul da ke ta amsa wa Akarsh barkwancin da yake jan su da shi.

Sai da suka nutsu sannan ya Maido hankalinsa kan Dr A ya yi gyaran murya ya fara masa magana cikin harshen turanci. “Dr! Abdul ya faɗa min ka chanza ra’ayi baka son aikin, anya kana lafiya doctor?” Sai da ya fesar da numfashi da ƙyar sannan ya jinjina masa kai, cikin kamilalliyar muryarsa ma’abociyar nutsuwa ya ba shi amsa a taƙaice. “Yeah! Akarsh I don’t need it anymore now, Thank you for your kindness I truly appreciate”.

Tagumi Abdul ya yi ya zuba masa idanuwa kamar zai yi kuka, Yana matuƙar jin tausayinsa, Komai na rayuwar Ahmad Baya yinsa cikin jin daɗi rayuwar ƙunci yake ba kamar da ba. Akarsh ne ya yi ƙarfin halin faɗin “But Dr What about your Mom ka son zata damu sosai ka yi tunani lokaci na kurewa wannan damar ba ta wasa ba ce.” Yanda ya ƙarashe maganar Yana haɗa hannayensa alamun roƙo da murmushi kan fuskarsa ne sake narkar musu da zuciya. Ya sauke numfashi a hankali ya ce “ko yanzu na rasa rayuwata ba zan ta’ba mantawa da karamcinku ba, Sai dai ku yi haƙuri Ƙaddara da na nata tsarin haka Allah ya so rayuwata ta kasance. Thank you, thank you There’s no words in this world to thank you! may Almighty Allah reward you”. Yana gama faɗar haka ya miƙe a nutse ya ruƙo Abdul shi ma ya tashi, alamun ba zai sake magana ba, jiki a sanyaye Abdul ya yi wa Akarsh ɗin Sallama suka fice.

Driving ɗin ma Abdul ke yi, gabaɗaya Jikin Abdul ɗin ya gama yin sanyi, wannan karon ya karaya sosai da Al’amarin Dr muryarsa na rawa ya tambaye sa, “Ina za mu je?” Ya kalli titin kadan ya ce “Gida daga nan gurin su Baba”. Ya gyaɗa masa kai suka nufi Gidansu Dr. Ya yi Parking ya tsaya ciki motar ya shiga sharp-sharp ya ɗauko jaka ya fito. Wata sabuwar Unguwa me kyau suka shigo sai da suka shiga ciki sosai sannan ya yi horn bakin wani ƙaton gate ɗin wani gida me dogayen katangu da ƙaton gate me faɗi, Securities ne suka buɗe suka shigo Kasancewar an san su, kuma suna respecting ɗinsu duk da har lokacin ba su san gidan na Ahmad ba ne, Ya yi Parking suka fito. Gidan marayu ne me kyau da tsari bakin gwargado manya da yaran marayun suna samun wadatar da ilimin boko da na addini. Ma’aikatan da ke kai-kawo harabar Parking space ɗin ne suka fara gaishe da Dr da Abdul cike da girmamawa. Securities huɗu ne suka biyo bayansu suna take musu baya, har zuwa ciki inda aka yi musu gine-gine masu kyau na gurin cin abinci, inda ake ɗaukar karatu da clinic da sauransu. Ƙanan Yaran da ke wasa ne suka lura da Dr suka rugo da gudu suka rungume shi suna murnar ganin shi, yana murnushi ya ɗaga ɗaya daga cikinsu sama yana masa wasa, sai dariyar murna suke ta yi suna ƙanƙame shi.

Ya ajiye yaron yana shafa kansa, suka haɗa baki suna gaida shi, “Uncle A ina kwana” ya sakar musu murmushi kamar Yanda ya saba alamun amsawa. Biyo shi yaran suka yi har kan kujerar da ya zauna, ya bada Jakar Abdul da securities ɗin suka Shiga suna rarraba kuɗi, sai addu’o’i ake masa da Abdul sai da suka jima, shi kuma yana tare da ƙananun yara suna mi shi fira sannan suka miƙe sua nufi ciki ɓangaren ɗakunan Maza tsofaffi marasa ƙarfi.

Ya buɗe ƙofar wani tsoho suka yi sallama suka shiga, yana jin muryar su ya washe haƙora yana faɗin “Abdul tare kuke da mutumina ne ko muryarsa ce ke mini gizo?” Abdul bai ba shi amsa ba sai murmushi da yake yi, Dr ya matsa dab da shi, sai tsohon ya ɗauki sandarsa ya ɗan dake shi kaɗan ya yi ihu marar sauti “ai na san kai ne dama so kake ka hawalar da ni ne”.

