Nafi na kwance kan gado ita kaɗai ta yi ɗaiɗaya sai dariya take yi kamar me matsalar ƙwaƙwalwa. Da ta tuna irin taɓargazar da ta danƙara a rugarsu sai ta kuma fashewa da dariyar, da kuma irin yadda Inna Hure ta saita ta lokaci ɗaya ta nutsu ta sha wahala.
Ta wani cije leɓe cike da zallar mugunta tana hararo irin rashin mutuncin da za ta shuka musu idan ta samu dama. Hinde da ke shigowa ta tsaya tana kallon ta, cikin zuciyarta tana ayyana irin yarintar da ke ɗawainiya da Nafin da rashin. . .