Ya kwantar da kansa kan jikin tsohon yana lullumshe idanuwa, ya ce “Haƙuri!” kicin-kicin da fuska tsohon ya yi ya ce, “Ba za ayi ba.”Ya kama kunnuwansa ya marairaice, sai da tsohon ya ja hancinsa sannan ya ce “Me yake damunka ne kwana biyu Ahmadu ka daina leko mu, ka bar ni da kewarka”. Ya yi Ɗan murmushi yana gyara kwanciyarsa, tsohon bai ji haushi ba dan ya saba da halinsa. Sai da suka jima sosai a gidan sannan Abdul ya maido su masarauta.


Hinde ce ta fara tashi ta yi alwala tai sallah sannan ta fara tada Nafi. Sai kiran sunanta take yi amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi ba, ta buga pillown da take kwance kai da ƙarfi, ta tashi tana murza ido tana jan ƙananun tsaki. A masifance Hinde ta ce “Nafi Dan uwarki ni kike ma tsoki?” Sai lokacin ta wartsake ta yi saurin girgiza kai tana faɗin “Ban shan ke ce ba” “Dalla tashi ki je ki yi Alwalla ki sallah har gari ya fara wayewa.”

Ta miƙe Hinden na gaba tana binta suka shiga banɗakin, Nafi cikin ranta sai haushin Hinden take ji kamar ta shaƙe ta. Ta nuna mata yadda za ta yi komai ta fito ta bar ta.

Nafi na ganin ta fita ta ja tsoki ta samu kujerar da ke gaban madubin toilet ɗin ta yi zamanta ta ci gaba da rama barcin da ba ta samun yi. Shiru-shiru Hinde ta ji ta har ta je Kitchen wurin Ma’u ta dawo, tana gama fere doya ta nufo ɗakin tana ƙwala mata kira, “Nafi! Nafi…” Cikin barci ta ji kiran sunan cikin kanta saboda ta sa abun a ranta, ta yi firgit ta tashi ta datse ƙofar ta fara wanke fuska cikin sauri ta yi tsaka-tsami ta fito ta waske kamar ba daga barci ta tashi ba. Hinde ta gani riƙe da ƙugu alamun ta murɗa ƙofar ta ƙi buɗuwa, ta sunne kai ƙasa ta raɓa ta ta wuce, kallonta kawai Hinde ke yi, tana aika mata da harara, “yanzu haka ba ki yi sallar ba kina chan kina aikin naki mts! Ni fa dama dan ki zama me sa a shi ya sa na ce ki yi lallai ashe har kin ma iya wanke fuska iye! Dan ni ma ba wani damuna ta yi ba, tashi mu je Kitchen mu taya Ma’u ki ga yadda ake aiki”.

Ba haka Nafi ta so ba, so ta yi ta bar ta, ta huta wahalar jikinta ba ta gama ba.

Ta miƙe sum-sum ta bi ta. Parlourn ba haske sosai dan Mutanen gidan ba su tashi ba, suka nufi ɓangaren haggu inda kitchen ɗin yake suka shiga, ƙamshin girkin Ma’u da wani Kuku namiji sai shiga hancin Nafi yake tana ta haɗe yawu ta gaishe da Ma’u ta amsa Hinde ta shiga taya su, ita kuma ta yi tsaye, tana ta bin su da Kallo. Ma’un ce ta ga yanda Nafi ke ta kallonsu kamar ta cinye su ta ce “baƙuwa sai da Hinde ta taso ki ai da ta bar ki kin huta, ko za a zuba miki abin da aka gama ki je ki ci?” Kamar jira take ta ɗaga mata kai, Hinde sai harararta take amma ko ta kanta ba ta bi ba, Ma’u ta zubo mata Chips da sauce ta fice ta koma ɗaki, bisa Kujera ta zauna cikin ɗan madaidaicin parlourn ta sa hannu ta fara ci ta ji mugun daɗi ta cinye tas ta koma suɗe yatsunta. Ita kaɗai kawai ta tuntsure da dariya har da riƙe ciki, ta yi sauri kamar an tsikare ta ta fito saɗaf-saɗaf ta dawo Main Parlourn ƙofofin ɗakuna ta gani jere masu kyau madaidaita kamar nasu, ta bi ta fara bubbuga musu da ƙarfi kamar zata ɓalla, ta kwasa da gudu ta koma nasu ɗakin tana murmushin mugunta.

Mazauna ɗakunan ne suka fara tashi a fusace suna tunanin wane ɗan rainin wayaun ne zai musu wannan bugun haukan wasu kuwa har lokacin ba su tashi ba, cikin sauri Hinde ta baro kitchen ɗin ta shigo ɗakin jikinta har rawa yake, ta ƙarasa inda Nafi ke zaune tana lasar kwano kamar ba ta san komi ba. “Wa ya ce ki buga ma mutane ƙofa wai anya kina da hankali? Wallahi masu ɗakunan nan sun fi ki bala’i” Ta marairaice fuska tana nuna kanta cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce “wace kofa kuma? na rantse ni ban ma fita ba tun da na dawo” Ta tsare ta da idanu tana faɗin, “Kin tabbata?” ta ɗaga mata kai alamun ta E, ta kuma fadin “To amma idan ba ke ba waye zai buga ƙofofin me share-share ya riga ya gama babu kowa sai mu uku kuma muna Kitchen sai kuma ke”.

Sai da ta rantse mata sannan ta yarda ta ce, “Kila ma cikin fitsarrun ‘Yan’matan ne, tashi ki je ki yi wanka bari na kawo miki kaya” cikin jin daɗi ta amsa ta shige bedroom ɗin, ita kuma Hinde ta fice daga ɗakin. Fitilu ta ga an kunna Tara saura, kuma tana da tabbacin duk ‘yanmatan na dinning area, kai-tsaye ta haye saman bene ta yi knocking ɗin ƙofar parlorn daga ciki ta ji muryar Gaye ya ce ta shigo.

Ta buɗe ƙofar ta shiga fuskarta cike da fara’a ta ƙarasa inda yake zaune suka gaisa ta ce “Gaye Dan Allah wajen Hajjaju na zo ta tashi?” Sai da ya juya idanuwa sannan ya ce mata, “Ta tashi mana, ke ba ki san manyan baƙin da ke gare mu ba da dare? Ai yau Ranar samu ce Hamshaƙan Masu kuɗin Ƙasar nan za su kawo ziya a sirrince ke ma kin gane eh dai”. Daɗi ne ya ƙume ta, ta ce “Da gaske kai Gaye amma qur’ani na ji daɗi, yi mini iso dai na fara ganawa da ita na fito”.

Yana kwarkwasa ya buɗe ƙofar ƙayataccen Bedroom ɗinta me tsananin kyau wanda aka Narka wa dukiyar da ake kira dukiya, ya ci uban Parlourn kyau nesa ba ma kusa ba, Ya shige ciki sannan ya yi Knocking wata ƙofa daga ciki ta ba shi izinin shigowa. Ya shiga ya nutsu sosai ya isar mata da saƙon Hinde, tana daga bisa kujerar da ta gama breakfast ta lumshe idanuwa, Sleeping dress ɗin jikinta sun yi tsananin kyau wanda ya zarce iyaka Maroon sai hularta fara kayan masu sulɓi ne sai shinning suke y, sun yi daidai murjajjen jikinta da yake zuƙar arziƙi da hutu da gyara.

Ya yi sauri ya fita, ya faɗa wa Hinde ta shiga. Cike da zumuɗi ta yi Knocking ɗin ƙofar daga ciki Hajjaju ta bata izinin shigowa Ta shiga, cikin girmamawa ta gaishe ta, ta amsa tana buɗe idanuwanta kan Hinden. Sai da ta gyara zama sannan ta ce “Hinde ina Yarinyar nan ta tashi? ,me ye ma sunanta?” Hinde ta gyara tsayuwa tana faɗin “E ta tashi, Nafi take, dama zuwa nai na karɓar mata kaya”, “Yawwa Hindatu zauna ki saurare ni; Yau Baturiya za ta zo, ina so ki kular mini da Nafeesa sosai, dan da dare akwai Shahararrun baƙin da zan yi na ban mamaki, Ni nake son yarinyar, kuma ina son ta samar mini maƙudan kuɗaɗe dan tana da jikin girma sosai kuma ki ƙara wayar mata da kai kamar yadda kika saba, amma kar ki fayyace mata komai, idan kin shirya ta ki kawo min ita.”

Sai da ta gama jin ta sannan ta zauna cikin farinciki tana faɗin, “An gama Hajjaju za ayi yanda kike so”. Mikewa ta yi ta jawo wani trolley bayan gadonta me girma ta damƙa mata, ta ce “ki je ku shirya da wuri ki mata shafa daidaidai me tsari, sannan ki fada ma ya so ina nemansa”. Ta amsa mata tana ta godiya ta miƙe ta fice. Tana gama faɗa wa Gaye saƙon Hajjaju ta sauko daga kan benen ta koma ɗakinsu.

Toilet ta ƙwanƙwasa ma Nafi daga ciki ta ce “na kusa” Buɗe ƙofar ta yi ta shiga ita kai Nafi ko a kwalar rigarta dan da zane take wankan ɗaurin gaba sai watsa ruwa take. Dafe kai ta yi tan faɗin “Wai wa ya ce miki da kaya ake wanka? Nan fa ba Rugarmu ba ce kaya ake cirewa ayi wanka a wanke ko ina a fito tsaf.”

Sai da ta dasa aya Nafi ta fashe da dariyar kamar za ta shiɗe, duk yadda ta so riƙe dariyar ta kasa ta dara sosai har da zama ƙasa. Sai da Hinden ta sake mata magana sannan ta tsayar da dariyar da ƙyar dan ita iskancin ‘yan birni ya fara bata dariya komi na Samarin rugarsu iri-ɗaya ne wajen badaƙala wai sai an cire kaya. Soso da sabulu ta ɗauko ta murza ta sa ruwa kunfa ya fito ta wanka ƙafarta ta nuna mata yanda za ta dirje jikinta ta miƙo mata Towel sannan ta kunna mata mata ruwa ta tara mata ta ce ta shiga cikin jaccuzi ɗin ta tara mata ruwan me yawa sosai sannan ta fito ta bar ta.

Ba ƙarya Nafi ta yi wankan da kyau jikinta ya fita hasken fatarta da ƙazanta gami da wahala suka dafe ya fara dawowa da kuma jan jikinta sai sheƙi take, ta ɗaura towel ɗin ta ƙwala ma Hinde kira tana faɗin “Na gama” Ta shigo tana kallonta ita ma cikin jin daɗi ta ce “Ko ke fa ba ki ga yadda kika ƙara Ja ba, yanzu gashinki kawai yai saura a wanke”.

Ta sunkuyar da kanta ƙasa dan ita kanta wata irin Ni’imtacciyar iska ke ratsa ta abun ba a magana ma. Ruwa masu ɗumi ta haɗa ta ce ta zauna ta sa Tsadadden shampoo me aiki babu algus ta fasa wanke mata gashin tana yi tana haɗawa da Shampoo ɗin maganin amodari da Kwarkwata, dan ta gan su kanta. Ta dirza sosai ta wanke tas har sai da Shampoo ɗin ya ƙare sannan ta ƙara ɗauraye mata kan da ruwan gishiri ta sa mata towel ta rufe mata kan. Gashin ya yi kyau sosai san tana da Baƙin gashi me tsayi sosai, Hinde ta yi mata bayanin yadda zata rage gashin jikinta cikin hikima ta nuna mata, daga ƙarshe ta bar ta ta yi, sannan ta sanya mata wata humra cikin Ruwan Wankan da zata ƙara watsawa da turaren wanka a ciki, ta yi yadda Hinde ta sanya ta ta kuma tisa wankan.

Wani irin sassanyan ƙamshi jikinta ke fitarwa ko ina, ga fresh air ɗin da ke shigarta babu jarabbabben ƙaiƙayin jikin da take ji da na gashi, ita kanta sai da ta burge kanta, Ta fito tana nishi don ta gaji ita kanta da wankan da ta yi, Hinde ta matso kusa da ita tana murmushi, “Yawwa Nafita kin yi yadda na ce ko? Ni ma na ji har ƙamshi kike yi, mun manta da abu guda yi haƙuri mu koma ki sake dirje haƙoranki.” ta ɗaga mata kai kawai tana chanza fuska dan ta gaji, Suka koma tare Hinde ta watsa ruwa inda ta ɓata, sannan ta sa mata mark-clean ta fara dirje haƙoran tun suna jini har suka daina da ta wanke sai ta ɗauraye Hinde ta ƙara mata mark-clean har sai da ta chanza Brush sannan ta ɗauraye bakin da ruwan ɗumi masu gishiri daga ƙarshe suka fito.

Man shafawa me tsada da kyau ta shafe ta da shi, sannan ta fesa mata roll-on ta busar mata da gashin kanta da hand-dryer, ita dai Nafi tana zaune kan kujera tana ta bin ta da ido ne dan ta gajj ga yunwa tana ji. Sai da ta shafa mata Man gashi me kyau da kashe cuttutuka, sannan ta ba ta Doguwar riga ta sanya ta yana mata mayafi, Cikin Ranta tana yaba Irin ƙirar da Allah ya yi mata lallai za ta samu Alheri me tarin yawa. Cikin ƙanƙanin lokaci Nafi ta chanza, ainahin zallar madarar zumar kyawunta ya sake bayyana fiye da tunanin mutum idanuwanta masu tsananin kyau da ƙwayar ciki sun fi girgiza mutum sabon sirrin kyawunsu kamar alajana, Hinde ta ja ta ta zauna gaban dress mirrow tana kallon kanta. Sai dariya ta fara surutai tana faɗin, “kai wace wannan, kambu Qur’an kamar Nahin Baffa”.

Sai kuma ta sa dariya tana tattaɓa jikinta, ita ma Hinde dariyar shirmenta take tana jin daɗin yadda ta saki jikinta, da kuma ƙauyancin da ta ɗan rage.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Zuciya 4Zuciya 6 >>

1 thought on “Zuciya 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×